Author : TARE DA ALK'ALAMIN Category : Complete Novels
kokawa,ni kuma na
tunkud'e ta ban san cewa rijiyar zata fad'a ba,don Allah ka taimaka kayi hanzarin
ciro ta kar ta mutu ta rataya a wuya na in shiga uku in lalace".
Duk da takaicin da ya kume k'irjin Sunusi hakan bai sa yak'i jin tausayin Amina
ba,domin ya san itan tana son ayi zaman lafiya,Harira ce ta cika fitina har bai san
yadda zai yi da ita ba,shi kansa ta gama addabarsa darajar Inna kawai take ci da
kuma maraicinta da yake duba wa.
Yana nan tsaye ya rasa abinyi sai Amina da ke kuka.Lek'a kansa ya sake yi cikin
rijiyar,gani yayi Harira ta daina motsi gabad'aya da alamun ko suma tayi,da wani
irin hanzari ya ture Amina daga gefensa yana salati yayi hanyar fita waje domin
neman mafitar yadda za a ciro Harira daga rijiya.
************
Kimanin kwana biyar da faruwar lamarin bayan an tsamo Harira daga rijiya,wadda taci
bak'ar wahala duk ta gwaggwabje jikinta ya k'warzane,bakinta ya sake karkacewa
daman ba hak'ora.
Kwance take lamo cikin akurkun d'akinta,zaune ta tashi tana amsa sallamar Habiba da
ta shigo cikin d'akin,Habiba ta k'araso da sauri fuskarta cike da jimami da
tausayawa take kallon Harira ganin duk ta fita daga hayyacinta,zama tayi kusa da
Harirar tana fad'in.
"Sannu Harira ashe haka wannan abu ya faru?Innalillahi wa inna ilaihir
raji'un ,sannu kinji Allah ya mayar kaffara"
Harira ta yatsina fuska ta dubi Habiba da lomammen bakinta ta ce.
"Hmmmm! ni me zaki ce dani Habiba?wannan ibtila'i ya faru dani amma kika sa zuwa
akan kari ki dubani har yau kwana biyar,anya kuwa aminci da zaman tare yace haka
Habiba?"
Habiba tayi ajiyar zuciya ta sauke mayafinta kan kafad'a tanai wa Harira nuni da
k'asusuwan wuyanta sannan ta ce.
"Ni ma idan kika dubeni tsaf daga sama har k'asa Harira bana cikin wata nutsuwa da
kwanciyar hankali,a halin da ake ciki fa yau saura kwana shida rakkin a d'aurawa
Babalalo aure Harira"
Harira ta gwalalo idanu tana dafe k'irji ta ce.
"Abin ya zo kanki kenan Habiba?to shi Babalalon dan uwatar da wane kud'in zaiyi
auren?ko ba naji ance kwanaki azal ta fad'a masa yayi gobara ba?kai gaskiya Habiba
maza ba k'ananun jarababbu bane,ban da toshewar basira wannan bala'in ya same shi
amma ba zai iya hak'ura da auren ba?"
Habiba ta fara matsar hawaye zuciyarta cike da k'unci take kuka tana fad'in.
"Ni Harira kwata kwata ba auren ne yafi d'aga min hankali ba ma yanzu,yadda auren
ya zamo auren cin amana shine yafi damuna,gabad'aya na rasa in da zan tsoma raina
naji sanyi Harira"
"Kamar ya ya auren cin Amana Habiba? Harira ta tambaya cike da mamakin jin kalaman
da suka fito daga bakin aminiyarta Habiban Babalalo.
Habiba ta fyace majina da gefen mayafinta hawaye na sharara ta ce.
