Advertisements
Chapter 45 Reading Gurbin Ido Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Gurbin Ido Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   45 / 67

132K to 135K   out of 200.8K words

Ya tabbatar da cewa kallon da yake matan ya wuce yadda ya kamata,don haka yayi qoqarin tattara hankalinsa ga amna,yana saurarenta yana kuma lumshe idanu gami da gyada kai,kusan shine amsarta,don ya tabbatar idan yace zai biye ma surutunta zata bashi ciwon kai a daren,saboda hirar amna bata qarewa.

Cikin qoqari da jarunta ta tattara nutsuwarta ta soma serving dinsu,yana ankare da ita yadda take ta loda musu abinci a plate,caraf ya riqe hannunta ganin abincin yayi yawa kamar bata kula,a razane ta saki warmer din tana dubansa,wani abu tsarga mata tun daga yatsun qafarta zuwa kwanyarta,ya kumma kunno mood din da taketa qoqarin ganin ta danneshi.

Hannun nata ya saki ya sulale a hankali sannan yace

"Enough mana, yayi yawa" yayi maganar don baya tsammanin shi zai iya ci,baisan taste dinta ba,kuma bashi da tabbacin abincin zai dace dashi,duk kuwa da qamshin spices da ya cika wajen.

Sakin spoon din tayi,ta koma da baya a hankali ta zame saman kujerar,sai yaja plate daya,ya sanya spoon ya matsar gaban amna

"Uhnnn....bismillah" murmushi ta saka sanann ta dauki cokalin ta soma diban abincin tana kaiwa bakinta,wani murmushin ta kuma yi
"Yummy...." Ta fadi tana duban fuskar ja'afar

"Daddy,mucu, you will enjoy it over" murmushin gefan bakin dai ya kuma saki

"Ki cimin amnee,tunda ya miki dadi" qememe ta tubure kan shima fa sai yaci din,ta haura saman table din ta dauko masa wani spoon din,sanan ta tsareshi da idanu,tilas ba don yaso ba ya diba abincin dan kadan ya sanya a bakinsa yana taraddadin abinda zaiji.

A hankali dadin abincin ya fara zagaya harshensa ya kuma gauraye bakinsa gaba daya,sake diban second spoon yayi,sai ya kuma jin real taste din fiye dana dazu,sannu sannu sai gashi yana ta kaiwa cikinsa abincin yana kuma sauraren hirar amnan yana amsa mata da ka,kafin kace meye wannan sai ga plate din wayam babu komai.

Idanu amna ta fitar tana duban ja'afar

"Daddy,a qaro ne?" Kai ya girgiza yana shafa cikinsa,ta wani sashen kuma yana cika da mamakin yawan abincin da yaci,duk da dama shidin bamai wasa bane da cikinsa musamman idan ya samu abincin daya dace da taste dinsa

"No.....am full amnee, thank you"

"Thanks to anty moon,ga kifin dad" sai yayi kamar bazaici ba saboda qoshin da yaji yayi,amma shima yana tabin farko ya bude cikinsa yaci kifin sosai,har sai da sukaci kusan rabi,sannan ya dakata,ya yagi tissue ya goge hannunsa daya baci

"Anty bakici komai ba,ba kyau fa zama da yunwa" sai a sannan hankalinsa yakai kanta,ya kalli plate din abincin nata,kusan babu abinda ta taba a ciki

"Daddy kace mata taci" miqewa yayi ya zube hannayensa a aljihunsa,kana ya saukar mata da dukka nauyin idanuwansa yana kallonta

"Eat it" ya fadi a gajarce

"Daddy yace kici anty moon" saita jinjinawa amna kai

"Zanci amna" a hankali ya janye idanuwan nasa yana mamakin kansa,baisan me yasa ya maida kallonta one of his favorite thing to do ba a duk sanda zasu hadu a muhalli guda,bayason hakan ko kadan,sai ya kama hannun amna suka fice da sassan nata.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana hade hannayenta waje daya da qarfi,abinda take ji cikin jikinta yana qara qarfi,tuni kowacce gaba ta jikinta ta fara amsawa,hakanan launin idanunta suka fara sauyawa,ko kusa ko alama babu wata yunwa da takeji,infact cikinta ma a cunkushe yake,sai ta tashi zuwa bakin fridge ta dauko sassanyan ruwa ta balle ta soma sha tana tsammanin ko zataji sauqin abinda takeji din.

