Author : TARE DA ALK'ALAMIN Category : Complete Novels
a gidan Iya ne naga yadda take
wa masu nak'uda,da an kirata tayi musu turaren suke haihuwa"
Da yake Kamilun a rud'e yake kuma mafita yake nema nan da nan ya yarda da batun
Harira,da sauri ya d'auki abin da zai samo garwashin ya fice can bakin layinsu
wajen masu tsire domin ya samo,Sunusi ya bi shi a baya yana jinjina batun
Harira,shi dai zuciyarsa bata amince ba da dai asibitin aka tafi zai fi...
Suna fita Harira ta shige ktcheen d'in Shafa tana dube-dube,har ta ci karo da abin
da take so wato BARKONO, d'ebowa tayi a hannunta sannan ta fito,Amina rik'e da
Shafa'atu sai sannu take mata tana tausaya mata,lokacin ne su Kamilu suka dawo da
garwashin sun samo,Harira ta karb'a tace su fita waje su jira,Kamilu ya kama hannun
Sunusi suka yi waje,Ita kam Harira shiga da garwashin tayi har falon Shafa,Sannan
ta dubi Amina ta ce.
"Hajajju makkatu rik'e ta zaki yi sosai fa"
Amina duk ta d'auka abin arzik'i ne ta sake rik'e Shafa gam, Harira ta fakaici
idanuwan su ta watsa wannan Borkono a cikin garwashin,tana zubawa ta dubi Amina ta
ce.
"Aiki ya same ki an sukuta,ni bari naje daga tsakar gida maza ki cigaba da rik'eta"
tana fad'in hakan da sauri ta fice saboda yadda hayak'i me mugun yaji ya fara
turnuk'e d'akin,k'ofa ta ja ta kulle su ta waje tana dariyar mugunta,Harira fad'i
take a zuciyarta .
"Dole ma yau ki rame Amina 😂 dan Wallahi ba zan bud'e ku ba sai kinyi tari kin
rame wannan k'ibar ta zube dan wahala"
Kafin wani lokaci tarin Amina da Shafa ya fara yawa,wani irin lukutin tari Amina
take kamar ta shid'e tana ihun Harira ta bud'e su,amma Harira dariya kawai take
shek'awa 😂.
*Gaskiya Harira ke azzaluma ce* 🤣🤣🤣🤣
Coments
share
vote
pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI DA NA ASHIRIN DA TAKWAS*
PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️
*KUYI HAK'URI ZAN TAK'AITA LABARIN SABODA GABATOWAR WATAN RAMADAN,GA ABUBUWA SUN
MIN YAW BANI DA LOKACI KO KAD'AN* 👏
*** Wata irin lukutar atishawa da tari kawai Amina ke saki,yayin da Shafa me
nak'uda ke cikin wani yanayi na azaba da wahala,ga bala'in ciwo ga kuma hayak'in
barkono,ita kanta Harira da ke tsakar gidan hayak'in ya dameta ta fara tari da
atishawa,amma bak'ar zuciya da mugun nufi da ke d'awainiya da ita ba zai sa ta fasa
k'udurinta ba.
Tun daga waje Kamilu da Sunusi suke jiyo wani irin yaji da hayak'i,har su ma
suka fara tari kad'an kad'an suna rufe baki,kamar kuma daga sama Sunusi yake jiyo
muryar Amina na ihu da kururuwa,hakan yasa da hanzari ya juya ya shige cikin gidan
har da d'an gudunsa,shi ma Kamilu ya rufa masa baya.
Harira suka iske tsaye a tsakar gida tana d'an tari tare da shek'a dariya,sam
bata lura da shigowarsu ba sai da taji tari a bayanta sannan ta waiwaya a firgice
tana zare idanuwa,wani irin mugun tari ne ya sark'afe Kamilu da Sunusi ,cikin
k'arfin hali Kamilu yake tambayar Harira cewar.
"Wannan wane irin yaji ne?daga ina yake tasowa?"