"Ai kin san k'awata Rauda ta bayan layi ko? wadda mijinta abokin Babalalo ne,to
wallahi in tak'aice miki labari da Rauda da mijinta sune suka nanawa Babalalo Yayar
Raudan,wata bazawara ce har da d'anta wai ita Abida,yanzu fa har an gama komai
saura kwana shida a d'aura auren,wai duk yadda nake da Rauda shine taci amanata
bayan har da had'in bakinta wajen tunzirani dan na cuzgunawa mijina,ashe munafuka
tana can tana had'a min bomb d'in da zai tashi da ni,yanzu a yadda ake Babalalo ya
sauya min baki ga wulak'ancin da yake min ba,kuma yace muddin nayi wani yunk'uri
wallahi saki uku zai min,iyayena kuma sun ce min idan na kashe aurena to baza su
karb'eni ba sai dai na shiga duniya,ni yanzu gabad'aya abin duniya ya isheni
Harira,ina nadamar abubuwan da suka faru a baya,shiyasa nace bari na shigo na
dubaki sannan na baki labarin abubuwan da suke faruwa dani,ya kamata mu gyara
halinmu Harira mu zauna da kowa lafiya dan kyautata rayuwar auren mu,ki duba kiga
yadda Zahra'u da K'asimu rayuwarsu ta canja suna zamansu lafiya,sannan ki juya ki
kalli rayuwar Saratu da Salisu ta dawo suna zaune lafiya suna cin soyayyarsu har
tayi kyan gani cikin kwana biyar,ga Shafa'atu da Kamilu su ma suna d'iga tasu
soyayyar,yanzu ni da ke ya rage Harira,mu ma ya kamata rayuwarmu ta daidaita da
mazajenmu da abokan zamanmu,kiyi hak'uri tunda Amina tana son ku zauna lafiya ki
bata had'in kai ku cigaba da zama,na tabbatar har yanzu Sunusi yana sonki duk da
halayenki marasa kyawu Harira,nima nayi alk'awarin zama da kishiyar da za a kawo
min lafiya in sha Allahu,abin da nake dubawa mutuwa bata sallama Harira,kar muje mu
mutu muna masu sab'awa Allah a lahira mu shiga wuta,ki duba yadda kika tsallake
rijiya da baya,da kin mutu lokacin da kika fad'a rijiya me kika tanada da zaki
fad'awa Allah Harira?ni dai na rok'e ki mu ajiye duk wani iskanci da muke ji da shi
mubi hanyar Allah muyi bautar aure"
Sai da Habiba ta kammala jawabinta tsaf sannan Harira tayi kabbara kamar gaske.
"Allahu Akbar! me karatu na gaba,Habiba kenan,ke yanzu kina nufin duk wad'anda suka
cuceni in k'yalesu kenan ba tare da na d'auki fansa ba?"
Habiba ta girgiza kai ta ce.
"Harira babu wanda ya cutar da ke,kece kika cuci kanki da kanki,kuma ina mai baki
shawarar ki ajiye makamanki ki fuskanci rayuwa ta zahiri tun lokaci bai k'ure miki
ba"
Harira tayi shewa,Habiba ta bita da kallo.Sai da ta gama shewarta sannan ta dubi
Habiba tana tamke fuska ta ce.
"Billahillazi Habiba ko zan shiryu sai na d'auki fansa akan mutane guda biyu,kinga
Amina ko,yadda ta azabtar da ni cikin ruwa ni kuma sai na azbtar da ita cikin
wuta,daman kuma ita ce sanadiyyar rasa hak'orana,to yadda ta rabani da hak'orana na
rantse da Allah sai na rabata da kunnuwanta domin sai na cizge su,duk da dai bayan
an ciro ni daga rijiya na dawo hayyacina tazo har gabana ta tsuguna tana kuka ta
bani hak'uri,na nuna mata kamar na hak'ura amma abinda bata sani ba shine na
k'ullace ta a raina,kuma sai na d'auki fansa babu ragayya" Ta sauke numfashi yayin
da ta dasa aya akan maganar,ita dai Habiba kallonta kawai take,Harira ta gyara zama
ta cigaba da magana.
"Sai mutum na biyu wato wancan matsiyacin takurarren mutumin,Idrees yake ko wa?
shima har yanzu yana nan a raina yadda ya sabauta ni ni ma sai na sabautashi daga
shi har tsinanniyar matarsa,alk'awari nayi kafin su bar layin nan kuma sai na cika
aikina"
"To ai kuwa kin makara Harira"cewar Habiba kenan kafin ta cigaba da cewa.
"Yau kwana biyu kenan da tashin Idrees da Hauwa daga layin nan,kuma babu wanda ya
san unguwar da suka koma,dan kuwa ko sallama baiyi da mak'ota ba wayar gari akayi
aka ga sun tashi basa nan"
Harira ta zabura tana fad'in " Kan ubancan ! wai da gaske kike Habiba ko dai wasa
kike?"
