Advertisements
Chapter 64 Reading Gurbin Ido Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Gurbin Ido Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   64 / 67

189K to 192K   out of 200.8K words

ni nakeso" kafada ta maqale tana murmushi

"Ban yarda ba,nafison me kama dakai gsky" ido ya zaro

"Angel......kina kallon kanki da kyau kuwa,kinsan yadda Allah ya tsara halittarki?,duk sanda na kalleki saina yima daada addu'a da fatan dawwama a aljanna data haifomin ke" murmushi tayi tana sake lumshe idanunta,farincikin samun miji d'aya da d'aya kamar ja'afar na sake kamata,bata da abinda zatace da anni itakam a rayuwa,ta gama mata komai data hadata da d'an jikan nan nata,wanda ya hada komai na rayuwa,ko a aljanna shine zabinta

"Ko baki qoshi bane naga kina wani kallona qasa qasa?" Ya fada cikin sigar tsokana yana kai hannuwansa saman qirjinta daya soma cika sosai saboda yanayin ciki,hannuwansa ta ture tana bata fuska hadi da turo baki

"Nifa yunwa nake ji Allah,a bani abinci ko kuma na cinyekan" tattausan murmushi ya saki yana dora kansa saman cinyarta ta tadda zai iya ganin fuskarta sosai

"Bana gajiya dake angel,bana gajiya da kasancewa tare dake,you are my world angel" a hankali ta dora tattausan lips dinta akan nasa,ta bashi wani hot kiss,sai ya lumshe ido yana fadin

"Wash Allah amma,zata kasheni" dariya ya bata sosai har tana qyalqyalawa,gami da sanya hannunta ta rufe fuskarta.

Babban hijab ya dauko mata yace suje taci abincin a wani wajen,daga nan tadan tattaka ta miqe qafart,hakan yayi mata,taji dadi sosai,don tunda ta kwanta ciwon bata fita ba.

Leqawa tayi ta gayawa baaba tabawa zasu fita,tayi musu adawo lafiya tana binsu da kallo,murmushi kwance akan fuskarta tana mamaki.lallai mata suna da wata babbar baiwa da daraja,mutum kamar ja'afar amma yarinya kamar maimunatu ta sukurkutashi,inda wani na waje aka baiwa wannan labarin zai qaryata,captain ja'afar a kitchen yana sakun dan wake(🤣🤣kadan daga aikin mata,munfi gaban haka,talaka ko mai kudi ko malami dukka a tafin hannun mata suke,Allah dai ya qara mana albarka da juriyar haquri da mazanmu,ya qara mana qauna da fahimtar juna a tsakaninmu,ameen)

A hanya yake gaya mata ya sama mata malama da zata dinga zuwa kullum,qarfe sha daya na safe zuwa biyu kullum suna karatu,muhimman subjects da take buqatar samu a waec neco da jamb dinta,in sha Allah karatunta bazaya tsaya ba.

Qwararriya ce sosai matar,hasalima hausa kadan kadan takeji,sunanta miss serah,sosai taji dadi, hankalinta kuma ya sake kwanciya,don yanzu babban burinta a yanzu shine ta zama full house wife,ta kyautata masa matuqa kamar yadda taga daadarta tanayi sanda take raye,gata da soyayyar da ja'afar ke nuna mata babu wani abu da zata saka masa dashi face nuna masa zallar soyayya da kulawa.

Wannan eatery din mai tsada daya saba zuwa ya kaita,yace yau sai ya qureta,ta zaba duk abinda takeso a kawo mata

"Zan baka mamaki"

"Haka nakeso" ya fada yana zube mata idanun nan nasa,ta kuwa zaba abinci kamar hauka, waitress din ta kalleshi

"Sir,total din fa da yawa" fuskarsa a dan daure kamar yadda ya saba zama boss dinsa duk sanda ya fito ya kalleta

"Kiyi aikinki kawai,ba ruwanki da abinda za'a charger"

"Ok sir" ta fada tana juyawa a ladabce,cikin zuciyarta tana jin inama ace itace maimunatu,tunda suka shigo idanunta yana kansu,wata irin madarar soyayya take gani suna zubarwa zallarta(haka dan adam yake,a duk sanda kaga wani ya zama wani,ko ya taka wani muqami,burinka kawai dama kaine shi?,shin kasan irin qayoyin daya taka ya wuce a hanya kafin ya iso bigiren da yake kai?,so duk wanda ya zama wani akwai qalubale taf daya haura kafin yakai tudun nasara,jajircewa haquri da juriya gaskiya da amana suke kai dan adam duk wani mataki a arayuwa,kamar yadda amanar maimunatu ta sake baiwa anni sha'awa wajen hada iri da ita).

