Author : TARE DA ALK'ALAMIN Category : Complete Novels
ko zai ga wani abun amma
bai ga komai ba,juyowa yayi ya dawo cikin gidan yana sauke numfashi,yana shigowa ya
jiyo muryar An gayu daga band'aki tana k'wala masa kira.
"Malam...Malam kawo min ruwa a buta zan yi tsarki"
Tsaki ya ja sannan cikin fad'a ya d'aga murya ya ce.
"Wai ke baki san babu kyau magana a bayan gida ba?idan mutanen na mu suka wurgoki
waje ke kika sani babu ruwana,kuma dan wulak'anci ma me ya sa zaki shiga bayan gida
babu ruwa?"
Yana jiyo muryar An gayu tana ce wa.
"Yo Malam baka ga yadda na shigo gidan a (tiri sittin ba) baka san bala'in da ya
koroni ba ne,ni ka mik'o min ruwa in yi tsarki ko kuma na fito a haka kayi min
tsarkin da kanka"
Wata muguwar harara Malam Arabi ya bankawa k'ofar band'akin,ya nufi in da buta take
ya zuba ruwa sai sababi yake.
"Allah ya tsareni da wanke miki gayad'i An gayu,na jikina ma dan ya zame min dole
ne na wanke shiyasa"
A haka ya d'auki butar yaje ya kai mata ya d'an bud'e k'ofar ya zura mata butar
yana toshe hanci saboda warin da ya bugo shi.
Can jimawa An gayu ta fito tana sauke wahalallen numfashi,Malam Arabi da ke tsaye
ya dubeta cike da takaici,musamman da yaji ta ce masa.
"Malam ashe kashi bala'i ne,aradu shingin kad'an nayi a buje na"
Hararta yayi ya ce.
"Tsakani da Allah An gayu kin firgitani,kina matar Malam ki shigo gida da gudu babu
sallama?me ya firgitaki haka daga shigarki mak'ota ki fito? Allah yasa dai baki yi
musu halin ki na tusa ba,domin ke dai mazaunanki ba iya rik'e rihi suke ba,ga
maganin basir nan na jik'a nayi nayi da ke ki d'auka ki sha amma kin k'i,wani
lokacin takaicin ki kamar ya sakani kuka wallahi,ke ki d'ura min takaici a
makaranta ma ban tsira ba,shakiyyan d'alibai sai tsula iskanci suke,duk wadda tayi
laifi da an doketa sai ta fad'i tana shure shure wai aljanu,to duk za su ci ubansu
ga sabuwar bulala nan na siyo na shafeta da manja,babu munafukar yarinyar da zan
saurarawa,duk wadda ta kuma yi mana aljanu jikinta zan tsamama mata"
An gayu ta nemi waje ta zauna tana zare idanu,sannan ta ce wa Malam Arabi "
Hmmmm ! mai gida yau ni naga abinda ya isheni,daman akwai maza ma masu aljanu ne?
gidan da na shiga fa ina jin mai gidan Aljanu ne da shi,kaga yadda ya dinga
zambarwa yana zare min idanu kamar tsohon kwarto kuwa?shine fa ya hautsina min ciki
da ihunsa har ban san lokacin da na tako a guje ina sakin tusa ba,kai Allah buwayi
gagara misali ban tab'a ganin tijararren mutum irin wannan mutumi ba,matsiyaci
fuska duk jijiyoyi,Allah ya isa tsakanina da shi gantalalle mara mutunci,domin ba
k'aramin d'aukar hakkina yayi ba"
Malam Arabi ya matso ya zauna kusa da An gayu cikin mamaki ya ke fad'in.
"Wai wanene haka?me ya faru ne?"
An gayu ta kaikaice ta fara bashi labarin abin da ya faru,sai ga Malam Arabi na
muguwar dariya har da rik'e ciki,fad'i ya ke.
"Maganinki kenan uwar gantali da cusa kai....!
