Author : Khadijah Al'Eeman Category : Complete Novels
ni idan ba abincinta naci ba bana jin dad'i, ya mike ya tura kujeran dining d'in ya juya yace inkin gama ina sama,......
Ta bishi da kallo, tabbas boka beyi k'arya ba daya ce shiga tsakanin su ba abu bane me sauki, sannan koda anshiga ba lallai bane ki rink'a samun yadda kike so ko da yaushe domin su *Had'i daga Allah* ne....
Yanxun ita tuna ninta d'aya ne tason Nasrin ta bar gidan nan, yadda zata ji dad'in juya Na'im yadda taga dama, toh ta ya ya zata samu biyan buk'ata dan ta lura Nasrin ma ba kanwan lasa bace....
Amma tayi ma kanta alk'awarin sai ta yi duk wata kissa da kisisina, da Neman kwararen boka da zai taimaka mata ta raba Auren Na'im da Nasri....
Ko zata samu wannan daman ko baza ta samu ba oho, Ku cigaba da saurarona, nice dai *AL'EEMAN*
*EDITED BY*
π NUSNIM ( *TWIN SIS*)π
π *DEDICATED TO*π
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you allπ
.
[1/25, 7:58 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*121 - 125*
*************
β"Haka rayuwa taci gaba, Hidaya na nan na kulle kullenta na ganin ta kora Nasrin amma abin ya gagara duk wurin bokan da zata je sai ya fad'a mata cewan "*Nasrin ta rik'e ibadah sossai, ga yawan azkhar da takeyi, ko me za'a mata bazai ta'ba kamata ba, ta rasa ta inda zata 'bullo ma abin gashi k'awarta dake bata shawara bata k'asar tabi wani Alhaji Dubai sai next week zata dawo.....
"A 'bangaren Na'ima kuwa ta samu mommy ta shaida mata cewan Nasrin fa nada ciki, tayi murna da farin ciki sossai, Na'ima kuwa cewa tayi Mommy me zai hana ki d'auko tah ki dawo da ita wurinki dan ni banyarda da Hidaya nan ba, haka neh Na'ima ni kaina abin na damuna dan yarinyar bata kwanta min a rai ba, amma kinsan me za'ayi? Ta girgiza kai, zan bari sai anyi kwana biyu zan shirya inje inga meke faruwa a gidan, sannan kuma zan kirata inja mata kunne akan ta kulla sossai da cikin kuma kar ta sanar ma kowa sai ya fito kowa zai gane ma idon sa, tace toh shikenan Mommy Allah yasa mu dace, Ameen.....
"Yau two weeks ya cika dai dai, Hidaya kuwa murna ya cika ta domin Haulat na kan hanyan dawowa.....
Ita ko Nasrin daga school sai d'aki, ta shiga ta rufe abinta tayi karatu idan ta gaji ta kira 'yan gidan su suyita hira a waya,ba abinda ke fitowa da ita sai girki, tsayawa takeyi a wurin sai ta gama ta juye a food warmer ta haura sama dashi......
Sannan koda Na'im ya sameta da maganan cewa Hidaya zata siya kwanakinta, cewa tayi ta barshi kawai ta tashi taje ta samu Hidaya a d'aki tace _kwantar da hankalinki amarya, kinsan ke baki saba jin dad'i da d'umi irin wandda kikaji a 'yan kwanakin nan ba, sannan kuma na fahimci cewan kin fini buk'ata da kuma kwad'ayi tare da sha'awa, lastly but not the list ina shaida miki ni Nasrin Uwar Gida a gidan Na'im na bar miki miji har sai randa zakiji ya isheki sai ki dawo min dashi, maganganun Nasrin sun ta'ba Hidaya sossai zuciyarta taji tana zafi_.....
_ta d'aga hannu zata mareta Nasrin ta rik'e hannun tace wa zaki mara ni lallai kam, marinah shine babban kuskuren da zaki tafka a rayuwarki, menene laifina dan na baki abinda kike buk'ata ai godiya ya kamata ki min bawai ki min sakayya da mari ba, ta sauke hannunta ta juya ta kai dai dai saitin k'ofa ta juyo tace_ " _Amarya asha Amarci lafiya_ ta fice abinta......
