Advertisements
Chapter 43 Reading Gurbin Ido Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Gurbin Ido Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   43 / 67

126K to 129K   out of 200.8K words

hana yarwa,yana taba amfanin gonar manoma,saiki biyasu" daga haka laulo yayi gaba abinsa ba tare daya tsaya bi takan inna furera ba.

Kamar zata fadi haka don baqinciki,haka ta nufi shiyyar dakunanta ta dauko.musu kudin,qarta qartan samarin fulani ne majiya qarfi sun zuba mata idanu,banda haka bataga abinda zai sanyata biyan wadannan kudaden ba bayan asarar data tafka goma da ashirin.

Da qyar tayi sallar magariba ta hadeta da isha'i,tana zaune a wajen,ita ba addu'a ba ita bata bar wajen ba,sai qiyasta girman asarar da take tafkawa takeyi,tunda maimunatu tabar hannunta komai ya sake tabarbare mata,tun bayan tafiyarta take qunzuge kudaden da anni ke aiko mata,taqi daukan mai mata kiwon,ta tilasta gajee fita kiwo ita da laulo,da sunan gajeen takewa tanadin kudin daki dama na biki gaba daya,don tace bata ga abinda ubanta yake dashi ba da zai kai mata gidan aure.

To gajen dai ba'a son ranta ya fara fita kiwon ba,don dama gaba daya bata saba ba,a sangarce ta tashi,uwa uba kuma ita aure kawai takeso da himu,wannan yasa gaba daya ita da dabbobin suka shiga wahala,babu kulawa me kyau,a hankali suka fara lalure lalure,sai kuma haka siddan suka fara mutuwa,yau wannan gobe waccan,kudaden da taketa tarun su ta dunga diba tana musu maganu tare da karbo taimako na kambun baka da maita,waiko mayu ke kadar mata da garke,ita kuwa gaje ba abinda ya shalleta,idan suka fita kiwon sai tayi batan dabo,shi dai laulo baisan ina take zuwa ba,amma dai bata dawowa yawanci sai gab da zasu koma gida,tun inna furera bata gane meke faruwa ba,har ta gane,qaura wambai ta fadi ina take zuwa amma ta qeqashe qasa taqi fada,har inna ta haqura ta zubawa sarautar Allah ido.

A hankali ta bayyana wani baqon bafullatani take bi su fice daga shiyyar abinsu,haruna kyakkyawan bafulatanine wanda yake ruwa biyu,wani irin kyau ne dashi don hatta qwayar idanunsa launinta daban yake,idanun haruna a bude suke,sabida sunyi yawon kiwo gari gari qasa qasa,don haka babu wuya ya yaudari yarinya ta fada soyayya dashi,da wannan kyan nashi yake amfani,ya yaudari 'yammatan dashi kansa baisan iya yawan adadinsu ba,da haka ya yaudari gaje ta fada soyayyarshi da sunan aurenta zaiyi,tana da son abu me kyau,don soyayyar himu fiye da rabinta kyansa ne yake janta,sai gashi ta samu wanda ya fishi.

Hankalin inna furera ya tashi qwarai,ta tashi haiqan don rabasu amma a banza,da sun fita kiwo suke jonewa,kuma gashi ta gaza hanata fita kiwon,saboda bata dame fidda mata dabbobin,daga qarshe ta yanke shawarar bari kawai ta samu daadar himu da maganar aurensu,gwara ayi a daura,duk tsiya idan tasan da igiyar wani a kanta kome zai yanke,shima harunan bazai bita ba.

Sai data gama maganarta tsaf sannan daadar himu ta watsa mata wani kallon banza

"An gaya miki shashasha nike?,ko ba'a cikin garin nan nake ba ai nasan kome ke faruwa,da farko kinso kai diyarki birni ki hana dana,saboda kina ganin acanne zata samu me arziqi,da hakan bai yiwu ba sai kika haqura,yanzun kuma diyarki ta gama lalacewa....ta gama bidar maza shine kikeso ki joganawa dana?,bazai yiwu ba,nima na fasa hadin,dana fita zaiyi duniya ya nemi arziqi kamar kowanne namiji,ko nima zan kere sa'a cikin rugar nan" sosai ran innafurera ya baci,ta dinga zage zage tana cewa daadar himu ta yiwa diyarta sharri,daga abun arziqi sai ya zama na tsiya?,idan himu bazai auri gaje ba ai basai ta hada da sharri ba.

