Author : TARE DA ALK'ALAMIN Category : Complete Novels
ya soma rawa saboda ta san jarabar Idrees,ba k'aramin aikinsa bane ya
dalle ta da mari,gashi dai d'an tsurut da shi sai shegen zafin hannu,dan k'annensa
ma har wani kirari suke masa da (me hannun kunama)dan idan ya mareka sai kaji kamar
kunama ce ta d'alle ka a kumatu,sassauta murya tayi jikinta na tsuma ta ce.
"Don Allah kayi hak'uri Hubby,wallahi ban gane abun da kake nufi ba ne shiyasa,amma
ina neman afuwarka".
Ganin yadda ta marairaice sai yayi tsaki ya d'an sassauto ya dubeta ya ce.
"Wannan matar mara kyan fasali nake tambayarki,wacece ita?kuma daga ina take?wajen
wa ta zo?" Ya jero mata tambayoyi idanuwansa a kanta.
Hauwa cikin inda inda ta fara yi masa bayanin An gayu,bata ma kammala ba taga
Idrees ya mik'e a sukwane yana muzurai,bai tsaya bin ta kanta ba kawai ya nufi
falon da sauri,k'irjin Hauwa ya bada rasss! a hankali ta juya ta bishi falon
jikinta sai rawa yake.
Idrees na fitowa ya tarar da An gayu har da kashingid'a kan kujera tana lumshe
idanu taji laushin (kushin),ya kwaye murya ya daka mata wata razananniyar tsawar da
ta firgita ta,sai ga An gayu ta bud'e idanu a gigice tare da fad'owa k'asa daga kan
kujerar rigijibbb!
"Ke ! me ya kawo ki gidan nan dan ubanki?"
An gayu ta razana sosai ,bata san lokacin da ta d'aga hannu sama bakinta na rawa ba
ta ce.
"K'arar kwana....!
Idrees ya k'ara tamke fuska yana nuna ta da yatsa ya ce.
"Idan k'arar kwana bata kawo ki ba k'ila rabon wahala ne ya kawo ki,baki da labarin
na hana shigowa gidan nan ne?ko baki da labarin duk wanda ya shigo gidan nan baya
fita k'alau sai ya karb'i kid'an janaral?to bari kiji in fad'a miki kin kawo kanki
in da zaki karb'i tsarabar kulki da tiyagas".
An gayu ta d'ora hannu aka ta rafka ihu had'e da salati,cikin kuka ta ce.
"Ranka shi dad'e dan Allah kayi hak'uri,wallahi ni zumunci ne ya kawoni ba gulma ko
kinibibi ba,don Allah kayi min rai in sha Allahu ba zan sake shigowa ba" ta juya
tana kuka tana kallon Hauwa tana rok'onta akan ta bawa Idrees hak'uri,Hauwa tayi
shiru domin ta san idan tayi magana bala'in kanta zai dawo,sai dai sosai An gayu ta
bata tausayi ganin kukan da take sharb'a,sai shab'une take fuskar tayi dama dama da
hawaye da majina,hakan ya k'ara fusata Idrees ya cigaba da masifa da hargowa.
"Ke dalla malama rufe mana baki,in dai jumurinku bibiyar gidajen al'umma za ku jima
kuna cin na akuya kuwa,y'an iskan mata magulmata munafukai,wutarku daban take ko a
lahira matsiyata,wallahi ba don ina ganin mutuncin mijinki ba da sai na sa ammiki
fiye da abin da na sa aka yiwa tinkiyoyin baya,sai na sa an zagargazaki fiye da
inda bakya zato,k'azamar banza k'azamar wofi cikon benci cikon lissafi,tashi ki
kwashi tsalolin k'afafuwanki masu kaushi da faso ki fice min daga gida tunda ba da
gadon gyatuminki aka had'a aka kama hayar gidan ba"
A gigice An gayu ta mik'e har zanin jikinta na niyyar salub'ewa ya fad'i
k'asa,garin ta ja zanin sai ya hard'eta ta wuntsila ta kifa a k'asa,tsawa Idrees ya
sake sakar mata wadda ta yamutsa mata y'ay'an hanjinta sai ga wata k'atuwar tusa ta
fito b'urrrrrr.....b'urrrrr...b'urrrrrr...... wani azababben d'oyi ne ya daki
hancin Idrees ya zabura yana toshe hanci cikin zare idanu ya ce.
