Advertisements
Chapter 2 Reading ABULLE ANNOBA Sirrin Kauyen Bala'i by Mss Flower BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABULLE ANNOBA Sirrin Kauyen Bala'i by Mss Flower

Author :  Mss Flower Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 17

3K to 6K   out of 49.1K words

na dubu daya, dubu daya tacire taba zugar yaran dake mata tallah suka"

"karba suna tsalle tareda mata godia,"

"Bintalo ta kalle Abulle, ""iya Abulle yaushe za'a kuma yin wani""sai gobe Amman kuzo da wuri"

"""to iya Abulle"" suka wuce suna tsalle,"

"Abulle har takama hanyar gida tatuna Idan taje tuwo zata ci kuma gaskiya yunwa take ji, canza akala tayi zuwa gidan mai gari, a zaure ta iske shi zaune da babbar Riga kamar wanzami, wani mugun kallo ta balla mai nan da nan ya zube kasa yana ""Allah y taimaki Abulle wallahi daman yanzu nake cewa azo akaimiki zabin nan tinda nasan yanzu kindawo yawon sa'anar yagama tareda"

"sharce zufar dake tsatssafo masa kamar ankama malam a gidan karuwa,"

"Harara ta kuma zabga masa tareda cewa ""bani su nan"" aguje ya ruga ya dauko kwarya biyu ta farar"

"saka saikuma zabi bakwai, warcewa tayi daga hannunsa tareda kama gaban ta ranta fess,"

"Tana tafiya mai gari yafashe da kukan bakin ciki yana ""Allah y tsine ma hansatu da isuwalle duk sune suka ja mana wannan annobar."

"Wallahi dole mu kashe abulle ina haka bata barin mu muzauna lpia,"

"Gida tashiga ta jawo turmi tazauna tareda kwala ma hansatu kira da gudu ta karaso, turus tayi"

"tareda sakin bakin tana kallon Abulle sai tandar Zuma take,"

"""Ungo wannan soye zakimin yanzun nan Don yunwa nake ji.........."

Mss Flower & Mrs Abdool

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA

SIYAN LITTAFIN NAN_

"*NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA"

ILMANTUWA*

"_ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_"

SAI MUN JIKU

"[8/14, 11:34 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

05

"Hansatu ce dauke da zabin da Abulle tashigo dasu don yankawa,"

"""Ke hansatu guda ukku zaki yankamin ki ajemin sauran hudun gobe zakimin dabge dasu""Cewar"

Abulle har lokacin sai tandar Zuma take kamar sabuwar mayya.

"Guda ukku hansatu ta ware gefe guda, tazuba sauran a wani tsohon keji, nan da nan ta hau yankawa don Abulle tace tayi sauri yunwa takeji,nan ta dafa ruwan zafi tafige tayi tafashe sannan"

"tahau suya,"

"Abulle dake hakimce tana bin hansatu da umurni, zabga wata uwar hamma tayi kamar tsuwar"

"mayyar da ta Kwan bataciba jin kamshin soye yafara gauraye gidan,"

"Isuwalle ne ya kwado uwar sallama tindaga soro, sannan ya karaso cikin gidan, zaune ya iske"

"Abulle kan turmi tana karkada kafa, ""isuwalle Dan karbomin lemo a gun idi mai shago"","

"""wani irin lemo kuma Abulle"" cewar isuwulle yana kallon ta"

"""Wanda kasani kuma kalar baki nan nake so karda ka karbo wanda bashiba kadeji Mena cemaka"""

"tabashi amsa,"

"Babu yanda ya iya haka yanufi shagon idi, tsayawa yayi bakin shagon don takaici duk ya ishe shi, kamarshi da girman shi ace Yarinyarshi tana aike shi cikin iko da gadara Idan kuma mutum baije ba ta Aiko masa macizai suna shi bacci mtswww duk a zuci isuwalle ke wannan maganar, ganin yana bata lokaci yasa yace ""idi Abulle tace kabata lemu baki"" Allah sarki Idi jiki na rawa yace"

"""guda nawa"" ""guda biyu""tace isuwalle yabashi amsa"

