Author : TARE DA ALK'ALAMIN Category : Complete Novels
Inna daman maganarda zanyi ita ce, gaskiya ayi wa wannan dank'areriyar
matar magana kar ta sake ce min Yaya Harira,ta kirani da Harira ta kawai,kalleta fa
shirgegiya kamar buhun kwaki,wani ma ya kalleta sai ya zaci kakar babana ce,ni dai
bana son wata Yaya ta daina gayamin kawai"
Inna tayi murmushi tace.
"Ban da abinki Harira girma fa ta baki a matsayin ki na uwargida,kuma kowa ya
kalleku ai yasan kin girmi Amina,garun jiki ne kawai da Allah ya huwace mata,amma
Amina ai yarinya ce kin fita shekaru nesa ba kusa ba"
Sai lokacin Sunusi yayi magana cikin fushi da b'acin rai ya ce.
"To Inna ba gara ma Aminar ba,ita fa kalleta duk a tsotse uwa Akuyar mayu,ai tafi
ma kama da tsofaffin na rantse da Allah,wani idan ya dubeta ma ba sai ya za ci ta
bawa shekaru sittin baya ba,daman ga bakin duk babu hak'ora"
Amina dai shiru tayi kanta a k'asa,a zuciyarta tana cewa.
"Au Harira bata nutsu ba kenan?lallai kam za ta koya mata hankali ta nutsar da
ita,domin ba zata d'auki renin hankali da iskanci ba,tilas ta mik'e tsaye dan ta
nunawa Harira ita d'in ba kanwar lasa ba ce"
Nan dai Inna ta cigaba da yi musu nasiha,musamman Harira ita aka fi ambata saboda
ita ce mai matsala,daga nan kuma Inna ta taya Harira shigar da kayan ta cikin
akurkin d'akin da aka bata,wanda Harirar ta sha alwashin sai ta san yadda ta fitar
da Amina daga gidan domin ta koma d'akinta na Asali da yardar Allah.....!
Comments
Share
Vote
pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*BABI NA GOMA SHA BIYAR DA NA GOMA SHA SHIDA*
PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️
*AYI DARIYA KAD'AN BA MAI YAWA BA* 😂
***Zahra'u ta shirya tsaf a lokacin da Nana ta shigo domin rakata gidan kitso,suka
fito ta kulle gidan suka tafi tana takawa a hankali Nana tana rik'e da jakarta,suna
tafe suna d'an tab'a hira kad'an kad'an har suka k'arasa,tun daga k'ofar shiga
gidan suke jin hayaniya da tashin muryoyi kamar ana fad'a da kokawa,a haka suka
shiga gidan Nana a gaba Zahra'un K'asimu tana biye da ita a baya har suka shiga
tsakar gidan,sai rafka sallama suke amma babu wanda ya amsa musu,sun tarar da mata
kusan uku a tsaitsaye rik'e da k'ugu sai faman sababi suke, ga kuma Tarasulu me
kitso a gefe ta rik'e hab'a fuskarta cike da damuwa tana sauraran matan da ke tsaye
kowacce ta cakari k'ugu,su Zahra'u suka tsaya cike da mamaki da tsoro suna duban
d'aya daga cikin matan da ta d'aga wata y'ar roba da wani kwab'ab'b'en abu
bak'ik'k'irin a ciki tana nunawa Tarasulu me kitso tana ce wa.
"Na rantse da Allah Tarasulu yau sai munyi maganin Munafuka,daga yau Gimbiya ba
zata sake zuwa gidan nan tayi gulmarmu ba,yau har gidanta zamu dira mu ci ubanta mu
dirje bakin munafuka,kinga wannan abun kashin awaki ne da gishiri muka kwab'a, da
shi za mu je mu dirje bakin munafuka,daga yau idan an ce tazo gidan nan ta k'ara
yin gulmar mu ba zata sake yi ba"
D'ayar tayi shewa ta ce.