"Kutumar uban can,ke dan kan uwarki anan zaki mana rihi? Ya juya kan Hauwa da itama
ta toshe hancinta saboda d'oyin da ya cika falon har mak'ak'i take ji a mak'oshin
ta, daka mata tsawa yayi ya ce.
"Ke shiga d'aki ki mik'o min wayar cajar nan da alamun matar nan sai jikinta yayi
tsami za ta .....
Kafin ma ya k'arasa wuf An gayu ta mik'e da hanzari tana ta ta ta ta fice daga
falon,ga tusar kuma tak'i tsayawa tana tafe tana sakin abarta b'urrrrrrrr !
A haka a daddafe ta samu ta fice daga gidan zuciyarta kamar ta fad'o k'asa saboda
tsoro,ta bar Idrees yana ta bala'i da masifa,har kuma ya juya kan Hauwa yana sauke
mata na ta fad'an,wai wallahi dole sai ta wanke kujerar da An gayu ta zauna da
kafet d'in da ta taka na tsakiyar falon,sannan yace ta je ta d'auko air preshner ta
feshe gidan gabad'aya da shi,ita dai Hauwa tsit tayi saboda tana tsoron ta tanka ya
lafta mata hannunsa me cike da murd'ad'd'un jijiyoyi ya safa mata kumatu.
***************
Tunda Salisu yayi wa Hajiya Maimuna waya akan gashi nan ya tawo zuwa gidanta
take ta d'oki,nan da nan ta tura gidan malam me almajirai aka yi mata kiran
Saratu,domin tana son ta had'a su waje d'aya ne tayi musu nasiha,haka nan ta taushi
Salisun domin ya mayar da Saratu d'akinta su cigaba da zaman aure.
Haka Saratu ta tawo tsolai tsolai da ita babu wanka balle wata kwalliya,dan
idan ma tayi kwalliyar ba kyau take ba saboda tsabar rama da lalacewar da tayi,har
wani doro me kama da k'usumbi ne ya fito mata,ita ma Hajiya Maimuna bata ce Saratun
ta gyara jikinta ba,saboda tafi son Salisun ya ga yadda Saratun ta koma k'ila hakan
zai sa yaji tausayin ta yafi mai da hankali akan ya mayar da ita d'akin ta, Saratu
ta shige falon Hajiya Maimuna ta zauna ta takure,ga carbinta a hannu tana
ja,burinta kawai tayi ido biyu da Salisu ko zai tausayawa halin da take ciki,domin
ba k'aramar wahala take sha zamanta cikin gidansu ba,rayuwarta ta zama tamkar ta
akuyoyin cikin gidan tunda cikinsu take rayuwa.
Hajiya Maimuna ta fito daga band'aki kenan rik'e da buta a hannunta taji
sallamar Salisu,ajiye butar tayi a gefe ta fara washe baki cike da murna take amsa
sallamar sa,shigowa yayi shi ma cikin fara'a sosai,Hajiya Maimuna ta rik'e hab'a
cike da mamaki take fad'in.
" Tubarkallah ma sha Allah Salisu haka ka k'ara yin shirgegiyar k'iba?ko dan dai na
jima ban ganka ba ne?"
Salisu yayi y'ar dariya yana fad'in " Wallahi kwanciyar hankali kawai na samu
Hajajju,ina shan sharafina yadda nake so shiyasa na k'ara wata k'ibar akan ta da"
Dariya Hajiya Maimuna tayi tana girgiza kai,sannan ta ce.
"To babu laifi Allah ya k'ara wadata,shiga ciki bari na zo mu gaisa mu tattaunar
maganar da na kirawo ka akanta ko?"