To itama daadar ba baya bace,sai ta tasowa inna furera,suka fito har tsakar gida suna yi,yuuma na jinsu bata ce musu ta tafas ku sauke ba,sosai daadar himu ta tasar mata,har ta fara bankada sirrin inna fureran,da roqarta da tayi kan ta rufa mata asiri,shine silar alqawarin da ta yiwa daadar himu na bawa himu gaje don su samu suci dukiyar a tare asiri a rufe

"Barni yuuma,rabu dani na nunawa matar nan nima ba kanwar lasa bace" daada tace da yuuma sanda ta taso tana shirin kashe rigimar,saboda yadda suka fara tonawa junansu asiri,da qyar ta samu ta raba,bayan mutane 'yan gulma sun fara marmatsowa,kowa yana son jin abinda ya shiga tsakanin tsaffin aminan,tun daga sannan sukayi baram baram,aka rabu dutse a hannun riga(dama duka tarayyar da babu Allah a ciki,to tabbas qarshenta kenan koma fiye da wannan).

Ajiyar zuciya inna furera ta saki,sai ta miqe tana zura takalmanta,ta kuma nufi turken dabbobin,tsaiwa tayi tana qare musu kallo,baqinciki na sake sudarta,wai me yasa komai yake shirin tabarbare mata ne?,watsewar wadan nan dabbobin dai dai yake da watsewar dukka farincikinta da kuma kima da daraja data samu a baya cikin qauyen ta dalilinsu,kuma hanya ce da zata bawa maqiyanta kamar su daadar himu damar yi mata dariya gami da zundenta,kai ta girgiza da sauri,ba zata taba barin hakan ta faru ba,ko ta yaya sai ta dawo da garkenta kamar yadda yake ada,amma kuma ta yaya?,ina taga kudin da zata sake siyan wasu dabbobin ta cakuda da nata?.

"Maimunatu" shine sunan daya fado mata,tabbas!,wannan itace amsa,tun daga kan kayan lefe sadaki da irin mutanen da suka je daurin auren yarinyar ta tabbatar ta taka wani babban shinge,kuma koda bata gani ba,jikan tsohuwa anni ai ba wasa bane,tunda tasan anni,sani na daga ni sai ke ba sanin shanu ba,ko daga motocin dake shigowa da ita garin da irin rabon da take zakasan ba qananun mutane bane.

Murmushin samun mafita ne ya subuce mata,ta saki ajiyar zuciya,hankalinta kuma taji ya kwanta sosai,dole ta nemo gidan maimunatu,tana da tabbacin zata samu dukkan kudaden data yanka mata,ai dai komai lalacewarta ita taci gaba da riqonta bayan bacewar ubanta da kuma gushewar uwarta daga doron duniya,idan ta kama ma sai ayi lissafin din abincin data dinga ci da ita har zuwa sanda aka aurar da ita,da wannan tunanin ta juya zuwa cikin gida,saidai abu daya da take ganin zai kawo mata tarnaqi shine,ina zata samu kwatancen gidan maimunatu,daga nan har garin gombe?.
"Yuuma mana" tsukakkiyar kwanyarta ta bata amsa,take kuma ta gamsu,don haka ta dage katifar ciyawa dake dakinta tana laluben sauran kudaden data adana,ta lissafa taga nawa suka rage mata?,tunda tun bayan auren maimunatun anni tace yuuma ta shaida mata,kudin aikatau an gama biyansu,tunda a yanzu tana gidabta tana zaman aure bautar Allah bata mutum ba,a ranta take qiyasta adadin kudin zasu kaita gwambe?,don bata tunanin kudin dawowa,tasan ko a jirgi tace tanaso a dawo da ita za'a kawo ta.

Barazanar daukewa numfashinta yake daga qirjinta sanda ta daga wajen ta kuma kakkabe katifar taga wayam

"Hukumullahu min zalika" ta fadi kalmar da ita kanta batasan cikakkiyar ma'anarta ba,yadai fadane kurum,gumi ne ya fara tsargo mata,ina kudadenta suka shiga?,cikin lokaci qalilan tayi gumi kashirban,ta koma bakin itacen gadon ta zauna tana sauke numfashi kuka kamar zai qwace mata,ta xurfafa tunaninta kan waye yabi dare yabi rana ya dauke mata kudinta?.