"K'warai kuwa Jummai,wallahi yau ko sama da k'asa za ta had'e ba zamu saurarawa
Gimbiya ba,in dai gulma da munafunci ne aikinta to za ta yi ritaya daga yau idan
muka dirje bakinta da kashin awaki,gidan nan ma sai ya gagareta shigowa balle ta zo
tayi gulmar mu"
Tarasulu ta sauke numfashi a tsorace tana d'aga hannuwa tana rok'on su da cewa "Don
girman Allah ku rufa min asiri Jummai,yanzu duk in da akaje cewa za a yi a gidana
aka had'a wannan ruguntsumin,ni kuma ba don kuyi fushi na fad'a muku abin da
Gimbiya ta fad'a a kanku ba,don Allah kar ku tada wata husuma ,kar kuje gidanta
kuyi hak'uri maganar ta mutu anan" ta juya tana duban d'aya matar da ke gefenta ta
rik'o hannunta tana ce wa.
" Saude ki saka baki ki basu hak'uri dan naga Jummai da K'udisiyya sun d'auki zafi
akan lamarin,ta k'ak'a za su ce wai sai sunje sun dirje bakin Gimbiya da kashin
awaki?kuma har gidanta dan neman tashin hankali"
Saude ta fizge hannunta tana sakin tsaki sannan ta ce .
"Ai na su kad'an kika ji,su iya kashin awaki ne kawai makamin su,ni nan da kika
ganni da askata nake tafe,wadda zan wa Gimbiya k'aton bille da ita"
Dafe k'irji Tarasulu tayi cike da zaro idanuwa ta ce "Bille kuma Saude? wane irin
bille kuma?don zatin Allah kuyi hak'uri"
Saude ta ce "k'warai kuwa bille zan taya mata,ba a gabanki ta zo tana cewa wai
billen mahaifina ya zanu ba?daga ganinsa rannan ya zo gidana duba Salim an masa
kaciya tai ta kallon fuskarsa tana dariya,shine dan wulak'anci tazo gidan nan tana
gulma wai da alamun da gatari aka yiwa mahaifina bille saboda ya zanu,to ni kuma
yau za ta gani,dan wallahi bayan su Jummai sun dirje mata baki sai nasa sun danne
min ita na tsaga fuskarta nayi mata bille irin na fuskar uban na wa"
Gabad'ayan su suka kwashe da dariya,yayin da Tarasulu me kitso take basu hak'uri
kamar ta tsuguna musu,amma suka yi banza da ita suka juya a fusace za su fita su
nufi gidan Gimbiya, Zahra'u da Nana suka matsa a tsorace ganin tamkar wad'annan
matan za su bangaje su,yayin da Tarasulu ta bisu tana rik'o su da basu hak'uri su
kam ko sauraranta basu yi ba suka fice ,k'irjin Zahra'u na tsananin bugawa ta dubi
Nana suka had'a ido,a zuciyar ta tana fad'in "Yau na sake shigowa wani cakwalin
bala'in,wai shin kowane gidan kitso sai an samu irin wannan tarangahumar ne?"