Tun tana ci cikin marmari yana tsokanarta har ta fara zare idanu,dariya irin wadda ya jima baiyi ba ya dinga mata,har sai daya sanya hannayensa dukka biyu ya rufe fuskanshi,Allah yasa babu kowa a kusa dasu.

Sautin kukanta kawai yaji,ya daga kai da sauri yaga tana hawaye

"Ya salam,me kuma akayi miki?"

"Ba kaine ba kakemin dariya saboda ban cinye ba?" Lallai shagwaba ta sake gaba,haka don dole ya danne dariyarsa ya dinga rarrashinta,ya lallaba kayarsa suka biya bill suka wuce.

Yanason cika umarnin abbi,don haka ya biya gidan umma sa'adah ya ajjiye maimunatu yace zaije ya dawo,ta gaida umman,cikin murna da zumudi ta shige cikin gidan yaja motar kai tsaye zuwa gidansu unaisa.

Yana shiga gidan guard din suka fara rige rigen gaidashi,kafin a shiga cikin gida a gayawa haj Aayah zuwansa,babban parlor din da ake sauke baqi na musamman a gidan tasa aka kaishi,ta dubi unaisa wadda tunda taji ance captain ja'afar ya iso ta miqe ta zauna daram,zuciyarta gaba daya tana gareshi,ta gaji da dakon zuwansa,ta kira wayarsa har sau babu adadi bai daga ba,shi yasa ya samu daddynta da maganar,shi kuma ya gayawa abbi wanda da farko baisan me ake ciki ba.

Cikin shigar alfarma haj Aayan koda yaushe take,macace mai izza taqama da fadin rai,duban unaisa tayi,tana jin haushinta yana cikata yadda taga ta rikice daga cewa yazo,tana jin bacin ran yaron a ranta,diyarta kamar unaisa ta zauna wannan auren jeka nayi kan,ga yaran qawayenta 'ya'yan wasu wadanda takeso ta aura mata su amma fir yarinyar taqi sa taimakawar qanwarta anty talatu,yau zata kawo qarshen komai

"Ki zauna,ni zanje na ganshi" kai unaisan ta daga badon taso ba,haka kawai taji ita hankalinta bai kwanta da ita ba,amma sai ta koma ta zauna kawai.

Ko zama baiyi ba,yana tsaye a falon ya baiwa qofa baya yana duba wata calendar dake dauke da hotuna da bayanan shugabannin da suka mulki nigeria yaji sallamar haj Aayah maimakon unaisa.

A nutse ya juyo suka hada ido ita dashi,ta zuba masa idanu tana karanto abubuwa da yawa da suka janye hankalin diyarta a kanshi,bata taba masa kallon tsaf ba sai yau,tabbas ya cika namiji,inda unaisa zata samu yadda takeso a game dashi babu abinda zaisa ta shiga lamarinsu,yayin da shi kuma kallon farko ya karanci akwai abinda ta shigo dashi,sai ya sake dai daita kansa,ya tattara dukka wani izza da kwarjininsa waje guda
84

Kallon kallo suka yiwa juna na wasu daqiqu kafin hajiya Aayah ta janye idanunta,ta sake tabbatar da izzar sa da kuma jin kan da akace yana dashi,ta sani,jinin gidan marwan akko ne,kuma jikoki ga maryam farouq kumo,ta wani fannin kuma shi din jinin sarautar wani yanki ne na qasar gombe daya gada daga kakansa mahaifin aishatu mahaifiyarsa,bai tsintsa a qasa ba

"Sai yau suka turo ka ka maidata kenan?......" Ta fada tana dubansa kai tsaye cike da burin nuna nasa martaba da darajae diyarta,daure masa kai maganar tayi,kafin yace wani abu duk da baida niyyar tofawar ta sake magantuwa

