Advertisements
Chapter 7 Reading Bahagon Layi Sabon Salo by TARE DA ALK'ALAMIN BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bahagon Layi Sabon Salo by TARE DA ALK'ALAMIN

Author :  TARE DA ALK'ALAMIN Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 9

18K to 21K   out of 26.5K words

zai faru sai alkairi,Allah zai dubi niyyata ta alkairi ya bani
nasara akan k'udurin zuciyata,ina kishin in ga y'an uwana mata suna wannan rayuwar
ta tumasanci wallahi,tunda na d'and'ana irinta babu komai cikinta face wulak'anta
kai da zubewar mutunci had'i da sab'awa Allah,don haka ni dai idan har kayi min
izini zan yi wannan jihadin,kuma ina da yak'inin in sha Allahu Allah zai bani
nasara akan niyyata".

K'asimu yaji dad'in bayanan da Zahra'u tayi,hakan ya sa ya runtse hannuwanta cikin
nasa idanuwansa a kanta yana murmushi ya ce.

"Na yi miki izini Uwar gidana,Allah yayi miki jagoranci akan niyyarki ta alkairi".




*************




*‫*فصل ف الحيض‬
(Fasali a cikin Haila)

Wannan shine darasin da Malam Arabi yake biyawa d'alibansa da suka kasance sun fara
zama y'ammata,a cikin littafi (Ahalari),ya zage sosai yana ta jera musu bayanai ta
yadda za su fahimta,hatta wankan hailar sai da ya koya musu tare da bayanin wadda
ta saba da wadda ta fara, to da yake karatun ya shafi wani b'angare na kunya duk da
dai babu kunya a cikin addini,sai d'aliban suke ta sunkuyar da kai suna dariya
k'asa- k'asa. Tun Malam Arabi bai gane dariyar da suke ba har dai da ya fad'i wata
kalma sai yaji an shek'e da wata y'ar iskar dariya,a fusace ya d'ago kansa yana
kallonsu sai duk suka sunkuyar da kai k'asa,sosai ransa ya b'aci ya mik'e tsaye
yana muzurai ya dube su ya ce.

"Wace Shakiyyiyar ce take min dariya a aji?".

Tsit suka yi babu wacce tayi magana,ya d'ago bulalar hannunsa zambad'ed'iya ya nuna
su da ita cikin fushi ya sake ce wa.

"Ba magana nake da ku ba?nace wace shakiyyiyar ce take min dariya a cikin aji?Za ku
fito min da ita ne ko sai na had'aku nayi muku wankan jego?Kun san dai ni ba'a yi
min had'in kan tunkiya ko?gara tun wuri ku fito min da ita a cikin ku kafin in
tsamama muku jikin ku"

Wasu da yawa daga cikinsu sai da gabansu ya fad'i jin Malam Arabi ya ambaci wankan
jego,duk lokacin da ya ambaci wannan kalmar to fa ya shirya tsiya ne,domin wankan
jego na nufin ya rufe mace da duka ko ta ina baya ji baya gani,hakan ya sa hankalin
su ya tashi sosai,sai dai kuma suna tsoron su tona wadda tayi dariyar,saboda
Azara'u ba k'aramar masifaffiya ba ce,duk wanda ya tona ta idan aka tashi daga
makaranta za ta iya tare mutum a lungun (kaci uwaka) ta jibgi banza,shiyasa kaf
ajin tsoranta ake yi.
Ganin sunyi shiru sai Malam Arabi ya jijjiga kai ya nuna wata d'aliba mara
yawan magana,saliha ce sosai,yace da ita "Ke Salama mik'e tsaye" ,A rud'e Salama ta
mik'e jikinta na rawa sosai,ya kalleta yace mata.
"Duk ajin nan da ke kad'ai na yarda zaki fad'a min gaskiya,dan na lura sauran y'an
ajin duk taron munafukai ne,bud'e bakin ki ki fad'a min wacece tayi dariya ina
karatu?"

Salama tayi tsuru -tsuru ,musamman da suka had'a ido da Azara'u ta dank'ara mata
harara alamun kar ta sake ta fad'a,idan ba haka ba ta san sauran,ganin tayi shiru
sai Malam Arabi ya ce.

