Advertisements
Chapter 3 Reading ABULLE ANNOBA Sirrin Kauyen Bala'i by Mss Flower BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ABULLE ANNOBA Sirrin Kauyen Bala'i by Mss Flower

Author :  Mss Flower Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 17

6K to 9K   out of 49.1K words

fargaba"

"""So kai, Hansatu ni ai da sam bani maganar aure ma, ashe fa na zama budurwa"" ta 'kara kwashewa"

da dariya tana hantsilawa

"""Ai aure shine cikar mace"" Isuwulle ya fad'a"

"""Kwarankwatsa za'ayi budiri da auren Abulle, kada ku damu nan kusa za'a sha shagali, nan kusa"

"zan fidda miji"" ta fad'a tana murmushi"

"Wani farinciki ne ya 'kara kama iyayen Abulle, cikin zumud'i suka ce ""Allah ya kaimu"""

"Abulle ceh ta tattare buje, ta daka uban tsalle tace ""za'a fara 'yar tsere, yanzu za'a fara wa'ka kafin a gudanar da wasa kamar yanda aka saba"" ta fad'a tana daddagewa tana baya kamar an ri'ke"

"kafafunta sanan ta wage murya "" A bada fili fili"" "

"""Filiya!!"" Suka ta'kar'kare suka amsa fuska kamar kashin shanu"

"""A bada filin wasa "" Abulle ta kuma fad'i"

"""Filiya "" suka amsa suna matsawa domin bada filin"

"""Duk wanda bai bayar ba "" Abulle ta fad'a tana direwa"

"""Filiya "" suka amsa suna tafawa"

"""Uwarsa 'yar kamasho ceh "" Abulle ta fad'i"

"""Filiya "" suka amsa suna 'kara matsawa"

"""Ubansa d'an kamasho ne "" ta fad'i tana tafi"

"""Filiya "" suka amsa suna watsa mata harara ta 'kasan ido"

"""Daren yau ya kwan da cinnaku "" ta 'karashe tana taka rawa"

"""Filiyaaaaa!!!!!!"" Dukkansu suka ta'kar'kare iya 'karfinsu suka amsa"

"Abulle dariya ta she'ke da ita sanan tace "" kunci wanan, toh a jaaa layi"""

"Nan suka shata layi, suka tsaya 'ki'kam kamar sojoji"

"Abulle ta kallesu tayi murmushi sanan ta fara musu cewa ""Mai tsumma "", ai sai suka d'aga 'kafar"

hagu

"""Mara tsumman "" suka d'age 'kafar dama"

"""Mai tsumman, mara tsumman Hansatu ya baki d'aga ba? "" Cewar Abulle. Cikin sauri Hansatu ta d'age 'kafa sanan ta makata 'kasa da 'karfi, ai kuwa zafi ya ziyarceta ta dur'kushe tana yarfe"

hannu ...........

Mss Flower & Mrs Abdool

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA

SIYAN LITTAFIN NAN_

"*NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA"

ILMANTUWA*

"_ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_ SAI MUN JIKU "

"[8/14, 11:40 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

"_HEY LOVELIES!! KUYI SAURI KU BIYA DOMIN SAMUN DAMAR SHIGA INDA ZAKU KARANTA ABULLE, DOMIN FREE PAGES NA GAF DA 'KAREWA, KADA KU MANTA"

"ZAKU SHA DARIYA, ZAKU ILMANTU."

08

"Kyakkyawan saurayine dogo mai kimanin shekaru 32 a duniya, sanye yake cikin suit Dark blue"

"mai mugun kyau, hannunsa na dama daukeda brief case sai dayan hannun kuma daukeda suit din saman, yarage dagashi shi sai long sleeve light blue da butterfly neck tie,"

"Tafe yake cikin sassarfa yana duba time a hannunsa dake makale da kyayyawan agogo, kofar exit din katafariyar asibitin yake tunkara,harya fito yaji ringing din wayarsa, da sauri ya dauka ganin"

"""first love"" dauka yayi tareda karawa a kunne,"

"""Hello Mom on my way, wallahi aikine yad'an min yawa shiyasa but in the next 20mins Ina gida"""

"Banji me taceba, kawai yakashe wayar, da sauri yashiga motarsa ya tada yabar harabar asibitin."