Comments
Share
Vote
Pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*BABI NA ASHIRIN DA D'AYA DA NA ASHIRIN DA BIYU*
PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️
*SAK'ON FATAN ALKAIRI DA BANGAJIYA GA MARUBUTAN DA SUKA HALARCI TARON MARUBUTA NA
(BAKANDAMIYA)ALLAH YA CIGABA DA BAWA MARUBUTA NASARA,ALLAH YA K'ARA MUSU BASIRA DA
HAZAK'AR KAWO LABARAI WAD'ANDA ZA A K'ARU DA SU,ALLAH YA NUNA MANA WATA SHEKARAR DA
RAI DA LAFIYA* 🥰👏
***Washe gari misalin k'arfe tara na safe,Habiba Zaune a tsakar gida kan
tabarma sai hamma take,kana ganinta kasan yunwa take ji,Babalalo ne ya shigo da
bak'ar leda a hannunsa yana sallama,da sauri ta amsa tana kallon ledar hannunsa sai
tand'ar baki take tana zare ido,mik'a mata ledar yayi sannan ya shige cikin falo
kai tsaye,da sauri ta karb'a jikinta na rawa,yunwa take ji sosai gashi ranar basu
tashi da komai ba da za ta dafa,shiyasa tace Babalalo ya taimaka ya siyo mata shayi
can k'asan layin su,mik'ewa tayi ta nufi ktcheen d'in ta ta d'auko k'atuwar mod'a
da zata juye shayin,sai faranti da ta d'auko a zatonta cikin ledar har da
indomie,dan kuwa kafin ya fita tana ta had'ashi da Allah akan ya siyo mata indomie
marmarinta take.
Sai da ta dawo ta hakimce kan tabarma jikinta har rawa yake,burinta taji
indomie ta baje a bakinta,yayin da zata kora da shayi had'in kauri,tana bud'e ledar
ta ci karo da farar leda da aka d'aure Koko a ciki,sai wata takarda da ta warware
taga K'osai mai zafi a ciki yayi jajur da shi,wani bak'inciki ne ya daki zuciyarta
take ta b'ata fuska,babu abinda ta tsana irin Koko,amma shine Babalalo dan
wulak'anci ya siyo mata shi,d'aukar ledar tayi ta juye kokon a mod'ar da ta
d'akko,sannan ta figi mod'ar ta fad'a cikin falon tana buntsura baki da hura hanci.
Babalalo ta tarar ya jona k'arfen guga yana goge kayansa da zai saka ya
fita,taji kamar ta juye masa Kokon a gadon bayansa,daurewa tayi cikin nunk'ufurci
tayi magana tana rik'e k'ugu da hannu d'aya.
"Gaskiya ni Babalalo ka gama da ni,sai da ka bari na gama sa rai zanci indomie
kawai sai ka had'ani da koko?"
Ya cigaba da gugar sa ko kallonta baiyi ba,sai dai ya bata amsa da cewa.
"Gani nayi kinfi dacewa da Kokon shiyasa na had'aki da shi"
Ranta ya b'aci da jin maganarsa,cikin hargowa ta ce.
"Wallahi kaima kasan k'arya ka fad'a,ko a gidan ubana shayi nake sha ba Koko ba"
Tana direwa ya amsa da ce wa.
"To yanzu ai ba a gidan ubanki kike ba,gidan aure kike,kuma dole kiyi hak'uri da
abinda ya samu,sannan ina umartarki da ki kauce a kaina idan ba haka ba na juyo
billahillazi sai na b'arar da ke"
Habiba ta harari k'eyarsa ta kauce da sauri,dan ta san idan tijararsa ta motsa
wulak'ancinsa yawa ne da shi,fita tayi daga falon da Kokon a hannunta,ban da yunwar
da take ji sosai babu yadda za a yi tasha wannan Kokon,dan dai bata da ko kobo ne
da shayi za ta siyo da kanta,har gara a bata kunu da a bata Koko,kunu kam da kanta
ma tana damawa amma ta tsani Koko,zama tayi ta fara kurb'ar Kokon tana had'awa da
k'osan.
