Author : TARE DA ALK'ALAMIN Category : Complete Novels
ta daban,daga ni sai Shafa'atu fa yanzu,ita d'in ma ba ganinta
nake ba saboda takunkumin da Babalalo ya sa ka min,wallahi Rauda bani da kwanciyar
hankali duk a k'untace nake ji na"
Rauda tayi murmushi tana sauke mayafin ta daga kanta zuwa kafad'ar ta,sannan ta
dubi Habiba tace.
"Ai Lokacin da abin nan ya faru nayi takaici Habiba,sosai naji Haushi fa,kuma ba
Haushin kowa naji ba sai haushin ku,ban da ku mahaukata ne ku zauna wani shirgegen
k'ato ya dinga laftarku ku wajen hud'u,ba kwa wawuso k'afafun Arne ku nanashi da
k'asa,ai sarkin yawa yafi sarkin k'arfi Habiba,gaskiya kun bani mamaki,duk
shaid'ancin ku amma ku ka zauna wani D'an iska ya dillik'e ku a banza a wofi,ai
wallahi da ina cikin ku lokacin da kunga aiki da cikawa".
Habiba ta sauke tagumi ta dubi Rauda ta girgiza kai tace.
" Hmmm! zance kawai kike Rauda,in ba haka ba waye ya isa ya ja da Hukuma?ai Hukuma
ta shallake tunanin kowa"
Da sauri Rauda ta manna mata harara ta katseta da cewa.
"Za ki sa na dannawa Hukumar zagi me sifirin,ai ko shi D'an sandan Yayi muku
hukunci ne ba bisa k'a'idar aikinsa ba,kuna matan Aure d'ima d'ima amma ya keta
muku haddin Aure yayi muku hawan k'awara?
Habiba ta D'an yi dariya tace.
" wane irin Hawan k'awara kuma Rauda?sai kace wad'anda yayi wa fyad'e".
"To menene bambancin?"
Rauda ta katseta da tambaya,sannan ta cigaba da cewa.
" Ai bambancin kad'an ne Habiba,mutumin da aka ce har tsalle ya dinga yi yana
tumami a ruwan cikin ku yana cafar nonuwan K'irjinku".
Habiba ta zaro idanu tana dafe k'irji cike da tsoro,cikin rawar baki tace.
"Inji wane tsinannen mak'aryacin Rauda?a ina kika samo wannan labarin k'anzon
kuregen?
Rauda ta tab'e baki tace.
" Yo zancen duniya yana b'uya ne?ni ma a gari naji".
Habiba ta girgiza kai tace.
"Kai mutane an yi tantagaryar munafukai kuma magulmata,wallahi hannuwansa basu kai
jikin mu ba,na san dai lokacin da ya gama kirb'ar mu ya sa hannunsa yana ta
tunkud'o k'eyar mu waje,ban da haka bai tab'a jikin mu ba wallahi".
Rauda ta D'an rage murya kad'an tace da Habiba.
" Wai kuma da gaske mijin Amaryar ne ya kirawo D'an sandan aka tarfa ku cikin gidan
sa?
Habiba ta ce.
"Hmmm!shine wallahi Rauda,bak'in matsiyaci ba"ta fad'a fuska cike da jimami.
Rauda ta ce.
" Kuma har yanzu suna layin nan basu tashi ba ko?naji an ce gini yake ba za su jima
ba za su tashi.
Habiba ta tab'e baki tace.
"Suna nan har yanzu bak'ak'en munafukai,ai kin san damunar bana tayi gyara,ginin da
ya fara ne ya rushe ya dawo baya,shine har yanzu basu tashi ba"
Rauda ta numfasa tace.
"Ya kamata kafin su bar layin nan ku d'auki fansar abin da yayi muku,wallahi idan
baku rama ba kun yi asara duniya da lahira,ai rama cuta ga macuci ibada ne,ya
kamata ki nemi Saratu da Harira da Shafa'atu ku had'a kai ku d'auki fansa,duk da
dai ba Saratu a cikin ku lokacin da abin ya faru, amma na san zata taya ku yin
yak'in,sai ta wakilci Zahra'u kawai"
Habiba tayi kasak'e cikin tunani,zuciyarta na kai kawo,ta k'urawa Rauda ido tace.