"Mintina ashirin ya iso bakin wani kantamemen gate, horn ya danna da 'karfi daga inda mai gadin yake zaune ya danna remote nan da nan kuwa gate ya zuge, kutsawa yayi, kaitsaye ya perker"

"mortar a inda aka tanada ya bud'e ya fito d'auke da jakarsa,"

"Direct apartment d'in mahaifiyarsa ya tunkara, handle d'in ya murza tareda yin sallama, budurwar"

"dake zaune a falon ta wani amsa masa a da'kile, shi da baima lura da ita ba direct hanyar stairs ya nufa don shiga d'akin mahaifiyarsa,"

"Ahankali cike da yanga ta kirsa tace ""Doctor barka da dawowa"", tsayawa yayi tareda juyowa sai a lokacin ya lura da akwai mutum a palon, bai ko amsata ba, sai kallon ta yayi sama da 'kasa tana sanye cikin riga da wando damman mu sai wani juya ido take irin na 'yan duniya, tsaki kawai yaja"

"tareda hayewa kan stairs d'in,"

"'Dakin mahaifiyarsa ya bud'e tareda zama akan cushion d'in d'akin, kana ganin sa kasan a gajiye"

"yake,"

"Kallonsa tayi cike da 'kauna tace ""son yau ka dad'e dayawa, tinda dazun Meema tazo tana jiranka"""

"'Bata ransa yayi yace"" Mom is that why u have been calling?, plss mom wai meyasa matan nan suke damuna ne plss su 'kyaleni na huta mana, when it's time zanga wacce nake so da kaina, duk bana son su kar nasake ganin 'kafar kowace shegiya a gidan nan inba haka ba zan mata rashin mutunci, I can't marry such type of gals ba class bare kamun kai, God forbid ma"" ya 'karashe"

maganar ransa a d'an 'bace.

"Mom itama da abun saddiq yafara damun ta tace ""son yaushe ne zaka cikamin burina naganin matarka, its high time fa shekarunka 32 a duniya fa idan ba yanzu ba sai yaushe, I am sick and tired of ur attitude plss enough, kowa baka so then wa zaka aura?!!"" itama ta 'karashe maganar"

"ranta na 'kuna,"

"Mi'kewa yayi ya koma kusa da ita yakama mata hannun ta ""plss Mom just pray for me kinji koh, so nake na samu yarinya mai tarbiya da hankali wacce zata kula dake, Mom u won't understand it's only u I have am doing this all because of u, meyasa bazaki gane ba kinsan insonki banson na auro wacce zata baki problem kingane koh Mom to plss calm down just pray for me, cos ur prays matters a lot, bazan ta'ba yin abu don na 'bata miki rai ba, kinson banson 'bacin ranki ko yaya ne"

"kiyi ha'kuri ki yafe min kinji Mommy na"" ya 'karashe maganar kamar zeyi kuka."

"Murmushin jin dadi tayi "" I know my son kullum Ina maka addua Allah y baka tagari Allah kuma yayi maka albarka"" tafad'a tana murmushi tareda saka hannu cikin curly hair d'inshi tana murzawa"

kamar wani yaro.

"""Yanzu tashi muje kaci abinci yau favorite d'inka na dafa ma"" tafada tana kallonshi tareda 'kara"

fad'ad'a murmushin fuskar ta

"Ware idanuwansa yayi ""wow really, u are the best Mom ever, I love u so much"" ya fad'a cikeda"

"farin ciki yana hugging d'inta,"

"Zamewa tayi, tayi gaba yana biye da ita har suka sauko stairs d'in, kallon falon yayi yaga Meema"

"bata nan it means ta gaji tawuce abunta,"

"Dining yawuce ya zauna, serving d'insa tayi lafiyayyar fried rice da coslow tareda liver souce, ci yayi sosai har ya 'koshi suna fira, kallon ta yayi yace ""Mom u are the best cook ever wallahi"

"banta'ba cin abinci mai dad'in naki ba"" ya karashe zancen yana kai lomar shinkafa baki,"

"Fashewa tayi da dariya tareda cewa ""kaide ci bance kamin santi ba"""

"""Allah Mom Idan zanyi aure sai tazo ta koya kalar girkinki don shi zata rin'ka min"""

"""To naji, maza cinye ka tashi kaje ka dibo 'kanwarka batada lafiya inaga ciwonta ya tashi"""