****************
A daren ranar da Harira ta dawo Amina da kanta ta umarci Sunusi da ya tafi d'akin
Harirar ya kwana,domin a lissafinta ranar Harirar ce ke da miji,takaici ya ishi
Sunusi kamar yayi kuka,kwata kwata baya son ya matsa daga inda Amina take saboda
tsabar shagwab'ashin da tayi,in dai za su yi bacci sai ta san yadda tayi ta
mammatsa masa jikinsa tayi masa tausa mai kyau saboda ta san aikin da yake yi na
bulo akwai tarin gajiyar da ake kwasa,idan kuma ta kammala tausar haka take
lankafeshi a zundumemen k'irjinta yasha baccinsa har da minshari da yawun bacci,duk
inda ya kai hancinsa jikin Amina sak'o da lungu sai dai ya kwashi k'anshin Humra
y'ar gaske,har cusa kansa yake tsakanin hammatar ta dan ya shak'i k'amshi me tafiya
da hankalinsa,amma hammatar Harira fa?ni da (summun bukumun😂),Iya laushi da
taushin da yake ji a luk'ek'en k'irjin Amina ko katifa albarka,har baya son Asuba
tayi ya mik'e yin sallah saboda ya san lokacin dad'insa ya k'are,birgimar da yake
yi da dadumar abubuwa son ransa yana cika hannunsa da su ya k'are,tilas haka yake
mik'ewa ba don ransa yaso ba,to kuma wai yau d'in Aminar da kanta take umartarsa da
ya tafi wajen Harira su kwana tare,ya san kwanan azaba kawai zaiyi,yadda ya saba da
kwanciya cikin k'amshi ba zai iya kwana cikin d'oyi da samami ba,shi fa ko kallon
fuskar Harira yanzu baya son yi,musamman idan ta wage masa baki da sunan murmushi
sai yaji d'umbun takaici ya kama shi,ba k'aramin muni take a idanuwansa ba dalilin
rashin hak'oran bakinta.
Da yaga ba zai iya yiwa Amina musu ba tilas haka ya hak'ura ya fito daga
d'akinta,amma ya gwammace yayi shimfid'a a tsakar gida ya kwanta da ya shiga d'akin
da Harira take,sai da ya fuskanci Amina ta fara bacci sannan ya lallab'a ya koma ya
d'auko bargo da matashi ya shimfid'a a tsakar gidan daga gefe ya kwanta,ya
cukuikuye a cikin malum malum d'in da ke jikinsa ya lullub'a saboda gudun kar
saurayen da ke tsakar gidan suyi masa illa,bai jima da kwanciya ba kam nan da nan
bacci yayi awon gaba da shi ya fara sauke numfashi.
Ita kam Harira duk abinda yake yi tana sane,bak'inciki duk ya cika ranta ta
kasa bacci,ba k'aramin takura tayi a d'akin ba saboda k'aramine babu fad'i sosai
balle tsawo,ga ta ita masha Allah tana da tsawo kamar samfalwa,ko ya ya ta mik'e
k'afafuwanta sai su tokare babu alawus,ga d'akin duk ramukan kiyashi da cinnaka,ta
kasa bacci amma daga in da take tana jiyo munsharin Amina tun daga d'akinta me kama
da munsharin rago,takaici na k'ara cin zuciyarta tana jajantawa Saratu a
zuciyarta,na tsawon lokacin da ta d'auka tana fama da minsharin da Salisu yake
yi,to wai daman mutum yanayinsa yanayin munsharinsa kenan?idan kai lukuti ne haka
munsharinka ma zai zama d'an lukuti?to amma ya aka yi Sunusi ba shi da k'iba amma
shi ma yake ta kwarara munshari?kuma a lokacin baya baya yi,to ko dai zama da Amina
ne yasa ya koyi munsharin shiyasa yanzu yake ta sakin abinsa?ita ta kasa bacci amma
su sai baccin su suke shak'a sun barta da susar wuya da cinya?tabbas dole ta d'auki
matakin farko ba zaiyiwu su suna sharar bacci ita tana cikin wahala da azaba
ba,tilas ta d'an sammusu yanayin da take ciki ko suma sa d'and'ana.