"Ashe dai kema kin zama munafukar ko?to babu shakka kuwa yau zan miki wankan jego
na hak'ik'a idan baki bud'e baki kin fad'a min gaskiya ba".

Babu yadda Salama ta iya,haka ta bud'e bakinta yana rawa tayi magana.

"Malam Azara'u Lawan ce tayi dariya"

Gabad'aya y'an ajin sai da suka kalli Salama a tsorace,ita kuwa mai ya kaita tonawa
Azara'u masifa asiri?lallai yau jikin Salama zai yi tsami kenan,ita kam Azara'u
jijjiga kawai tana hango yadda zata shak'e Amina ta lodeta,yayin da Malam Arabi ya
bawa Salama umarnin zama,sannan ya kalli Azara'u ya bata umarnin ta mik'e tsaye,da
k'yar ta mik'e sai wani ciccin magani take tana botsaro baki gaba da jijjiga
jiki,ya k'are mata kallo tsaf sannan ya tanka.

"Ke ga fitsararriya ko?ina karatu a aji kina dariya,idan ubanki ne yake koya miki
karatun za ki yi dariya ne?"

Cikin rashin kunya Azara'u ta ce.

"Ni gaskiya malam ka daina ambato mahaifina dan kuwa yana k'abari a kwance,dariya
kuma ai ita tazo da kanta bani na gayyato ta ba,akan me zan koreta ta koma na k'i
yi?"

Wani takaici ya kama Malam Arabi,cikin matuk'ar fushi ya ce.

"Ni zaki kawowa tijara da d'ibar albarka?ko nayi miki kama da sa'an wasanki,to dan
ubanki fito nan ko in zo nan in miki wal mukalifatu,domin naga d'umaninatu
(nutsuwa) bata wadace ki ba"

Kawar da kai tayi tana shan k'amshi,kafin kuma ta fara takowa tana tafiya cikin
izza da tak'ama,har ta takewa wata daga cikin y'an ajin hannun ta da ke k'asa.

"Wash ! shine abin da Shukra ta fad'a tana yarfe hannu fuskarta a b'ace dalilin
azabar da ta rasa yatsun hannunta,cikin jin zafi ta dubi Azara'u da tayi gaba ta
ce.

"Azara'u baki lura bane kin take min hannu?"

A fusace Azara'u ta juyo ta gallawa Shukra harara,cikin masifa ta ce.

"Na taka d'in ko kina da matakin da zaki d'auka ne?"
Shukra ta sunkuyar da kai k'asa a tsorace bata ce komai ba,Azara'u ta saki mugun
tsaki sannan ta juya ta nufi Malam Arabi da ke tsaye yana kallon iskancin da
take,tana zuwa ta tsaya masa k'erere a ka bata tsuguna ba,ajin yayi tsit kowa ya
zubawa Malam Arabi da Azara'u idanu ana jiran ganin abin da zai faru.

Malam Arabi ya shammaci Azara'u ya d'aga lafceciyar bulalarsa da ya shafe ta da
manja ya zumbud'a mata a gadon baya,wata zambarwa tayi ta durk'ushe k'asa ba tare
da ta shirya ba,sosa bayanta ta shiga yi idanuwa a waje ta kalleshi ta ce.

"Kai kai kai ! me nayi maka za ka dake ni?"

Malam Arabi ya ce.

"Ban sani ba mara kunya fitaararriya,saboda baki da ladabi da biyayya ni zaki zo ki
tsayawa k'erere a ka?to yau zan sauke miki tashen balagar da yake damun ki dan
gidanku"

D'aga bulalar yayi zai sake zumbud'a mata,wuf ta mik'e a gigice ta rik'e bulalar
jikinta na rawa,cike da fitsara take dubansa ta ce.

"Na rantse da girman Allah ka sake dukana za ka ga abin da zai faru"

Takaici ya sake kama Malam Arabi,yayi yayi ya fizge bulalar amma Azara'u ta rik'e
gam tak'i saki,hakan ya fusata shi ya d'aga hannu ya dalla mata wani gigitaccen
mari da ya saka Azara'u sakin k'atuwar k'ara da ta firgita y'an ajin,take kuma ta
fad'i kwance a k'asa tana shure -shure da bige-bige tana sakin wani irin
yare,alamar dai Aljanu ta tayar.

