Advertisements
Chapter 1 Reading HA'DI DAGA ALLAH Kaddarar So by Khadijah Al'Eeman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

HA'DI DAGA ALLAH Kaddarar So by Khadijah Al'Eeman

Author :  Khadijah Al'Eeman Category :  Complete Novels

Chapter   1 / 10

1 to 3K   out of 29.9K words

[1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫

*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN

" _Da Sunan Allah mai Rahma mai jin 'kai_"
Wanan littafin "true life story" ne ban kwafa na wani ko wata ba, kuma banyi dan cin zarrafin wani ko wata ba.

**********
1 - 10
✍🏻 Wani tangamemen gida na hango mai girman gaske, gida ne Wanda ya amsa sunan sa gida, _na bude get din gidan a hankali na shiga_, gabanah sai da ya fad'i saboda gidan ya bala'in haduwa daga gani anarka kud'i a cikinsa, kuma duk Wanda ke zaune a gidan nan ba kara min attajiri bane, juyawan da zanyi sai na hango mutane nata kaiwa da komowa sai kace gidan sarkin Katsina.. Lol, ina karawa gaba sai na ga ashe ma'aikatan gidan ke kaiwa da komowa, kuma na fahimci cewan duka ma'aikatan kowa da bangaren da yake aiki, both of Maza da Matan.

Masu gadin gidan mutum biyu ne, Masu bama flowers ruwa da ban, masu kula da tsaftan tsakar gidan daban, haka zalika masu kula da fanin cikin gidan daban, _na kara shigewa ciki don in bama idona abinci_, na kalla cikin fallon da kyau naga ya hadu sossai colour din fallon red and white nace _woow_ na juya naga dining area shima ya bala'in haduwa, çan kuma sai na hango wata yarinya tana gyara dining din, ta jera wasu had'add'un kuloli, daga gani ba abinci kala daya bane aka dafa ba.

Sai kuma naji taku daga bayana, ina juyawa naga wata kyakyawar mata ta d'an manyanta, fara ce sol, kayan jikinta kadai ya isa ka gane cewa Matar gidan ce, ta karasa saukowa daga stairs din, tace *Nasrin* kin kammala hada break fast din ne?, tace eh Hajiya na gama komai, toh Ma shaa Allah, Jeki ki kira min *Na'im* amma fa idan baki Gandhi a falonsa ba karki shiga ciki ko ki kwankwasa ki juyo kawai ki dawo abinki, tace toh Hajiya, ta juya tana cewa a cikin ranta _ni mai zai kaini shiga ko kuma in kwankwasa mai kofa wanan mai shegen bakar zuciyar tsiya, shi kamar ba d'an gidan nan ba_ da wanan tuna nin ta karasa cikin fallon, colour Fallon kuwa gaba daya white ne, ta shiga da sallama yana yana zaune yana danne danne a Laptop,yasa three quartern wando da rigarsa short slip kayan white gaba daya *Na'im*(white man) kenan first born a gidan *Alhaji Harris Saif* amma su yan biyu ne dayan macece, ko dagowa beyiba sai dai ya amsa sallaman da tayi ciki ciki fuska a murtuke, tace Hajiya tace kazo angama hada komai, yi yayi kamar be jita ba, sai da ta maimaita maganarta sau uku tukunna ya Daka mata tsawa Wanda yasa ta firgita sossai yace ance miki banji bane ke mayya ce wai?, nan da nan sai hawaye a fuskanta tace kayi hakuri naga baka amsa bane shiyasa na maimaita.

Yace sai anyi magana ki wanni sadda kai kasa mtsw *poor girl* kawai, inda sabo ta saba da bala'in sa kullum sai ya zageta koh ya dakka mata tsawa, ta juya da nufin tafiya yace kice bantashi ba, tace toh cikin sarkewan murya.

Sai sukaji ance kai Yaya Na'im karya bata dace da kai ba wlh, kuma ni na rasa mai Nasrin ta tsare maka a gidan nan, kaita hantaranta kamar ba mutum ba, kuma nidai naga da arziki da talauci duk dayane a wajen Allah, domin shine mai badawa, *NA'IMA* kenan 'yar uwar haihuwan Na'im, dukansu zasu kai shekara ishirin da takwas, Nasrin na jin abinda ta fada ta juya da Saudi ta bar wurin, shi kuma Na'im ya tashi yana nunata da yatsa yace ni wai tsaran wasanki ne?, ya bita zai duketa ta ruga da gudu a haka suka kai har dining area ta tsaya kusa da *HAJIYA NABILA* tace mommy kinga _white man_ koh, yace me wayace ki kira sunan nan, ni sa'anki ne wai, Dady kana jin abinda Na'ima take min amma kayi shiru sai Mommy tace kai dai wlh anyi baban banza, Dady yace a'a karkice haka, ki bincika kiji meya had'asu.

