Author : TARE DA ALK'ALAMIN Category : Complete Novels
kamar tana bacci"
Umman Saratu tayi kasak'e,sai can ta dubi Hajiya Maimuna tace.
"Baba Laminde kuma?a gidan nan?
" Eh mana Baba Laminde dai ta k'auye,ba ita ce kwance kan tabarma a tsakargida tana
bacci k'uda na bin bakin ta ba?"
Girgiza kai Umman Saratu tayi,cikin takaici tace.
"Ni rabo na da Baba Laminde tazo garin nan ai an jima,Saratu ce fa take bacci,kama
tayi miki da Baba Laminden ne?"
A zabure Hajiya Maimuna ta dafe k'irji tana fad'in.
"Wace Saratun?kina nufin Saratunki ce ta mommole ta zama tsohuwa haka?bata da
lafiya ne?ko dai cutar k'yanda take? Ta jero tambayoyi cikin gigita.
Umman Saratu ta girgiza kai cike da damuwa tace.
" Yo ban da abin ki Hajiya Maimuna manyan mutane suna k'yanda ne?k'yanda ai sai
yara,lafiyarta k'alau kawai duniya ce take ladaftar da ita,tak'i zaman Aure sai
iskanci iri iri takewa mijin,shi kuma ya gaji ya sako ta,gashi nan har iddarta ta
cika amma ya k'i ya maida ita d'akin ta "
Hankalin Hajiya Maimuna a tashe tace.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, wallahi bani da wannan labarin Fatsima,da
yake na jima bana gari ina Maiduguri ziyarar y'an uwa,amma banji dad'in wannan
magana ba,me yasa kuka bari Saratu take cikin wannan yanayin,na rantse da Allah na
zaci Baba Laminde ta k'auye ce,tana yarinyar ta da ita amma duk tsufa ya sakko
mata,nifa kamar har furfura na gani a gefen kanta,daman an ce tashin hankali yana
kawo furfura Ashe da gaske ne?"
Umman Saratu tayi murmushi tace.
"Haba dai furfura?tatar Koko ta gama yi min,ina ji k'ullun ne ya shafe ta kika ga
kamar furfura,ni kaina da bana tausayin ta saboda ta b'ata mana rai,amma yanzu har
na fara tausaya mata wallahi, haka kawai ma fa tana kwance sai kiji tana ihu kamar
mahaukaciya,dukan da ta sha a hannun mahaukaci yana dawo mata a k'wak'walwar kanta"
"Wane mahaukaci kuma?" Cewar Hajiya Maimuna.
Nan Umman Saratu ta kwashe labarin komai ta fad'awa Hajiya Maimuna, takaici kamar
ya kashe ta Dan Haushi,ga kuma dariyar da ke cinta,Umma bata kammala rufe baki ba
suka jiyo ihun Saratu daga tsakar gida tana zambarwa tana fad'in.
"Ku zo ku cece ni Mahaukaci zai kashe ni,Salisu kana ina ne?ka taimaken jijjib'in
mijina,D'an lukutina abin alfaharina,inna fatahna laka fathan mubina,na shiga uku
mahaukaci zai kashe ni"
A zabure Hajiya Maimuna ta mik'e tana Neman wajen b'uya,domin ihun ya gigita
ta,bata san lokacin da ta take k'afar Umman Saratu ba,umman ta zuba wani mahaukacin
ihu saboda azaba,ihun ya k'ara razana Hajiya Maimuna ta kifa akan cinyar Umman
Saratun,da azaba ta ishi Umma kawai sai tasa bakin ta ta dank'o wata Tsoka da ke
gefen wuyan Hajiya Maimuna dai dai k'eyar ta,ta sakar mata cizo a wajen.
Hajiya Maimuna ta zabga ihu,a dai dai lokacin da Saratu ta fad'o d'akin da gudu
tana ihu.