Shikam Sunusi k'ofar d'akin da su Amina suke ya nufa yana kacaniyar bud'ewa,saboda
ihun ta da yake jiyowa da atishawa da kakkauran tarin da take yi,Harira ta zabura
tana dakatar da shi daga k'ok'arin bud'e k'ofar tana fad'in.
"Kar fa ka bud'e k'ofar nan,turaren nak'uda nake wa Shafa kuma na san yanzu zata
haihu"
Wata muguwar harara Sunusi ya lafta mata yana k'ok'arin cigaba da bud'e
k'ofar ,sannan ya ce.
"Turaren nak'uda ko turaren mutuwa?muguwa azzaluma haka kawai ki kulle su a d'aki
ki bula musu hayak'i ke kin fito daga ciki,me ya sa ke baki zauna ciki ba?idan
Shafa'atu ce me nak'udar ita Amina nak'uda take yi da za ki kulleta a d'aki tare da
me nak'uda?"
Dai dai lokacin ya bud'e d'akin yana shirin shiga,Kamilu ma ya ja k'afa suka afka
d'akin yayin da wani mugun yaji da hayak'i ya bulesu,suka fara jero atishawa ba
k'ak'k'autawa tafi guda saba'in 🤣.
Harira kam tab'e baki tayi tana fad'in.
"Ni me zai kaini rik'e me nak'uda ta b'allani a banza,ita dai Aminar da take y'ar
sukuta ita ce mai k'arfin rik'e me nak'uda amma ba ni ba,kuma ko ba komai idan taji
azabar turaren barkono ita ma ta kasayar da gayad'in da ya cika mata wannan k'aton
tumbin na ta"
Juyawa tayi da hanzari ta fice daga gidan ta koma gidanta tana dariya,saboda ta san
muddin Sunusi ya fito daga d'akin zai iya bajeta ba tare da ta ankara ba😂.
Cancakar Kamilu ya ciccib'o Shafa'atu da tayi balance a k'asa ko'ina na jikinta ya
saki tsabar wahala,uban gumi take sharb'awa wahala ma ta sa ta daina atishawar,sai
wata muguwar rama da tayi har wani gantso ne na musamman ya fito mata,babu abinda a
ke gani a fuskarta sai hak'ora kacarrrrr da su,kumatunta sun lotse sun burma ciki
tsabar wahalar nak'uda da turaren barkono,haka Kamilu ya ciccib'o abar sa ya fito
da ita tsakar gida ya shimfid'eta,da sauri kuma ya d'ebi ruwa yaje ya zubawa
garwashin da ke hayak'i domin ya kashe shi.
Shi kam b'angaren Sunusi kacaniyar d'aga Amina yake yi amma ya kasa,jikinta ya
sake mugun nauyi duk ya saki ta jibge kamar buhun kwaki,fuskarta tayi jajawur kamar
wainar fulawar da ta sha manja😂ko kuma k'osan Angayu 🤣 da k'yar ya iya kamota suka
fito tsakar gida su ma.
A daidata sahu Kamilu ya fita ya nemo har k'ofar gida,ya ciccib'i Shafa'atu da ke
k'ok'arin suma don tafiya asibiti,da shi da Shafa'atun da Amina suka shiga
baya,yayin da Sunusi ya mak'ale a gaba kusa da me tuk'i,nan da nan suka bar
BAHAGON LAYI suka nufi asibiti dan ceton ran Shafa'atu da ke cikin matuk'ar wahala
da azaba,Amina kam zuciyarta bak'ik'k'irin har hango irin babbar fansar da za ta
d'auka kan Harira ta ke.
Basu jima da zuwa asibitin ba Allah ya sauki Shafa'atu lafiya.
***************
Washe gari ne bayan Zahra'u ta kammala aikace-aikacen gidanta tare da taimakon
Nana,sai tayi shiri domin zuwa gidan kitso don aiwatar da k'udrinta bisa sahhalewar
mijinta K'asimu,duk da yadda take jin jikinta yayi nauyi kamar wadda zata haihu a
lokacin hakan bai sa ta hak'ura da zuwan ba,Nanan dai ta sake d'auka domin yi mata
rakiya,nan da nan sai gasu a gidan kitson ba tare da b'ata lokaci ba.