Zumbur ta mik'e ta k'aro hasken fitilar da ke gefenta tana dariyar mugunta,a
hankali ta tashi tsaye ta nufi kwandon wanke wankenta da ke gefenta,ludayi ta zura
hannu ta d'akko sannan ta nufi gefe in da ramukan cinnaku da kiyasai suke,babu
tsoro haka tasa hannu tana tsintar cinnakun tana zubawa cikin ludayin da sauri
sauri,sai da ta zuba kusan guda goma sha biyu sannan ta mik'e tana salallab'awa ta
fito daga d'akin,wani farinciki ya tsirga mata da ta hangi k'ofar falon Amina a
bud'e,tsallake Sunusi tayi ta nufi d'akin Aminar ta d'aga labulen ta shiga cikin
d'auke numfashi da tafiya a hankali dan kar ta farka,saboda k'arfin hali irin na
Harira har k'uryar d'aki ta shiga da ludayinta a hannu cinnaku fal a ciki,nan ta
tarar da Amina tayi him a gado sai kwasar bacci take duk ta cika gadon, Harira ta
k'unshe dariya a zuciyar ta tace"Wannan matar da saniya ce za a kwashi
nama,musamman a samu wani gidan su yankata da babbar sallah a matsayin layya,wuuuuu
gaskiya da anci nama mai yawa kuwa,iya cinyarta d'aya ta isa ayi dambun nama a cika
fanteka da shi"
Lallab'awa tayi ta isa inda Aminar take,baki a bud'e hanci a bud'e sai
gurnanin munshari take, tana zuwa ta d'ebi cinnaku tasa mata d'aya kan hanci ,d'aya
kan leb'en k'asa,d'aya a kumatu,d'aya a goshi,ganin Amina ta fara mutsu mutsu da
sauri Harira tayi hanyar fita daga d'akin ta fito,tana zuwa tsakar gidan ta matsa
kusa da Sunusi ta d'aga babbar rigar da ya lullub'a a hankali,dai dai k'eyarsa ta
samu ta watsa masa ragowar cinnakun ,da sauri kuma tayi wuf ta shige cikin d'akinta
tana rufe bakinta dan kar dariyar da ke cinta ta kufce har a jiyota.
Ko cikakken minti uku bata yi da komawa d'akinta ba taji motsin Sunusi ya faraa
buge buge da karkad'e malum malum sai zabga salati da hailala yake,matsawa tayi a
hankali ta k'aramar tagar da ke d'akin tana lek'en tsakar gidan, sai ta hangi
Sunusi a tsaye sai zare idanuwa yake yana susai k'eya,can kuma sai ga Amina ta fito
da sauri zuwa tsakar gidan sab'atar sab'atar da ita,rigar baccinta iya gwiwa ta
cika ta tayi dam,Harira ta rufe baki dariya na cinta,a zuciyar ta cewa take "Wannan
ina ma iyayen ta ba Amina suka sa mata ba,don tafi dacewa a kirata da Maman Sumbi"
A tsorace Sunusi ya juya ya dubi Amina,zaiyi magana kenan Aminar ta riga shi
sai susar hanci da kumatu take " Me gida k'aik'ayi nake ji da wata irin azaba a
fuskata,an ya kuwa ba cinnaka ne ya cijeni ba?"
K'irjin Sunusi ya buga damm,ya matsa kusa da Aminar yana cewa " Nima yanzu na
farka a gigice bakiji yadda k'eyata da bayana suke min zugi ba,kamar wanda kunama
ta d'alla a....
Kafin Sunusi ya k'arasa maganarsa Amina ta zabura ta kai hannu ta daki goshinta
tana sosawa,azaba ta ishe ta kamar ta mutu,idan ta sosa kunci sai ta sosa
goshi,leb'en bakinta na k'asa kuwa ya kumbura yayi suntum jajawur da shi,ji take
kamar ta tsinkeshi ta yar da shi don azaba,shi kam Sunusi k'eyarsa wani irin
bird'in bird'in tayi kamar wanda ya k'one, sun rasa menene ya cije su da suke jin
wannan azaba haka,safa da marwa kawai suke a tsakar gida kowa na fama da kansa,
Harira na lab'e cikinta kamar ya fashe dan dariyar da ke cinta,tana kallo Sunusi
yana ta fatali da kayan jikinsa,ya yar da malum malum,ya cire jallabiyyar jikinsa
ma ya yar,hatta singleti sai da ya cire ya watsar,ya kama gajeran wandon zai cire
Amina ta rik'e masa hannu a gigice da kumburarriyar fuskar ta ta ce "Mai gida a
tsakar gida muke fa kar kayi tsirara" Sunusi ya fizge hannunsa ya kai bayansa yana
susa idanu jajir,shi kad'ai ya san azabar da yake ji.