Ta koma d'aki tana zaune Na'im ya shigo, me yasa zaki ce kin bama Hidaya kwanakin duk da take buk'ata? Ta dago kai ta kalleshi tayi murmushi to ai ta fini buk'ata, naga naima takeyi da kud'inta ma amma kuma sai na mata adalci taje har sai ka isheta, nice na bada wannan izinin, zai yi magana kenan ta hango Hidaya na zuwa tayi sauri ta mik'e tasa bakinta akan nasa, tuni salon labarin ya canja......
Hidaya kuwa tsabar bak'in ciki ya hanata tayi magana da gudu ta juya ta nufin 'bangarenta tana kuka, ta d'aga waya ta kira k'awarta, Hello k'awata wlh ba lafiya a gidan nan kiyi Maza Maza ki zo, toh shikenan ina jira ta kashe wayan tana kaiwa tana komowa.....
Nasrin kuwa data lura cewan ta tafi da sauri ta zare jikinta ta matsa gefe, ta had'a rai, ya juya yana kallonta yasa gwiwowinsa a k'asa yana rokonta dan Allah kar ta bari ya kwana a wurin Hidaya wlh haushi take bashi amma sai ya kasa magana, tayi shiru tana nazarin maganan sai ya bata tausayi, ta d'aga shi ta kama mai hannu suka Shiga bedroom ta rufo k'ofar.....
Hidaya kuwa Haulat ta iso, suka shige d'akinta a nan Hidaya ta bata labarin komai, toh ke k'awata zama kikayi kika zuba musu ido kina kallo koko mene cewar Haulat, toh bari in baki shawara na farko dai ki tada musu da hankali, na biyu kuma wa'inan kujerun naki sunyi tsufa ba wai cewa zakiyi ya canja ba a'a inkika ce ya canja zai canja muku gaba d'aya, kananzir zaki samu ki watsa musu ki babbake shegu kinga ko a nan kin cusa mata bak'in ciki za'a canja miki kujeru amma ita banda ita sannan kuma jibi idan Allah ya kaimu zan kaiki wurin bok'a kurukus a bayan Layin mu yake aikinsa kamar yankan wuka....
Alla k'awata cewar Hidaya suka tafa, toh kinga Haulat yanxun ya za'ayi kinsannk da buk'ata gashi kuma yana wajenta, abinda za'ayi shine kizo muje tare da Alhaji Mai Gidan Daulah nake, muje ki yakici iya abinda zaki iya na barmiki shi na yau dai d'aya tak.....
Allah k'awata suka k'ara tafawa tashi muje wlh a matse nake , suka kama hanya suka fita........
*EDITED BY*
π NUSNIM ( *TWIN SIS*)π
*DEDICATED TO*
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you allπ
[1/25, 7:58 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*126 - 130*
*************
βNasrin da Na'im ana can ana soyewa, Naarin koh abin ya mata dad'i ko ba komai ta kuntata ma Hudaya, tunda suka shiga basu fito ba, sai da gari ya fara haske tukunna sannan Nasrin ta fito to had'a musu break fast ta koma ta kulle k'ofa......
"A 'bangaren Hidaya kuwa bata dawo ba sai wajajen d'aya, a lokacin Nasrin ta fito har ta musu lunch ta koma, saboda saida suka biya wurin boka tukunna, ya bata magani tasa mai a abinci amma yace musu karta bari yayi bissimillah.....
"Ba wannan bane ya dameta, abinda ya tsaya mata arai shine sanda tace ya bata maganin da zata kora Nasrin a gidan, cewa yayi bazata koriba saboda ta rik'e Ibadah, sai dai a gwada zubar da cikin da ke jikinta, gaban Hidaya ne ya fad'i, yaushe Nasrin ta samu ciki bata sani ba, lallai tayi sake ba d'an kad'an ba........
Ta juya ta kalleshi boka yanxun ya za'ayi? Ya mik'o mata wani bak'in igiya yace wannan ki warware shi a k'ofar d'akinta ta tsalaka magana ta k'are cikin zai zube......