Habiba ta ce.
"Wallahi da gaske nake miki,ke bama Idrees da matarsa ba hatta Malam Arabi da bai
jima da dawowa layin ba to shima jiya jiyan nan ya tashi ya bar unguwar,dan shi a
yadda naji ma wai k'auyensu ya koma,kin san yayi abin kunya ashe y'ammata yake
latsewa a makarantar daren da yake koyarwa,shine aka ganeshi malamai suka yi masa
fata fata da korar kare,duk unguwa ta d'auka ba damar ya fita sai yaran unguwa su
dinga yi masa d'an kira suna tsokanarsa,nadama ta isheshi ya rasa yadda zai yi,ba
shiri shima jiya suka had'a komatsen su shi da matarsa Angayu suka arce daga
BAHAGON LAYIN nan zuwa k'auyen su"
Bala'in takaici ne ya cika zuciyar Harira,bata damu da tashin Malam Arabi daga
layin ba domin bata da case da shi,amma tabbas tashin su Idrees ya mugun tsaya mata
a zuciya,matuk'a gaya taci burin d'aukar fansa,amma in dai ba bangon duniya suka
tafi ba tana ji a ranta koma me zai faru sai ta nemo in da suke dan gabatar da
k'udurin zuciyarta.
Duk yadda Habiba ke bata baki Harira k'in ji tayi,mahaukaciyar k'wak'walwarta da
muguwar zuciyarta suna ta kitsa mata sharri,har dai Habiba ta gaji tayi fushi tace
ta k'yaleta taje ta aikata duk abin da tayi niyya,tunda dai ta fita hakkinta ta
gaya mata gaskiya amma tak'i d'auka,ta tashi tayi tafiyarta ta bar Harira na k'ulle
k'ullen sharri a zuciyarta.
************
Kwanaki suka shud'e abubuwa da yawa sun faru,ciki kuwa har da k'arin auren da
Babalalo yayi,amma bai had'a su gida d'aya da Habiba ba,sai ya ware wa Amarya Abida
gidanta daban suke shan sharafin soyayyah,yayin da Habiba tayi nadama sosai akan
rayuwar da tayi a baya,ta nemi afuwar Babalalo shi kuma bai yi k'asa a gwiwa ba
wajen yafe mata ,ganin tayi nadama da gaske,suka cigaba da zamansu lafiya da
kwanciyar hankali,idan yayi kwana biyu a gidan Habiba sai yaje gidan Amarya yayi
kwana biyu.
B'angaren Saratu( Baba lamindeπ) da nata gwarzon wato Salisu (d'an lukuti
π) ,suma suna zaune lafiya ana cin soyayyah da tsinke,tuni Saratu ta murmure ta
soma mulka k'iba ita ma,har Salisu na tsokanarta da y'ar lukuta ta d'an lukuti
π
,Zaman su gwanin sha'awa babu raini sai girmama juna,tuni ya ajiye zancen k'arin
auren da zaiyi a gefe ganin babu abin da ya nema ya rasa gurin Saratu,tana masa
ladabi da biyayya dai dai gwargwado.
Shafa'atu ma zaman lafiya ne ya cigaba da wanzuwa a tsakanin ta da mijinta Kamilu
da babyn da ta haifa,tuni kuma ta fita daga harkar Harira ita ma,musamman da ta
ankara da cewar ba son gaskiya Harirar ke mata ba,tunda taso kasheta da turaren
Barkono a yayin da take cikin halin nak'uda,tuni Harira ta fice mata daga rai,ta
mayar da hankalinta wajen biyayyar aure da rainon babyn da ta haifa.
Zahra'u kuwa ko a can baya mace ce me kyautatawa miji,domin bata raina K'asimu ba,a
yanzun ma ta saka d'amba da sake d'amarar kyautata masa da rainon babyn da ta haifa
ita ma,zaman su lafiya da kwanciyar hankali babu hargowa.
Idrees da Malam Arabi kuwa tun da suka arce daga BAHAGON LAYI babu wanda ya sake
jin d'uriyar su π.
**************
Harira zaune a d'akinta taji sallamar Amina ta shigo,ta amsa tana gyara zama,Amina
ta k'araso tana fad'in.