Na'ima zatayi magana kenan sai *SHUREM* dake zaune ya tab'e fuska yace, _I am Hungary_ na gaji da jiranku ni zan fara cin nawa gaskiya, sai Labiba tace kullum sai fada kamar wash Tom and Jerry, sai Na'im ya kallesu ya galla musu harara, yace shiyasa nake son *SAFIYYA* ita ba ruwanta da surutu, Ku kuma kullum sai cacacaca like parrot, Dady yace toh anji Ku zauna muci abinci, suka zauna sukayi adu'a suka fara cin Abinci..

Iyalan gidan Alhaji Harris Saif kenan, shahararen mai kud'ine mai fada aji, ya mallaki manyan kamfanoni, da gidan biredi, yana da gidan ruwa, ga kaddarori da yake da su, yana da gidajen da yake bada haya, yana kuma business tsakanin Nigeria, Ghana,India da kuma Dubai.

Matarshi daya Hajiya Nabila, mata mai mutunci da karamci ga son mutane ga tausayin talakawa,
Allah ya azurtasu da yara Biyar, Na'im da Na'ima (twins) ne sunyi karatu a Malaysia, inda Na'im ya karanta business admin, Na'ima kuma Doctor CE a bangaren mata,Sai mai bi musu mai suna Labiba,tana karanta micro biology a B.U.K Kano wanan shekaran zata gama, sai mai bin ta Safiyya,tana karanta mass com a A.B.U zariya,tana Three hundred level, sai Autansu Shurem,yana Hampos international scul, s.s 3, sun taso cikin gata da kulawa,ga tarbiya Ilimin boko da na Islamiyya dai dai gwargwado sun samu,sai dai Na'im yana da wasu d'abi'u , toh koma mene ne d'abi'unsa zakuji.

*EDITING BY*
NUSNIM (twin sis)
*DEDICATED TO*

Anka,Maman shakur,Munay,Mamu,Afrah and Rash kadam.. Luv u all😘
[1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH* 👫

*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN

*11 - 15*

*************

✍🏻Alhaji Haris Saif suna zaune a u/rimi lowcost ne, 'yayyansa ba masu son fita bane akwai su da son mutane,amma in ka cire mutum daya wato Na'im, shi a rayuwarsa baya son talaka, kuma duk kudinku idan ya ganka sai ya rainaka,burinshi befi ace kullum yafi kowa ba, abokanasa ma hakuri sukeyi dashi, kuma halinsa ne yasa sauran abokanan sa suka gujesa, don baza su iya da wulakancinsa ba...

Wanan dalilin ne yasa baida budurwa kwata kwata, gani yakeyi har yanzun be samu daidai dashiba, abokanansa kuwa yanxun biyu ne kwata kwata daga Ahmda sai Lukman, suma ayi fad'a a shirya, yawan zuwa gidan da sukeyi ne yasa Ahmad yaga Na'ima ya 'kyasa, a yanxun kowa yasan cewa Ahmad da Na'ima na son junansu....


Shiko Na'im anyi anyi ya fito da mata ya'ki waishi bega wadda yake so ba har yanxun, iyayensa kuwa nason suka sun had'a su da Na'ima amma har yanxun shiru.....

Na'im ba wance ya tsana a cikin gidansu, sai mai aikin 'bangaren abincinsu, wato Nasrin,ya dauka tsanan duniya ya d'aura mata ba daman ta sake indai Na'im na wurin, al'amuran dake faruwa kenan a cikin gidan Alhaji Haris Saif.


*WACECE NASRIN*
Nasrin yar gidan *Mallam 'kasim* ce, suna zaune suma a u/rimi a layin rafin dad'i, sunan mahaifiyarta *Fatima*,tanada 'Kanne uku, *Habib* ke binta,sai *Salim*,sai autansu me suna *Nadra* , su talakawa ne sossai, sai sai mahaifinsu ya fita ya samo da kyar, tukunna zasu samu abin sawa a baki....