54

Kudin da iya su kenan cikin abinda ta mallaka?,sai ragowar dabbobin da suketa sulalewa suna qarewa daya bayan daya,sauran kuma suna bushewa kamar ana lasarsu?.

Sallamar jauro yayi dai dai da tunanin daya darsu a ranta na cewa tabbas shine ya debe mata kudin,domin kuwa taga yana ta gyaran bangare daya na cikin gidan,idan bashi ba bataga wanda zai debar mata kudi ba,tunda dai saman katifar suke kwana,kwana biyu ne ma yayi qaura yabar dakin saboda fushin da yake da ita kan abinda ke faruwa game da gajee.

Zumbur tayi ta miqe ta fito,tayi tsaye a bakin qofar dakin nata,hannuwanta a qugu tana kallonsa,sai ta zare hannuwan nata ta miqa masa tana dubansa da idanuwanta dake cike taf da rashin kunya da diban albarka,bin hannuwan nata yayi da kallo cikin mamaki,don baisan me take nufi ba

"Meye hakan ke kuma?"
"Ai kafi kowa sani,kudi na....kudi na nake so ka tafen ka bani,kuma wallahi sisi idan yayi ciwon kai sai ka fiddoshi" kallon mara cikakken hankali yake mata,don shi gaba daya kwana biyun nan kamar a zare kuma a firgice yake ganinta

"Kanki daya kuwa?" Ya soma da tambayarta,saboda yasan ta inda zai kamo maganganun dake bakinsa

"Ras nake jauro,kuma babu abinda zaka layancemin,kudina kawai nake da buqata,zaa cuceni a ha'inceni,har an tada gini ban sani ba" qare mata kallo tas yayi,yadda take girgije girgije ya tabbatar masa da gaske take maganarta,shikam a yanzun bashi da magana da ita,burinsa kawai ya gama gininsa lafiya Lau a daura masa aure da bazawararsa sadiya,ya tabbatar zatayi dai dai da furera da kuma dukka iskancin dake kanta

"Allah ya baki lafiya furera,na fuskanci tunda dabbobin marainiya suka fara kama gabansu aka soma taba naki tunanin,Allah ya kawo manzan sauqi,amma ki sani,koda zanyi sata bazan saci dukiyar haram dukiyar marayu irin taki ba,na dirkawa cikina wutar sa'ira,zan shiga dakina,kada kuma ki kuskura ki biyoni ballantana kice zakimin hauka,kije can ki nema inda dukiyarki ta salwanta" ya dire maganar tasa cikin tsananin kaushi da tsaurara harshe,sannan yayi gaba abinsa dauke da jakar buhun da ya dawo da ita daga cin kasuwar cikin wani qauye dake gaban nasu.

Binsa tayi da kallo,tafi kowa sanin jauro,kuma yadda yayi maganar ya sagar mata da gwiwa,tare da debe tunanin shi ya dauka kudin,sai ta koma bakin karan gadon ta zauna gwiwa a sanyaye tana zurfafa tunaninta kan inda kudinta suka shiga.

Zumbur ta sake miqewa tana kama sunan gaje,sai a sannan ma ta tuna yarinyar bata shigo gida ba har yanxu,mayafinta taja sannan tayo waje ba tare da neman izini ko ta tsaya gayawa jauron zata fita ba.

Tana tafe a hanya tana surutai ita kadai tare da tuna cewa dazu da safe sanda take fitowa daga bandaki taga fitowarta wuff daga dakinta,saidai bata kawo komai ba,ta dauka sauri take ta dauki kununta ne zata kada dabbobin su fice.

*GWAMBE*

Suna idar da sallar la'asar cikin masallacin dake cikin katafariyar ma'aikatar tasa ya dawo third floor,inda anan makeken office dinsa yake,direct ya isa saman freezer ya dauki agogonsa ya daura,sannan ya dauki hularsa yana gyara karinta,a hankali yana tuna abubuwan da suka faru a yau din,dukka abubuwane masu tsayawa a rai,kai qararshi zuwa ga anni sai abunda yafi komai tsaya masa a rai ba tare da yasan dalilin hakan ba.....irin kallon da yaga khalid yana jifanta dashi,kallon titsiye kallon qurilla kuma kallon haramun,lips dinsa na qasa ya cije yana jin kamar yanzun abin yake wakana,ya daga hannunsa da niyyar sanya hularsa saman kansa Jabir ya turo qofa ya shigo office din,wanda a yau wannan shine shigowarsa karo na wajen hudu,abinda kusan ba al'adarsa bace.