"Sannu da hutawa Yaya Harira"
Harira ta amsa fuska cike da fara'a kamar gaske,Amina ta cigaba da cewa.
"Akwai aikin da zan yi miki ne yanzu?
Girgiza kai Harira tayi ta ce.
"Ah ah babu abin da zakiyi min"
"To bari naje na d'an kwanta kafin azahar tayi,jikina ke min ciwo nasan idan na
samu hutu zai warware" cewar Amina kenan yayin da ta nufi k'ofar fita dan tafiya
d'akinta.
Tana fita Harira ta kwashe da dariyar mugunta tana fad'in " zaki huta a k'iyama kam
dan yau sai naga bayanki matsiyaciya,kin d'auka washe miki bakin da nake yi da
gaske sonki nake ko?to ai duk duniya bani da mak'iyiyar da ta kai ki,shegiya y'ar
iska ,lukutar banza sukutar wofi".
Sai da ta bari Amina tayi minti arba'in da fita sannan ta mik'e,janyo galan d'in
man k'uli tayi da kasko ta fito tsakargida ta nufi d'akin girki,har a ktcheen d'in
tana jiyo munsharin da Amina ke saki alamar ta samu bacci mai nauyi,hakan yasa tayi
dariyar mugunta,tana hango yadda zata toya hallitar Amina da man k'uli soyayye.
Wuta ta had'a ta d'ora man,har da yanka albasa a ciki kamar wadda zata toya man da
za a ci wake da shinkafa,tana tsaye har man yayi toyu albasar tayi jajir da
ita,saukewa tayi a hankali sannan ta fito daga ktcheen d'in ta nufi tagar d'akin
Amina da ke tsakar gidan,a hankali ta lek'a tagar sai ta hango Aminar tayi shirim a
gado sai kwasar bacci da munshari take duk ta cika gadon,Harira tayi murmushin
mugunta a zuciyarta ta ce.
"Bak'ar arniya ji be ta kamar an kayar da wani bijimin sa,wannan baccin sai da ki
farka ki ganki cikin k'abari,kuma in sha Allahu idan walakiri ya zo miki sai ya
fara gaggab'e miki hak'ora kamar yadda kika gaggab'e min"
Koma wa ktcheen d'in tayi ta sa tsumma ta d'auko uban man k'ulin da ta soya wanda
yafi kwalba uku,dan so take tayi wa Amina wanka da shi tun daga guntun kanta zuwa
gundumemiyar gangar jikinta har k'afafuwanta,yadda tayi balance a gado tana zuwa
shek'a mata kawai zata yi.
A hankali take tako wa har ta fito daga ktcheen d'in,wata k'usa da ke gefen ktcheen
d'in ce ta ja hannun rigar Harira,bata yi aune ba kawai sai ji tayi kamar an
fincikota tayo baya ta zame,kan ta ankara tayi k'asa gabad'aya toyayyen man da ke
hannunta ya shek'o mata a ilahirin jikinta π³ ,wani irin masifaffen ihun azaba da
Harira ta saki sai da karad'e ilahirin unguwar ma ba layin ba.
A gigice Amina ta farka tana dirowa daga gado tayo hanyar waje a firgice saboda ba
k'aramar razana tayi ba jin ihun Harira da ya farkar da ita,tana fito wa tayi arba
da Harira tana wata irin birgima cikin fitar hayyaci fatar jikin ta na
salub'ewa,Amina ta d'ora hannu a ka ta zunduma ihun neman taimako,yayin da tayi
waje a gigice kanta ko d'ankwali babu tana ihun a zo a taimaka musu.
Kafin ka ce me gidan ya cika tab da mutane ma masaka tsinke,har Sunusi an masa waya
ya tawo da hanzari,babu kuma wanda zai iya tab'a jikin Harira saboda jagwalewar da
yayi sakamakon birgimar da take yi,gabad'aya ko ina na jikinta ya soye da man
k'uli,tun tana ihun azaba har ta sume a wajen.
Tilas motar asibiti aka kirawo ta kwashi Harira aka nufi asibiti da ita,duk
k'ek'ashewar zuciyarka idan ka dubi Harira sai ka ji tausayinta saboda ta soyu ba
da wasa ba,k'awayenta na BAHAGON LAYI kuka suka dinga yi da hawayen su saboda
tausayin ibtila'in da afkawa Harirar.
