Author : Khadijah Al'Eeman Category : Complete Novels
burin su, kuma sai na canja maka halinka, sanan in koya maka sona duk da nasan nima ba sonka nakeyi ba amma zanyi hakuri, zan jure watarana zai zama labari, tayi kwafa ta tashi ta cire kayanta tasa night gown ta kwanta......
A 'bangaren Na'im kuwa tunda ya shiga 'bangarensa ya canja kaya ya kwanta, yana ta tuna nin yanxun haka zai cigaba da rayuwa da wanan 'yar talakawan, gaskiya Mommy ta cuceshi, shi wallahi ya tsaneta ko 'kaunar ganinta ma bayayi, mtsw ko da yake ma next week zai fara zuwa office, ya huta ta ganin ba'kin ciki ya kwanta.......
*WASHE GARI*
Nasrin ta tashi ta kimtsa ko ina, ta gyara gidan tas, ga wani turare da ta bad'e gidan dashi, ta yi wanka tayi kwalliya, tasa wani atampa red and white, yayi mata bala'in kyau, ta feshe jikinta da turare ga d'an kwalin nan an nad'a shi kamar gwagwaro, ta na zaune a fallonta tana kallo.....
Na'im kuwa ya tashi yayi wanka, yasa red polo da white jeans, ya bud'e kofar bedroom d'insa wani 'kamshi ya daki hancinsa, ya ja numfashi, yace "woow" irrin wanan 'kamshi haka, shi dai yana bala'in son 'kamshi ga son tsafta kamar ba namiji ba....
Ya fito ya shiga fallonta hankalinta na kan t.v bata ma lura dashi ba sa ji tayi ance daka mata tsawa "ke mayya, anzo an sami kallo an wani zauna kamar wata wawiya, gida ba a da irin shi, ba'a saba ganin irinshi ba, kin wani 'kura ma t.v ido sai kace wata doluwa,......
Ta tashi tazo ta d'an rusuna tace "ina kwana" ya hankad'eta saura kad'an ta fad'i yace da ban kwana ba zaki ganni, ya kalleta ya kalli kayan jikinsa yace toh fa, wato har kaya zaki rinka sawa iri d'aya da nawa, saboda kin raina min wayau to tashi kije ki cire shi ki canja wasu tun kafin na tattakaki a nan wurin, kuma ki dawo ina jiranki......
Ta tashi ta wuce d'aki ta d'auko wani material blue and white tasa ta 'kara feshe jikinta da turare ta fito, ya kalleta yayi tsaki zaiyi magana kenan aka kwankwasa kofa, ya juya yace ke 'yar aiki uban wa zaije ya duba miki, ta juya ta tafi ta bud'e 'kofan, Nafeesa mai girkin gidan su Na'im ce ta yanxun d'auke da basket, suka gaisa ta mika mata tace inji Hajiya, ta amsa tace ki gaisheta, ta juya ita kuma ta koma ciki....
Taje dining ta ajiye ta koma sama tace Nafeesa ce ta kawo abinci wai inji Mommy, yace muje dining d'in, suna zuwa ya daka mata tsawa yace "ni zanja kujeran"?, tayi Sauri taja mai kujeran ya zauna, zata zauna kenan yace "waye tsaran wasanki da zakici abinci tare dashi"?, sai a bari sai naci na rage tukunna....
Taja ta tsaya tana kallonsa, ya harareta, ta bud'e kulollin chips ne da egg, sai ferfesun kan rago, flask d'in kuma kunun gyad'a ne a ciki, ta zuzuba mai, ya fara ci, sai da ya 'koshi tukunna sanan ya tashi ya wuce, ko kallonta beyi ba.....
Ta girgiza kanta, ta koma ta zauna tana tunani hali irin na Na'im, amma komai lokaci ne with time, taci ta 'koshi taje ta wanke kayan ta goge dining d'in ta koma sama, bata dad'e da zama ba ta fara jin bacci, ta tashi ta shiga cikin d'akinta ta kwanta sai bacci, tana bacci taji an watsa mata ruwa ta mike da sauri Na'im ne a tsaye yana huci, yace to atashi ayi sallah, daga ci sai bacci, ba'a saba cin irin wanan mai dad'i ba, kinzo kin kwanta, ni zan fita kafin na dawo a gyara min d'akina idan ba haka ba jiki yayi tsami, saura kuma a je ana ta'be ta'be yar aiki kawai, ya juya ya fita abinsa.....