Babbar sa'a tayi,domin kuwa a ranar ma dukkan su suna gidan kitson har ma da
Gimbiyar da aka yi wa tambarin gulma da munafurci,suna tsaye cirko-cirko sun saka
Gimbiyar a tsakiya tana sharar hawaye ana mayar da yadda aka yi,sai balok'ok'o da
masifa suke yi kamar za su daki Gimbiyar,bakin K'udusiyya har kumfa yake yi wajen
kallon Gimbiya tana dungure mata kai da fad'in.
"Munafuka algunguma,idan kere na yawo zabo na yawo ai dole wataran za su
had'u,ranar da muka je gurzar bakinki ai guduwa kika yi muka nemeki muka rasa,to
yau gashi mun tarfaki a dandalin da kike zuwa ki sauke kwandon gulmarki,to
albishinki,ki ce goro,ranar farko da guzurin kashin awaki muka tawo ki kasa muka yi
asarar sa,to yau tattaki muka yi muka samo kashin alade da shi zamu gurje bakin
munafuka,dan haka jummai ku tala min ita ku danne min matsiyaciya ku ga aiki da
cikawa"
Wani irin gigitaccen ihu Gimbiya ta saki tana basu hak'uri a sanda suke k'ok'arin
dannetan,gabad'aya ta gigice dan bata san wane irin hali zata shiga ba muddin
kashin alade ya ziyarci bakinta🤣,haka mai kitso ke ta faman basu hak'uri amma suka
ce idan bata yi shiru ba wallahi za su had'a da ita,ganin da gaske sun danne
Gimbiya da kokawa suna shirin loda mata kashin aladen da suka ce a bakinta hakan ya
sa me kitso ta bud'e murya ta kwarara ihun neman taimako,a dai dai lokacin da
Zahra'u da Nana suka kawo kai cikin tsakar gidan.
Bayan sallamar da Zahra'u tayi sai ta daka musu wata gigitacciyar tsawa tana
basu umarnin su d'aga Gimbiya,cikin mamaki suka tsaya cak suna kallonta,y'ar
k'arama da ita a gabansu da tsohon ciki da alamun ma duk sun girmeta,fuska a d'aure
ta k'araso gabansu tana fad'in "Ku d'aga ta" Sai kuwa suka bi umarnin Zahra'un suka
d'aga Gimbiya wadda ke ta faman shure-shure da ihun neman taimako,tana jin sun
d'aga ta kuwa tayi wuf ta mik'e da sauri zanin jikinta na yararin fitsarin da ta
saki na tsoro,neman hanyar fita take yi kawai daga gidan dan ta tsira,sai da
Zahra'u ta daka mata tsawa akan ta nutsu,sannan ta tsaya jikinta sai rawa yake yi
tana zare idanuwa.
Dukkansu kallon Zahra'un suke yi suna son jin dalilin da ya sa ta dakatar da su
daga aikata k'udurinsu,gyaran murya Zahra'u tayi sannan ta janyo wata kujera da ke
gefe ta zauna dan ba zata iya jure tsayuwa ba,ta umarce su da su ma su zauna,sai
gashi kuwa sun zauna sun zuba mata idanuwa,su kansu mamakin kansu suke yi saboda
sun san babu mai gaya musu suji,ko mazajen su hak'uri suke da su,amma y'ar ficiciya
a gabansu ta zo tana basu umarni kuma suka bi,ita kam Zahra'u bata yi mamakin bin
umarninta da suka yi ba,tasan wannan tasirin addu'a ne,kafin ta tunkaresu sai da ta
rok'i Allah sosai akan ya bata nasara a kansu,tana da burin zama tsani wajen
shiriyar su kamar yadda Allah ya shiryeta a baya,kuma Allah ya ga zuciyarta shiyasa
ya fara bata nasarar,domin tun a fari ta hango za ta cimma nasara da yardar Allah.