*_UNAISA_*

Tun bayan sallar isha'i ta gama dukkan wani shiri nata na tarbar ja'afar,girke girke tasa aka masa har kala uku,ta kuma fece kwalliya bayan ta sallami dukka masu aikin nata,ta qwame tana jiran jin shigowarsa ko kuma wani motsi nasa.

Lokaci lokaci tana tana duban agogonta,har awannin suka fara nisa,ta fara debe tsammani da xuwansa,wani girman ksi hadi da maganganun da suka fara da haj munubiya suka sauko mata,suka sanya mata wani bala'e'en haushi da takaici,ta kuma shiga safa da marwa amma sai ta kasa daurewa,don haka taja wayarta ta kira anty talatu

"Karkiyi gaggawar zuwa wajensa,ki sake jira daga nan har xuwa sha daya ko sha biyu mu gani,duk wayon ango dai dole yazo hannu ai,yana zuwa hannu kuma ai ya gama yawo,da wannan ta koma din ta zauna tana kada qafa,idanuwanta a kan tv,duk da hankalinta ba'a kai yake ba.

Da qyar ta samu ta tsakura farfesun kifin,saboda abincin bata jin zai shiga cikinta,ta kwashe komai ta maida kitchen,ta gyara ta kuma wanke kwanukan,dukka a daddafe take komai,saboda zuwa sannan gaba daya mararta ta daure tamau,sai danshi da taji tana zubarwa,wanda tayi tsammanin ko period ne yake zuwar mata.

Bandaki ta shiga ta duba jikinta,saidai kuma ba period din bane,wani ruwa ne daban,tsarki tayi tana cije lebe ta fito ta baro toilet din tana takawa da qyar,kayan bacci ta canza tana duba kokaci,amna tana ranta,saidai tunda tasan tare suke da daddynta ba buqatar sai ta dami kanta,sai ta saita freshner din dakin sake fesa kansa da kansa duk bayan wasu sakanni,ta saisaita hasken wutar dakin zuwa dim light,sannan ta haye gadon a hankali taja duvet zuwa qugunta tana cije lebanta hadi da hade qafafunta waje daya.

Ajiyar zuciya unaisan ta saki sanda ta kalla agogo,qarfe goma dai dai na dare agogon ya buga,awanni biyu masu zuwa da anty talatu sai takejin sun mata nisa,ba zata iya bari ba,don haka ta miqe ta nufi bedroom dinta,ta fidda kayan jikinta ta wuce toilet don ta sake shiryawa,ta gama tsara cewa fitar zatayi ta taddashi a duk inda yake.

Hannunsa guda daya yana saman kan amna,yana shafa sumarta a hankali,yayin da dukka hankalinsa ke kan tv yana kallon news a tashar al_akhbaar,yaqe yaqe ne kawai ke tashi tako ina a duniya,abun akwai daukar hankali sosai.

Ajiyar zuciya ya sauke sanda suka kai qarshen labaran,ya janye idanunsa ya maida kan fuskar amna,kallonta yake,sosai take tuna masa da shaheeda,ta wani sashe tana dan diban kamanninta,duk da idonta lips dinsa da skin color irin nashi ne,sai ya tofa mata addu'a sannan ya sunkuya a hankali yayi kissing din goshinta sannan ya miqe ya sabata a kafadarsa ya taka a hankali yana ficewa daga falon.