"Mika masa yayi harda sakawa a leda sannan ya karba yatafi, yana shiga lokacin kuwa hansatu"

"tagama soye sai kamshi suke,"

"""Juye min a kwanan nan kikawo su nan"", haka ko tayi tadire mata su agabanta, ""to daukomin yajin nan mai tafarnuwa Wanda zanyi Dangwale tareda plate dinda zan saka miki naki, mikewa hansatu"

"tayi don yin umarnin Abulle,"

"Miko mata ledar isuwulle yayi, tako karbe ba sannu bare nagode,"

"Hansatu mikomata yajin tayi tareda plate din, nan Abulle tazabe kawunan da kafafun tasaka musu ""kici keda isuwulle"""

"Isuwulle yace yanzu Abulle Kai zaki bamu, cikeda tsiwa tace ""to daka samu ma nabaka koh, Idan baka ci bani"" tsinto fukafuki tayi tace hansatu ladan suya, karba tayi suka koma gefe, shima"

"isuwalle saboda tsabar kwadai saida yaci,"

"Abulle kuwa 'kasa takoma don taji Dadin cin naman tabude yajin ta tareda balle robar lemu tanaci tana korawa, saida tacinye su tass ta shanye lemun sannan ta saki wata uwar kara alamun ta koshi, gantsarewa tayi ta narko wata uwar gyatsa irin ta yara marasa tarbiya sannan ta Mike ta karkade"

"bujenta tayi da'ka abinta,"

Hansatu ce dake wanke wanken kwanukan da Abulle tagama cin abinci ceh ta saki tsaki tana cewa

""" Allah wadarai"""

"""Ai kece abin Allah wadarai Hansatu, kece sanadin komai tubda ke kika haihota, ni dai tsakanina dake sai dai na ce Allah sakamin"" cewar Isuwalle da ke zaune bisa turmi yana tsotsar 'kafafun"

zabbi

"""Isuwalle ai kaine musababbin komai, da kan na haifeta wani wula'kanci ne bakamin ba kai da danginka, kai ka tasoni gaba dole kasa na kauce hanya kai da danginka"" cewar Hansatu dake"

mi'kewa

"""Yarinyar da kika haifa mana yanzu ai gashi tazame mana annoba, tun shekarar data wuce data karya 'kugun Baaba har yanzu Baaba jinya takeyi, sam ta'ki bani fuskar magana da ita duk saboda abinda 'yarki ta jawo, ni dai kin cucan Qur'ani, ga uban ci kamar gara kullum kusan kwano biyu na hatsi take ci, duk ta 'kararmin da kadara, ga ba'kin jini data jawomin a al'umma, duk inda naje"

"zumd'ena akeyi ana ja min Allah ya isa"" ya 'karashe yana tura kan zabo baki had'i da sakin kuka"

"""Dallah rufen baki, duk abinda ake maka yayi rabin nawa ne, ina ce..."" Hansatu shiru tayi ganin"

Abulle ta fito daga d'aki tana kallonta

"""Jar uba! Yau za'a kuma 'yar tsere a gidan nan kenan"" ta fad'a tana wage baki saboda hamma"

"""Abulle ni dai bakiji nace komai ba ko?"" Cewar Isuwalle domin ranar da akayi 'yar tsere kwanakin"

baya shiya fad'i kuma shi ya azabtu daren ranar.......

Mss Flower & Mrs Abdool

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA

SIYAN LITTAFIN NAN_

"*NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA"

ILMANTUWA*

"_ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU "

"[8/14, 11:34 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

*07*

""" Abulle na ro'keki da Allah ki rufan asiri, wallahi 'kashin 'kafata ya turgud'e"" cewar Hansatu tana"

'bare baki wiwiiii

"""A dakata to, bari Hansatu ta huta"" cewar Abulle tana zama"

"""Abulle 'kafata, wayyo Allah ta turbud'e 'kafata"" Hansatu ta 'kara fasa kuka"

"Isuwulle ne ya mi'ke ya nufi Hansatu da keta yarfe hannu tana matsar 'kwalla, 'kafarta ya ri'ke"