Salisu ya jinjina kai ya wuce tink'is tink'is zuwa falon mazaunansa sai rawa
suke,Hajiya Maimuna kuma ta nufi ktcheen domin ta d'akko masa ruwan sha.
Da sallamarsa ya shiga falon duk da baiyi tunanin zai tarar da wani mutum a
ciki ba,saboda kamata yayi duk in da za ka shiga ya kasance kayi sallama,ga
mamakinsa kuma sai ya tarar da tsamurarriyar tsohuwa a zaune ta takure da carbi a
hannunta tana ja,cikin barkwanci ya nufe ta yana murmushi da fad'in.
"ah ah ! Goggo Laminde saukar yaushe?ashe kina ciki?aikuwa ko jiya munyi waya da
Malam amma bai shaida min kin zo ba,ai da tuni na zo na kwashi gaisuwa"
Gaban Saratu ya yanke ya fad'i,ita kuwa wace irin lalacewa tayi da kowa yake
kwatantata da Baba Laminde?Baba Laminden da a k'iyasi ta ba wa shekaru saba'in
baya,idan kowa ma bai shaidata ba ai bai kamata Salisu ya kasa shaidata ba,wani
hawaye mai zafi ya tawo mata,ta sunkuyar da kai tana sharewa. Shi kam Salisu
matsawa yayi sosai gabanta ya tsuguna yana y'ar dariya yana kallon carbin hannun
ta,sannan ya kuma ce wa.
"Dad'i na da ke y'ar tsohuwar nan akwai ibada,to salatin da kike ne ya saki kuka ko
me?ni dai kar a manta dani a sakani a addu'a,domin akwai albarka a cikin bakin
nagartattun tsofaffi irinku".
Lokacin ne Hajiya Maimuna ta shigo falon rik'e da ruwa a hannunta,Salisu ya juya
yana murmushi ya kalleta ya ce.
"Hajajju ashe Goggo Laminde ta zo bani da labari,ai da kin fad'a min da na tsaya
nayi mata tsarabar goro me kyau,dan kuwa na wuce ta wajen masu siyar da shi naga
daushen goro mai kyau da gani zaiyi dad'i"
Ajiye ruwan Hajiya Maimuna tayi ta samu gefe ta zauna,ta mayar da hankali kan
Salisu tana fad'in.
"Ikon Allah! kaima Salisu baka shaida wannan ko wacece ba kenan ?har kake tunanin
Baba Laminde ce?"
Salisu cikin mamaki ya ce.
"Au wai ba ita ba ce?wallahi ni na zaci ita ce,to daman tana da wata k'anwa ne mai
kama da ita?
Murmushin takaici Hajiya Maimuna tayi,sannan ta ce.
"Abin da nake so kazo ka ganewa idanuwanka kenan Salisu,wannan dai da kake gabanta
ba Baba Laminde ba ce,ni ma da na dawo daga mai duguri ganin farko da nayi mata na
za ci Baba Laminden ce,sai da aka sanar da ni wai ashe Saratu ce ta koma haka"
Kan Salisu ya toshe ya rasa ma wace Saratun ake nufi,kallon Hajiya Maimuna yake
kawai da mici micin idanuwansa da suka shige loko,Hajiya Maimuna ta jijjiga kai
cikin tabbatarwa ta ce masa.