57

A hankali ta sake dawowa saman gadonta tana runtse idanu tare da sake cije lebanta ta kwanta a hankali kamar wadda ke da gyambo a jikinta,karo na uku kenan tana shiga bandaki tana canza pant dinta tare da sake tsarki,sai a sannan ta tuna da maganin dazun da tasha na wajen anty maama,ta tuna yadda ta tankwabe gorar daga hannun laila dake niyyar sha,filo taja ta dora kanta tana sake tuna abinda anty maama tace da laila

"Baki da hankali ne laila?,baki gane me nake nufi ba kenan?,to kika sake kika sha wannan yau saidai abbi ya bada sadakar aurenki ko babu sadaki" tana kaiwa nan wasu hawaye masu dumi suka silmiyo mata zuwa saman filon,batasan wannan aikin zai mata ba,batasan abinda zai sanyata ji ba kenan,mugun feelings kamar zata fashe haka takeji,inda ta sani ta kuma fahimci maganar anty maama koda wasa ba zata shashi ba,sai ta sake takurewa waje daya tana cusa fuskarta cikin pillow,tana jin yadda mararta ke sake daurewa,ta dafeta sosai tana fidda hawaye,dai dai lokacin ya dora hannunsa akan handle na qofar,ya kuma turo qofar dakin sannu a hankali,cikin wasi wasi,don ko daya baiso ya samu bata falon ba bare ya bata amna ya koma ba.

Tattausan qamshin dake gauraye da sanyin ac madaidaici wanda baiyi yawa ba,kana baiyi kadan ba yaa doki hancinsa,cikin qamshin ya iya tantance qamshin turarenta da take amfani dashi,take wata kasala ta saukar masa,ya soma takawa a hankali qafafunsa na nutsewa cikin tattausan carfet dinta daya dauki sanyi sanyi.

Yana iya hangen direction da gadon yake,don haka bashi da buqatar haske,ya qarasa a hankali ya tsugunna a gaban gadon ya kwantar da amna,ya dora hannunsa saman kanta idanunsa suka sauka a kanta.

Yana iya hangenta saboda fararen kayan bacci dake jikinta,wanda a ido kawai zakasan suna da wani sulbi,silk ne masu asalin santsi da daj taushi taushi,milk duvet dinta ya tsaya iya qugunta,sassalka baqa kuma yalwatacciyar sumarta ta baje saman filon,baka iya ganin ainihin fuskarta saboda nutsata da tayi cikin filo.

Idanunsa ya kauda daga kanta ya lumshe su yana jin wani iri cikin jikinsa,gaba daya weather din dakin ya fara canza masa yanayi,ya kammala mata addu'ar ya tofeta da ita,sai ya laluba babu pillow kusa da ita.

Can ya hangi filon dab da gwiwarta,yana jin cewa tayi bacci,don tunda ya shigo baiga ta motsa ba,don haka ya haura saman gadon a hankali,ya sanya hannu yadan xame filon

"Wayyo Allah na" ta fada cikin wata iriyar wahalalliyar murya tana kai hannu da niyyar damqe filon,duk da batasan waye ya shigo na,saidai cikin rashin sani ta kama hannunsa gam ta riqe cikin tattausan tafin hannunta dake da wani irin dumi,motsa filon tamkar ya motsa mararta ne,don ta jingina qafarta ne dashi wai ko zata zamu relief.

Hannunsa dake cikin nata ya kalla kafin ya maida dubansa gareta,sai a sannan ya lura da yanayin kwanciyarta,yakai hannunsa a hankali saman kafadarta yana yunqurin juyota,saidai sam taqi yarda da hakan ya faru,don ya zuwa yanzu lallausan night scent dinsa ya gaya mata waye cikin dakin,ba zata so kuma yaga yanayin da take ciki ba,duk kuwa da cewa ita kadai tasan meke faruwa da ita.