Kimanin sati biyu da k'onewarta amma jiki yak'i dad'i,kullum k'una k'ara jagwalewa
take,idan ana mata dreesing kaf asibitin cika shi da ihu da kururuwa take dan
azaba,babu mai iya dosarta saboda tsananin d'oyin da jikinta yake yi,tabbas Harira
a wannan lokaci taga azabar duniya,shiyasa idan zaka gina ramin mugunta ka gina shi
kad'an,domin idan baka yi wasa ba kai za ka afka a cikin sa.
Ranar da jikin Harirar yak'i dad'i da bakinta ta dinga rok'on Sunusi akan ya kirawo
mata dukkan k'awayen ta na BAHAGON LAYI,ba tare da b'ata lokaci ba dukkan su suka
hallara har da mazajen su,Zahra'u da K'asimu,Habiba da Babalalo,Saratu da
Salisu,Shafa'atu da Kamilu,sai Mijinta Sunusi da kishiyarta
Amina,cikin jin jiki Harira ke kuka tana neman afuwar kowa,a lokacin ne kuma ta
fallasa kanta ta gaya musu cewar reshe ne ya juye da mujiya,domin Amina ta so ta
k'ona sai sharrin ya dawo kanta,shi daman sharri kuma d'an aike ne,wataran kanka
zai dawo.
Ba k'aramin mamaki dukkansu suka yi ba,Harira ta dinga wani irin kuka tana neman
afuwa,nan kowa yace ya yafe mata ko dan ta samu sassauci,tun a duniya ma kenan tana
shan wannan bak'ar azabar ina ga an je lahira? Allah kayi mana kyakkyawan k'arshe!
π
Bayan sun tafi likitoci suka shigo domin yi mata dressing,ana cikin yi mata tana
wannan ihun da zabure zabure Allah ya karb'i ranta,Harira ta mutu cikin wani irin
yanayi mara dad'i,Allah kasa mu cika da kyau da imani πAllah ka tsarkake mana
zukatanmu ka k'ara mana imani da biyayya a gareka ya Allah! π
Mutuwar Harira ta girgiza mutane da dama,duk da halayenta marasa kyau sai dai anyi
kukan sabo,kuma an yi mata addu'a sosai,ana mata fatan samun rahamar Allah tunda ta
nemi afuwar wad'anda ta zalinta kuma sun yafe mata,kuma mijinta ma ya yafe
mata,tsakanin bawa da ubangijinsa kuma ba a shiga.
Rayuwa ta cigaba da tafiya tana mik'awa,mutuwar Harira ta k'ara nutsar da zukatan
k'awayen ta,suka k'ara laushi da mik'a wuya zuwa ga Allah.
*K'ARSHE*....!
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!
INA GODIYA GAREKA SARKI ALLAH,ALLAH KA K'ARA TSIRA DA AMINCI GA SHUGABANMU ANNABI
MUHAMMAD (S A W) DA ALAYENSA DA SAHABBANSA. NA GODEWA ALLAH DA YA BANI LAFIYA DA
DAMAR KAMMALA WANNAN LITTAFI,GODIYA GAREKU MASOYA MASU BIBIYATA TARE DA FATAN
ALKAIRI,NAGODE SOSAI HASSANA D'AN LARABAWA TAKU CEπSAI KUMA MUN HAD'E A SABON
LITTAFINA MAI CIKE DA WANI IRIN DARASI DA RAYUWA TA ZAHIRI MAI TSAYAWA A
ZUCIYA,KAMAR KULLUM SHI MA SALON SA NA DABAN NE, *(HAYATUL K'ADRI)* YA ZO DA WANI
IRIN SALO DA RAYUWAR DA IDAN AKA BIBIYE SHI TABBAS ZA A K'ARU FIYE DA K'ARUWAR DA
AKA YI A BAYA,SHIN MASOYA KUN SHIRYA KUWA...?
IDAN KUN SHIRYA TO NIMA NA SHIRYA,KUYI HIMMA KU BIBIYENI NI HASSANA D'AN LARABAWA
DA YARDAR ALLAH π
NAGODE! πππ
BY HASSANA D'AN LARABAWA βοΈ