Harira taji ina ma da zata sakawa Amina cinnakun a cikin rigar baccinta ta
saka mata, kan zunduma zunduman nonuwanta,ta tabbatar da Amina ma sai tayi tunb'ur
yadda Sunusi yayi,aikuwa da ta sha kallo ashe,ya za a ga Amina a tub'e?ina ruwan
banu lukutuna 😂.
Da taga suna ta safara a tsakar gida hakan yasa ta d'aga labulen d'akinta ta
fito da fitila a hannunta,sai mik'a da hammar k'arya take kamar wadda ta farka daga
barci,juyowa suka yi suna dubanta yayin da ta k'arasa garesu tana fad'in.
"Wai lafiya nake ta jin motsinku da magana a tsakar gidan nan?me yake faruwa ne?"
tana magana tana haska fuskar Amina da fitilar hannunta,ta wani zabura kamar zata
yar da fitilar tana fad'in.
"Kai ! an sukuta me ya sameki haka a fuskarki da leb'enki?kinga goshinki kuwa?uwa
na wata yarinya Samiha da nake wa kitso lokacin baya, dan ita ma Allah yayi mata
baiwar k'aton goshi wallahi"
Amina tayi mata banza ta cigaba da safa da marwa dan azabar da takeji kan fuskarta
ta isheta,bata da lokacin tasayawa kula wata Harira mara kan gado,Harira ta juya ta
dubi Sunusi da ya lafe jikin bango sai gurza bayansa yake a jikin bangon yana cije
baki idanuwa k'ulu k'ulu kamar su fad'o k'asa,saura kad'an wandon jikinsa ya fad'i
k'asa dan mazarin da jikinsa yake yi,Harira ta k'unshe dariya tana fad'in.
"Wai Sunusi me ya sameku ne?ko dai gamo kuka yi da aljanu da tsakar daren nan.....
Wuf taga Sunusi ya daka tsalle zuwa gaban Amina har da d'an ihunsa yana fad'in "
wihuhuuuu Amina dan Allah sosa min bayana da k'eya ta" Harira ta matsa ta haska
bayan Sunusi da fitilar hannunta,ta zaro idanu cikin mamaki ta ce .
"Sunusi ai wannan cizon cinnaka ne,subuhanallahi aikuwa in dai kuna son ku daina
jin azaba to sai kun aikata wani abu tukunna"
Da sauri Amina ta ce " To dan Allah me za mu yi mu daina jin zafi,wallahi ji nake
kamar na cire fuskata na yar na huta dan azabar da nake ji"
Harira ta maze kamar gaske ta ce.
"Rikodar d'akin ki kawai zaki d'akko in saka muku disco,ku taka rawar amada 😂 ko
etigi 😂 ko sabada😂 na rantse da kunyi zaku nemi azabar da kuke ji ku rasa"
Wani mugun takaici ne ya kama Sunusi,ga azabar da suke ji ga rainin hankalin da
Harira ke musu, bai san lokacin da ya d'ago a fusace ya gaurawa Harira mari me
shegen zafi ba,fitilar hannunta ta fad'i,ta wage baki za ta saka ihu kenan Sunusi
ya k'ara dunk'ule hannu ya kaiwa rub'ab'b'en dadashin bakinta naushi,sai ga Harira
kwance riris ta fad'i tana birgima da shura k'afafu.....🤣
Comments
Share
Vote
Pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*BABI NA GOMA SHA BAKWAI DA NA GOMA SHA TAKWAS*
PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️
*ASLM FATAN KUN WUNI LAFIYA HARYANZU DAI MUNA KARA TALLATA MUKU SABUWAR CHANNEL DIN
DA ZATA RINKA KAWO MUKU LITTATTAFAI KALA DABAN² DAN ALLAH KU DANNA MANA SUBSCRIBE*
DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
*K'awayen An gayu da Saratu ku fito yau fejin naku ne* 😂😂😂😂
***Sallama ta ringa rafkawa tun daga k'ofar shiga gidan har ta dangana ga tsakar
gidan,a nan ta ci burki tana sake d'aga murya tana kwad'a sallama da zazzak'ar
muryarta,Hauwa da ke cikin ktcheen ta lek'o tana amsawa,bin matar da ke tsaye tayi
da kallo cikin rashin sani,ta k'urawa fuskarta idanu sosai bakinta a sake, An gayu
ta washe bakinta wanda ta rambad'a Jan jambaki me suna (Kan ta kile), Hauwa ta
k'arasa fitowa daga ktcheen idanuwanta akan An gayu,kafin kuma ta bud'e baki cikin
rashin sanayya tayi magana.