Hankalinsa yaji yadan tashi,kada dai ace yarinyar bata da lafiya?,take zaune a daki zata kashe kanta,wannan tunanin yasa ya qara qarfinsa kadan,sai gata ya birkitota gaba daya, tashin farko kuma ta afka jikinsa gaba daya,ta samu kyakkyawan masauki a faffadan qirjinsa dake cike da lallausan gashin dake bada wani ni'imtaccen qamshi na musamman,gashin da duka gaza boyuwa ta tsajiyar maballan pyjama dinsa masu salki,gashin kanta kuma ya baje masa saman fuska,daddadan qamshin hair mist dinta ya ratsa hancinsa zuwa qwaqwalwarsa,take kuma ya aika da wani muhimmin saqo,ya sake nutsa fuskarsa zuwa tskaiyar kanta ba tare daya damu da yadda gashin ke shige masa baki da hanci ba.

"What's wrong with you?" Ya mata tambayar da wata irin kwantacciyar murya,wadda shi kansa baisan yana da ita ba,maimakon ta amsa masa saita sake qanqame hannunsa dake cikin nata har yanzu,wata sabuwar qwalla na zarto mata daga idanunta,dumin qwallar da ya sanyashi jin hankalinsa ya tashi,ya hada dukka qarfinsa waje guda ya dagata da niyyar sake tambayarta,saidai a wannan karon ma sake shigewa tayi cikin jikinsa da kyau,don bata qaunar hada idanu dashi ko kadan,gani take idan ya kalleta zai iya karanto ko meye ke damunta,idan kuwa har ya fahimta batasan wanne irin abun kunya ta barwa kanta ba,samun gurbinta cikin jikinsa yasa haduwar wasu sassa na jikinsu waje daya,take kuma suka aika da saqo xuwa ga kowanne sashe na jikinsa shima,kowanne sashe kuma ya amsa

"Tell me what's going on?" Ya sake qarfin halin tambaya,don so yake ya fara sanin matsalarta kafin yasan maganin da zai bata ko yasa a rubuta mata.

Hannunsa kawai takai saman mararta ba tare data shirya ba,tunaninsa take ya rabu gida biyu,yanayinta yana alamta wani abu,amma kuma tunaninsa yafi karkata ga cewa ko period ne,saidai kuma yadda mood dinta ya canza fa?,period na sanyasu haka?.

Da qyar ya samu ya gyara zamansa ya fidda wayarsa,ya kuma turawa hisham tex bayan ya riqeta sosai cikin jikinsa,duk da yadda yakejin wani abu na taso masa,kowacce jijiya a jikinsa na harba jini da sauri tana kuma aike masa da saqonni.

Saqon na shiga ya samu reply,ya duba ya miqe zai kwantar da ita,saidai taqi sakinsa, kitchen yakeso ya shiga ya dauko abinda hisham yace dashi amma taqi sakinsa,tausayinta ya saukar masa saboda gumin da yaga tana hadawa,duk da sanyin ac mai dadi dake zarya a dakin,dole ya koma ya zauna,ta kuwa kifa fuskarta akan cinyarsa da kyau,abinda yasa numfashinsa ya kusa daukewa,sai ya sanya hannunsa ya dauketa,ya maidata saman pillow din yana gyara mata kwanciya.

Ko kusa ranso baiso,amma dole bashi da wani zabi da ya wuce yayi mata uterus massage,ya matso dab da ita,ya sanya hannunsa yana dauke rigarta daga saman shaffen cikinta,wanda kwata kwata baiyi kama da cikin dake cin abinci ba.

Lallausan tafin hannunsa ya dora saman marar tata,daga ita har shi sai da suka qwaci numfashinsu da qyar,ta runtse idanunta sabbin hawaye na kunya suna fita,ya motsa hannun nasa a hankali ya fara shafa marar

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta jin yana niyyar loosing control dinsa,sai ya runtse idanunsa yana aro jarumta,tare da tunawa kansa wasu abubuwa da suka taimaka wajen riqeshi da riqe kansa.

Lokaci mai tsaho suna a haka,sannu a hankali yaji jikinta ya saki gaba daya,yanayin fitar numfashinta ya canza,sai ya bude idanunsa a hankali akan fuskarta,bacci ne ya dauketa,duk da bata bar fuskarta a saitinsa ba,ta kauda fuskarta daya bangaren ne,ta yadda ba zasu iya ganin juna ba saidai idan leqawa zaiyi.