Comments
Share
Vote
pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*BABI NA GOMA SHA D'AYA DA NA GOMA SHA BIYU*
PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️
***Hajiya Maimuna ta ruk'unk'ume Umman Saratu jikinta na rawa tana ganin kamar
kanta Saratu za ta yo,k'eyarta na zugi da rad'ad'i sakamakon hak'oran Umma da suka
kaiwa naman k'eyar ziyarar bazata😂,ita kam Saratun tana shigowa zata nufo su cikin
k'arfin hali Ummanta ta saki naman k'eyar Hajiya Maimuna ta kwaye murya ta daka
mata tsawa da k'arfi tana zazzare idanuwa.
"Ke Saratu !Dan ubanki dakata nan kar ki k'araso nan,shiga taitayin ki ki dawo
nutsuwarki kafin ki sa na kirawo Malam yanzun nan yayi min maganin iskancinki".
Chak! Saratu ta tsaya jikinta na rawa tana k'ik'k'ifta idanuwa, ta daina ihu da
surutan da take yi,Umman ta k'ara dubanta tace .
"Nemi waje ki zauna a nan in da kike kuma ki nutsu".
Aikuwa sai Saratu ta zame ta zauna a inda take tsaye,sai kallon Hajiya Maimuna take
yi wadda tayi ragajeje kwance a cinyar Umma,gabad'aya gab'ob'inta sun sage ta kasa
mik'ewa tsabar matsanancin tsoron da ya rud'a ta,sai lokacin Umman Saratu ta dubi
Hajiya Maimuna ta D'an yamutsa fuska cike da takaici ta ce.
"Don girman Allah Maimuna ki d'agani,ina fama da jinyar k'afafuwana amma duk kin
taushe min su"
A hankali Hajiya Maimuna ta ja jiki ta d'aga Umman Saratun,ta koma gefe ta rakub'e
tana satar kallon Saratu k'irjinta na tsananin bugawa tana sauke numfashi,gabad'aya
a tsorace take,Dan ita tunanin ta Saratun Haukacewa tayi ta shigo za ta lode su,sai
da ta gama mayar da Numfashin tsoro da jigata sannan ta dubi Umma tace.
"Kiyi hak'uri Umman Saratu,domin ni ban san ma lokacin da na haye kan k'afafun ki
ba wallahi,na tsorata da ihun da take zabgawa ne k'warai da gaske,amma dai gaskiya
ya kamata a kai ta asibiti a duba k'wak'walwar kanta,kar fa wata matsalar ta samu
daga haka,wannan ai ba k'aramar sukutar masifa ba ce".
Umma ta sauke numfashi ta dubi Hajiya Maimuna ta ce.
"Ni ma nayi wannan tunanin,amma da na fad'awa Malam sai yace min wai babu asibitin
da za a kaita, tsabar iskanci ne kawai take ji da shi shiyasa take mana wannan
ihun,rannan fa da tana yi kinga dukan da yayi mata?ni gashi ba k'afafu ba balle na
tashi na k'wace ta,sai da yayi mata lilis,kuma yace duk randa ta kuma wannan ihun
da surutai wai zai sa gardawan almajiransa su d'aga ta sama ya Zane ta ciki da
bai, ni kam mamaki ne ma ya kamani da jin lafazin sa,shiyasa na dube shi nace da
shi.
" Malam da girmanta za a sa gardawa su d'aga ta a zaneta"
Sai ya ce min wai in bari ta sake yi d'in a gabansa zan ga aiki da cikawa,to in
tak'aice miki labari muddin yana nan yanzu bata yi,amma da zarar taga ya fita zata
addabeni da ihu da surutai,hakan yasa na tabbatar da maganar Malam cewa Saratu
iskanci ne abin na ta,don taga ni ban da k'afar da zan tashi na luguiguita mata
jikinta ne kawai".
Hajiya Maimuna ta ja ajiyar zuciya ta kalli Saratu da ke rakub'e jikin bango sai
zare ido take,fuska duk ta yamushe kamar ta Akuya,kamar ta da Baba Laminden k'auye
ta k'ara fitowa rad'au,ta girgiza kai a Zuciyar ta ta na ce wa.
"Amma kin cuce ni fad'uwar gaban da kika sakani Saratu,ba Dan ina jin tausayin ki
ba har gaban abada ba zan yafe miki ba"
A fili kuma sai ta dubi Umman Saratun ta ce.