A tsorace y'an ajin duk suka mik'e tsaye,Malam Arabi ya daka musu tsawa akan
kowacce ta nemi waje ta zauna,jikin su na rawa duk suka koma loko suka takure suna
kallon Azara'u da ke iface -iface da birgima.

Malam Arabi kallonta yayi ya nad'e hannun rigar sa yana fad'in " Ni zaki kawowa
iskanci da an dakeki ki fad'i kina birgimar k'arya wai ke Aljanu,da ke da Aljanun
kun ci bantan ubanku,kuma yanzun nan zanyi maganin tak'adirancin ku"

D'aga bulalarsa yayi iya k'arfinsa ya zulawa Azara'u a k'irji saitin nonuwanta,ta
saki wata irin k'ara da zambarwa,ya sake d'agawa ya nufi bayanta dai dai mazaunata
ya tsula mata,nan ma wata irin mik'a tayi ta saki bahaguwar k'ara,haka Malam Arabi
ya dinga lodar Azara'u,kuma babu in da yake duka sai k'irjinta da mazaunanta.
Idanuwansa sun rufe wajen tafkarta har bai ankara da sanda tayi zambarwa ta
mik'e ba,kawai ji yayi kamar wanda aka d'aga sama cak,sai kuma yaji an yi wurgi da
shi😂 bai tashi tsintar kansa ba sai a tsakiyar d'alibai 🤣 durum ya ji shi ya sauka
akan muk'amuk'in wata d'aliba,yayin da gabad'aya d'aliban suka razana suka dare
suna ihun tsoro,ita kam d'alibar da ya danne wani azababben ihu ta saki jin tamkar
mak'ogoron ta zai cire😂Malam Arabi yayi ragajeje kan mak'oshinta,da k'yar ta samu
ta ingije shi musamman da ta samu ta gallara masa mintsini.

Ita kam Azara'u da ke tsaye nufoshi tayi gadan -gadan,hankalinsa a tashe ya fara
matsawa yana zazzaro idanuwa,d'alibai suka kwasa da gudu suka fice daga ajin suna
ihu da kiran sauran ragowar malaman,Malam Arabi dai tsintar kansa kawai yayi a
hannun Azara'u ta shak'o wuyansa😂 bata yi wata -wata ba ta samu rungumemen kansa
ta garashi da garu,azabar da ta ratsa tsakiyar kan malam Arabi har bai san lokacin
da wata lukutar Atishawa ta fito masa ba,ji kuke (ekichifffffff 🤣),a loko Azara'u ta
matse shi,yayin da yatsun ta guda biyu suka matse mak'wallaton da ke wuyan sa ta
shak'e shi 😂 ,kakari yake sosai idanuwa a warwaje yana fad'in "Ya
Subahanallah...Innalillahi salasa....inna atuni minal tona tone....😂"

Malam Arabi ya hango lahira,cikinsa ya hargitse,sai ga wata irin gudawa(zawayi) mai
shegen d'oyi ta zubo yarrrrrrrrr a wando 😂😂😂.
Comments
Share
Vote
Pls




*BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️



*BAHAGON LAYI*

(SABON SALO)


*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA


*BABI NA ASHIRIN DA BIYAR DA NA ASHIRIN DA SHIDA*


PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️


#SANARWA👇
*NI D'IN MAI YAWAN SABGOGI CE DA UZURURRUKA,HAKAN YA SA KWANA BIYU KUKA JI NI
SHIRU,AYI MIN AFUWA👏 KUMA IN SHA ALLAHU ZAN TAK'AITA LABARIN DAN MUYI SAURIN
KAMMALAWA KAFIN RAMADAN,GODIYA NAKE MASOYA* 🤝🥰




***Saura kad'an numfashinsa ya bar gangar jikinsa tsabar shak'ar da ya ji.Shigowar
ragowar malaman makarantar cikin ajin da sauri shine ya ceto malam Arabi daga
hannun Azara'u.