"""Mom kinsan dai bana zuwa can sasshen saboda Umma banson abubuwan da takeyi"""

"""kayi hakuri kaje saboda Allah ai taimako zakayi"""

"""To shikenan"" yafada tareda mi'kewa ya wuce part d'insa, kayan sa yacire ya shiga wanka tareda"

"d'auro alwala don an rigada anyi sallar zuhr a masallatai, agida yayi nashi yasaka jallabiya mara nauyi ya nufi hanyar apartment d'in Umma,"

"Da sallama yashiga falon, amman ba kowa wuce wa sama yayi d'akin Sultana, kwance yaganta ta"

"du'kun'kune da duvet tana rawar sanyi,"

"Da sauri ya yakice duvet d'in yana ""Sultana meke damunki?"""

"Ahankali ta bud'e idonta tareda d'an mi'kewa ta jingina da gado cike da 'karfin hali tace ""Ya"

"Saddiq ina ta neman lambarka baya zuwa"""

"""Am sorry sis nashiga thearter shiyasa, how are u feeling now?"""

'Dan gyada masa kai tayi kawai numfashinta na fita sama sama

"""Sultana bakijin magana kinsan lalurarki but kina wasa da lafiyar ki gashi baki shan drugs, Ina"

"umma take?"""

"""Tafita tin d'azu"","

"""Kinci abinci?"" ya tambayeta, girgiza masa kai tayi,"

"""Toh meyasa?"", yasake tambayarta"

"""Yaya banason abincin da aka dafa ne"" ta fad'a tana d'an yatsina"

"""Zaki ci fried rice?"", gyad'a masa kai tayi yace"

"""toh Ina zuwa"" yafita"

"Babu dad'ewa sai gashi tareda plate d'in abinci, taimaka mata yayi taci sosai sannan ya d'auko box"

"d'in magugunnan ta yabata,"

"""Ki huta yanzu Idan kinji wani abu call me kin. """

"Bai gama magana ba yaji hayaniya daga bakin kofa wanda ko bai juya ba yasan Umma ce, ""muryar wani kwarton namiji nake ji a dakin 'yata"" juyawa yayi zai fita ta tare shi ""wai kai wani irin mara zuciya ne wato harkafara shigomin d'akin 'yata bana nan ko, to ahirr dinka, kar na sake"

"ganin 'kafarka cikin gidannan banzaye masu asiri"""

"Fashewa Sultana tayi da kuka ""haba Umma Yaya taimakona yayi fa banda lafiya, wallahi Umma"

"karki kara zagin Yaya meya miki saboda kawai baki son Mom shine zaki had'a dashi?"""

"Rushewa Umma tayi da kuka tana ""shikenan Allah y isa tsakanina da Amina wato banda mutanen"

"gidannan dana gari yanzu har 'ya'ya na ma ta asirce su nashiga ukku na lalace wallahi da sake"" ta 'karashe da kururuwa"

"Sunkuyar da kai saddiq yayi yana ""Allah y baki hakuri Umma"""

"Cikin masifa tace "" fice min d'aki tsohon munafiki kawai kamar mutumin kirki sai wani sun sun"

"da kai yakeyi"""

"A hankali ya ra'ba ta gefenta yafita yana girgiza kai,"

"'Kara fashewa Sultana tayi da kuka, wani mugun kallon Umma ta watsa mata ""munafuka kema"

"daya sai kitayi tinda na kori ubanki"" tafitana tana banko kofa."

"""Ai Umma Yayana ne kuma baki isa ki raba mu ba duk duniya banda kamarshi, kuma inasonshi."

*ABULLE POV*

"""Abulle to kinyi shiru munata sauraronki, ai kwarankwatsa ki fidda duk wanda kikeso a nan,"

"wallahi sai an aura maki, in bayada gida ma ni zan bashi"" cewar Mai gari"

"Dariya Abulle ta she'ke da ita sanan ta girgiza kai irin abun na mata dad'i, chan ta mi'ke ta fara tattakawa tayi gaba tayi baya tana 'karewa jama'ar wajen kallo, murmushi ta saki sanan tace "" duk"

"'kauyen nan wa yafi kud'i?"""