*Dalilin da yasa ta fara aiki a gidan Alhaji Haris Said*

Shine Mahaifinta yazo ya fara rashin lafiya,ba mai fita yaje ya nemo,sai 'kanwar mahaifiyarta *Aisha* wadda dama tun farko ita ke aikin irrin abincin gargajiya a gidan Alhaji Harris Saif, itace ke kawo musu abinci......

Ita ta dauki Nasrin ta kaita makarantar Primary, ta gama ta sata a secondary, daga nan ta kaita makarantar koyon abinci, Nasrin yarinya ce mai Haza'ka gata da farin jini mutane na sonta sossai.....

Ta gama makarantar koyon abincin, ba abinda bata iya dafawa ba, ciwon mahaifinta yayi tsanani sossai, Ashe ciwon ajaline sunyi kuka ita da mahaifiyarta da 'kanenta sossai, haka sukaci gaba da rayuwa,'kanwar mahaifinta ke samowa ta basu suci, mahaifiyarta ta fara sana'ar d'anwake ita ma,kuma Alhamdulillah suna samu sossai, ana haka Innarta Aisha wato 'kanwar mahaifinta ta fara ciwon 'kafa,har ta kai ga bata iya fita taje wurin aikinta.....

Hajiya Nabila kuwa ta shirya taje har gida ta gaisheta, anan ne Inna Aisha ta roketa akan Nasrin ta maye gurbinta, ta bata labarin karatun da Nasrin tayi, tace ba matsala,aka kira Nasrin ta ganta, ta dauketa suka tafi, Hajiya Nabila ta lura Nasrin akwai natsuwa ga tarbiya, tana da hankali sossai, Hajiya Nabila na matu'kar son Nasrin, har mamakin son da Hajiya take nuna mata takeyi....

Da haka Nasrin ke samu suci abinci, kuma take biya ma 'kanenta kud'in makaranta, ta na Neman ma Inna Aisha maganin ciwon kafa, kar wai kuce mahaifinta beda wasu 'kanen, a'a yanada wasu 'yan uwan, mallam barde da mallam shu'aibu kuma sunada rifin asiri daidai gwargwado, amma basu damu da iyalan d'an uwansu ba,wanan kenan.....


Alhaji Harris Saif na kishin gid'e a falonshi na sama Hajiya Nabila ta shigo ta zauna tace Daddyn yara kana nemana gani,yayi murmushi yace Hajiya wai bakya ma yaronki magana ne akan aure ?, tace wlh Ina masa amma haryanxun shiru,amma ka d'an kara masa lokaci In shaa Allah zeyi, yace toh ba damuwa, Allah yasa mu dace,ameen....

Yau ta kama Monday Alhaji ya fita haka Hajiya taje wani meeting na Ummul-khair foundation, yaran kuma kowa ya koma school, daga Na'im,Na'ima sai masu aikin gidan,Nasrin ta gama abinci ta had'a komai a dining ta gayawa Na'ima ta fito zata shiga bangaren Na'im kenan taji ance mayya dawo nan ya daka mata tsawa,ta juyo da sauri tana kallonsa, yace uban me zakiyi min a 'bangare, jiki na rawa tace abinci ne daman na gama zan kiraka, yace zonan, ta juyo ta bishi har dining d'in, lokacin kuma Na'ima ta sauko ta zauna a dining d'in, Na'im yace me kika dafa?, tace fried rice ne da farfesun kayan ciki, yaja tsaki yace kije ki dafa min _jalouf rice with cabbage da farfesun hanta_ Na'ima zatayi magana yace wlh I will deal with u stupid kawai, will u get out of here, ya daka ma Nasrin tsawa, da sauri ta bar wurin, ya juya ya kalli na'ima yace idan ina magana kina sa min Baki sai na karyaki, tace mommy ma ta karyaka wlh, yaja kula ya fara zuba abincin, tace Yaya Na'im abincin da kasa ayi maka fa wa zaici?, ya ce ina ruwanki, tayi shiru ta fara cin abincinta.....

**********
After one hour Na'ima ta gama cin abincin ta koma ta zauna ta kunna kallo shi kuma ya d'auki wayan shi yana Dane dane , haryanxun yana kan dining din be tashi ba, ta dauko kulan ta fito daga kitchen d'in....