Nasrin ta girgiza kai tana murmushi, tace zanyi maganinka ne wallahi, daga yau ka daina min masifa, ta tashi ta Shiga toilet tayi alwala tayi sallah, ta fito ta shiga d'akinsa komai tsab, bata san mai zata gayara ba.....
A haka dai ta 'kara gyarawa ta share tayi moping, ta sa turare, tabi ko ina na gidan ta gyara duk da bai 'baciba, ta zo wurin dining taga abinci , har ya zuba ya ci ta bud'e taga p
Fried rice ne da ferfesun kifi, sai pineapple juice, taci ta 'koshi ta gyara wurin sanan ta shiga ciki tayi wanka, ta fito ta yi sallah tana idarwa ta d'auko wani dogon riga a cikin English wears d'inta, 'kasan shi ta baya da tsagu, saman shi a bud'e ana hango dukiyan fulaninta, rigan colour d'inta purple ne, ta matseta sossai, sannan rigan shara shara ce, ta dauko hula white tasa, ta zubo da gashinta ta baya, ta 'karshen gashin tasa d'an 'kara min ribbon white and purple, tayi simple make up, ta feshe jinkinta da turare gashi ta shafe jikinta da humra, ta dubi kanta a madubi, tace anya zan iya kuwa......
Wata zuciyar tace mata "karki manta ga lada, ga kuma burinki da kike so ki cimma, ki daure ki cire kunya, ki nemi lada, ki jawo hankalinshi, ki faranta ma mutanen da suke so su kyautata miki", tayi murmushi, ta d'auki cewing gum mai 'kamshin tom tom, tasa a bakinta, ta d'auko sim d'inta da Sabon wayar da aka sa mata a lefe dama ta riga da tayi charjinsa ta fita taje falon 'kasa ta zauna tasa, ta kira gida, sukayi waya da kowa.....
Ta kira Mommy suka gaisa, tace mata komai lafiya koh?, tace "eh mommy ba komai tace yanxun zan aiko Nafeesa da abincin daren ku tace toh mommy, sukayi sallama, tana kashewa Na'im na shigowa....
Ya kalleta sama da 'kasa ya watsar, ta ce mai sannu da zuwa, ya juya yace "ke ni tsaran wasarki ne, dawa kike?, tayi murmushi "tace da Na'im nakeyi mana, idan banyi da kai ba dawa zanyi, ya tsaya yana kallonta da mamaki, yace "ke 'yar talakawa, wawiya, yaushe kika samu dama a gidan nan har kike kallon fuskana kike gaya min magana" .....
Ta d'aura 'kafa d'aya kan d'aya, tayi murmushi, tace daga ranan da aka d'aura mana aure, d'inbin al'umma suka shaida, ta mike tana taunar cingum ta kai dai dai kan step, tace Na'im inaso kasani daga yau Nasrin ta daina jin tsoronka, kuma wallahi duk zaman da zakayi dani I am ever ready for dat, ta juya ta haye sama ta barshin a nan yayi mutuwar tsaye.....
*EDITED BY*
πNUSNIM ( *TWIN SIS*)π
π *DEDICATED TO*π
Nafee Anker, Mm shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you allπ
[1/25, 7:57 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*51 - 55*
**********
βπ»Na'im yayi shiru yana mamakin Nasrin, yaushe yarinyar nan ta zama haka, dama tana da baki?, wallahi bazan yarda da wanan iskancin ba, yaushe ya bata dama har ta fara mishi rainin wayyon nan, yayi kwafa ya bi bayanta zuwa d'akinta.....