Sai kuma ina son inja miki kunne karki sake ki ma Mijinki maganar cikin nan idan ba haka ba zai lalace, Ku tashi Ku tafi Ku bani wuri,ta ajiye mai makudan kud'i suka kama hanya suka tafi.....
Tunda Hidaya ta dawo take jiran fitowan su basu fito ba ta rasa ya zatayi, maganan Haulat ne ke dawo mata, da sauri ta d'auko kalanzir d'in data siyo ta 'boye ta yayyafa a jikin kujerun ta k'yasta a shanan a jikin kujerun nan da nan suka kama, sai dai me, ta tsorata sossai da ganin yadda yake ci.......
Da gudu tayi hanyar k'ofan Nasrin ta fara bubbugawa tana ihu "wuta wuta", Na'im ne ya fara jin abinda take cewa, ya fad'a ma Nasrin da gudu suka fito aikuwa wuta ya kama sossai, ya d'aga waya da sauri ya kira fire Bridget ya basu address........
Mai gadi kuma ya bud'e ma Lukman da Ahmad get kenan suka hango hayak'i ai da gudu suka fito ko gama parking basuyi ba, mai gadi na lafiya? Ya hango hayak'i shima da gudu yabi bayansu......
Sun shiga kitchen direct suka nufa suka had'a ruwa da omo, suka dinga watsawa, Allah ya taimaka kujeru uku kawai suka kama, kuma wutan ya mutu, ajiyan zuciya sukayi dukansu a daidai lokacin motan fire Bridget d'in ta shigo, Ahmad ne ya tashi ya je ya samesu dan Na'im ya kasa ko motsawa a wurin, Ahmad ya samesu ya basu hakuri tare da gaya musu yadda abin yake, sunce Allah ya tsare ya kuma k'ara kiyaye gaba sannan suka wuce......
Ya dawo ya samesu ya fad'i musu yadda akayi sai dai me Na'im yaga stain a sauran kujerun da basu k'one ba, saboda kujerun leather set ne, ya matsa zai ta'ba bai kai ga ta'bawa ba ya fara ji, ya kai hancinsa yana sunsuna d'agowan da zeyi ya kalli 'bangaren Hidaya wadda jikinta keta rawa itama shi take kallo, ya nuna ta da yatsa yace "ya akayi kalanzir yazo gidan nan? Sannan kuma ya akayi yazo kan kujerun nan dan nasan gidan nan ba'a anfani da kalanzir?
Hidaya tayi shiru tana kallonsa, idonsa ya kad'a yayi ja, Lukman ne ya dafa mai kafad'a yace "pls be a man" ka kwantar da hankalinka k'ila ita ma bata sani ba, Ku zauna dukan ku kubi a hankali har a gane abinda ke faruwa.....
"Na'im yace wlh munafuka ce wannan yarinyar, ba kowa a gidan nan daga ni sai ita sai Nasrin, wa zai shigo har nan ya kuma rasa abinda zaisa sai kalanzir? Idan wanine toh wlh sai dai yayi anfani da fetur kuma dika gidan nan za'a zuba shi......
Sannan na tabbata Baba maigadi bazai ta'ba barin wani ya shigo ba tare da izininah ba, sannan sanin kanku ne ba ta inda wani zai shigo gidan nan ba tare da naganshi ba kun fini sannin wannan ko ta yaya ne ba sai na muku bayaniba Ahmad da Lukman.......
Ya k'ara juyawa wurin Hidaya zaki fad'a min ko bazaki fad'a min ba sai na tattakaki a nan yanxun nan?
Ta juya ta nuna Nasrin ita ta zuba, Nasrin da sauri ta d'ago kanta ta kalleta, kuma kowa dake wurin da mamaki a fuskansa, Ahmad ya katse shirun yace Hidaya, ya za'ayi kice Nasrin ta k'ona kujerun nan, duk cikin mu ba Wanda zai yadda da magananki saboda mufi kowa sanin halin Nasrin, mun zauna da ita ba shekara d'aya ba, ba zaman yanxun bane tsakanin mu da Nasrin tun a lokacin bata nuna mana irin wannan halin ba sai yanxun ina Impossible Hidaya ki sake tuna ni dai......