"Lallai kam bata kyauta ba in dai haka ne,amma ina ganin damuwa ce tayi mata yawa
fa,ya kamata a nemi Salisu a bashi hak'uri a daidaita su ta koma d'akin ta,zamanta
haka kara zube babu fa'ida,tabbas Saratu tayi ba dai dai ba amma ayi mata Afuwa,na
tabbatar ba zata sake aikata irin hakan ba in sha Allahu ,saboda bala'in da ta gani
kad'ai ya isheta ishara a rayuwa"
Umman Saratu ta ce.
"Hmmm!yaushe rabon wani Salisu da gidan nan,sai fa yayi wata d'aya bai zo ba,sannan
kuma ko yazo a waje yake tsayawa su gaisa da malam ya wuce,baya shigowa gidan nan
ko don ma kar yaga Saratun, ai Salisu yayi fushi sosai kan abin da ya faru,Kuma ni
banga laifinsa ba,tunda a gabansa har uwar sa take ambatowa ta zaga,tana ambatar ta
iya me ido d'aya,kinga kuwa duk d'a na halak ba zai jure cin mutuncin iyayensa ba
Hajiya Maimuna".
Hajiya Maimuna ta girgiza kai cike da takaici ta ce.
"Tabbas haka ne,ban da abin Saratu ma iyan da tuni ta riga ta mutu menene na
ambatota?Allah dai kawai ya kyauta,abin da ya faru ya riga ya faru,sai a guji gaba
kawai,yanzu dai zan samu nayi kiran Salisun gidana tunda mutumina ne,lokacin da
yayi almajiranci a gidana yayi aikin wanke wanke da shara da wanki,har yanzu kuma
yana ganin mutuncina yana zuwa ya gaisheni,Yanzu ma Dan nasan bana gari ne shiyasa
baya zuwa,amma zan sa a kirawo min shi ko na kirashi a waya mu tattauna akan batun
in sha Allah,kuma za a samu mafita da yardar Allah"
Umman Saratu ta ji dad'i Sosai da maganar Hajiya Maimuna, ta dinga yi mata
godiya,domin ita kanta ta gaji da zaman Saratun tare da ita,burinta ta koma gidan
mijinta.
******************
Har soro ta rako shi ta na tafiya da k'yar,sai da suka zo soron k'arshe sannan ya
tsaya ya waiwayo yana duban ta cike da tausayawa a fuskar sa,yayi murmushi ya ce.
"Sannu kinji ,Allah ya raba lafiya,koma ciki ki huta don ni fa bana son naga kina
Aiki da yawa,tausayin ki nake ji Zahra'u na"
Zahra'u tayi murmushi tana langab'e wa ta kalli K'asimu ta ce.
"Haba maigida,kullum fa naje awo likitocin suna fad'a mana mu dinga motsa jikin
mu,idan nak'uda ta zo mana za mu samu sauk'in haihuwa,kuma ba za mu yi doguwar
nak'uda ba,shiyasa kaga bana son zama na jab'e,nafi son in ganni a tsaye ina aiki
ko wani abin"
Ya D'an matsa kusa da ita ya d'aga rigar yana k'arewa cikinta kallo,Wanda yayi
tirtsetse kamar y'ay'a biyu ne a ciki,shafa cikin yayi yana washe baki ya ce.
"Allah yasa ki haifo min mace in sa mata suna Zahra'u, ko domin riritani da kike yi
kamar wani k'wai"
Zahra'u tayi Y'ar dariya,sannan ta rik'o hannun sa ta ce.
"Ina so in anjima yarinyar mak'otan nan Nana zata rakani nan bayan layi gidan
kitso,kaina duk ya dameni so nake ayi min kitso,kasan kuma tun dawowar mu unguwar
nan Atika ce take min,ita kuma kwana Ashirin da Auren ta kenan,na rasa wata
budurwar da zata dinga zuwa tana yi min,shine Nana tace min akwai wata mai yin
kitso a bayan layin nan kuma ta iya,sai dai ita matar Aure ce bata zuwa gidan mutum
tayi masa sai dai mutum ya taka yaje da k'afafuwan sa"
Sai da K'asimu ya kammala sauraronta sannan ya sauke ajiyar zuciya, ya kalleta ya
ce.