"Ta ya ya kike tunanin Hakan za ta faru Rauda?nifa Yanzu tsoron duniya nake ji
domin ta koya min hankali,amma kuma kina zuwa da wannan shawarar naji ta kwanta
min,yanzu me kike tunanin ya kamata ayi?"
Rauda tayi murmushi ta matso jikin Habiba sosai ta kai bakin ta kunnen Habiban tayi
mata rad'a,Habiba ta d'ago ta kalli Rauda bayan ta gama jin maganar ta,suka kwashe
da dariya suka d'aga Hannu suka tafa……!
Rauda ta tsagaita da dariyarta ta dubi Habiba tace.
" Ke na manta muna ta zance ban yi miki jaje ba,Ashe Shagon Babalalo na Aski ne ya
k'one,wai gobara da tsakar dare ko? ni sai jiya Shafi'u yake fad'amin,dalilin
zuwana kenan ma"
Habiba tayi murmushi tace.
"Ai ba jaje ya kamata ki taya ni ba,Murna ya kamata ki taya ni Rauda"
Rauda ta zaro idanu tace.
"Murna kuma?asara ta samu mijinki amma kice a tayaki murna Habiba?ke kuwa wace irin
zuciya ce da ke da kike murna da samuwar asara akan mijinki?"
Habiba tayi shewa tana buga cinya tace.
"Yo murna mana Rauda,Ai Babalalo mugunta ya so shirya min yayo min kishiya,can
danginsa munafukai aka bashi wata tsomalalliyar Yarinya me zubin y'an ruwa,har fa
ya ta da ginin filinsa kad'an ya rage ya kammala wannan ibtila'in ya same shi,gurin
Neman abincin sa ya k'one k'urmus,yanzu tilas haka yayi gwanjon gidan da ya fara
ginawa ya siyar ya samu kud'in da ya gyara shagon sa,kinga ai yanzu tilas ya
hak'ura da Auren da ya jajibowa kansa ko?tunda babu y'an matsabbai a hannunsa da
zaiyi hidimar auren da su,in kuma ba kan Uwatar zai siyar yayi hidimar Auren ba".
Rauda ta tuntsire da dariya kamar za ta kifa,sannan tace.
" Amma Habiba baki da mutunci wallahi,kuma fa da Babalalo zai siyar da kan Babarsa
da ya samu kud'i,don naga kan nata har rinjayar jikinta yake saboda girma".
Habiba ma ta shek'e da dariya ta ce.
"Yo baki ga shi ma Babalalon gadon k'aton kai yayi ba,kwanaki da muka zabga karo ya
buga min kansa wallahi na zaci dutsen Dala ne ya rufto min,sai da na kwan uku ina
jinyar ciwon kai,ai Allah yayi musu baiwar gingimemen kai,ni da Atiringim".
Suka kuma kwashewa da dariya suna tafawa,a dai dai lokacin suka ji ana zabga
sallama a soro,Habiba ta Amsa da fad'in "wanene?"
" Bak'uwa ce"Aka amsa daga soron.
"To shigo Bak'uwa" inji Rauda kenan.
Ta shigo tana murmushi, duk suka bi ta da kallo basu shaidata ba,banda kallon
fuskarta babu abin da suke yi,tasha kwalliya hoda fururu,ga jambaki bak'i ta lafta
tamkar wata Y'ar daba,d'aurin nan cokoko dashi a gaban goshi,Habiba ta matsa mata
ta zauna kusa da ita kan tabarmar da take zaune,bayan sun gaisa ne Bak'uwar ta dubi
Habiba da murmushi ta ce.
"Na san baki shaidani ba ko?Ni sunana An gayu,jiya muka tare a layin nan gidan da
aka tashi,ni matar Malam Arabi ce,kuma na shigo mu gaisa ne mu saba da juna a
matsayin mu na mak'ota a yanzu".
Ambatar sunan Malam Arabi da tayi yasa k'irjin Habiba bugawa da k'arfi,har abada ba
zata manta da wannan matsiyacin mutumin ba,duk lokacin da ta tuna shi sai ta hango
azabar da ya ganawa bakinta da lab'b'anta😂…….!