Duk shigowarsa ta dazun yayine don yaji wani abu daga bakinsa,saboda yana da masaniya akan kiransa da anni tace zatayi,da goyon bayansa ma ta aikata hakan,saidai ko a fuskar gogan bai nuna masa ba,duk da cewa ya karanci akwai wani abu a qasan ransa,uwa uba kuma basa boyewa junansu komai

"Fita zakayi ne?" Jabir ya fada,saboda yasan lokacin tashinsa bai qarasa ba,saura kusan one hour,shanyayyun idanunsa ya daga ya kalleshi

"Eh,i have to go,ina da uzuri"

"Munyi maka,mu masu mace daya ma muke samun kanmu cikin irin wadan nan uzurorin balle kai me biyu?" Yayi maganar ta manufa biyu ne,da kuma salon jan zance tare da neman tsokana,ya sani sarai,amma sai ya shareshi,baiko daga kai ya kalleshi ba bare ya biye masa suyi,saima yaci gaba da gyara hularsa,sannan ya qarasa gaban dan madaidaicin madubin dake manne da bango cikin office din,zaka zaci ma wani abune a wajen idan baka sani ba saboda design din da aka masa,ya kafa hular da kyau a gaban goshi,sai gashi ya fito fes da wani irin kyau me daukar hankali tare da kwarjini

"Allah ya gyaraka,yasa ka koma ja'afar dinka na asal" Jabir ya fadi a fili,a wannan karon waiwayowa ja'afar yayi ya kalleshi

"Wait.....wai me yasa yau ka takura min ne?"

"Saboda yau kake ango" ya furta yana danne dariyar dake cinsa,maganar tasa ja'afar qarasa waiwayo gaba dayansa,ya zuba masa shanyayyun idanun nan nasa

"Daina kallona haka malam,ba maimunatu ko unaisa bane"

"Duk wani zagon qasa da akemin na fuskanci dakai ake shiryashi ko?"

"Dai dai kenan,munason ka zama mutum kamar kowa,ka ajjiye wannan son bayan rai din,ka fuskanci reality,ka kuma yima shaheeda soyayya ta gaskiya ta hanyar samarwa kanka farinciki ka kuma dawwama da yi mata addu'a,da kula da abinda ta bari" kashe bakinsa gaba daya jabir yayi,ba wanda yasan abinda yakeji sai Allah,yana tsintar kansa a matuqar damuwa da qunci duk sanda ya tuna yadda ya wofantar da kulawa da soyayyarta,bai tashi fargar jaji ba sai daya rasata,wannan yafi komai damunsa da hanashi dukkan wani sukuni da walwala,akwai ciwo ya zamana kayi rashin mutumin dake maka soyayyar gaskiya,baka tashi gane hakan ba sai daka rasashi,ya tafi,yayi maka nisa,nisan da babu dawowa,koda zaka salwantar da dukka abinda ka mallaka don ganin dawowar tasa.

" Ga sauran agreement din nan,ka duba idan komai yayi ka sanya hannu,munata loosing opportunity dinmu,bansan a kwanakin nan me yasa ka kasa concentrating akan aiki ba,is there any problem?"

"Nop" ya amsa masa a taqaice,ya ciro wayarsa yana turawa driver dinsa tex kan ya fidda mota zai sauko

"Okay....i hope so" jabir din ya fada shima yana miqewa,ja'afar bai sake komai ba suka fito tare suna tattaunawa.

A parking lot suka rabu,jabir din yayi motarsa,shima ja'afar ya shiga tasa,ajiyar zuciya ya sauke sanda suke fitowa a company din,idanunsa na bisa titi yana wani tunanin na daban.

Maimunatu bata wani jima sosai ba a gidan su laila suka dawo,sai gidan ya rayu ya cika da hayaniya,don an jima ba'a hadu ba,rabonta da gidan tun kafin a koma makaranta,da aka dawo din nan kuma ta dawo da rashin lafiya,bata fito zuwa gidan ba sai yau.