"yana 'ko'karin jaa aikuwa ta tsallara ihu tana fad'in "" Isuwulle azaba, jaa da kyau, cikata haka"" sai sumbatu take tana 'ko'karin janye 'kafarta"

"""Isuwulle ri'ke 'kafar ka ja ta da kyau, matseta sosai kada ka cika"" cewar Abulle tana ta d'irka"

dariya harda hantsilawa

"Hansatu ba 'karamin kuka tayi ba sanan Abulle tace "" yau na rushe 'yar tseren kowa ya huta"" ta fad'a tana cigaba da dariyar mugunta, Hansatu tana d'ingisawa ta samu ta d'ora ruwan zafi domin"

gasa 'kafarta

"Abulle zaune bisa tabarma ga kayan kwalliya birjik a kusada ita danginsu jar hoda, kwalli, barbad'a kumatu, ga kanta kile jambaki, ga kuma ba'kar jagira, kwalliya ta rambad'a fuskarnan taji uwar jar hoda, ga ba'kar jagira da aka sha guduma sanan aka bi aka d'iddige fuskar da ba'ki, sanan ta rambad'a jambaki a saman ido da baki, Isuwulle da Hansatu dake gefenta sai kallonta suke kamar sunga sabuwar halitta domin kwalliyar Abulle idan ta tashi yi ta kere ta kowa muni a 'kauyen, madubi ta kalla ta turo baki sanan ta she'ke da dariya tana dad'awa da shewa sanan tace"

"""kai jama'a irin kyau haka, yasin mijin Abulle ya cha'ba"" ta fad'a tana mi'kewa"

"""Abulle wane mijin hala, ko sai a dandali zaki fitar da gwanin naki"" Isuwulle ya tambaya"

"""A'a Isuwulle ni ai na fidda gwanina tun jiya, yau in aka tashi daga dandali ka sanarma zan wuce gidan mai gari, wallahi kowa ya taru da yaro da babba duk wanda bai je ba zaya sani"" Abulle ta"

fad'a tana karkad'e kayan jikinta

"""Abulle mi za'ayi a chan ne"" Isuwulle ya tambaya"

"""Zan fidda gwanina"" ta basa amsa sanan ta wuce tana tsalle, dan'kam ta tadda 'yammatan 'kauyen 'kofar gidansu kowacce ta sha kwalliya da d'amara haka suka kama hanya suna hirarrakinsu har"

suka 'karasa dandali

"Bayan samarin da suka tadda sun gaida Abulle aka fara gudanar da gad'a da wasanni, bayan"

"angama ya zamana saura lokacin hira, haka kowa ya ja budurwarsa gefe suna zance banda Abulle da Bintalo dake zaune kan wani dakali suna 'yar hira, chan Abulle ta mi'ke ta dubi Bintalo tace """

"zo mu zaga mu ga ko za'a samu 'yan iska"", Bintalo mi'kewa tayi suka fara zaga 'yammatan da"

"samarin suna ganin abinda sukeyi, idon Abulle ne ya sauka akan wajen ciyayi, gani tayi kamar mutane dan haka suka nufi wajen cikin sand'a"

"""Mati da zafi kake sha fa"" cewar wata muryarta kamar zatayi kuka, Mati kam bai kulata ba sai"

faman matseta yake

"""Jar ubancan! Dama Dije ke 'yar iska ceh, yau zaku ci ubanku, maza ku fito"" cewar Abulle"

"Mati iya rikicewa yayita, hawaye yake ya fara magiya cewa shi hira yakeyi amma Abulle sai d'ure"

d'uren ashar takeyi ta 'ki sauraronsu

"""Abulle dan girman Allah kiyi ha'kuri, na rantse da Qur'ani izihi sittin ni ba komai nakewa Dije ba,"

"ai ga tanan a tamba..."" Bai 'karashe ba yaji wani gigitaccen mari bisa fuskarsa kamar an maka masa itace mai uban nauyi"