"Wato ga mara galihu wadda aka gaji da ita aka baka sadakarta,kq koromin diya gida babu abinda ta aikata maka,bayan ka jingineta cikin gidanka ba sid'i ba sad'ad'a.....lallai munubiya tayi gaskiya,duk sai yanzu zancanta ke bayyana sosai,na yarda nayi sake dana bar unaisa tabi zabin ranta......to wai shin ma kai ke aurenta ko wadan can tsofaffin da ka baro a gida?" Kai tsaye ya qanqance idanuwansa cikin nata yana dubanta,mai takeson fada?,martaba da muhibbar mahaifansa take shirin tabawa ko kuwa yaya

"To bari kaji,ina raye unaisa ba zatayi zaman boranci ba,yanda suka rayu ba wanda ya takura musu haka 'yata zata rayu,kaje ka gaya musu,indai sun shirya zama da diyata dole su martaba ta su kimantata su kuma daukaka darajar ta,don ita din me daraja ce,indai kanason zamanka da ita dole kasan darajar ta da kimarta"

"Idan kuma akaqi fa?" Ya fada yana jin wani abu na tsaye masa a wuya saboda taba masa ababen da duk duniya bashi da kamarsu,cikin mamaki take kallonsa

"Saika sawwaqe ma diyata,tunda dai aisha ko maryama ne suka haifamin ita ba" gam ya runtse idanunsa,tabbas da haduwar hanya sukayi da matar nan ba abbi bane sila sai ya nuna mata zallar kuskure da kuma wautar data tafka yau din.

Da gudu kuma cikin kuka unaisa data gaza gamsuwa da tahowa mommyn nata ita daya,ta biyo bayanta ta kuma labe tana sauraren abinda ke afkuwa ta afko dakin cikin kuka

"Haba mommy.......ya zakice haka?" Da mamaki take kallonta

"Ai biyoni kikayi?,to idan bance haka ba me zance,shashasha kin tsaya kamarki namiji na wahal dake kamar shine autan maza,to indai bazai sanyaki a gaban kowacce diya mace ba ciki harda uwarsa wallahi bazan bari kici gaba da zama dashi ba,don ke din mai daraja ce" idanu ya zubawa unaisan yana son hango darajar da hajiya Aayah ke magana akanta tattare da unaisa,hala bata da masaniyar komai,darajar daya tabbatar babu ita sam,amma zai basu assignment mai wahala,zai kuma bar musu tabo,ya zaro hannunsa dake dunqule a aljihunsa,wanda sai sannan yaji saman receipt din da aka basu a wancan eatery din ya dora,ya maida hannunsa ya zaro reciept din tare da ciro wani irin biro mai hade da pen perfume.

Yana dora hannunsa saman takardar unaisa ta saki mommyn ta taho da sassarfa tana isowa gareshi

"Don Allah kada ka aikata,zan zauna zan kuma zama duk yadda kakeson gani na,wallahi mommy laifina ne,nice nayi masa laifi,ni na jawo yacemin na taho" ta fada cikin kuka gami da dana sanin gayawa haj Aayah duka magangun da haj munubiya ta kitsa mata,hadi da janyo hajiyar tazo har gida ta sake tsarawa mommyn tata zance,duk tayi hakane don a sake azawa ja'afar rashin gaskiya,a kuma yi masa kaca kaca a nuna masa martabarta,ta yadda zai riqeta da kyau,kuma kowa a gidan ya shiga hankalinsa,yasan ita din ba abar banza bace.

"It's too late" ya fada a ransa,bai gama ayyanawa ba haj Aayah ta dakawa unaisan tsawa

"Kika sake kika isa gabansa ko kika sake furta wani abu sai na tsine miki albarka,nono na kuma da kikasha ban yafe miki ba,ya sakekin,da ana aure kafin a gama idda zakiyi aure".

A nutse ya rubuta mata saki uku kyawawa,ya tura kardar gefe,sannan ya maida abun rubutun aljihunsa,har yayi taku biyu ya dakata

"Ko gobe kikeso zaki iya daura mata aure,don ban dora mata idda ba,amma ban sani ba ko tana buqatar yin istibra'i,saiki tambayeta"

"Istibra'i ba idda ba?" Hajiya Aayah ta fada tana maida dubanta ga unaisa dake riqe da takardar baqinciki kamar zai kasheta,wadda sai dafa fara duba bayanta dake dauke da sunan maimunatu abincin da taci da kudin daya kashe na abinda suka biya,da yake haka tsarin reciept din nasu yake,har yaushe maimunatu diyar ruga baqauyar bafulatana qanwar cikinta ta samu wannan matsayin a wajensa?,gashi ita ta buge da saki sakinma na wulaqanci har guda uku?.