Can ta jiyo muryar Babalalo yana tsaki da sakin maganganu,ta kasa kunne sai
taji yana fad'in.
"In dai Koko ne kin had'u da shi,ni zaki kawowa tantiranci wai bakya shan Koko,ni
yanzu ma tunda na samu a layin nan ana siyarwa ai na huta da siyan gero ko siyo
shayi,Kokon naira ashirin k'osan talatin ya isa in siyo miki ki karya da shi"
Habiba tayi shiru ranta duk a b'ace,tunani take wane gida ne a layin ake sayar
da Koko?sai can ta tuna da matar malam Arabi wato An gayu,dire mod'ar Kokon tayi da
hanzari ta mik'e ta fad'a falon a gigice,Zabura Babalalo yayi yana cillar da dutsen
gugar saboda yadda ta dira a gabansa ta tsorata shi,
"Ke lafiya?wannan wane irin wulak'anci ne zaki tsoratani?da kin sa na k'one fa?"
inji Babalalo.
Cikin zare ido Habiba take tambayar sa.
"Don Allah a ina ka siyo wannan Kokon da K'osai?"
Tsaki yayi yana d'aga dutsen da ya wurgar,sannan ya ce mata.
"Daman abinda za ki ce min kenan kika firgitani?ke dai naga randa za ki yi hankali
Habiba, to nan mak'ota ne da suka tare matar malam Arabi ke siyarwa"
Wani bala'in tashin hankali ne ya ruftowa Habiba,take idanuwanta suka hasko mata
curarren tasonon da ke hancin An gayu da koriyar majina shar,wani azababben amai ne
ya yunk'uro mata ta dafe kai,take ta fara shek'a shi a kan gogaggun kayan da
Babalalo ya goge zai saka domin ya fita.
Tsalle Babalalo yayi gefe guda yana dafe kai cikin matuk'ar takaici yasa k'afa
ya haure Habiba da ke shek'a amai ya gara kanta da garu,cikin bala'in b'acin rai ya
ke sababi.
"Kan uban can kayyasa! idan ba sai kin wanke min kayana ba shege uwata ta
haifeni,in wanke kayan in goge amma kiyi min amai akai dan wulak'anci?kin tashi ko
sai na saka k'afa nayi ball da ke?"
Habiba da k'yar ta mik'e jikinta na rawa sosai,ta kwashi kayan ta fice har lokacin
zuciyarta tashi take yi,Babalalo ya bita tsakar gidan ya saka ta a gaba sai tijara
yake mata har ta wanke masa kayansa fes yana tsaye a kanta.
************
A gefe guda kam Harira cike take da takaicin abin da Sunusi yayi mata,kuma a
ranta ta d'au alwashin bashi ya d'auka domin sai ta fanshe,tunda sanin kansa ne
ba'a tab'a ta ta k'yale,babu abin da ke d'aga mata hankali irin yadda kowa idan ya
tashi dukanta bakinta yake hari,an maida bakinta wajen gwada k'wanji,ko wane shege
da me lukutin hannu da me siririn hannu duk k'ashi da sun d'aga hannu su sauke mata
shi a dadashinta,aikuwa ta daina ragawa kowa,duk d'an iskan da yayi mata sai ta
rama.
Tana zaune tana wannan tunane -tunanen har ta hango hanyar ramuwa,murmushi ya
sub'uce mata,ta k'ara gyara zama tana janyo wata leda mai cike da kayan miya da
Innan Sunusi ta harhad'o mata,kayan kad'i ne irin su Kuka da kub'ewa har da su
waken miya da gyad'ar miya,tana cikin lalubawa ta ci karo da abin da take son gani
wato (Kalkashi) .
Tun a lokacin ta fara dariya saboda ta san muguntar da zata had'awa Sunusi zai
ji jiki,ta san ba zai jima ba zai shigo,kofi ta d'auko ta jik'a wannan kalkashi me
mugun yauk'i,tsayawa tayi a bakin tagar k'aramin d'akinta tana lek'a tsakar
gidan,tana kallo Amina ta fito daga d'akinta da d'aurin zani a k'irjinta,ga kuma
bokiti da kwandon wanka da alamun band'aki zata shiga tayi wanka,akan idanunta
Amina ta bud'e rijiya ta saka guga ta janyo ruwa ta cika bokitin taf,sannan ta
d'auki ruwan ta shige band'aki domin yin wanka.