Harda anty maama suka dawo ita da yaranta,duka a falon anni suka yada zango,sai maimunatun ta dinga jinta sakayau,zaman kadaici sam baiyi ba,hirar tasu ta dinga debe mata kewa,duk da ba kasafai take sanya musu baki ba

"Kiri kiri manya yaqi kawomin ke,kusan shekara daya tunda hisham ya kawoki har yau baki sake dawomin ba,shi yasa nima nayi fushi naqi zuwa gidanku" anty maama tace da maimunatu wadda ke lallabewa 'yar anty maama ta uku kanta da manyan kalba, yarinyar tana da suma,amma kuma batason kitso kwata kwata.

Murmushi tayi

"Makaranta yasa bai kawoni ba,amma zanzo anty in sha Allah"

"Ina zuba ido" ta amsa mata tana bude wata leda me dauke da wani babban tambari da kuma suna,wasu kayayyaki ne a ciki,ya fiddosu ta ware wasu,sai ta dubi maimunatu

"Allah yasa kina amfani dasu,siya nayi daga baya kuma dana duba naga sunmin yawa,kada su lalace ban shanyesu ba,kwashe wadan nan kiyi amfani dasu" kunya ce sosai ya saukarwa maimunatu sanda ta kalli kayan,ko wanda baisan na meye ba idan ya duba jiki zai gane,magunguna ne irin na ma'aurata,da bayaninsu balo balo a jiki,a kunyace ta debe tana cewa

"Na gode anty"
"Ba komai,amma akwai wani a ciki miqo in gani,ki shanyeshi,don idan yakai gobe tace zai lalace" ba zata iya cewa da ita komai ba,saboda kunya da kuma nauyinta da takeji,hakanan ta karba takai bakinta a hankali ta fara kurba.

Sosai abun yayi mata dadi a baki,tana sha gardinsa yana ratsa harshensa,shi ba gardin madara ba bana kwakwa ba,a hankali sai gashi ta gama dashi,dai dai sanda laila ke shigowa dauke da babban plate data shiga kitchen da kanta ta zubo musu abinci

"Me akasha ba'a rage mana ba,naga wani hadadden bottle haka a hannunki matar yaaya" tayi maganar tana ajjiye tray din tare da miqa wuya tana leqawa

"Matsa malama,ba irin naku bane,saiki jira sai anzo kanku"

"Don Allah a bani na dandana,da gani abun dadi ne wallahi anty maama kika sata a loko ita kadai kika bata" laila ta sake fada tana daga robar zata kai bakinta.

Buge roban anty maama tayi tana harararta

"Baki da hankali ne laila?,baki gane me nake nufi ba kenan?,to kika sake kika sha wannan yau saidai abbi ya bada sadakar aurenki ko babu sadaki" ta qarashe fada tana sake zabga mata harara idanunta kamar zai fado.

Dariya laila ta saki tana qunshe bakinta,ita har ga Allah tunaninta baikai can ba sai da tayi mata dalla dalla,nadiya dake chart ta sauke wayarta tana harararta itama

"Wannan inda abbi bai karba kudin aurenki ba,ina jin kanki da kanki zaki kai gidan auren,duk gidan nan banga mai jarabar son aure irinki ba" dariya sauran suka saka mata,saita bata fuska

"Nifa Allah ban gane na meye ba,shi yasa nace a bani nasha,naga yamin kama da milkshake ne"

"Ke kika sani dai fitsararriya" nadiya ta sake fada tana gyara zamanta

"Anty.....ki mata magana don Allah" laila ta fadi tana duban anty maama

"Ke nadiya.....kiyi ta kanki,banason shashancin banza,idan bataso aure ba boko zata so irin naku?,aini walle duk cikin jikokina ba wadda ta burgeni kamar laila?aure ai shine cikar mutunci da kamalar mace,ko wacece ita a duniya kuwa....ehe" Anni wadda shigowarta falon kenan ta kuma datsi maganar ba tare da tasan akan me suke tattaunawa ba tace laila,da wannan ta kashe bakin maganar,dole kowa yayi shuru,saboda sunsan halin anni,yanzu sai ta baro musu aiki.

Abincinsu suka

43 / 67