"Wannan dai da kake gani ba kowa ba ce face Saratu matarka"
Sai ga Salisu yana niyyar mik'ewa a gigice,nauyin da jikinsa yayi masa ne ya hana
shi mik'ewa ya koma jab'ar yayi zaman y'an bori yana zungura kai .😂
Comments
Share
Vote
Pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*BABI NA GOMA SHA TARA DA NA ASHIRIN*
PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️
*AYI HAK'URI RASHIN JINA KWANA BIYU,HIDINDIMU SUNYI YAWA GA KUMA MAKARANTA,A DINGA
YI MIN UZURI MASOYA* 👏🥰
***Hajiya Maimuna ta zubawa Salisu idanu ganin yadda yayi jab'ar sai zungura
k'eya yake yana zare idanuwa yana kallon Saratu wadda kanta ke sunkuye idanuwanta
na zubar da hawaye,da k'yar Salisu ya iya bud'e baki cikin k'arfin hali ya ambaci
sunan Saratu,d'agowa tayi ta kalleshi tana shesshek'ar kuka,ya tsurawa fuskarta
idanu wadda ta zama kamar ta yamushasshen b'era irin ya takure d'innan zai shuka
b'arna,Salisu bai san lokacin da ya tuntsire da wata mahaukaciyar dariya ba har da
rik'e ciki,dariya yake bil hak'k'i har da hawaye,Hajiya Maimuna ta bishi da kallo
ganin har da kwanciya a gaban Saratun yana birgimar dariya,idan yayi dariya ta
isheshi sai ya d'ago ya kalli fuskar Saratu ya ce "Saratu" Idan ta d'ago ta
kalleshi tana kuka sai yaga fuskar ta koma masa tamkar ta zomo ba b'era ba,sai ya
kuma kwashewa da dariya,wannan dariya ita ta kuma raunata zuciyar Saratu ta sake
fashewa da matsanancin kuka,ita kam Hajiya Maimuna suguri tayi tana kallon Salisu
cike da mamaki.
Sai da taga dariyar ta sa tayi yawa sannan ta dakatar da shi da fad'in.
"Haba Salisu da girmanka za ka zauna kana dariya har da birgima?maimakon ka
tausayawa halin da take ciki na bala'i da masifa sai ka zauna ka dinga shek'a mata
dariya?"
Salisu ya tsagaita da dariyar tare da goge hawayen da ya ratso masa,ya dubi Hajiya
Maimuna ya ce.
"Wato a rayuwa mutum ya gama shuka shakiyancinsa Hajiya,akwai ranar da Allah zai
kama shi,dubi dai yadda wannan baiwar Allah ta zama sai kace mai lalurar k'anjamau"
Hajiya Maimuna ta ce "Hmmmm ! kai dai bari kawai Malam Salisu,in fad'a maka fa
ranar da na ganta na zaci lalurar k'yanda take,ni shaf ma na manta da cewar yara ne
suke wannan ciwon sai da mahaifiyarta ta ankarar da ni" Hajiya Maimuna ta d'an yi
shiru tana numfasawa cike da tausayi da alhinin halin da Saratu take ciki,Sannan ta
d'ago kanta ta sake kallon Salisu tana marairaice fuska domin dai ya amince da
abinda za ta fad'a masa.
"Akan wannan dalilin ne yasa nace bari na kirawo ka mu tattauna,ka dubi girman
Allah da darajar karatun Alk'ur'ani mai girma wanda mahaifin yarinyar nan ya koyar
da kai tun kana yaro har ka girma a wajen sa,ka dubi raunin da mace take da shi,ka
dubi sauyawar kamanni da wahalhalun da wannan baiwar Allah take ciki,haka nan ka
dubi fushin da mahaifinta yake da ita,da ma wasu abubuwan da dama,duk su za ka duba
ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi kayi hak'uri da duk wasu abubuwa da suka faru a
baya,a sasanta domin ka mayar da matarka d'akin ka Malam Salisu"
A gigice ya zuba wa Hajiya Maimuna idanuwa zuciyarsa na tafasa,idan da abinda
ya tsana bai wuce ace ya mayar da Saratu gidansa ba,shi kad'ai ya san wahala da
k'angin da ya shiga a dalilin zama da ita,da wata ce tayi masa wannan zancen ba
Hajiya Maimuna ba zai iya bajeta a wajen nan take,take ransa yayi mugun b'aci yayi
kicin kicin da fuska kamar ba shine me tuntsira dariya har da birgima a yanzu ba..