Amina bata jima da fara wanka sosai ba Harira tana nan tsaye ta jiyo muryar
Sunusi daga soro kamar yana waya,da wani irin sauri ta fito domin aiwatar da
nufinta dan kar ta rasa damar,k'ofar d'akin Amina taje ta juye wannan ruwan
Kalkashi me mugun yauk'i,ta sa tsintsiya ta damalmala wajen,motsin Sunusi yasa tayi
hanzarin komawa d'akinta tana k'unshe dariya,saboda ta san babu inda Sunusin zai
nufa idan ya shigo sai d'akin Amina.
Sunusi kam bayan ya gama wayarsa sai ya fad'o tsakar gidan da sallamar sa,cikin
farinciki kuma ya nufi k'ofar d'akin Amina yana runtse idanuwan sa wai shi bai
yarda ba lumshe ido yake🤣 Cikin jin shauk'in soyayya kuma ya d'aga murya ya fara
rairowa Amina wani baitin wak'a da Umar m sharif yayi.
*Ina kike masoyiya?*
*Na duba gabas ban ganki ba*
*Na duba arewa ban ganki ba*
*Na duba kudu ban ganki ba*
*Na duba yamma ban ganki ba*
Sai kuma ya juya kan wak'ar Nazifi asnanic cikin wak'ar sa ta.
*Amina Amina y'ar auta Amina tauraruwar mata*
Yana yi yana tafiya a hankali idanuwa a runtse da nufin Aminar ta fito ta
tarbeshi,ko domin tayi masa masauki a lafcecen k'irjinta mai cike da abubuwa,Ita
kanta Aminar jin muryarsa yana rairo mata baitoci tuni shauk'i ya kamata,nan da nan
ta zundumi ragowar ruwan bokitin ta shek'a a jikinta ta figi zani ta d'aura da
nufin fitowa domin tarbar mai gida Sunusi.
Shi kam Sunusi Angon Amina baiyi aune ba idanuwa a rufe kansa tsaye ya tunkari
k'ofar d'akin Amina,shi dai da wani mugun santsi ya kwashe shi sai ji yayi kamar an
d'aga shi sama an nunawa Allah shi an fyad'a shi da k'asa,wani gigitaccen ihu ya
saki domin ba k'arya dandamalin k'eyarsa ya bugu ainun,ihunsa ne ya saka Amina
cillar da bokitin hannunta ta fito da gudu daga band'aki a gigice tana sab'ar
sab'ar daga ita sai d'aurin k'irji,ganin Sunusi yayi balance a k'asa bata san
lokacin da ta kwaso sauri ba hankali a tashe,dab da zata iso gareshi domin ta d'aga
shi ita ma santsi ya kwashe ta,kamar wadda akayi wurgi da ita sai gata akan ruwan
cikin Sunusi rigijib,Sunusi ya k'walla wata razananniyar k'ara yana jin kamar zai
kasayar da kayan da ke cikinsa,zaman y'an borin da Amina tayi akan cikin Sunusi sai
ta kasa mik'ewa jikinta yayi mata nauyi,shi kuma Sunusi ya kasa ture ta sai ihu
yake yana fad'in a taimake shi gingimari ta danne masa ciki😂,haka Amina ta dinga
k'ok'arin zamewa daga kan ruwan cikin Sunusi da k'yar,ta dinga turo mazaunanta
saitin fuskarsa tana niyyar mik'ewa,da dai azaba ta ishi Sunusi yaji kamar zai mutu
ai sai ya samu tsakiyar d'uwainiyar Amina ya kafa kaifafan hak'oransa ya dinga
cizgo tsokar wajen,Amina taji sukutar azaba ba shiri tayi wani zillo ta fad'o k'asa
timmmm ta wargaje har zaninta na kwancewa 😂Shi kam Sunusi numfashin azaba da
wahala kawai yake saukewa yana jin kamar k'eyarsa ba a jikinsa take ba,ga cikinsa
na kartawa dalilin ziyarar da ya samu na d'uwaiwukan Amina😂 .