"Kina ambatar gidan kitso sai da na tuna da BAHAGON LAYIN mu da muka taso,ni dai ba
don an rasa mai kitso ba babu dalilin da zai sa na k'ara barinki zuwa gidan wani
kitso,matattarar y'an iskan mata da gulmace gulmace,wace irin gwagwarmaya ce ba a
sha gidan Harira mai kitso ba?abubuwa da yawa sun faru wad'anda ko tuna su bana
son yi,sai da Harira ta wargaza layin nan sannan hankalin ta ya kwanta,shiyasa naji
dad'in Auren da Sunusi yayi,har na bashi gudummawa mai Tsoka, sai yanzu zai san
yayi Aure,domin da ba Aure yake ba wasan yara kawai yake da shirme"
Zahra'u ta jijjiga kai tana sauke numfashi, tabbas sun shuka tsiya a BAHAGON
LAYI ,har bata son tunawa da abubuwan da suka faru,musamman dukan da suka sha a
hannun ofisa,wannan rana ba zata tab'a mantawa da ita ba,shiyasa tun da suka bar
BAHAGON LAYI suka dawo wannan unguwar bata tab'a sha'awar shige shigen mak'ota
ba,kuma ita ma kulle k'ofarta take yi bata bari a shigo mata in dai ba yara ba,suma
d'in ba ko yaushe ba,Yarinya d'aya ce ta san sun yi Sabo sosai,kuma tana aikenta
cefane ko siyo wani abin,ita ce( Nana),yanzu babu Ruwan ta da rayuwa irin ta
BAHAGON LAYI, ba zata sake biyewa irin su Harira su Habiba su kaita su baro
ba,domin ba don tayi sa'a mijinta yana sonta ba da tuni sun gurgud'e mata Aure,
yanzu ga Saratu can gidan iyayen ta,tana girbar abin da ta shuka.
K'asimu ne ya dawo da ita daga tunanin da ta afka,ta hanyar rik'o hannayen ta,ta
sauke ajiyar zuciya ta dubeshi ta ce.
"Ni kaina bana son zuwa gidan kitson mijina, duk da dai ba kowane gidan kitso ne
zai kasance irin na Harira ba,kuma in sha Allahu zan tsare maka kaina da
mutuncina,har naje na dawo babu abin da zai faru"
Ya ji dad'in maganarta,ya shafa kumatun ta yana murmushi ya ce.
"Yawwa y'ar Albarka, haka nake son ji,don Allah ki kula min da kanki,kinga dai
tsohon ciki gare ki,ni ina ganin ma zuwa zan yi na koyo yadda ake kitson,sai na
dinga yi miki a gida ba sai kin fita ba ko?"
Zahra'u ta shek'e da dariya,K'asimu na taya ta dariyar,daga nan suka yi sallama ya
fita zuwa kasuwa,ita kuma ta juya ta shige cikin gida tana takawa da k'yar saboda
yadda cikinta yayi girma haihuwa yau ko gobe.
***************
Salisu zaune a shagon Babalalo,shi kuma Babalalon yana yi masa aski,suna D'an tab'a
hira kan yadda shagon askin ya k'one,lokaci guda Salisu yaji wayar sa na k'ara
alamar kira,Hannu ya saka cikin aljihun sa ya zaro ta,yana dubawa sai yaga sunan
uwar d'akin sa ce wato Hajiya Maimuna…..
Da hanzari ya d'aga wayar ya kai kunnen sa ya rafka sallama cike da girmamawa.
Comments
Share
Vote
pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*BABI NA GOMA SHA UKU DA NA GOMA SHA HUD'U*
PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️
***Kamar yana gaban ta haka ya D'an russuna yana gaishe ta cike da girmamawa,saboda
ganin k'imarta da girmanta da yake,yayin da Babalalo ya koma gefe yana jiran ya
kammala wayar ya cigaba da yi masa askin.