Itace mana dama tun randa aka kawoni cikin gidan nan take ik'irarin sai taga bayanah gashi kuma ta fara, Na'im ne ya daka mata tsawa k'arya kike munafuka wlh bazata ta'ba akaita abinda kike cewa tayi ba, amma tunda na lallabaki ki gaya min kink'i, ki tafi gidanku karki dawo har sai kin fad'a min yadda akayi....
*EDITED BY*
π NUSNIM ( *TWIN SI*)π
*DEDICATED TO*
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you allπ
[1/25, 7:58 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*136 - 140*
*************
βNa'im ya rik'e kanshi ya dad'e a haka sannan ya saki kan nasa, Hidaya tayi shu'umin murmushi daga nan ta fara sarrafa shi yadda takeso, ta lura sossai maganin yayi tasiri a kansa, nan da nan ta kira Haulat ta fad'a mata suka dinga ihu a waya.....
Tunda ga ranan Nasrin taga canji a wurin Na'im, baya kwana a wurinta bata ganin shi, idan ma ta ganshi ko kallo bata isheshi ba, abin na bala'in damunta, a makaranta tana zaune a k'asan wata bishiya tana abinda ta saba wato tunani, taji andafata, ta d'ago kai tana kallon ko waye, Zainab ta gani a tsaye tana murmushi, ta nemi wuri itama ta zauna.....
Tace wai Nasrin kwana biyun nan meke damunki? A class idan muna lectures hankalinki baya wurin, kullum kina cikin tunani, duk kin rame kinyi bak'i wai meke damunki ne? Kinsan dai ba'a son mai ciki na tunani koh? Tayi shiru ba komai Zainab kawai yanayin karatu ne, kinsan dole in damu na k'osa wlh mu gama gashi yanxun 200 level muke, abin da k'osawa wlh....
Zainab ta ce haba Nasrin karki maidani k'aramar yarinya mana wlh karatu baya baki wahala kuma baya saki damuwa, kawai ba kyason fad'a min abin da ke damunki ne, kuma wlh ni ba haka na d'aukeki ba nayi tunanin zamu iya fad'a ma juna matsalar mu, mukuma maganceta ta hanyar bama juna shawara mai kyau, tunda ke ba haka kika d'aukeni ba shikenan, Allah ya yaye miki damuwarki, ta mik'e zan koma class sai kin shigo.....
Ta ruko hannunta da Sauri k'awata ki saurareni da kyau kiji wlh ba haka nake nufi ba, ni dai ina son inga ina kare mutuncin Aurenah ne, saboda komai a Aure yana buk'atar sirri, amma ba wai ina 'boye miki saboda wani abu bane, kiyi hakuri dan Allah....
Tayi murmushi Nasrin wlh kina da gaskiya Aure idan ba sirri ba Aure bane, gaskiya kin birgeni kuma na k'ara sonki a matsayinki na k'awata, sai dai wani hanzari ba guduba akwai lokacin da dole sai kin bud'e wannan sirrin amma fa ba kowa zaki fad'a mawa ba, saboda k'awa da kike ganinta sai ta kaiki ta baro dole sai kinyi taka tsantsan, dan haka ba kowani magana zaki kwashe ki fad'a ma kowace k'awa ba, dan haka yanxun mai ya faru ki fad'a min na miki alk'awari zan rik'e miki sirrinki In shaa Allah, kuma zan baki shawaran da baza ta cutar dake ba.....
"Nasrin tayi a jiyan zuciya ta kwashe labarin tun daga aurenta da Na'im har zuwa yanxun da suke zaune, Zainab "tace dank'ari! yanxun k'awata kina nufin baisan ma kina da ciki ba? Watan cikinki shida da sati biyu har kin fara zuwa awo amma be sani ba? Amma in tambayeki ita mahaifiyarsa fa? Nasrin tace muna waya da ita sossai ban ta'ba nuna mata wani abu na faruwa ba, kuma koda zan fara zuwa awo, tare da Na'ima mukaje asibitin, garkuwa mukaje kinsan a nan take aiki......