Tana kaiwa dining d'in yasa mata kafa ta fad'i abincin ya zube, ya tashi ya ce sai ki kwashe ki juye a Leda ki tafi dashi gida, dama babu...

Ya harareta ya wuce, Na'ima ta taso tazo ta d'agata tace bakiji ciwo ba koh, ta gyada kanta, tace ki daina jin tsoron shi , inya miki ki rama, mommy na nan ba abinda zai miki...




*EDITED BY*
🍒Nusnim ( *TWIN SIS*)🍒


📝 *DEDICATED TO*📝
Nafee Anka,Mm Shakur,Munay,Mamu,Afra and Rash Kadam
Love u All😘
[1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAHH*👫

*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN

*16-20*

*************

✍🏻Nasrin tace haba Ni'ima ta Yaya kike tunanin idan ya min abu zan rama, ai a 'kar'kashin shi nake, komai zaiyi min sai nayi hakuri, nasan komai lokaci ne,zai daina watarana, kuma ko ance watarana ma ya ganni ya min bazai min ba......

Na'ima tayi dariya, tace Nasrin wanan haka yake,shima d'abi'a ce ya d'aukota lokacin da muke Malaysia, baya tarayya da 'ya'yan talakawa sai na masu kud'i, kuma ya wulakanta mutum a wurinsa ba komai bane,kinga nima kaina ba wai ya barni bane, idan ya tashi muguntashi yi yakeyi har akaina, sai dai wani abunda ke birgeni shine,nice kad'ai abokiyar shawaran Yaya Na'im, kuma yana matukar sona.....

Kiyi hakuri da halinsa mu dai muna sonki,kuma In shaa Allah baza mu wulakantaki ba, ki cigaba da aikin ki Allah ya taimaka, tace Ameen Na'ima nagode......

Sai sukaji gyaran murya suna juyawa Mommy suka gani a tsaye tayi murmushi, tace halan ya mata wani abun ne?, Nasrin tace a'a bakomai......

Mommy tace haba Nasrin ai a tunanina babu abinda zaki 'boye min, tsakanina dake ba wani 'boye 'boye, ta juya ta kalli Na'ima tace meya faru ne?, a nan ta 'kwashe komai ta fad'a mata, tace babbar magana, Na'im bazai taba canjawa ba, amma komai lokacine,nasan wata rana zai bari,Allah ya shirya suka amsa da Ameen, tace je ki had'a abinci, tace toh ta juya ta wuce...

Na'ima tace ni tausayi ma take bani wlh, duk ya bi ya takura ma rayuwarta, ba daman yaga tana walwala, Mommy gaskiya kiyi wani abu akai idan ba haka ba wata rana zai mata abinda yafi haka wlh, ga yarinyan akwai hakuri, kuma tana bala'in tsoron shi.....

Mommy tayi murmushi tace na samo mafitan yadda zai daina tsanan mata bama Nasrin kad'ai ba, rayuwarsa ta dawo sabuwa,dan nagaji da hali irin na Na'im wlh, kullum abinda yake tsurowa dashi da ban....

Na'ima tace Mommy menene shi tace karki damu zakiji kome nene idan na gama shawara da Daddyn Ku, Allah yasa mu dace, tace ameen mommy...

Na'im tunda ya shiga d'aki be fito ba sai bayan sallah la'asar, ya sauko yazo ya zauna kusa da Shurem, shi kuma shurem ya na buga game da wayan mommy, ya daka mai tsawa yace ban hanaka buga game ba, ba gobe ne zaku fara waec ba?, ina tanbayanka kayi shiru, yace to Yaya Na'im ai ina karatu kuma ban taba zuwa ko na biyu ba, na d'aya nake zuwa, aikuwa ya sa hannu ya kama kunnensa yace daga yau sai yau na'kara ganin zakayi exam kazo kana game sai ba 'ba'bbalaka stupid kawai, Shurem kuwa ya tsala wani irin ihu....

Sai ga Mommy da Daddy sun sauko da sauri, Na'ima da ke kitchen Nasrin na koya mata dambun nama suka fito da gudu tare da Nasrin din, kowa na tanbayan lfy, Na'im yace yaron nan bazaiyi karatu ba sai ya kwaso muku f9 tukunna, wai game yakeyi...