Comments
Share
Vote
Pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*BABI NA BAKWAI DA NA TAKWAS*
PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️
***Habiba ta yank'are hak'ora zuciya a jagule tana zuba yak'e tace.
"Ayyo! Ni kam da yake ban tab'a ganinki ba shiyasa ban shaida ki ba,na kan ji
Labarin ki dai a wurin yara,kece mai sai da k'osai da safe ko?
An gayu tace.
" Eh wallahi kuwa,k'osai da awara duk ina toyawa da safe,haka nan ina siyar da
gasarar kunu,dafatan kuma za ku zamo d'aya daga cikin kontoma na ku dinga siya"
Habiba ta rik'e baki tace.
"Kontoma kuma?menene kuma kontoma?
Rauda da ba ta saka musu baki ba sai lokacin ta kwashe da dariya ta dubi Habiba
tace.
" Ke ina jin dai Costomer za ta ce ko?"
An gayu ta buga cinya ta k'yalk'yale da dariya da k'arfi,sannan tace.
"Ai kuwa kamar kin sani K'awata,Kastoma nake nufi"
Habiba kam dariya tayi,daga ganin wannan matar shuda ce bata da cikakken
saiti,domin zama tayi ta dinga zuba musu zance soki burutsu,idan tayi wata maganar
sai ta dubi Rauda tace "Hakane ko K'awata?"
Ita kam Rauda sai biye mata take suna shan Shafta da kwasar dariya,domin ta fahimci
An gayu irin matan nanne masu shegen surutun tsiya,komai ya fito bakin su fad'a
suke yi babu tantancewa.
Habiba dai takaici ya ishe ta,An gayu tak'i tashi ta tafi gashi basu gama hirar su
da Rauda ba,karad'in ta kawai ake ji tana buga zance,sai da ta kusan awa d'aya
sannan wani yaro ya shigo yana fad'in "Wai An gayu ta zo in ji Malam Arabi"
Aikuwa da hanzari ta mik'e ta shuri silifas d'in ta tana fad'in.
"Bari naje na amsa kiran maigida,yanzu zan dawo,K'awata ai zan kuma tarar da ke
ko?"
Habiba ta zaro idanu ta fakaici idanun An gayu ta laftawa Rauda Harara,Rauda ta
gane abin da take nufi shiyasa tayi murmushi tace.
"Ah ah ba lallai ki sameni ba K'awata,wataran za mu sake had'uwa ai,ni ma bani da
nisa tsiran mu layi d'aya ne,ina layin makarantar Daren da mijinki yake koyarwa"
Nan An gayu tace Aikuwa za ta kaiwa Rauda ziyara,suka yi sallama ta fice da
sauri,suka bita da kallo Rauda na dariya sai Habiba da take sakin tsaki tana
hararan Rauda.
Rauda tana dariya tace.
"Wai ni me nayi miki ne kika isheni da harara?ni fa bani na sa mijinta ya jibgeki
yayi miki ganda ba balle kice"
Habiba ta sake sakin tsaki ta tofar da yawu tace.
"Wai ke Rauda baki lura da wani curarren tasono da koriyar majina a hancin matar
nan ba,an ya kuwa kanta babu motsi,babba da ita babu gyara ki dinga fitowa haka ana
kallonki,ni wallahi duk ta tayar min da zuciya ma kamar nayi Amai"
"Kika sani ko mura take yi?" Rauda ta fad'a tana tuntsira dariya.
Habiba tace.
"Kin manta Uwar mura take yi,ko in ce miki frinji ne a kanta k'arewa mura,to ko
muran take yi ma ba za ta dinga gyara hancinta ba?ni wannan da abinci nake ci ai ta
haramta min wallahi,kuma wai a haka ance miji na kira ta zabari k'afa ta tafi,taf!
Wannan miji zai yi kyakkyawan gani,ke daga ganin matar nan kin san ladan noma
ce,k'ila Noma malam Arabin yayi wa gyatumin ta aka bashi ladan ta daga
k'auye,wannan aba haka babu fasali"
Rauda ta keb'e baki tace.