Zainab tace dank'ari a gaisheki Nasrin wlh kinyi k'ok'ari ba kowacce mace bace zatayi abinda kikayi ba, na jinjina miki tunda ko mahaifiyar da ta haifeki baki fad'a mata ba lallai a gaisheki......
Amma wani hanzari ba gudu ba, be kamata ki zauna ki zuba ido kina kallonta bah! Nasrin ta kalleta da sauri kina nufin nima inbi 'yan subbu kenan kai Zainab bazan iyaba wlh, ta dafa ta ba abinda nake nufi ba kenan, ina nufin ki tashi tsaye ki soma adu'a, saukan Al'qurani, yawan yin azkhar kome kikeyi, ki rinka yawan sa ma gidan ki karatun al-qur'ani hakan zai rage wasu masifu da bala'in cikin gidan nan, sannan duk wani asiri da ikon Allah zai karye ba kuma ke kadai zakyi ba, dole sai kin had'a da iyayensa ya kamata ki fad'a musu Susan halin da ake ciki, suma su tashi tsaye domin tasu ma sai yafi kar'buwa tunda su iyaye neh a gareshi, nima zantayaki In shaa Allah zakiga anfanin haka, sannan ki k'ara sama zuciyarki salama ki cire komai a ranki ki kama Allah, zakiga anfanin haka....
Tace nagode sossai k'awata zanyi abinda kikace, wlh kawata ina alfahari dake a matsayin k'awa harnaji damuwar da nake tare da ita ta wuce tunda na samu mafita, ba komai k'awata, k'awancen gaskiya kenan idan kaga d'an uwanka zai fad'a wani hali kayi k'ok'arin cirosa, tashi mu tafi kinji, suka tashi suka kama hanyar class domin lokacin lecture ya kusa......
*EDITED BY*
π NUSNIM ( *TWIN SIS*)π
*DEDICATED TO*
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam
Love you allπ
[1/25, 7:58 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*131 - 135*
************
βtsugunawa tayi tana rok'onsa dan girman Allah kayi hakuri, wlh sharrin shaid'an ne ka rufamin asiri dan girman Allah, kallon banza yayi mata ya juya zai bar wurin Lukman yace kayi hakuri tunda ta fad'i gaskiya, juyowa yayi toh me yasa zata yi haka anmata wani abun ne, ko kawai dan taga 'baccin raina zata aikata haka, Ahmad yayi murmushi kasan halin mata suna da kishi sai hakuri, kishi Ahmad wani irin kishi ne haka mara kangado da har zatayi yinkurin sa wuta a gida?
"Nasrin ne ta matsa kusa dashi ta rik'e hannu shi haba " _Namijin zaki, haba tauraronah, haba abin alfaharinah, mijin da kowacce mace take da burin Aure a rayuwarta_ ina hakurinka yake ni nasan kana da hakuri karka zama mara yafiya a rayuwa mana, ka zama mai yafiya a koda yaushe, dan Allah kayi hakuri ka yafe mata laifine ta riga tayi kuma ta baka hakuri, ka saurareta mana ka hakura please......
Ya juyo yana kallon Nasrin naji na hakura amma bazan canja mata kujeru ba haka zata zauna, Nasrin ta girgiza kai a'a canja kujeru ya zama dole amarya ce fa, haka za'a dinga zuwa a naganin k'onanin kujeru? Bazai yuwu ba kayi hakuri ka canja mata, naji zan canja, amma yanxun koh, tunda ga friends d'inka kuje yanxun ku siyo, yayi murmushi toh naji Uwar gida sarautar mata, Allah yayi miki albarka, Ku muje sai mundawo, toh Allah ya tsare cewar Nasrin, ita koh Hidaya binsu tayi da harara, ta juya ta kalli Nasrin tayi tsaki ta wuce, murmushi tayi ta koma 'bangarenta abinta.....
Sunje sun suyo kujerun blue black da flowers a jiki golden colour, inda ya siyo su suka kawo a mota suka shiga dashi suka sa, a ka fita da wa'incan.........
Da ta fito