"Aikuwa jama'a suka d'aga murya har suna rigegeniyar furta "" Mai gari"""

"""Gonakin wa suka fi yawa"" Abulle ta kuma wage murya ta tambaya"

"""Mai gari"" Jama'a suka dad'a amsawa. Mai gari kam zufa duk ta ji'kashi bai san lokacin daya zamo"

daga kujera ba

"""Abulle ai gonar taki ce, ki za'bi miji sai na barmasa"" cewar Mai gari"

"Wani kallon zakaci ubanka Abulle tayi masa, sanan ta kuma tambaya "" wane ne ya ta'ba zuwa"

"binni?"""

Ai ko suka kuma d'auka sunan Mai gari

"""Jama'a to ni Abulle na tsaida Mai gari matsayin mijina, domin shi yafi cancanta ya zama mijin"

"Abulle"" ta fad'a tana washe baki"

"Mai gari wasu zufa da hawaye ne suka kuma zubomasa, rarrafawa yayi gabanta, gwiwoyi 'kasa"

"yace "" mi zaki yi da tsoho?"""

"""Shine za'bina"" Abulle ta fad'a..........."

"_Few pages to last page, ku garzayo ku biya naku, kada ayi babu ku_"

Mss Flower & Mrs Abdool

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA TA

SIYAN LITTAFIN NAN_

"*NAIRA 200 NE KACAL, ZAKI MORE KARATUNKI, KI SHA DARIYA GAMIDA"

ILMANTUWA*

"_ZAKI BIYA TA WANAN ASUSUN 0104322069, SAKINA ABDULLAHI, ACCESS. IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKI TURO KI TUNTU'BEMU TA WANAN LAYIN 08167888934_"

SAI MUN JIKU

"*YAN NIGER NAKU 300F NE KACAL, KU TURAMA WANAN LAYIN +22795045822, SAI KUYI SCREENSHOT ZUWA WANAN LAMBAR 08167888934*"

"[8/14, 11:40 AM] Mss Flower : *ABULLE ANNOBA* "

(Sanadin neman haihuwa)

_Na_

_*Mss Flower*_

_&_

_*Mrs Abdool*_

EJ- 1D' FE-1D' 'DDG E3(

*                                                                    *

& *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* &

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*                                                                        *

*12*

"Mai gari tagumi ya zabga yana tunanin irin azabar da zaya sha, ta lafiya da ta dukiya in akayi auren nan, a kwanakin nan da zazza'bi yake kwana domin Abulle ta sako shi gaba, cikin dare har zabura yakeyi domin mafarkanta ne yake ta yawan yi tun bayan lokacin da ta fiddashi matsayin"

mijin auranta

"A 'bangarensu masu dukkan Abulle kuma, bayan tayi ligi ligi dasu aka kwashesu kai tsaye kemis aka wuce dasu Yagwalgwal aka fara dubawa kasancewar ita tsohuwa ce, diresin d'in kanta akai mata inda taji mummunan ciwo, sai ihu take a haka aka saka spirit da uban bandeji aka d'ad'daure"

"kan,"

"Ita kuwa Amarya banda kururuwa babu abinda kakeji nata, likitan chemist d'in na duba ta yace"

"""subhanallah baiwar Allah ya akayi hakan tafaru ne, kinga yanzu cikin nan yasamu matsala saura kadan ya 'karasa 'barewa"", wani mahaukacin ihu tasake tareda cewa ""shikenan Abulle kin kashe ni, Yagwalgwal Allah ya isa tsakanina dake duk ke kika kawo mana wannan muguwar shawarar gashi"

"yanzu kin ja min asara wayyo ni na bani na lallace"" haka take ta maimaitawa cikeda azaba"

"Likitan ne ke ta bata baki yana kiyi ha'kuri don Allah, nan da nan aka firda saura cikin aka mata"

"duk abinda yadace,"

"Ita uwargida bama tasan inda kanta yake ba, saboda mummunar karayar datayi a 'kafa an dai samu"

an mata d'ori da 'kyar ankuma shafa mata magunguna.

Maigari dake zaune cikeda jimami duk duniya ya ishe ya kifa uban tagumi sai zufa yake sharcewa

"akai akai,"

"Wani matashi ne ya fad'o fadar Mai gari hankalinsa a mugun tashe sai nishi yake, zubewa yayi"

"yana ""ranka ya dad'e akwai matsala fa, ga iyalinka can a kemis d'aya tayi karaya d'aya kuma tayi 'bari"""

"Mi'kewa Mai gari yayi a zabure yana ""ina kasamu wannan labarin?, suna ina ne?, meya samesu?"""