"Karfa ki manta kin saba da zama da k'azamai Habiba,babbar aminiyar ki Harira ma ai
k'azama ce ta bugawa a jarida wallahi,kuma koma ladan nomar ce ba shi yaga zai iya
ba"
Habiba ta kama girgiza kai da Hannu ta na cewa.
"Lala lala al mandudu kalas!billahillazi huwar rahmanu duk k'azantar Harira ba zaki
ganta da tasono da mijina a hancin ta ba,ita dai kawai k'asanta ne bata gyarawa
yake d'oyi da wari,sai kuma d'oyin hammata,kuma kwanakin baya kan abubuwan nan su
faru har turaren tsuguno da miski ta siya gun zahra'u,kinga kuwa ai ta d'akko
hanyar gyara ko…!?
Rauda za ta yi magana kenan wayarta ta soma k'ara,ta bud'e Jakarta ta fito da ita
ta na dubawa,Ashe yayarta ce ke sanar da ita sun zo bata nan suna k'ofar gida,nan
Rauda tace su jirata gata nan zuwa,domin bata yi nisa ba tana kusa.
Tana kashe wayar ta fara k'ok'arin mik'ewa tana gyara mayafin kanta,ta dubi Habiba
tace.
" Habiba bari na wuce gida,yaya Abida ce suka zo bana nan,ni ban ma san da zuwan su
ba wallahi,k'ila yayen D'an ta Imamu ta kawo min Dan jiya mun yi waya da Umman mu
tace min an yaye shi yau za a kawo min shi,to ban ma yi zaton da Uwar D'an za a zo
ba"
Habiba ta sauke numfashi tana mik'ewa tsaye ita ma,sannan ta dubi Rauda tace.
"Wai ni kuwa Rauda ya kuka k'are da wannan tsinannen mutumin mijin Abida?haka kawai
ya zamar da ita k'aramar bazawara haihuwa d'aya,amma dai kun maka D'an iska a kotu
ko?
Rauda ta ce.
" Aikam dai yana nan yana zabga nadamar abin da yayi,kullum yana sintiri akan ta
dawo gidan sa ita kuma ta k'i komawa,Yaya Abida ta sha wahalar wannan
mutumin,kullum fa sai ya sha giyarsa yake zuwa ya tanana mata jikinta kamar wani
d'anyen nama,hmmm…bari na wuce Habiba hirar ba zata k'are ba,in muka kuma had'uwa
ma k'arasa "
Rauda ta fad'a tana yin gaba.
Habiba ta bita har Soro tana yi mata rakiya,suka yi sallama,Rauda ta wuce ita kuma
ta juyo cikin gida ta fara k'ok'arin wanke waken kulelen da za ta yi.
**************
Amina Zaune a tsakar gidan Shafa'atu ,ta tasa Shafa'atun a gaba da d'irmemen cikin
ta haihuwa ko yau ko gobe ta zabga tagumi,a hankali shafa ta gyara zamanta kan
tabarmar da take kai ta yatsune fuska,tana D'an jin ciwo kad'an kad'an kamar me
nak'uda,sai da ciwon ya lafa ta d'ago ta dubi Amina tace.
"Wai ni me yake Faruwa ne Amina?duk na ganki ba yadda na saba ganin ki ba,ko dai
har kin fara shan gashi hannun Sunusin ne?waya gayamiki barno gabas take?kina murna
wai ke kinyi Aure zaki sha soyayya ko?an fad'a miki mazan yanzu mutuncine da su?
tattatun y'an iska ne fa wallahi,a waje soyayya kamar za a cinyeki,da zarar kin
shiga kin zama nama,kinga duk k'ibar nan ta ki ko,idan miji ya minnira miki wani
takaicin sai kin dawo kamar falwaya saboda rama"
Amina ta sauke numfashi ta dubi Shafa'atu tace.
"Ni fa Anty Shafa babu abin da ya shiga tsakanina da mijina kike ta wannan
subad'ad'in,muna zaman mu lafiya wallahi,domin idan dad'i da soyayya suka yi mana
yawa har goyani yake yi"
"Ya Goya wa?" Shafa ta ambata tana zabura har k'ugunta na amsawa,sannan ta cigaba
da magana cikin zare idon mamaki.