Gogar ta ku Harira kuwa na lab'e jikin tagar d'akin ta tana kwasar dariya kamar
wata zararriya🤣🤣🤣.
Comments
Share
Vote
pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*BABI NA ASHIRIN DA UKU DA NA ASHIRIN DA HUD'U*
PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️
*WANNAN FEJI SADAUKARWA NE GA MALAM ARABI NA ANGAYU😂DON ALLAH KAR KUYI MASA DARIYA
SOSAI🤣NIMA KAD'AN NAYI* 🤭
***Sai da aka d'auki tsawon lokaci kafin Sunusi ya dawo dai dai,kwata-kwata kuma
kunnensa bai jiyo masa dariyar da Harira ke shek'awa ba,amma ita Amina tana jiyo
Harira,hakan yasa ta gane duk abin da ya faru to da saka hannun Hariran a
ciki,gyad'a kai kawai tayi tana ji a zuciyarta bankin da take tara Harira a ciki ya
kusa cika,duk ranar da ya cika kuwa to tabbas Harira zata ga rayuwa,domin dai sai
tayi dana sanin zuwa duniya.
Bayan Sunusi ya gama mayar da numfashin wahala sai yake tambayar Amina
dalilin santsin da ya kwasheshi,nan Amina ta shiga bashi hak'uri ta d'auki laifin
ta d'orawa kanta,tace masa ta d'auko ledar kayan kad'in da inna ta bata ne shine
kalkashi ya zube,to kuma ta wanke gurin ashe bata sani ba bai fita ba,har ya zo ya
taka ya zame ya fad'i,nan ta shiga bashi hak'uri tana karkashe idanu,sai ga Sunusi
ya rud'e jikinsa ya fara mazari,musamman da Aminar ta janyo shi jikinta ta kai
hannu kan k'eyarsa da ta lunkuma tana mulmulawa,sosai k'eyar ta kumbura tayi
zungureriya da ita,haka Amina ta dinga mulmulawa tana masa sannu,Sunusi ya kai
siririn hannunsa kan murguza murguzan mazaunan Amina yana lailayawa da fad'in.
"Ni ma kiyi hak'uri Aminata,azaba ce ta isheni har ban san lokacin da hak'orana
suka kaiwa d'uwainiyarki ziyara ba"
Murmushi Amina tayi ,ta mik'e tsaye da k'yar.Sannan ta taimakawa Sunusi ma ya
mik'e,ta rungumeshi a gefen jikinta tana fad'in.
"Ai ni baka laifi a wajena mijina,muje d'aki ma in tausa maka jikinka tare da
mulmule maka k'eyar nan ko kumburin zai sace"
Dad'i ya ishi Sunusi,nan da nan ya sake lafewa a hammatar Amina kamar wani
tsuntsu,suka shige cikin d'aki suka bar Harira tsaye a bakin taga sakato da baki
tana bin su da kallo.
Wato hak'anta bai cimma ruwa ba kenan?ita da taso Sunusi ya fusata ya lodi Amina ko
ya zazzage ta,shine suka tura mata aniyarta suka b'ige da soyayya?lallaikam sun
d'au bashi,domin in dai tana da rai da lafiya ba zata bari su sakata su wala
ba,tana ji a ranta duk wani hali na matsi da ta shiga Amina ce sanadiyya,haka nan
ita ce sanadiyyar rasa hak'oranta take zaune da wawulo,wawulon da yake ja mata
raini gun Sunusi,dan ko yau da safe da zai fita da ta biyo shi tana tambayarsa
kud'in cefane kau da kai yayi,har da yi mata gargad'in in zata yi masa magana ta
daina kallonsa,domin wawulon bakinta na firgitashi yana jin kamar zata had'iye
shi,ire-iren wad'annan abubuwan suke k'ara bak'anta ranta,kuma ta d'auki alwashin
ko zata yi yawo tsirara sai ta san yadda ta kori Amina daga wannan gidan.