Sai da ta ga sun nutsu sosai idanuwansu a kanta sannan ta ce da su.
"Ni suna na Zahra'u,kuma ni y'ar uwarku ce musulma,na zo gareku ne domin nayi muku
nasiha akan tsoron Allah,sannan kuma na baku wani labari wanda nake fatan ya zame
muku izina wajen hango abin da kuke aikatawa ba dai dai ba ne"
Shiru suka yi har lokacin idanuwansu a kanta.Nan Zahra'u ta fara jero bayanai
cike da nutsuwa take fad'a musu illolin abin da suke aikatawa,ayoyi da hadisai ta
dinga janyo musu tana kafa musu hujja da su,tayi rantsuwar cewar ta san dukkansu
babu wadda ta tambayi mijinta kafin ta fito wannan yawon barbad'ar,to su sani cewar
dukkansu suna cikin fushin Allah tare da tsinuwar mala'ikun rahama,ta koma kan me
kitson ita ma ta dinga yi mata nasiha da wa'azi,ta fito mata da laifinta akan cewar
ta fi kowa laifi ita da take tara matan aure a gidanta ana gulmace-gulmace,haka nan
ta dawo kan Gimbiya tayi mata nasiha mai tsoratarwa akan hanin da manzon Allah (S A
W) yayi akan (GIBA) wato cin naman mutane idan basa nan,babu kyau munafurci ko
kad'an,duk mai gulma da munafurci ranar lahira ba shi da rabo mai kyau a wajen
Allah.
Daga nan ne ta gangaro kan cewar ita ma ta d'and'ana irin rayuwar da suke yi a
baya wadda babu alfanu a cikinta sai zubar da mutunci,ta kwashe labarinsu kaf na
BAHAGON LAYI ta basu,sannan ta cigaba da yi musu nasiha akan su gyara halayyarsu su
san mutuncin kansu. Dukkansu babu wacce bata yi hawayen nadama da danasani ba,sun
ji matuk'ar tsoro da kalaman da Zahra'u ta fad'a musu,zuciyarsu ta girgiza,nadama
ta rufe su,sai gasu suna hawaye da neman yafiyar ubangiji akan abin da suke
aikatawa,kuma suka yi wa Zahra'u alk'awarin sun daina da yardar ubangiji,kowacce za
ta cigaba da zama gidan mijinta bisa doron yadda shari'a ta shimfid'a,sun daina
yawace-yawacen da suke yi,haka nan Gimbiya ma ta ce ta daina gulma da munafurci,ita
ma me kitso tayi nadama ta ce in sha Allahu ta daina tara mata a gidanta ana gulma
da munafunce-munafunce.
Zahra'u taji matuk'ar dad'i a ruhinta ganin ta silarta matan duk sun yi nadama,a
gaban idanunta kowacce ta tashi ta tafi gidan ta,ita ma tayi sallama da me yin
kitson ta kamo hannun Nana suka dawo gida zuciyarta k'al cike da farinciki da
murna.
A yammacin ranar ne kuma ita ma Allah ya sauketa lafiya ta samu jaririn ta
namiji,ba tare da wata doguwar nak'uda mai wahalarwa ba.
*************
To kuma dai a yammacin ne Allah yayi dawowar Saratu cikin BAHAGON LAYIN a karo
na biyu,wadda ta tawo da niyyar zaman aure na hak'ik'a da yi wa miji biyayya bakin
iyawarta,babu ko d'iso a ranta na sha'awar maimai ta rayuwa irin ta baya,da gaske
ta dawo da k'arfinta wajen mayar da hankalinta kacokam kan rayuwar aurenta,ko ta
samu ta gyara laifuffukanta na baya.
Harira tun da taji labarin dawowar Saratu take zakwad'i da murna,nan da nan
ta jany o gyale ta fito daga gida dan ta je ta ganewa idanuwanta abokiyar shan
mirinda 😂 daman Amina ma bata nan tana gidan mai jego Shafa'atu,tun safe ta
fita,dalilin da yasa ita kuma tak'i zuwa gidan Shafa'atun taji labarin dangin Shafa
sun ce sai sun ci ubanta tun da tayi mata turaren barkono ta wahalar da ita wajen
nak'uda,hakan yasa tak'i shiga saboda kar suyi mata( walmukalifatu😆)ta bari ne sai
ranar suna ta sake shiga ta san tunda taron suna ne babu mai tab'a ta.