Lura da sauyawar da fuskarsa tayi sai Hajiya Maimuna taji gabanta ya fad'i,amma
duk da hakan bata sare ba,ganin Salisun yayi shiru bai ce komai ba sai numfarfashi
yake,ya cika ya batse dammm! k'iris yake jira yace tushhhh! domin ya fashe,Sai ta
k'ara gyara zama ta dubi Saratu da ke ta sharar hawaye,tausayin ta ya sake kama
zuciyar ta,ta sake mayar da kallonta zuwa kan Salisu da b'ata ran da yayi ya saka
kumatunsa huruwa kamar an kwab'a (Alkubus), Hajiya Maimuna bata tab'a lura da
manyan (Tayani muni)da ke fuskar Salisu ba sai a ranar,Daurewa tayi ta sanyaya
murya ta cigaba da magana domin dai ta samu nasara.
"Na san cewa a zamanka da Saratu kai take cuta,kuma daman dul lokacin da kaji ana
bawa mutum hak'uri to tabbas an cuce shi ne,kuma kar ka manta masu iya magana sun
ce (Babba juji) . Hakan ya sa kaine babba tilas sai kayi hak'uri da zamantakewar da
za ka yi kai da iyalinka,duk abubuwan da suka faru tsakanin ku naji labarinsu kuma
na tausaya maka domin kasha wahala tabbas,kuma kayi hak'uri,amma ina so ka k'ara
hak'urin Salisu,duk wanda yayi hak'uri zai ga riba a rayuwar sa,don Allah da Manzon
sa ( S A W) ka taimaka ka mayar da komai ba komai ba kayi hak'uri ku sasanta domin
ta koma d'akinta,zaman ku a haka ba shi da wani amfani ko fa'ida,aure shine cikar
mutuntakar mutum a rayuwa".
Sauke Numfashi Salisu yayi idanuwansa har sun sauya kala,maganganun Hajiya
Maimuna sun shiga jikinsa,sai dai abubuwan da Saratu tayi masa suna dawowa cikin
k'wak'walwarsa,raini iya raini da aibantawa da kushe halittarsa babu wanda Saratu
bata k'ware akai ba,ballantana a zo kan raina mahaifiyarsa da tayi,kai tsaye take
ambatar ta ta zageta duk da kasancewar bata raye tana cikin k'abarinta,amma duk da
hakan idan fitsarar ta ta motsa ambatota take da (Iya me ido d'aya) saboda kawai
idon ta guda d'aya hallararre ne ya samu matsala,bayan wad'annan abubuwan ga shegen
lek'e da ta k'ware a kai,tsayawa da maza suna hira tana wage baki kuwa har bai san
adadin da tayi ba,dan akwai ranar da ya tab'a tarfa ta a soro daga ita sai d'aurin
k'irji,sai wani yalolon mayafi da ta yafa,tana tsaye ta kirawo me siyar da kifi
(Sukumbiya) suna ciniki,sai shakiyanci suke suna tuntsira dariya,da ya bata kifin
har da cewa wai yayi k'ank'anta,gara ya duba ya nemo mata zundumeme me kama da
cinyar mijinta,shi kuma me kifin sai dariya yake suna ta shakiyanci dai saboda
rashin tsoron Allah da kamun kai.
Hajiya Maimuna ganin yayi shiru bai ce komai ba ta san tunanin abubuwan da
suka faru yake,hakan ya sa ta k'ara yin magana kafin ma ya tanka.