"ya fad'a zufa na tsatsafo masa saboda tsabar tashin hankali,"

"Matashine yace ""ranka ya dad'e ance sunje dukan Abulle ne shine hakan tasame su"""

"Mai gari zaman 'yan bori yayi tareda rushewa da kuka mai cin rai, nashiga ukku na abulle takasheni, saida nace su kiyayi wannan aljanar yarinyar suka 'kiya, ni kaina suna gani biyayya nake mata na zauna lafiya, amman saboda taurin kai shine suka tafi dukan ta yanzu ga irin ta nan"""

ya 'karashe zancen yana 'kara 'bare baki.

"""Mai gari yanzu ba lokacin maida zance bane muje tukun kaga halin da suke ciki"" cewar saurayin"

cikin muryar lallashi.

"Mi'kewa Mai gari yayi yana share 'kwalla tareda cewa muje, taka babbar rigarsa yayi Aiko ta tad'iyeshi ji kake timmm Mai gari a 'kasa, wani kukan yasake saki yana ""inalillahi wa innailahi"

"rajiun Abulle kashe ni zakiyi nima"""

"Da 'kyar aka d'aga shi suka nufi chemist d'in,"

"Mai gari shi ya biya kud'in sannan aka tattarosu Yagwalgwal aka nufi gida,"

"Mai gari komawa yayi fada ya zuba uban tagumi yana tunani, ""to tinyanzu nafara fuskantar"

"wannan barazanar ai Idan akayi auren ma kila kashe ni zatayi dole akiyin auren nan wallahi ko mai zai faru"" mai gari duk a tunaninsa a zuci yake wannan maganar,"

"A 'bangaren Abulle kuwa ko da ya fad'a mata sonta yake sai ta kece da wata uwar dariya, Mai Indomie kuwa nan da nan idonsa yayi 'kwal da hawaye domin a tunaninsa zata 'ki amincewa da shine. Chan Abulle ta dakata da dariyarta sanan tace "" bari nayi nazari akan wanan batu, ko mai"

"ake ciki zaka jini mai kama da ludayi"" ta 'karashe tana kwashewa da dariya"

*Dr Saddiq POV*

"Sanye yake cikin suit dinsa baka mai masifar kyau, yafito agaggauce kasancewar yakusa makara,"

"Part din mom din yashiga, yagaishe ta samasama, yajuya zaifata,"

"Kallonsa mom tayi tana ""a'a sadiq bazakayi break fast ba zaka fita"" mom wallahi nayi latti ne Ina"

"sauri Idan naje zanyi a can"""

"To ubangiji Allah y tsare Allah y taimaka, ameen Ameen mom nagode saina dawo,"

"Murmushi tayi tana daga masa hannu ""adawo lpia"""

"Kai tsaye motarsa yashiga, aguje ya isa Asibitin, ko parking bai gama ba yafito kasancewar kiran da ake tamasa akan zaiyi ma wata mata aiki,"

Fitowa yayi rikeda brief case dinsa ya nufi office nasa cikin sauri nurses dinda ke ta gaishe sa ma

"saidai kawai yadaga musu hannu ya wuce,"

"Mamakine yakama shi ganin office dinsa a bude, shiga yayi da mamaki cike a fuskar sa yana"

"kallon burdurwar dake kwance kan three sitter dinda ke office din,"

"Cikeda masifa yace "" ubanwa yace kishigomi min office without my permission, kina hauka koh, shin bance kar na sake ganin ki a gun aikina ba, ohh I know u want to tarnish my image koh arinka kallona mutumin banza koh, tunda daman already ke duk wanda ya ganki yasan ba mutuniyar kwarai bace daga kallon shigarki, cos a good lady can never dress to tempt a man, c'Mon get out"

"kafin na bude idona"" ya daka mata uwar tsawar da nikaina saida na tsorata."

"Mikewa tayi da sauri ta dauki handbag dinta tayi waje, ganin yanayinsa zai iya maketa,"

Kwafa yayi tareda saurin canza dressing zuwa na theaterya kwashi kayan aikinsa yafita dasauri

ya nufi thearter room......

*Mss Flower *

&

*Mrs Abdool*

_MASOYA MUNA JIRAN A NUNA MANA SOYAYYAR DA AKE CEWA ANA MANA

3 / 17