Da k'yar malamai guda uku suka k'wak'ule hannun Azara'u daga wuyan malam
Arabi,tana ta fizge - fizge da ihu da kururuwa,ragowar d'alibai suna tsaye daga
wajen ajin kowacce idanuwa a warwaje cike da matsanancin tsoro,fad'uwa k'asa
Azara'u tayi tana shure - shure da wasu irin maganganu,wai wallahi ba za su yarda
ba tunda malam Arabi ya dakar musu Nono da d'uwainiya,sai sun d'auki fansa.

Shi kam gogan yana jin an raba hannun Azara'u da wauyansa sufa yayi ya silale
a jikin malam Jibrin sai mirgina kai yake,da k'yar yake iya magana yana fad'in.

"Malam Jibrin duba min wuya na akwai mak'wallato kuwa?ko dai ta gutsire min shi?"

Takaici kamar ya kashe malam Jibrin saboda haushin malam Arabi,tunkud'e shi yayi
daga jikinsa ya fara masifa cikin rawar baki har ba'a fahimtar abin da yake
fad'a,da yake yana da saurin magana da in ina,shiyasa ma d'alibai har suna suka
saka masa wai ( Malam Abirbireshan😆).

Cikin masifa malam Jibrin ke fad'in.

"Allah ya sa beli ta cire maka ba mak'wallato ba,Arabi baka jin magana
wallahi,kwanaki har meeting muka yi a kanka akan wannan muguwar d'abi'ar ta ka ta
dukan mata a jiki,har doka mun kafa maka akan duk dukan da zakayi kar ya wuce yin
sa a hannu,ba'a ko'ina ake dukan mace ba,amma dan taurin kai ka k'i ka daina,har
wani alfahari kake da fad'in zaka yiwa d'aliba wankan jego,wannan ba k'aramin
iskanci ba ne da batsa,haihuwa suka yi da za ka dinga fad'in za ka yi musu wankan
jego?ko kai unguwar zoma ne?haka kawai kana zubar mana da k'imar makaranta ba gaira
ba dalili,saboda tsabar iskanci ka rasa in da zaka dinga dukan mace sai a k'irji da
mazaunai,wannan d'abi'ar malamin k'warai ce?to wallahi ba zamu lamunci wannan
ba,dole mu d'auki mummunan mataki a kan ka"

Malam Arabi yayi k'us sai zare idanuwa yake,wandon sa taf da zawayi duk d'oyi ya
cika wajen😂,hannunsa bisa wuyansa sai murzawa yake.

Ragowar Malaman tuni suka janye Azara'u gefe suna tofa mata addu'o'i,har Allah yasa
komai ya lafa ta fara dawowa nutsuwar ta,sai sharb'a gumi take,d'alibai suna ganin
ta mik'e zaune kowacce ta d'iba da gudu suka ranta ana kare,kowacce tayi hanyar
gidan gyatumin ta,Azara'u na waiwayowa suka had'a ido da malam Arabi,wata uwar
harara ta zabga masa,da sauri ya d'auke idanuwansa ya juya mata k'eya cikinsa na
k'ara karta masa tsabar tsoro,kuma kamar wanda aka d'aurewa k'afafu gabad'aya ya
kasa mik'ewa tsaye,ko yana gudun kar gudawar ta zubo ne oho!

Malam Zulyadaini ne ya fita yaje babban ajin y'ammata ya samo d'alibai guda biyu
wad'anda ya umarcesu su raka Azara'u har gida,haka suka rik'eta duk da su ma a
tsorace suke,suka fita da ita domin raka ta gidan.

Suna fita nan fa malamai suka rufar wa malam Arabi da fad'a kamar su cinye
shi,Malam Tukur shugaban makarantar fad'i ya ke.