"Salisu idan har za ka dinga tuna abubuwan da suka faru a baya to zuciyarka ba zata
yi sanyi ba,za ta dinga ciwo ne kawai a banza,ka manta baya da abubuwan da duk suka
faru,ka fuskanci gaba tare da addu'ar komai ya zama kaffara a d'ora sabuwar
rayuwa,ina tabbatar maka Saratu in dai ba ta amsa sunan Jaka ko Jahila bane babu ta
yadda za'a yi ta maimaita rayuwa irin ta baya,domin taga ishara ta d'and'ana rayuwa
ta wahala da tozarta duk da a gaban iyayenta take,ta gasu iya gasuwa,na tabbatar
rayuwar da ta d'and'ana ta hankalta,ba zata sake aikata wani abu mummuna a zaman
aurenta ba,kuma kafin ma na kirawo ka sai da na zaunar da ita muka yi
magana,wallahi Saratu tayi nadama sosai akan dukkan abin da ta aikata, ta wahala
sosai,baka ga yadda ta koma bane kamar k'warangwal? to tsabar wahala da yunwa
ne,domin Malam me almajirai baya bata abinci ta ci ta k'oshi,a yanzu da Saratu za
ta matso kusa da kai tayi magana uban d'oyin da bakinta yake sai ya gigita ka,yunwa
ce ta rarake mata ciki ta assasa mata miki cikin cikinta,numfashin kansa azabar
wari yake,ya kamata a duba domin a fitar da ita daga wannan k'angi haka ta horu da
yawa"
Salisu ya kalli k'aton tumbinsa da ke jikinsa,gashi an ce Saratu tana d'oyin
baki,idan ya mayar da ita d'oyin bakin na ta ya k'ara kumbura masa ciki ya zaiyi
kenan? Wata lukutar ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi ya dubi Hajiya Maimuna ya
fara magana.
"Hajajju naji dukkannin bayanan da kika yi,kuma ke d'in a matsayin mahaifiya na
d'auke ki tunda babu abinda baki yi min ba,wallahi a da na rufe babin Saratu a
rayuwata domin zamana da ita na tagayyara matuk'a da gaske,duk da kince kar na tuna
baya,a tun farko daman ita Saratu ba kalata take so ba,dan dai babu yadda za ta yi
da mahaifinta ne da ya zab'a mata ni a matsayin mijin aure,kuma taje ta had'u da
shakiyyan mak'ota suka dinga zuga ta suna d'ora ta kan bak'ar turba,tarbiyyarta ta
lalace,babu irin nasiha da ban baki da bana yi mata amma tak'i saurarata,shiyasa na
gaji da halinta har ta kaimu ga rabuwa,to amma Hajiya ni ba zan iya yi miki musu
ba,zan mayar da Saratu d'akinta mu cigaba da zama,amma bisa wasu sharad'ai da zan
kafa mata idan ta amince da su "
Kafin Hajiya Maimuna tace komai Saratu ta zabura cike da tsananin murna ta
rarrafa gun Salisu,cikin hawaye ta fara magana d'oyin bakinta na dukan k'ofofin
hancin Salisu,nan da nan ya matsa da sauri yana kawar da kai.
"Wallahi,wallahi,wallahi,na rantse maka da k'udura da irada ko me kake so zanyi
Yaya Salisu"
"Kambu!" Salisu ya ambata a ransa,lallai Saratu ta luguiguita tunda yau har ya samu
canjin suna,yau shi Saratu ta kirawo da (Yaya Salisu) Saratun da ta sanya masa suna
kala kala a baya na cin mutunci da muzanci,sunaye kala kala,irinsu d'an lukuti🤣 d'an
sukuti 😂 dindimijijjib'i
😂 😂k'olo 🤣gardi 😂 basamude🤣 da dai sauran su.
**************
Yana zaune a tsakar gida kan tabarma da wata zungureriyar bulala a
hannunsa,a gefe ga man ja da man shanu sai shafawa bulalar yake yi tayi jajur da
ita, A guje An gayu ta shigo gidan ko sallama babu,bata san lokacin da tayi fatali
da robar manjan da ke gabansa ba man ya b'are a k'asa,tuntub'e ta ci da k'afafun
Malam Arabi tana niyyar kifawa da hanzari ta mik'e tana rik'e zani tayi band'aki da
gudu ta fad'a tana nishi.
A gigice Malam Arabi ya mik'e tsaye yana zare idanuwa cike da tsoron da
yaji,ya dinga waige waige domin yaga abin da ya razana masa matarsa haka,a hankali
ya dinga tafiya salaf salaf har ya isa soro ya lek'a waje