Wata iriyar qatuwar ajiyar zuciya ta kubce masa,yanajin yadda ko ina a jikinsa ke motsawa yana qin yarda da ban haqurinsa,a hankali ya dauke hannunsa daga saman mararta yana dan duban wajen,red pant dinta ya fito ta qasan wandon rigar baccinta ya haska fara sol din fatarta,da baya da baya ya fara zame jikinsa yana sauka daga saman gadon,bayan ya sauka gaba daya sai yaja duvet din ya rufesu su duka,ya dauki remote na acn ya sake dai daita musu temperature din,sannan ya aje remote din yayi hanyar fita yana hada hanya.

Da zafi zafi ya dinga hada steps din bibbiyu yana haurawa samansa,yana shiga dakin ya fidda dukka kayan jikinsa,ya rage daga shi sai pant na maza daya sanya kafin ya fita,gaba daya zufa ke karyo masa sosai,bugun zuciyarsa na canzawa,tun ba yau ba yasan kanshi sarai,ta wannan fannin ba kasafai yake da dauriya ba,dabi'arsa kuma ta banbanta data sauran maza,wannan ya sanya ya riga kowa aure a cikin sa'anninsa.

Zama yakeson yi amma ya gaza zaman,sai ya matsa ya diba remote na dukka acn dake falo da kuma bedroom dinsa ya qure temperature dinsu,ya watsar dasu a gefe guda.

Dai dai lokacin da unaisa ke takowa zuwa saman nasa,duk taku daya tana yinsa ne da manufar practical na yadda zata tunkareshi,tana ji a ranta yau komai zai qare tsakaninta dashi,itama zata kai wani bigire da tsohuwar matarsa takai,zata tsallake shingen da take da tabbacin tsallakewarta zuwa nan wajen ne kawai zai bata soyayya da martabar da takeso daga wajensa.

Knocking ta fara yi,abinda yaja hankalinsa ya kuma bashi mamaki kenan,ya zubawa qofar idanu qwaqwalwarsa nason tuno masa waye yayi saura a gidan da xai doshi sashensa a wannan lokaci?,unaisa ya bawa kansa da kansa amsa,sai ya maida wandon pajama dinsa ya nufi qofar kawai kai tsaye,ya mance cewa babu riga a jikinsa.

Mutuwar tsaye tayi sanda sukayi arba dashi,idanunta qur bisa fuskarsa zuwa qirjinsa,wani abu ya soma zagaya jikinta,lallai kaman dai tazo da sa'arta kenan?,batayi qasa a gwiwa ba ta sakar masa murmushi,sannan cikin dabara ta turo qirjinta zuwa gaba tana karkacewa cikin kwarkwasa.

Koda bata ce komai ba shi din ba yaro bane qarami,dai dai gwargwado yasan mata ciki da bai,ya kuma karanci mabanbantan hali da dabi'a irin tasu,uw uba ma ya taba yin aure,don haka daga uya sleeping dress da ta saka a jikinta take tsaye kuma a gabansa ya isa ya gaya masa me take nufi?

"Zanyi maganinki" ya ayyana hakan a ransa yana mata duban baki da wayo,yayin da ita kuma ke masa duban so da kuma sha'awa........


58

Assalamualaikum

NAFISAT K ABDULLAHI
Is an actress in the kannywood industry

She's a singer and can sing all types of songs

You can't afford to miss her newly released song named *KADDARATA* part 1-4 on her YouTube channel *OFFICIAL FEENAT*

You can only click on this link and stand a chance to listen and watch her amazing video

https://youtu.be/t__84EwU7Fo

Dont only enjoy the emotional video but also *SUBSCRIBE* to anable you to be notified when ever she upload another video

Like and drop your comment under the video to encourage her do more of that .

The only way you can support and encourage her is by *SUBSCRIBING* to

45 / 67