*Tofah! lallai Hajiya Harira kin d'ebo ta da zafi* 😳😂
************
"Don Allah da gaske kake?"
Zahra'u ta fad'a tana kallon fuskar K'asimu cike da mamaki,Yayi Murmushi da
fad'in.
"Wallahi kuwa da gaske fa,d'azun nan Salisun ya kirani a waya yake fad'a min wai an
dai dai ta komai Saratu za ta koma d'akin ta"
Zahra'u ta sauke numfashi ta ce.
"Amma dai ba'a bahagon layi za su sake zama ba ko?"
K'asimu ya d'an sosa kunnensa da ke masa k'aik'ayi ya ce.
"Kamar kin sani kuwa tambayar da na fara yi masa kenan,sai yace min wai ya yanke
shawarar su cigaba da zama a BAHAGON LAYIN,ta haka ne kawai zai gane idan Saratun
tuban gaskiya tayi ko na k'arya"
Zahra'u ta ce,
"Tabbas kuwa yayi gaskiya,to Allah dai ya tak'aita,dan wannan layin ya zama bom,ni
dai Allah ya taimakeni da na bar cikinsa na samu ingatacciyar rayuwa"
K'asimu yayi dariya yana rik'e hannunta sannan ya ce.
"Wai ni kuwa kina ta cewa zaki bani labarin abin da ya faru ranar da kika je kitso
amma ban samu zama ba,me yafaru ne kika dawo ba tare da an miki kitson ba?"
Zahrau tayi ajiyar zuciya tana kyab'e baki ta ce.
"Hmmmm ! Ranar nan naga tijara da d'umamar yanayi,wai duk wani gidan kitso daman
haka yake tattara y'an iskan mata magulmata?ni tun da uwata ta haifeni ban tab'a
ganin inda aka yi brush da damammen kashin awaki da gishiri ba sai a GIDAN KITSO".
K'asimu ya zaro idanuwa yana son jin cikakken bayani,nan Zahra'u ta fayyace masa
komai na abin da idanuwanta suka gane mata,K'asimu ya dinga dariya har idanuwan sa
na hango masa yadda aka turmushe Gimbiya aka yi mata brush da kashin awaki 🤣.
Sai da yayi dariyarsa ta isheshi sosai,sannan ya tsaya yana sauraren bayanin da
Zahra'u ke masa.
"Ni da mai gida shawarar da na yanke,tunda nayi irin wannan zaman mara alfanu da
zubewar mutunci a baya,me zai sa in sake ziyartar wannan gidan kitso domin in
tattara wad'annan matan in basu labarin zaman mu a bahagon layi da abin da ya same
mu daga k'arshe,in yaso in musu nasiha ko zasu fad'aka su gyara suma?saboda ni dai
hankalina ya tashi da abin da na gani wallahi"
K'asimu yayi kasak'e yana jinjina zancen,sai can kuma yayi gyaran murya ya ce.
"To hakan ma wani abu ne me kyau,idan har kaga wani na aikata ba dai dai ba hakki
ne akan ka kayi masa nasiha a matsayinka na d'an uwansa musulmi,to sai dai kuma in
da gizo ke sak'ar su mata fa ba cikakken hankaline da su ba,kar aje garin neman
gira a rasa ido,kinga tsohon ciki ne da ke,ina tsoron kije ki fad'a musu gaskiya ki
musu nasiha a samu kuskuren fahimta su had'u su suburbud'aki,idan ba a gurje miki
baki da kashin awaki ba ai kinga a saki ki haifo abinda ke cikinki ta baki 😂 kinga
me gari ya waya kenan?"an b'ata goma d'aya bata gyaru ba".
Murmushi Zahra'u tayi da fad'in.
"Babu wani abu da