Bayan gaisuwar da ta shiga tsakanin Hajiya Maimuna da Salisu, sai Hajiyar ta
sanyaya murya cike da kyautatawa tana fad'in.
"Kwana biyu ka guje ni Salisu,yaushe rabon da na sanyaka cikin idanuwana?dafatan
dai ba wani laifi nayi maka ba?"
Ya D'an yi murmushi yana Sosa gefen kansa da aka aske ya ce.
"Ayi hak'uri Hajiya,wallahi yanzu ne ban cika shigowa unguwar ba ma kwata
kwata,abubuwa sun min yawa bana samun isasshen lokaci,amma kwanaki da na shigo har
gidan naki na zo na ganshi a rufe da kwad'o alamar bakya nan"
Hajiya Maimuna tace.
"K'warai kuwa an yi haka,bana nan naje Maiduguri ne lokacin ziyarar y'an uwa, don
ban jima da dawowa garin nan ba ma"
Salisu cikin murmushi yace.
"Ayya!to Hajiya ya aka baro mutanen gidan?dafatan kowa yana lafiya dai?"
Hajiya Maimuna ta ce.
"Lafiya k'alau Malam Salisu, mutanen gida duk sun ce a gaisheku ma,yawwa daman ina
son ganinka ne,shine nace bari na kira lambarka,don Allah ka samu lokaci kazo domin
ina son zamu tattauna wata magana mai muhimmanci ni da kai"
Ya gyad'a kai yana amsawa da cewa.
"To babu damuwa Hajiya,insha Allahu zuwa gobe zan samu lokaci na b'ullo,Allah dai
yasa lafiya?"
Hajiya ta D'an yi dariya tace.
"Lafiya lau, insha Allah kuma alkairi ne kiran kar ka samu damuwa,kuma ina nan ina
zuba idanu sai na ganka d'in"
Salisu ya amsa yana k'ara tabbatar mata in Allah ya yarda zai zo goben,daga nan
suka yi sallama da juna ya kashe wayar.
Sai lokacin Babalalo ya matso yana cewa.
"Ni duk ka tsayar da ni man inji na yana tafiya a banza Salisu,gaskiya sai ka k'ara
min kud'in askin nan naka"
Salisu ya kwashe da dariya ya mayar da wayarsa aljihu sannan ya dubi Babalalo yana
fad'in.
"Kai fa Babalalo yanzu na lura son kud'in ka yayi maka yawa gabad'aya,ba kuma komai
ya sa hakan ba sai don kana son ka k'ara Aure ko?"
Babalalo ya sauke numfashi ya girgiza kai,yayin da ya cigaba da yiwa Salisu aski,a
hankali yace.
"Wane Aure Salisu? Bayan komai ya rushe, gobarar nan da ta sameni ta tsayar da
komai,duk da k'addara ce amma gaskiya har yanzu ban gama farfad'owa daga k'uncin da
na shiga ba,a shirye nake tsaf zan angonce wannan k'addara ta afka min,ga Sunusi
nan har ya riga ni farke Amaryar sa a Leda ya barni da hamma "
Salisu ya Kuma tuntsirewa da dariya yana fad'in.
"An yi maganin mai zumud'i,na san yanzu ran Habiban ka k'al maganar Auren ka ta
kwanta ko? dan wannan mata tunda tayi aljanun k'arya akan kishi na sallamawa kishin
ta"
Babalalo ya saki tsaki yana fad'in.
"Kamar ka sani kuwa,ni sai naga ma kamar murna take yi da ibtila'in da ya sameni
fa,Amma idan ta san wata ai bata san wata ba,idan tayi nasara wancan karon wannan
karon kam tayi kad'an da yardar Allah"
Salisu yace.
"Wani abin za ka sake yi mata ne Babalalo?"
Babalalo ya share maganar Salisu bai bashi amsa ba,ya sako wani zancen yana cewa.