A lokacin Nasrin ta cire kayanta ta d'aura towel, ko ciyanta towel d'in bai kai ba, ta danna handle d'in bathroom d'in kenan ya bud'e kofa ya shigo ya ce "ke 'yar aiki, ta tsaya bata juyo ba, yace bazan yarda da wannan iskancin naki ba, kina jina koh, nan ba gidanku bane bare kice zaki rinka shiga irin yadda kike so, kuma ma a gidan naku ina kika samu matsayin sa kaya irin wa'inan masu tsadar gaske?,.....
Ta juya ta kalleshi zatayi magana kenan aka danna bell d'in fallon 'kasa, tace "heh relax" kwantar da hankalinka, menene na d'aga hankali da tada jijiyoyin wiya, ai ni banga abin fad'a an an ba, aure ne fa tsakanina da kai bawai zaman daduro mukeyi ba, duk abinda zansa halaliya tace don na tabbata da halal aka saye shi, tsada kuma da kake cewa akwai kwandalar ka aciki ne?, Iskanci kuma baka ga komai ba, nan gaba ma da ka fara son 'yar talakawa zan fara karuwanci, amma fa karuwanci mai lasisi, ga lada ga farin ciki, tace sorry sweet heart, kaje ka duba mana Nafeesa ce ke knocking kasan na fara jin yunwa, saboda abincin gidan su Na'im mai dad'i ne yanxun na fara cin irinsa, tayi mai blowing d'in kiss, ta shige bathroom ta rufe da 'karfi abinta.......
Yace "ohh ya Allah wai meyasa kwata kwata Mommy ta hanani dukan yarinyar nan ne, ni kawai anja min masifa an aura min yarinyar matsiyata, mtsww, ya juya ya fita yaje ya bud'e kofar, ya amsa basket d'in ya juya ya shiga ciki,.....
Ya kai dining ya a jiye, ya juya ya koma sama domin ya watsa ruwa, yana shiga d'aki wayarsa ce ta fara ringing, ya d'auka Ahmad ne yace "haba sirikina tunda ka agwance kwata kwata ko kira babu", Na'im yaja tsoki yace kai dai ka Sani wallahi ya gida, ina Na'ima?, daga d'aya 'bangaren yace gata nan laulayi ya sata a gaba, kasan na kusa zama baba, Na'im yace "inda kafi auki kenan wallahi, Allah ya raba lafiya, yace "ameen", Ahmad yace saura kai sai ka yi da gaske, yace kaga mallam sai anjima wanka zanyi, ya katse wayar ya wuce bathroom abinsa......
Nasrin ta gama wanka ta fito tayi shafa, ta shafe jikinta da humra mai d'aukan hankali, ta duba kayanta ta rasa wadda zata sa, sai can ta hango bum short red, ta d'auko da riga mai one hand iya cibiya ya tsaya, colour ta white tasa ta feshe jikinta da turare, ta dauki 'yan kunne red and white tasa, tayi kwalliya sossai tasa red lipstick, ta dauko white hula tsakiyar sa a bud'e tasa, tasa red ribbon a tsakiyar, ta sa mouth freshner mai 'kamshin kankana, ta juya ta fito, fitiwanta yayi dai dai da fitowanshi, yasa three quarter wando da shirt shima white, suna had'a ido ya d'auke wuta, da kyar ya had'iye miyau, ta matso da sauri ta d'aga wayanta tana cewa "zo muyi salfie" daman yau zaka bud'e min wasapp nima in fara, ko ya kagani?,....
Ya hankd'eta, yace "you are very stupid" kina haukane, ni tsaranki ne wai, 'yar talaka, 'yar aiki dake,zaki rinka had'a jikin ki dani,toh bari kiji idan ma sona kikeyi ni bana sonki, kuma karki ta'ba tunanin zan so ki idan ma mafarki kikeyi, "you better wake up", dan bazan ta'ba sanki ba....
Tayi murmushi tace "Na'im or white man" sunanka?, let me tell you the fact, bantaba sonka ba, yanda kake ganin an maka dole, nima haka aka min dole, amma ni ina da tarbiya kuma duk wani umarni iyayenah ina 'kokarin bi, domin su suka haifeni, sune gatanah, duk abinda zanyi bazan ta'ba biyansu ba, and let me tell you one thing, da talaka da mai kud'i Allah ne ya hallice su ba mutum ba, kuma shi ya ga dama yayi mai kud'i yayi talaka, Dan haka ni kud'inku basu a gabana, "to hell with you and your fucking money".....