"""Wa zaka maida 'yar iska, ca aka ce maka banganka ba, bare ka tsara, wato ka kama nonuwan yarinya kana sha ita ba shanuwa ba ko kuma kai ba jinjiri ba, salon ka ciremata su ka kasheta, to kwarankwatsa yau sai kaci 'kwal ubanka"" ta fad'a tana 'ballo tsumagiya lokacin masu hira duk sun"

yo caa hankalinsu ya dawo wajensu Abulle

"""Kai Saminu, Isiyaku ku d'aga min shi"" Abulle ta fad'a, Mati ko 'kara sautin kukansa yayi yana magiya amma haka aka d'agashi sama Abulle ta dinga zuba masa bulala, kafin tayi masa goma har ya sume, haka tasa aka bugo tu'ka tu'ka aka kwaranya masa ruwan, yana bud'e ido ta kuma cigaba"

da sambad'arsa

"Abulle ko da tagama ta buga uban tsalle tayi girgiza sanan tace "" Allah kuma ba ma wani sa'a naga yana 'ko'karin lalata da yarinya ko 'ko'karin tsinke mata nono yaga yanda zanyi dashi a garin nan"" ta fad'a tana dariya da buga 'kafa, nan kowa dai yayi tsuru tsuru, Mati kuwa jini duk ya 'bata masa"

riga gashi baya iya tafiya sai kuka kawai yake

"""Mai gari ya aikoni, yace na sanar da duk wani saurayi dake dandalin nan da yayi haramar zuwa gida ya shirya cikin ado, ya 'karaso gidansa cikin 'kan'kanin lokaci domin yau Abulle zata fidda miji, wanda bai zo ba zaya had'u da fushinsa da kuma na Abulle"" cewar d'an shela dake yawo da lasifika. Nan dukkan samarin suka fara watsewa fuskokinsu da fargaba yayinda 'yammata suka"

fara 'kus 'kus amma ba batun fiddo zance waje

Abulle ceh zaune kan kujera yayinda samari da dattawan 'kauyen sukayi dafifi a 'kofar gidan mai gari kowanne zuciyarsa cikeda zullumi da addu'ar Allah yasa kada Abulle ta za'besa musamman

samarin

"""Abulle ke ake jira ki za'ba, sanan ki saka lokacin auren"" Mai gari ya fad'a"

"Dariya Abulle ta she'ke da ita sanan ta fara kallonsu d'aya bayan d'aya chan tace "" za'bina"

shine...........

Mss Flower & Mrs Abdool

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA

SIYAN LITTAFIN NAN_

"*NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA"

ILMANTUWA*

"_ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_"

SAI MUN JIKU

*YAN NIGER NAKU 300F NE KU TUNTU'BI WANAN LAYI DOMIN BIYAN NAKU

+22795045822 IDAN KUN BIYA SAI KU TURO SCREENSHOT TA WANAN LAYIN

08167888934*

"[8/14, 11:34 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* (Sanadin neman haihuwa)"

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

"_HEY LOVELIES!! KUYI SAURI KU BIYA DOMIN SAMUN DAMAR SHIGA INDA ZAKU KARANTA ABULLE, DOMIN FREE PAGES NA GAF DA 'KAREWA, KADA KU MANTA"

"ZAKU SHA DARIYA, ZAKU ILMANTU. KU NEMI NAKU TUN KAFIN A BAKU LABARI_"

*06*

"""Kwarankwatsa sai anyi 'yar tseren nan"" cewar Abulle tana karkad'a 'kugu"

"""Abulle"" cewar Isuwalle da idanunsa suka kawo ruwa"

""" Kada kayi magana, ku jira na samo rake nadawo a fara"" Abulle ta fad'a tana ficewa"

"Tafiya take tana dirka tsalle, idan ta cilla 'kafa chan sai ta dire kamar wata 'yar rawar 'be'be, tana ta wa'ke wa'kenta tana tafa hannu. Sa'adu mai mangoro ne ya hangota, suna had'a ido ya zura"

takalma ya fara tura baron mangoro cikin sauri kafin ta taddosa dan akwai 'yar tazara tsakaninsu