"Wai ni kam yaushe zaka dawo da Saratu d'akin ta ne ?gaskiya ya kamata ka yi
hak'uri haka Salisu,ai ta horu da yawa matar nan,nifa labarin da ya iskeni tunda ka
saketa cikin tumakai take kwana,an ce har ta so ta fara zaucewa,gashi har iddarta
ta cika baka yi wani motsi ba,ya dace dai ka hanzarta a sake d'aura muku Aure ta
dawo ku cigaba da zaman ku,zaman ka haka babu mace bashi da wani amfani balle
fa'ida,aure rufin asiri ne da cikar kamalar mutum Salisu"
Nan da nan Salisu ya canja fuska,domin babu abin da ya tsana irin ayi masa maganar
Saratu,domin har yanzu bak'incikin ta bai goge a idanuwan sa ba,menene amfanin zama
da mace irin Saratu wadda ta zama tamkar balama sak'andama?wani zubin ko rufe idanu
yayi sai ya hango lokacin da Mahaukacin nan yake jibgarta babu kaya a jikinta,tana
birgima nonuwa na rawa da tsalle,take sai yaji ya k'ara tsanarta,ko son ganin
fuskar ta baya son yi,shi gabad'aya ma ji yayi baya son yin wani Auren,ganinsa duk
matar da zai aura ita ma wannan akuyancin zata zo ta dinga yi masa a cikin gidan
sa.
Ganin Salisu yayi shiru ya b'ata rai sai Babalalo shi ma yayi shiru ya shiga
taitayinsa,domin ya fahimci kwata kwata Salisun baya son ayi masa maganar Saratun,
yanzu sai ya daina walwala ya shiga kumbure kumbure yana hura lukutin kumatunsa,a
haka ya kammala masa askin sa yana zak'ulo masa wasu hirarrakin na daban.
**************
Lokaci guda motar akori kuran ta tsaya a bahagon layi daidai k'ofar gidan
Sunusi,Inna da Harira suka fito daga gaban motar,Harira tabi filin layin da kallo
tana washe baki tana jin matsananciyar murya a zuciyarta,ashe da rabon za ta dawo
layin ta cigaba da zama ba ta tafi kenan ba?.
Direba ya fito yana ta k'ok'arin sassaukewa Harira kayanta,kwanuka da tukwane sai
katifa da tabarma da kuma abin da ba za a rasa ba ragowar tsummokaranta,duk kayan
dai a tsiya ce basu da wani yawa.
A lokacin ne Sunusi ya fito daga gidan jin tsayuwar motar,kwata kwata baya jin
dad'in dawowar Harira gidan ,amma saboda kar Inna ta fahimta sai ya dinga murmushin
yak'e yana musu sannu da zuwa amma a fakaice sai zabgawa Harira mummunar harara
yake yi.
Da shi da direban suka dinga kwasar kayan suna shiga dasu cikin gidan har suka
kammala,Sunusi ya biya direba kud'in mota ya tafi,shi kuma suka shige cikin gidan
tare da Harira da Inna.
Tarba ta mutunci Amina tayi musu,sai faman sannu take zabga musu,har falonta ta
kaisu ta kawo musu ruwa,Inna dai ta sha amma Harira kam ko kallon ruwan bata yi
ba,sai kallon Amina take yi tana ganin yadda ta k'ara hab'akewa ta zundume ta zama
wata k'atotuwa kamar tifa,sai ta ganta wata y'ar tsurut kamar b'era a gaban
zaki,amma wai duk da hakan Aminar in zata bud'e baki tayi magana sai ta dinga zabga
mata (Yaya Harira) .
Inna da kanta ta had'asu tayi musu nasihar zama lafiya da juna da samun kwanciyar
hankali,sannan ta umarci Sunusi yayi adalci a tsakanin su banda wariya,hakanan tayi
wa Harira fad'a akan ta ja girmanta banda fitina,ita kuma Amina ta girmama Harira
tunda ita ce uwargida,sannan Inna ta nemi cewar idan da mai magana to bisimilla
yayi k'ofa a bud'e take.
Sunusi da Amina suka ce basu da magana,amma Harira uwar zirgilli karaf ta d'aga
hannu tace tana da magana.
Inna ta dubeta tace "To muna sauraren ki Harira"
Harira ta gyara zama tana kaikaicewa tace.
"Ni dai