"Wai Sunusin ne yake goyaki Amina?Sunusin da na sani me baya kamar allon mayya ta
k'ak'a bayan sa zai d'auke ki kina da girman buhun kwaki uku?sake zance dai Amina"
Amina ta b'ata rai ta d'aure fuska jin maganar Shafa'atu, nan da nan Shafa'atu ta
shiga taitayin ta ganin yadda fuskar Amina ta d'aure,kar taje ta haye tsohon cikin
ta ta saka ta haihuwar da bata shirya ba 😂.
Cikin k'ufula Amina tace.
"Ina ganin mutuncinki Anty Shafa, don haka kar ki sake cin mutuncin mijina
gaskiya,nazo ne na fad'a miki damuwata saboda naga kin fi kusa da ni a halin
yanzu,idan kuma ba zaki saurareni ba ne na k'ara gaba"
Shafa'atu ta yi saurin tare ta da cewa.
"Haba haba K'anwata,kiyi hak'uri wallahi zan saurare ki,menene yake faruwa da ya
sanya ki a damuwa?"
Amina ta yi ajiyar zuciya, ta k'urawa Shafa'atu idanu tace.
"Wani tashin hankali ne yake Neman tunkara ta ina zaune lafiya,jiya Sunusi yake
fad'a min wai Harira zata dawo gidan da nake mu cigaba da zama tare,to kin dai san
Halin Harira,kin ma fini sani tunda tare na ganku,Kuma nima kin san kamar zawayi
nake bani da hak'uri,shine nazo ki bani shawarar yadda zan zauna da ita,don gaskiya
ba zan d'auki rainin wayonta ba,ban auri mijinta ba ma ban d'auka ba balle yanzu?
idan tace zata kawon iskanci za mu ci uwar sabada ne ni da ita ……
Wani irin zaro ido Shafa'atu ta yi,cikin ta ya fara k'ululu,Harira zata dawo?tabbas
za a sha drama,musamman da jiya Kamilu yake bata labarin wai Malam Arabi ma ya dawo
layin su gidan da su Zahra'u suka tashi,tabbas BAHAGON LAYI zai k'ara shiga
chakwakiya kenan …….!
Comment
Share
Vote
pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*BABI NA TARA DA NA GOMA*
PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️
*Kar ku manta idan kun zo karatu ku fara yin fitsari saboda kar a samu matsala ya
kufce kuyi a wando kamar wancan karon🤣🤭sannan a tanadi (Jar Kanwa) saboda ciwon cikin
dariya*🤣🤣😆🤪🤪
"Wai da gaske kike yi Amina?da gaske Harira zata dawo layin nan da zama?" Shafa'atu
ta ambata a tsorace.
Amina ta cigaba da kallon ta cikin mamaki,ganin yadda duk ta firgice,ko menene abin
tsoro a wannan maganar oho!dan haka ta k'ank'ance idanu tace.
"Ya naga wai duk kin firgice ne?maganar da nayi ce ta firgitaki ko dawowar
Harirar?"
Nan da nan shafa'atu ta waske tana Sosa k'eya da cewa.
"Ah ah wallahi babu komai Amina,kawai ina tayaki kishi ne,bana son Harira ta dawo
ta takura miki Dan shegiyar kanta ce wannan matar"
Amina ta tab'e baki ta D'an harari Shafa'atu tace.
"Fad'i gaskiya dai,ko dai kike taya ta kishi tunda k'awarki ce?yo ni wata Harira ta
isa ta takura min a gidan mijina?wadda nanan masai ma tafi min daraja a kanta,ai
wallahi ta dawo mu zuba a gani,shege ka fasa,Idan ta kwantar da kanta muyi zaman
lafiya,idan ta zo da akasin hakan kullum zata dinga cin na Akuya ne a hannu
na,domin ba saurara mata zan yi ba"
Shafa'atu ta rik'e hab'a tana girgiza kai tace.
"Ah ah kar ki fad'i haka Amina,ta ya ya zan taya Harira kishi Dan a cutar da ke?kar
fa ki manta ke K'anwar mijina ce,ita kuwa ba dangin iya ba na Baba sai had'uwar
layi kawai,kinga kuwa ba zan tab'a barin ki Dan na bita ba,kuma insha Allahu ma
lafiya k'alau zaku zauna,Harira ai taga ishara,bayan dahuwar ganda da kika yi mata
ga dahuwar ragadada da yallab'ai me tiyagas yayi mata,ko in ce yayi mana,kinga kuwa
dole ta hankalta ku zauna lafiya"
Amina ta mik'e tsaye tana sab'a mayafin ta tace.