"Mun gaji da halinka wallahi,duk yadda muke ji a bakin d'alibai cewar kai d'an iska
ne ban tab'a yarda ba,amma yau na yarda da maganar su,kwanaki nan Malam Jibrin yake
fad'a min cewar ranar da Batula Kabiru ta tayar da aljanu kai ne me k'ok'arin danne
ta,yace min yana lura da kai banda latse mata k'irji babu abin da kake yi,ban yarda
da maganarsa ba saboda ina ganin kamar kuna y'ar tsama ne shine zai maka
sharri,haka nan ranar da Bushira ta zo makaranta tana ciwon kai suka bugar da ita
ta dinga ihu tana birgima ina kallonka har da rawar jiki ka fito daga ajinka tsabar
tsugudidi ka nufi ajin da take,akan idanuwana ka saka hannayen ka ka danne mata
mazaunai wai dan ta daina birgima,nan na k'ara tabbatar da cewar tabbas kai d'an
iska ne lamba d'aya,yanzu kuma kazo kana dukan d'alibarka a k'irji da
bayanta,saboda haka kayi na farko,kayi na biyu,yanzu kayi na uku,wallahi duk randa
kayi na hud'u sai ka bar makarantar nan,kuma sannan sai mun had'a ka da hukuma
domin a gyara maka zama"

Kunya ta ishi malam Arabi kamar ya nutse,ashe duk abin da yake yi malamai da
d'alibai na lura da shi kenan,tabbas amma yayi asara,haka suka sanya shi a gaba da
fad'a da tijara,idan wannan yayi ya gama sai wani ya kama,har dai daga k'arshe
Malam Jibrin yayi magana a fusace cikin in ina.

"Ttttt tashi ka kka bamu guri,jajj ja'iri fitsararre,kakkka cika mu da d'oyi dad da
samami,d'annnnnn iska kawai"

Mik'ewa malam Arabi yayi da k'yar cike da kunya kansa a sunkuye,dukkan su suka
toshe hanci suna hararasa,haka ya dinga jan k'afafu a hankali saboda yadda zawayin
yake biyo k'afafuwan sa,har ya fice daga ajin ya nufi gida.




**************


Isar sa gida ya tarar har Angayu ta fara bacci,shigewa yayi cikin d'akin girki
yana karafniyar duba ruwan zafin da zai wanke jikinsa,motsin da Angayu taji ya sa
ta farka a firgice tana tambayar .

"Wanene anan ne?"

Shiru yayi mata ya cigaba da dube-duben sa,ta sake d'aga murya tana da k'arfi ta
sake ce wa.

"Wai ba magana nake ba?nace wanene a nan yake min bud'e-bud'e?"

Da k'arfi malam Arabi ya d'aga murya a fusace ya ce.

"Ban sani ba,ki fito idanunki ya gane miki mana,mtswwww ,aikin b'ur in ji tusa
kawai"

Da hanzari Angayu ta wartsake jin muryar mai gida,ta kalli agogo tana mamakin har
yaushe ya shigo?bata san ta fara gyangyad'i ba ,tashi tayi ta fito tsakar gidan
tana hamma da mik'a,a lokacin shi ma ya fito daga d'akin girkin yana tsaye a tsakar
gida ya tala k'afafu ya cakari k'ugu,jikinsa duk ya dameshi zawayi kaca-
kaca,dubansa tayi tana sosa k'eya ta ce.

"Yi hak'uri malam ni ban ma ji shigowarka ba,gyangya.....

"Kina baccin asara daman ai ba zaki ji shigowata ba,ni dalla malama zo ki bani
ruwan zafi zanyi amafani da shi" ya katseta cikin sababi da kumfar baki.

Sai lokacin Angayu taji wani bala'in d'oyi ya cika tsakar gidan,toshe hanci tayi
tana fad'in.

"Malam wai baka ji wani mugun wari na tasowa ba?ko dai mushen bunsuru aka yar mana
a soro yake wannan warin?"

Cikin k'ufula malam Arabi ya ce.

"Mushen alade ne ba na bunsuru ba,ban da ina cikin wani yanayi tsaf idan na naushi
bakinki sai ganda ta fi shi kyan gani,tsabar wulak'anci nace ki bani ruwan zafi kin
tsaya yi min suratakai?yanzu da kika tsaya min a ka kina susar kwarkwata zaki bani
ruwan zafin ne ko kuwa?"

Ita dai Angayu mamakin uwar jarabar da malam Arabi yake zubawa take,lafiya lau
ya fita amma ya dawo mata da tijara,koma wa cikin d'aki tayi ta d'auko fitila dan
ta haska ta d'ora masa ruwan zafin,tana isowa dab da shi wani arnen wari me juya
kwanya ya buge ta,haske shi tayi taga yadda yake gumi sai k'walala idanuwa
yake,hannayensa rik'e da wandon jikinsa,k'asa ta haska sosai sai taga bakin wandon
jikinsa sai d'iga yake yi duk ya b'ata wajen da kashi,sakin fitilar tayi a k'asa
tayi baya da sauri tana d'ora hannu aka cikin kwaroroto ta ce.