Daddy yace to kai Shurem me yasa kake game tunda gobe zaka fara waec ai natsuwa zakayi kayi karatu domin ka fito da good result, ko ba kason kaje wajene kayi karatu?, Shurem yace Daddy ni irin nasu Aunty Labiba da Aunty Safiyya nakeso, nima bani da ra'ayin fita waje gaskiya, nan Kadsu ma ya isheni, Na'im yace ji baki a wurin, wai kai Auntah koh, Mommy tace ka barmin yaro dan Allah, haba kai haka akayi maka ne wai?, yace mommy kekike 'bata yaron nan wlh....

Na'ima tayi carab tace kai Yaya Na'im kai wa ya takura maka ne wai?, komai fa kakeso kayi kanayi, shima ka barshi yayi yadda yake so, kasan yaron akwai brain ai........

Lokacin ya juya yana kallon wurin da take, kawai ya hango Nasrin a wurin yace ke.....

Lallai ma uban wa ya baki izinin zuwa nan wurin, Family na magana kin wani kutso kanki didn't I tell u dat idan muna magana ki daina zama a wurin, kalleki kazama kawai bar nan kafin yanxun nan in bibbigeki wlh.....

Dady ya tsaya galala yana kallon shi, yace Na'im wai kai bazaka canja halinka bane?, tarbiyan dana baka kenan?, ashe Na'im bazaka ma kanka fad'a ba?, ni ina son talakawa kuma ina tausayinsu, haka mahaifiyarka, haka 'kanenka amma kace kai talaka ba abakin komai yake a wurinka ba, ka wulakanta mutum ba komai bane, to Allah ya shiryeka....


Ya juya ya bar wurin yana mamakin hali irin na d'ansa, abin na damunsa, ya rasa menene mafita, da tunanin ya koma d'akinsa......

Itako Mommy cewa tayi kai dai wlh Allah shi zai shiryeka ba kowa ba, ka canja halinka tunda wuri, ta juya ta Mara ma Alhaji baya.....

Ita kuma Na'ima tace kagani ko Yaya Na'im kullum ina baka shawara bakaji Allah ya ganar da kai, ta juya ta wuce ta koma kitchen d'in......

Ta ce Nasrin kiyi hakuri kinji, Nasrin tayi murmushi tace ai in da sabo na saba, karki damu, mu cigaba da abinda mukeyi.....

Shiko gogan naku kad'a kai yayi ya tafi Garden abinsa....

Mommy ta shiga d'akin Dady, tace Dadyn yara, niko ina da wata shawara in da zaka amince, yace menene shawaranki tace mai zai hana a had'a auren tsakanin Na'im da Nasrin, ya d'ago kai da sauri ya kalleta, yace mommyn Yara kina ganin idan mukayi haka bamu cutar da ita ba?, tace Nasrin ce kad'ai nayi imanin zata sa Na'im ya canja halinsa, domin tana da tarbiya, kuma na tabbata in na samu iyayenta zasu fahimce ni, zakuma su yarda da abinda zan fad'a musu....

Dady yaja dogon numfashi yace toh idan kuma shi yana da wadda yake so fa?, Mommy tayi murmushi tace Na'im d'in lallai kam, beda wata wadda yake so, idan kuma yana da ita kace ya fito da ita, ni kuma in dai da ita toh wlh zan janye maganata......

Yace to bari nasan yadda za'ayi, miko min wayata, ta mika mai, ya danna Number Na'im saida tayi kamar zata tsinke sannan ya d'auka, yayi sallama, ya amsa yace kasa meni a fallona yanxun nan, bai jira mai zaice ba ya kashe wayan.....

Na'im gaban shi ne ya fad'i, yace toh fa lpy irin wanan kiran, bari inje inji....

Ya fito zai shiga Main fallo kenan ya hango abokanansa wato Ahmad da Lukman suka gaisa, yace musu Ku shiga, ni bari inga Dady, Ahmad yace Na'ima na nan dai koh, yace baka da kirki ina suruminka baka jin kunyanah?, yace kunyan me zanji, a haka suka shiga daga ciki shi ya wuce wurin dady.....

Ahmad kuma ya kira Na'ima tazo suka Lula duniyan soyayya Lukman kuma na zolayansu....

Nasrin ta kawo musu abin mosa baki, Lukman yace woow wanan kyakya wan fa, Ahmad yace itace wadda take shan wahala a hannun Na'im wlh.....

Yace da za'abani ai da na aura,Na'ima tayi dariya, tace kai Lukman, ai kai kana

1 / 10