Cikin mota ya dinga sauke ajiyar zuciya,har ransa yaji babu dadi karon farko kuma tausayin unaisa ya ratsashi,saidai ci gaba da zama da ita abune da bazaiyiwu ba,inda batazo da alfasha ba,bata kuma dauki maganganu ba da zai iya haquri taci darajar soyayyar da take masa,a hakan ma sai idan ta yarda zata zauna dashi din,saboda yasan kansa da zuciyarsa,wani mahaukacin so ko qi garesu,wanda shi kansa baisan ta yadda zai canza kansa ba,indai zasu zauna tarenma cutuwa zatayi,bazai taba iya adalci ba,shi yasa ya yima kansa alqawari,indai ba wata babbar lalura ba ba abinda zai sashi zama da mata biyu,kamar yadda alqur'ani ya bawa maza shawara ga wanda yasan bazaiyi adalci ba,shima zai aikata hakan ne don gujewa azabar Allah ranar gobe qiyama.

Kai tsaye ya karya kan motar tasa zuwa unguwarsu,ya duba lokaci qarfe tara na dare,ya tabbatar abbi yana gida,gwara yakai.kansa da kansa,ya kuma shaida masa abinda yayi da kansa,duk hukuncin da abbin zai yanke masa ya yanke masa.

Tun a gate ya hadu da khadim,ya kuma gaya masa abbin yana ciki wajen anni,don haka ya bude murfin motar ya doshi sassan anni kai tsaye,ko kadan baya jin wata fargaba,yana da wannan tsaiwar tun quruciya,yana da juriyar karba da fuskantar hukunci,kuma a duk sanda yayi irin wannan din zaiyi wuya idan ba shine ke da gaskiya ba.

Da fari anni ta tsorata,ta dauka wani abune ya faru ganinsa qarfe tara na dare,sannan yanayin fuskarsa ba cikin walwala yake ba,kai tsaye ya zube gaban dr marwan

"Abbi......kayi haquri ka yafemin,nasan na maka na dai dai ba,na saki unaisa saki uku,gani a gabanka,kayimin duk irin hukuncin da kaga ya dace dani" duk da anni taji maganar wani iri,amma kuma batayi mamaki ba,tasan dama za'a rina,manya ne fa?,wanda zuciyarsa ke tsaiwa kan abu daya

"Innalillahi wainna ilahi raji'un" abbi ya fada,sannan ya dubeshi

"Mai ya kaika aikata irin wannan mummunan aikin ja'afar,abgadul halalu ilallah fa?" Fada sosai abbin ya rufeshi dashi, duk da yasan komai,amma bai nuna goyon baya ba

"Ya isa marwanu" anni ta dakatar da abbi,don batason fadan da yaketa faman yi,

"Kayi gaggawa manya,baka kuma kyauta ba,nan gaba koda wasa billhuwallazi karka ce zaka kwata,koda mummunan kallo kuwa" can qasan ransa dariya ta kamashi,yasan jirwaye mai kamar wanka take masa,kashedi kan maimunatun ta take bashi a fakaice,batasan a yadda yakejin maimunatu a ransa ba,zai iya sadaukar mata da rayuwarsa bama

"In sha Allah,a yafemin"

"Tashi kaje,Allah ya kiyaye gaba" anni ta fada,sai yaji wani abu mai sanyi yana saukar masa,kamar kuma an zare masa qaya,qaunar anni da martabarta na qaruwa a ransa,haka ya miqe ya fice yana yiwa Allah godiya da komai yazo masa da sauqi.

"Marwanu" anni ta kirashi bayan fitar ja'afar daga falon,ganin yadda yayi shuru yana nazari

"Na'am anni"

"Kada ka saka wata damuwa a ranka,duk da baka gayan ba nima nayi bincike akan yarinyar,kwata kwata ba kinin manya bace,kuma kaima ka sani ka boye ne kawai,to Allah ya dubi zuciyarsa,baida hakkin diyar kowa ya rabashi da aurenta,saboda haka kada ka wani damu,Allah yasa hakane yafi alkhairi" kai ya jinjina

"Tabbas anni,ni kaina na sani,amma minister yana da kima a idanuna,hakanan shi din na gari ne,bansan me zance masa ba,wanne bayani zanyi masa"

"Allah zai duba zuciyoyinmu ya kawo.mafita" da wannan suka rufe zancan sukaci gaba da lissafin nisabin zakkar da anni zata fidda a shekarar cikin dukiyarta data mallaka.