Da hanzarinta ta shige gidan Saratu tana kwad'a sallama da ambatar "oyoyo kina ina
ne abokiyar shan mirinda?"
Saratu da ke zaune a gaban Hajiya maimuna tana k'ara yi mata nasiha,jin muryar
Harira sai da gabanta ya fad'i,kwata kwata bata son wata alak'a ta sake shiga
tsakaninta da Harira,domin a baya ma duk ita ce musababbin b'ata musu rayuwa,Harira
na shigowa bakinta a washe ta tsuguna tana gaida Hajiya maimuna,sannan ta gaida
Saratu a zatonta wata goggon Saratun ce saboda yadda taga sunyi kama sai dai wannan
tsohuwa ce,gabad'aya tunaninta bai bata cewar Saratun ba ce😆 sai da ta gama
gaishesu sannan ta cigaba da k'wala kiran Saratun tana fad'in "Amarya ko lab'ewa
kikayi a d'aki ne?fito man na ganki an dad'e ba'a had'u ba k'awar shan mirinda"
Hajiya maimuna ce cikin d'aure fuska ta dubi Harira ta ce.
"Alamu sun nuna min kece Harira duk da ban tab'a ganinki ba,to k'awar shan mirindar
da kike kira ai gata a gabanki,da alamun kema baki shaidata ba kenan a karon farko
ko?saboda lalacewar da tayi,kuma ke ce musababbi,to bari kiji na fad'amiki,Saratu
ta dawo gidan mijinta ne dan tayi zaman aure na hak'ik'a ba yawon barbad'a ba,kin
san Allah idan baki fita daga harkarta ba to Kuliya manta sabo ne zai raba mu da
ke,daga yau kar na k'ara ganin lagutsattsiyar k'afarki cikin gidan nan dan
ubanki,shegiya gafalalliya mara tunani da hankali,duk shakiyancin da kika yi a baya
kika ga darasi har yanzu baki yi hankali ba,ke wace irin mace ce?to ahir d'inki ki
fita harkar Saratu idan ba haka ba ba k'aramin shiri muka yi a kanki ba,Salisu ma
kad'ai ya isa ya ci ubanki wallahi"
Takaici ya ishi Harira,haka kawai kowa sai a dinga d'ora mata laifi?to kuwa wallahi
hakan ba zata sab'u ba bindiga a ruwa,dole ta d'auki mataki akan hakan.
Korar kare Hajiya Maimuna tayi wa Harira,haka ta tashi ta fita k'afafu a
sanyaye,ita da take ta murna Saratu ta dawo domin ta samu su had'a kai da Saratun
da Habiba suyi shawarar yadda zata fitar da Amina daga gidanta,sannan kuma su
d'auki fansar yadda Idrees ya wulak'anta su,to amma ga wankin hula yana neman kai
ta tsakar dare.