"Baiwar Allah sannu da zuwa,amma ban shaida ki ba ko wani gidan kike nema?" Hauwa
ta tambayi An gayu.
Sake washe baki An gayu tayi ta sosa kanta sannan ta ce.
"Ah ah nan gidan dai na zo,ni bak'uwa ce wajenki na zo".
Mamaki ya kama Hauwa dan ita dai bata santa ba,ko mai kama da ita ma bata tab'a
gani ba,wata irin mace a hargitse babu gyara,amma dan kar ta ce ta wulak'anta ta
shiyasa ta d'an yi murmushi ta ce.
"To babu laifi sannu da zuwa,shigo daga ciki sai mu gaisa". Tana fad'in hakan ta
wuce falonta,yayin da An gayu ta bita jiki na rawa har hard'ewa take yi.
Bayan sun zauna a kujerun da suka kewaye falon sai suka gaisa,An gayu sai
kalle kalle take yi sosai falon ya birgeta,ita kuwa Hauwa babu abin da take kallo
sai koriyar majinar da ta cika hancin An gayu,wani irin k'yank'yami take ji domin
ko a hancin yaro ta tsani ganin majina balle a hancin babban mutum,har gara taga
bayan gida akan taga majina,haka dai ta daure ta kawar da kai ta yi magana.
"Baiwar Allah ina sauraronki,kiyi min bayani daga ina?domin ban shaidaki ba
gaskiya".
An gayu ta gyara zama ta dubi Hauwa tana murmushi ta ce.
"Ni dai Suna na An gayu matar Babban malamin nan wato Malam Arabi,na tabbatar kin
san shi domin kaf unguwar nan babu malami kamar sa,mun dawo layin nan da zama ne
shine nace bari na shigo muga juna domin mu k'ulla zumunci tsakani na da ke a
matsayin mu na mak'otan juna"
Hauwa ta bud'e baki zata bawa An gayu amsa sai aka d'aga labulen falon aka shigo da
sallama,da sauri Hauwa ta mik'e tana amsa sallamar tare da yi masa sannu da
zuwa,Idrees ya amsa sannan ya dubi sashin da An gayu take ya d'an kalleta,wani irin
yammmm ya ji a jikinsa sakamakon karo da curarren tasono da koriyar majina da
yayi,da sauri ya d'auke kansa yayi hanyar cikin d'aki da hanzari ko amsa gaisuwar
da An gayu take masa baiyi ba,Hauwa ta dubi An gayu tace mata.
"D'an jirani ina zuwa" Tayi hanyar d'akin domin bin mai gida Idrees.
Tana shiga ya juyo fuska a d'aure ya dubeta,a fusace ya tambaye ta.
"Ke ! meye wannan abun na ci karo da shi a falo?"
Hauwa ta rasa me yake nufi,dan bata gane hausar ba,shiyasa ta dubeshi cikin alamun
tambaya ta ce.
"Wane abu fa hubby?ban gane tambayar ba".
Ya hayayyak'o mata.
"Kan ban tsinke ki da mari ba shege nake,ina tambayarki kina tambaya ta dan kin
raina min hankali?"
Jikin Hauwa