"""Chalama!! Sa'adu akwai rowa kwarankwatsa, yanzu ko zanyi maganinka"" ta 'karashe tana tattare bujenta had'e da gyara murya, ta'kar'karewa tayi tana ""Sa'adu mai mangoro tsaya"", ai Sa'adu jin ta kirasa sai ya kuma daddagewa ya fara zuba gudu da baro, mangoro na fad'uwa yana d'agosu da 'kafa yana maidawa, yayi gudu mai nisan gaske sanan ya juya ganin Abulle bata bayansa yasanya ya koma 'kar'kashin wata makekiyar bishiyar kuka ya zauna yana haki had'e da maida numfashi, 'yar gorar ruwansa ya d'auko zai sha aikuwa sai yaga ruwa na tashi sama kamar ana zu'kosa ta saman bishiya, cikin kid'ima ya birkita wanda yayi sanadiyyar zubewar mangoronsa a 'kasa, d'aga"

idanunsa yayi sukayi ido biyu da Abulle tana murmushi

"Dirkowa tayi daga bishiyar ta ri'ke ha'ba sanan tace "" yanzu kai Sa'adu saboda ba'kar rowa shine kayita zabga gudu kada ka bani mangoro biyu zuwa biyar, lallai ka cika uban 'yan rowa"" ta"

'karashe tana zubewa tana dariya harda birgima

"""Kiyi ha'kuri Abulle ban lura dake ba ne"" ya fad'a idanunsa na kawo ruwa"

""" Bata shafan ba, kai ta shafa"" ta 'karashe da karka'be bujenta ta tsinci mangoro biyu daga 'kasa"

tayi tafiyarta tana tsallenta

"""Shegiyar yarinya mai zubin aljanu, ashe ma aljanar ce, ni naga ruwa iya sama ziiiiii ashe aljanar na bishiyar, Allah ka yayemana wanan annoba, yanzu ta jamin asarar murtala"" ya fad'a yana tsaki, sanan ya nufi mangoronsa da ya zube yana 'ko'karin kwashewa amma da ya kama sai ya koma dutse, haka yayita bin mangoron d'aya bayan d'aya suna komawa duwatsu, zaman 'yan bori yayi"

ya dinga kuka kamar zai shid'e sa'ilin nan ya mi'ke kamar an tsikaresa ya nufi gidan mai gari

yanata kumfar baki a hanya

"""Isuwulle ya kamata ayiwa Abulle aure kaga ta zama budurwa, ga kuma duk sa'aninta da tsarar"

"rakinta ansa musu rana, a nema mata miji"" cewar Hansatu"

"""Lallai Hansatu sai yau na tabbatar bakida hankali, yanzu uban wa kike tunani zaya auri Abulle,"

"wallahi ko mahaukaci aka ce za'a bawa na tabbata guduwa zaiyi, wai Abulle Annoba suke mata kirari, toh wa zaya kwashi annoba ya kai mahallinsa"" ya 'karashe da tsuka"

"""Ai idan kai son zama da ita kake kana wahala a banza sai kayita zama, amma ni nagaji da wahala,"

"azaba, da ba'kin jinin da nayi cikin mutane, bari ta dawo nace ta za'bi miji nasan dai ko yanasonta ko baiso sai ya aureta eheee"" Hansatu ta 'kare da murgud'a baki gefe"

"""Nima farincikina ne, Allah ya tabbatar da alheri"" Isuwulle ya fad'a"

"""Yanzu naji batu, da kana magana kamar son zama da ita kakeyi"" Hansatu ta fad'a"

"""Nadawo, me kuke tattaunawa"" Abulle da shigowarta kenan a guje"

"""Magana muke akan auren sa'aninki da za'ayi nan kusa, ke kuma shiru ba wanda ya turo"" cewar"

Isuwulle

"""Hehehehehe Qur'ani kun bani dariya, wayaga Abulle amarya"" ta fad'a tana kwashewa da dariya"

harda kifewa 'kasa

"""Abulle baki son auren ne"" cewar Hansatu cikeda

2 / 17