Washegari abbin yana zaune yana duba wani babban littafin fiqhu bidaayatul mujtahid wayarsa tayi tsuwwa,ya duba yaga minister ne,sai yaji nauyin dagawa

"Subhanallah,dan yau,dan yau sai addu'a" ya fada,har wayar ta katse bai samu qwarin gwiwar dagawa ba,sai kuma yaga gwara ya kirashi da kansa,don haka yaja wayar yabi kiran.

Bugu daya ya daga,yadda suka saba faran faran suka gaisa,saidai muryarsa sam babu karsashi,wannan ya tabbatarwa abbi akwai damuwa

"Ni naso na fara kiranka,kunya da nauyi suka hanani"

"Wallahi kada kaji komai doctor,kai ya kamata na bawa haquri,bansan haka diyata take ba na dauketa na bawa tsakakakken danka ba,abinda yaron ka ya aikata kuma shine dai dai,Allah yayi masa albarka,dama lalatacciya sai lalatacce,tsarkakakku sai tsarkakakke haka qur'ani ya fada" cikin rashin jin dadi abbi yace

"Subhanallah,wanne irin zance kake haka yallabai?,ka daina fada bai kamata ba"

"Dole na fada haka doctor,ace matar aure sa bin wani yaro zuwa dubai kwana da kwanaki?,ko sanda zasu dubai din su duka munafuntata sukayi akace an gayawa mijinta shi ya amince,ashe satar hanya tayi,ta kuma sake komawa a randa suka dawo din ba tare da sanin kowa ba ita da yaron,nima ina da laifi da giyar mulki ta rudeni na sakar musu daula suke zabar dukka qasar da sukaso karatu ko zama,duk da cewa yaran daya dakin aiba haka suke ba,kaga naga izina naga ishara ko?,ni banga laifin ja'afar ko in zargeshi ba ko kadan,ita kanta jiya ta fadi komai da bakinta,tsahon zamanta a gidan bai wulaqantata ba,bata rasa ci sha ko suttura ba, kulawar auratayya kuma tun kafin ta aminta da aurensa akayi mata bayanin sai tayi haquri ta koya masa sonsa ta jashi a jikinta,tunda kowa yasan matsalarsa,ta amince da hakan,ta yarda ko shekara nawa ne zata iya zama,kuma ya bata zabi tunda ya fuskanci ba zata iya jurewa zama dashi ba,duka ta fada,yanzu abokiyar zamanta ta tsinci kanta a wannan halin?"

"Ya salam,ya Allah, jarrabawa ce yallabai,ka daina fadan magangun da zasu sake munana abun" maganganun masu kwantar da hankali abbi yayi masa kafin daga bisani suyi sallama bayan sunyi dogayen maganganu,abbi ya ajjiye wayar tare da littafin hannunsa a gefe,sai yaji shima gaba daya hankalinsa ya karkata ga aurar da yaransa dake gabansa,sai yanzu yake sake ganin gaskiyar anni data tashi hankali kan a aurar dasu,duk da baya shayi ko shakkar tarbiyya ko daya daga cikinsu,dai dai gwargwado ya tsare yi musu addu'a da tarbiyya bakin gwargwado,yana musu kyakkyawan zato.


*BAYAN WATA BAKWAI*

Yammaci ne dake dauke da wani lullumi saboda haduwar hadari a garin,dai dai lokacin cikin private hospital din dake government house road din,dakin dake dauke da sunan amenity one,daga doguwar qawatacciyar varender data qunshi dakunan,tun daga amenity one zuwa four da asibitin ke dashi kana iya jin tashin hayaniya sama sama daga dakin.

Idan ka samu nasarar sanya kanka cikin dakin,zaka hangi mutane zaune cikin dakin,dukkan wanda ka kalli fuskarsa a cikinsu zai bayyana maka zallar farincikin dake kwance tun daga saman fuskarsa tasa har zuwa zuciyoyi.

Anni ammi anty maama,hajja su laila gaba dayansu harda matan kawun nan maimunatu guda hudu,a hannuwan laila da salma fararen shawula ne dake dauke da wasu kyawawan baby boys a ciki,wadanda dukka wanda ya kallesu bazaya so dauke idanuwansa daga kansu ba,wani irin kyau

64 / 67