Good sight d'ina kawai ka sani baka san bad sight d'ina, "from now hence forth" zaka san waye Nasrin, bani da kyau in aka kaini bango wallahi, ta harare shi ta juya ta koma d'aki jikinsa yayi sanyi sossai, yayi shiru ya girgiza kanshi kawai ya wuce dining, yaci ya 'koshi ya tashi ya tafi garden......
Nasrin kuwa tunda ta shiga d'aki ta ke kuka, inda ma to gode ma Allah duk masu cewa suna Sonta, 'bata ta'ba amincewa ba, da yanxun wula'kancin da Na'im zai rinka mata sai yafi mata ciwo....
Zata daina shiga harkan Na'im kwata kwata, zata roki Na'ima ta roka mommy a maida ta makaranta kawai, 'kila hankalinta zaifi kwanciya, ta bud'e fridge ta dauko five alive da icing cake 'kanana da aka zuba a ciki, taci ta 'koshi ta rufe kofarta ta kwanta.......
*EDITED BY*
π NUSNIM ( *TWIN SIS)*π
π *DEDICATED TO*π
Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you allπ
[1/25, 7:57 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*56 - 57*
**********
βπ»bata farka ba sai after sallah magrib, ta watsa ruwa tayi sallah, ta gyara d'akinta, ta fito ta gyara ko ina, ta lura kamar baya nan, ta shiga 'bangaren sa, ta gyara ko ina tasa turare, ta turare gidan, ko ina 'kamshi yake yi......
Taka abinci aka dining ta gyara mai zama amma bata ci ba, ta shiga kitchen ta dafa Indomie ta ci, ta wanke komai, ta gama ta koma d'aki, tayi sallah esha'e, ta sa night gown wandda dashi da babu duk d'aya suke, ta hau gado ta kwanta abinta......
Wuraren nine ya shigo gidan, ko ina tsab tsab, ya wuce dining area, ya bud'e abincin yaga bata ci ba, ya zauna yaci, ya tashi ya wuce sama,ya le'ka fallo bata nan har zai wuce d'akinsa, sai kuma ya fasa ya juyo, ya murd'a kofanta ya Shiga,'can ya hangota a kwance, tayi d'add'aya a gado, ya 'kare mata kallo ya bud'e fridge ya d'auko five alive me shegen sanyi, ya bud'e yana murmushin mugunta, ya watsa mata ta tashi a firgice, taje ta 'kan 'kameshi tana maida numfashi........
Ya tureta ta 'kara 'kan 'kan'kameshi, tana cewa "baby" sanyi nakeji wallahi, ya sa 'karfi ya hankad'eta yace ban hanaki ta'ba ni ba?, bance ki daina ta'ba min jiki ba, duk randa kika 'kara ta'bani "I will make sure I deal the hell out of you, stupid", ta kalleshi 'kasa'kasa tace "heart" to ba kai bane ka watsa min ruwa ina bacci cike da mafarkai kala kala, wai ni da kai muna ta wasa da ruwa,......
Ya watsa mata harara yace "uban wa kika banmawa wancan abinci da zaici?," tace kai fa kace abincin gidan ubanka ne, don haka nima naci na gidan ubana, dan haka ka had'a duka kaci bazan ciba,ya watsa mata harara, yaja gashinta da 'karfi suka fita tana ihu, wallahi "sweet love" akwai zafi, ka sake min gashina please, sai da ya jata har wurin dining d'in yaja kujera taki zama, ya zaunar da ita, ya jawo flasks d'in ya zubo mata tuwon shinkafa da miyan agusi, ya zuba apple juice a cup, ya ce ohya bismillah, ta kalleshi tayi murmushi a ranta tace "bakasan Nasrin bane inada bala'in wayau, karka ga ko university banyi ba, wallahi nafi mai dagiri iya shu'umanci".....