Tana komawa gida ta tarar da Amina ta dawo,tana durk'ushe tana wankewa Sunusi
kayansa,dan tsokana irin ta Harira kawai sai ta nufi gaban Amina ta sa k'afa ta
shure bokitin ya fad'i kumfar ta zube,A fusace Amina ta d'ago daman a cike take da
Harirar,dundumemen hannunta ta fitar ta faskawa Harira mari me shiga kwanya😂 wani
azababben zafi ya mamaye Harira tun daga kai har zuwa k'afafu,zaro idanuwa tayi
tana cukumar Amina dan k'arfin hali irin na Harira wai ba zata yarda ba,Amina ta ce
mata "Idan dai ba so kike na tsige miki ragowar hak'oran da ke bakinki ba to dan
jakar ubanki ki sake ni"
Harira ta fara kokawa da Amina tana fad'in "Ba zan sakeki ba dan .....uwarki,akan
me zaki d'auki hannunki me kama da k'irgi ki lafta min a fuska?wallahi ba zan yarda
ba sai na rama"
Nan da nan kokawa ta rincab'e a tsakanin su,daman Amina damar da take son samu
kenan,gashi tayi sa'a gidan babu kowa babu me k'watar Harira,nan da nan ta fara
kilar Harira nata kai mata naushi,Harira ta fara jin azaba tayi kukan kura ta tura
kanta cikin hammatar Amina ta sa gefen bakinta da yake da ragowar hak'ora ta cafko
fatar hammatar tana cizga 😆 Amina kuwa hannunta ta mak'e ta kaiwa kumatun Harira
naushi,sai ga Harira na gurnani tana neman fito da kanta daga hammatar Amina 😂
azaba ta ishi Harira ta d'aga hannunta ta kaiwa k'irjin Amina duka,nonuwan Amina
suka d'auki zugi kamar ta saki fitsari,ai bata san lokacin da tayi wurgi da Harira
ba,Harira bata sauka a ko'ina ba sai kan murfin rijiya,murfin ya goce sai ga Harira
tsundummmmmm cikin rijiya 😳😂😆
Dai dai lokacin da Sunusi ya rangad'a sallama ya shigo gidan,akan idanuwan sa Amina
ta cilla Harira cikin rijiya...😂
Comment
share
vote
pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*BABI NA ASHIRIN DA TARA DA NA TALATIN*
PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️
*BARKAN MU DA SALLAH Y'AN UWA MUSULMI NA DUNIYA,ALLAH YA MAIMAITA MANA YA KARB'I
IBADUNMU* 😍
***Sunusi ya d'ora hannu aka ya rafka salati da k'arfin murya yana zare idanuwa
kamar mage a kwali, da wani irin hanzari kuma ya d'ebi k'afafuwan sa zuwa gindin
rijiyar kamar ya kifa,yana lek'a kansa ciki idanuwansa suka gane masa Harira saman
ruwa sai facal -facal take ,ta rasa yadda zata yi.
Juyowa yayi yana duban Amina fuskarsa d'auke da mad'aukakin tashin hankali,ga
mamakinsa sai yaga Aminar ta juyar da kai alamar ko a jikinta ma abinda ya faru,sai
ma tsugunawa da tayi tana tattara kayan da take wankewa wad'anda suka zube a
k'asa.Sunusi bai san lokacin da ya daka wa Aminar wata razananniyar tsawa da ta
saka ta d'agowa a firgice ba,cikin b'acin rai yake kallon ta yana magana.
"Wai Aminatu anya kina da hankali kuwa?ko baki ga abin da kika aikata ba ne?an
fad'a miki kishi Hauka ne da zaki d'auki Harira ki cillata cikin rijiya?yanzu har
kishin da ke k'irjinki ya kai tunzira zuciyarki wajen aikata kisan kai Amina?"
Sai lokacin gaban Amina yayi wata irin fad'uwa jin maganar kisan kai,a zahiri
dukkan wani laifi Harira ce me dakonsa,amma idan silar fad'awar Harira rijiya y
janyo ajalinta babu wanda zai dubi baya ya hango laifin Harirar,illa ita da za a yi
ta yamad'id'i da ita cewar ta kashe kishiyarta saboda kishi,gidajen redio da
talabijin da y'an jaridu su samu abin yi,dumiya tayi mata tofin ala tsine duk da
cewar ita ke da gaskiyar,kowa ya tsaneta ,daga nan ta k'are rayuwar ta a gidan
yari cikin takaici da bak'in ciki,to me gari ya waya kenan?.
Bata san lokacin da wasu hawaye suka ratso idanuwanta ba ,cike da tsoro ta
matsa kusa da Sunusi da ke gindin rijiyar ta kamo hannunsa jikinta na mugu mugun
rawa,cikin saurin baki ta soma magana tana hawaye.
"Wallahi ni ba da gayya nayi hakan ba,ita ce tazo ta kamani da