"Malam me zan gani haka? kashi kayi a wando?"

Da yake malam Arabi cikin b'acin rai yake,ga Angayu na k'ara bak'anta masa,bai ma
san lokacin da ya ce mata " Ah ah ba kashi nayi ba,Tirmizi nayi" .

"Kan ubancan kayyasa" Angayu ta ambata da sauri,sannan ta d'ora da ce wa.

"Daga tambaya sai ka ambaci sunan ubana,to ko ba komai dai shi Tirmizin da ka
ambata ya fika daraja tunda kuwa ya ci sunan mai rawaito hadisai,kai kuwa ko a
majamu'ul bahraini banga in da sunan Arabi ya samu fitowa ba,ruwan zafi ne kuma ba
zan d'ora ba tunda abin na ka cin mutunci ne"

Tana fad'in hakan ta koma ta shige d'akinta,ta bar malam Arabi yana ta jaraba da
masifa,da jarabar ta ishe ta sai ta mai da shi mahaukaci ta dinga tuntsira masa
dariya tana mak'e murya har da raira masa wak'a,wai " Arabi me kashin wando" .

Da haushi ya k'ume shi tilas ya janyo bokiti ya fara d'iban ruwa a rijiya domin
wanke jikinsa da ya dame shi da k'aik'ayi,cikin d'aga murya kuma yayi magana yadda
Angayu za ta jishi,ya mayar mata da raddin ce wa.

"In dai kashin wando ne Uwarki ma da tana yarinya ai tayi 🤣.




**********


Misalin k'arfe tara da rabi na daren,Sunusi da Amina zaune a k'ofar d'akin
Aminar suna shan iska,sai hira suke yi cike da nishad'i da soyayya,Amina na yankewa
Sunusi farce shi kuma yana haska mata da fitilar wayar sa.

Ita kam Harira tana daga gefe zaune ita ma a k'ofar akurkin d'akinta,sai wak'e-
wak'en habaici take amma sun mata banza sun nuna ma basu san da ita a wajen ba sai
hirarsu suke suna tuntsira dariya,hakan ya sake b'atawa Harira rai sosai.

A tsorace dukkansu suka d'ago jin an fad'o tsakar gidan da gudu,Kamilu ne yana haki
duk ya had'a uban gumi sharkaf,Amina da Sunusi suka mik'e da hanzari suna tambayar
sa "Lafiya?"

A rud'e ya ce musu.
"Ku taimaka mu kai Shafa'atu asibiti,gata can sai nak'uda take ta wahala sosai har
k'arfinta ya k'are"

Harira ce ta fara zabura da gudu tayi hanyar waje tana fad'in "Wayyo k'awata ashe
an zo wajen" kafin ma su farga tuni har ta fice ta nufi gidan.

Amina ce ta d'auko hijabinta ta sanya,duk suka fito har Sunusin suka nufi gidan
Shafa'atun,Amina ta dubi Kamilu tana fad'in.

"Yaya Kamilu ai da ka sani Umma kayi wa waya ta tawo,kaga duk cikin mu yaran mata
ne babu wadda ta san kan yadda ake haihuwa"
Shi dai Kamilu da yake a rud'e yake bai ce komai ba,sai Sunusi ne ya ce "Gaskiya
dai kam haka ne,bari muga yanayin halin da take ciki in ma asibitin ne kawai sai a
samo d'an sahu mu wuce"

A dai dai lokacin suka shiga gidan,suka tarar da Shafa'atu sai juya kai take azaba
ta ishe ta,ga Harira tsugune a gabanta sai zabga mata sannu take yi,Harira na
ganinsu karaf ta mik'e ta dubi Kamilu ta ce.

" Yawwa Kamilu ai tana dab da haihuwa ma,a samo garwashi wani turare zan mata yanzu
za ta haihu da kanta in sha Allahu,ni ma da na zauna

7 / 9