Ke Nasrin ba dake nakeyi bane wai, ta juyo da sauri tace d'azun na bige hannu ko dagawa bana iya wa, to tayaya zan iya cin abinci?, yayi tsaki yace kisa bakinki akan plate d'in ki rinka ci, tace sai kace dabba, wallahi bazan sa ba, yace toh ai keda dabban banbancin Ku kad'an ne, ta d'augo kai da sauri tana kallonsa tace "Na'im ni kake kira da dabba, nan da nan hawaye ya sauko mata kan kumatu, tace mai na maka da zaka rinka kirana da dabba, kace min wawiya, banza, 'yar talaka amma ban ta'ba nuna maka ya dameni ba, Na'im da mahaifina nada rai ko sanina ma bazaka ta'bayi a rayuwa ba, amma saboda mutuwa tamana yankan 'kauna, kuma Allah ya ba mu 'yan uwan baba marasa zuciya, shine dalilin dana fara aiki a 'kar'kashin Ku, kake cin zarrafina yadda kake so.......
Iyayenka suka nuna suna son aure na da kai, mahaifiyata ta'ki yadda, amma saboda hujojin da ta kawo mata yasa ta amince, ta min magana a matsayinta na Uwa da ta d'auki cikina na tsawon wata Tara, ta haifeni lokacin da take nakuda tamkar zata mutu, ta raineni, cina, shanah, ta min komai a rayuwa, na yarda na mata biyayya, na amince da aurenka Wanda nasan ba abinda zai tsinana min sai ba'kin ciki da taikaici, saboda ban ta'ba sonka ba, amma saboda in faranta mata rai na yarda na amince da auren Wanda ya tsaneni saboda ni talaka ce, bani da gata, na yi auren 'kaddara, wallahi Na'im da banyi ma Ummanah a'kawarin zama dakai lafiya ba, da na nuna maka bad sights d'in Nasrin,......
Ta mike ta fara tafiya tana kaiwa dai dai wurin steps tace "Na'im rashin biyayya ga iyaye ba komai zai haifar maka ba, sai d'a mara ido, baza ka ta'ba gamawa da duniya lafiya ba", ta juya tayi hayewar ta sama.......
Na'im kanshi yaji ya fara sara mai sossai, ya rike yana fad'in " ~Innalillahi wa'ina illaihi raji'un~, a cikin 'kan'kanin lokaci komai ya tsaya masa cak......
*EDITED BY*
π NUSNIM ( *TWIN SIS*)π
π *DEDICATED TO*π
Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you allπ
[1/25, 7:57 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*58 - 60*
***********
βπ»Na'im tunda ya shiga d'aki ya kwanta, yake ta tuna nin maganganun Nasrin, abinda take fad'a masa fa gaskiya ne, shi wallahi besan ya akayi ya zama haka ba, shi dai kawai bai ga macen da zai zauna da ita bane har yanxun, "huh" abin na da munsa.......
Yau satin Nasrin biyu a gidan Na'im, amma in banda fad'a ba abinda sukeyi, kullum da rigiman da zasuyi, sai dai abinda ta lura dashi, shine ya rage zaginta da yakeyi, amma fa mugunta kala kala yake mata......
Nasrin na zaune a Fallon 'kasa taji anyi nocking, ta tashi ta bud'e, wa zata gani inba Na'ima da Ahmad ba, ta rugume Na'ima tana murna, suka shigo ciki, Ahmad yace Ina maigidan?, Nasrin tace "yana ciki yana bacci a taso shine?, yace gaskiya da zaifi ina son ganinsa, tayi murmushi tace ina zuwa, ta shiga d'akinsa ta ja bargon da ya lullube ta wurga mai, firgigit ya tashi yana salati, tace mallam sai ka tashi munyi ba'ki, ta juya zata fita, kawai taji an kama mata kunne, tayi 'kara sossai har 'kasa saida sukaji, yace haka aka koya miki tashin mutum a bacci ne wai, mai yasa kika rainani ne?, zatayi magana kenan Na'ima ta bud'e kofar ta shigo, ta fara salati tana fad'in wai kai Yayanah yaushe zaka canja halinka