"Atoh dai wannan ya rage na ta,ni dai a shirye nake tsaf da makaman ya k'i na,haka
nan na tanadi nukiliya Wanda zan tarwatsa duniyar ta muddin tace zata yi ya k'i da
ni,amma in ta zo da zaman lafiya ta yiwa kanta k'iyamullaili"
Shafa'atu ta amsa da cewa.
"In sha Allahu ma da zaman lafiyar za ta zo,ina da yak'inin hakan" sannan ta zarce
da cewa.
"Wai gida zaki koma ne naga kin mik'e?"
Amina tace.
"Eh gida zan koma,zan yi wa Sunusi wanki ne?"
"Wanki kuma?yanzu har wanki kike wa Sunusin?cewar Shafa'atu cikin mamaki.
Amina ta jijjiga kai tare da cewa.
" k'warai kuwa,to ba mijina ba ne?ai babu abin da na zan masa ba,kamata yayi na
share masa hawayen sa da suka dad'e suna zuba a dalilin rashin samun mace ta gari"
Shafa'atu tayi murmushin yak'e tace.
"Tabbas haka ne kuwa,Dan kuwa Harira ko D'an tofi bata tab'a wankewa Sunusi ba,wai
bata ga yadda za a yi ta wanke kayan gardi me d'auke da guntun kashi ba"
Takaici ya kama Amina,ta saki tsaki tana cewa.
"Don Allah ni daina yi min maganar wannan dabbar,danni Harira bambancin ta da
dabbobi kad'an ne,jaka jahila kawai"
Shafa'atu tayi muk'us ganin Amina ta fusata kar ta huce a kanta,daga nan suka yi
Sallama Amina ta wuce gidan ta tana cewa Shafa'atu "Allah ya raba lafiya,sai mun ji
kyakkyawan labari don da alamun nak'uda kike yi" ta bar shafa'atu da bin ta da
kallo tana hango yadda zaman Harira da Amina zai yiwu a muhalli d'aya,tashin
balagar D'an tsako kenan….!
******************
Da Sallamar ta ta shigo tsakar gidan,daga can cikin d'aki ta ji ana amsa mata,Dan
haka ta d'aga labulen rumfar ta shiga tana k'ara wata sallamar.
Umman Saratu da ke zaune a tsakiyar Rumfar ta sake amsawa tana fad'in.
"Maraba lale da Hajiya Maimuna, sannu da zuwa"
Hajiya Maimuna ta nemi gefen Umman Saratu ta zauna tana kallon k'afarta da aka
shafe ta da garin magani,cikin tausayawa ta amsa da .
"Yawwa Fatsima sannun ki,ya kika k'ara ji da k'afar ta ki?"
Umman Saratu ta ce .
"Sai godiyar Allah,ga k'afa nan muna lallab'awa tak'i takuwa,kullum Malam yana
hanyar k'auyuka karb'o min magnguna,ban da rubutun da kullum yake min ina sha,to
kin san an ce ciwo farat d'aya yake shiga,sauk'i kam sai a hankali"
Cikin jimami da tausayawa Hajiya Maimuna tace.
"Tabbas hakane Fatsima,to Allah ya mayar kaffara ya baki lafiya,Allah ya yaye miki
wannan ciwon k'afa"
"Ameen Ya Allah" Umman Saratu ta amsa,sannan ta zarce da cewa.
"Baki ga Malam d'in a zaure ba ko?ai baya nan sun tafi wani gida yin saukar
alk'ur'ani,sabon gida ne shine me gidan ya gayyace su shi da almajiran sa domin ayi
karatu a gidan"
Hajiya Maimuna ta gyara zaman ta tace.
"Aikuwa dai ban ganshi ba,sai dai wasu almajiran da suke karatu,yaushe Baba Laminde
tazo daga k'auye Fatsima?na ganta a tsakar gida kan tabarma