Author : Khadijah Al'Eeman Category : Complete Novels
Hidaya ce tasa aka turosu domin su lalata cikin da ke jikinta su kuma kasheta amma sai akayi rashin sa'a sun shiga jikinta amma tana yin aZkhar sossai wannan yasa suka kasa aiwatar da komai a kanta amma yanxun zasu fita ayi hakuri, ta fara wani bak'in amai, daga nan ta fad'i k'asa, mallam yace bacci ne ya d'auketa da ta tashi komai zai yi dai dai, Na'im ma bacci yayi awon gaba dashi, mallam yayi hamdala yana mai k'ara jadda da musu cewan da zaran sun tashi komai zai daidaita.....
Nice dai taku *AL'EEMAN*ππβ
*EDITED BY*
πNUSNIM ( *TWIN SIS*)π
*DEDICATED TO*
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam
Love you allπ
[1/25, 7:58 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*151 - 155*
*************
βSun kai gida Daddy daya ga Na'im saida yayi kuka, ya kira Alhaji Tofiq ya fad'a masa, sai gashi yazo da wani malami, yana kallonshi yace wannan aikin tsafi ne dan yafi k'arfin sihiri......
Ya d'auko ruwan zamzam da ya karata ayatul shifa'a, ya bashi ya sha ya d'auko wani magani da aka had'a dasu "man zaitun, habbatus sauda" da sauransu da yasha adu'oi ya bada yace a rinka bashi da safe cokali d'aya da yamma cokali d'aya ya bada garin habbatus sauda yace a rinka mai hayaki dashi, ya k'ara musu wani magunguna dana wanka, man shafawa da turare, kuma a dinga sa mai karatun alqur'ani mai girma yana ji, In shaa Allah komai nene a jikinsa zai barshi da ikon Allah, aka ce nawa za'a bashi? Alhaji kenan ai d'anka d'ana ne, ba sai abani wani abuba, ba komai Allah ya bashi lafiya, Alhaji Tofiq yayi sallama dasu akan zai dawo zuwa gobe domin yaga yadda jikin nasa yake.....
"A 'bangaren su Hidaya kuwa sunje wurin bokan ya basu layu su sami wani dutse su daga su saka, amma su tabbatar bawanda zaiga dutsen harma ya d'aga shi, sannan bayan tafiyarsu zai tura ma Nasrin bak'ak'en aljanu su zasu lalata cikin, suka ajiye masa kud'i suna murna suka kama hanyarsu ta komawa......
"Nasrin ne zaune ta gama ba Na'im magani ta tashi ta shiga bathroom kawai sai taga abu ya gitta ta gefenta bata San ko menene ba, wani tsoro taji da bata ta'ba jin irin shi ba, ta kwalla k'ara ta fad'i, mommy ne ta shigo d'akin domin kawo ma Nasrin d'an wake dan tace shi takejin ci, ta ji k'ara a bathroom da gudu tayi wurin tana shiga ta ganta a kwance numfashi da kyar yake fita, salati ta fara ta fito da sauri ta kwalla ma Na'ima kira da gudu ta shiga d'akin ta ja hannunta suka kamo Nasrin d'in suka kwantar da ita a kusa da Na'im da keta faman baccinsa, Na'ima ta shiga dubata komai normal cikin ba abinda ya sameshi, sai dai abinda ya basu tsoro kamanin Nasrin ya canja, sannan ba abinda takeyi sai kuka ko magana bata iyayi, kukan ma baya fita kwata kwata.......
Mommy ne ta shiga d'akin Daddy a kid'ime ta sanar dashi halin da ake ciki, da sauri ya tashi ya bita d'akin ba k'ara min d'aga mai hankali yayi ba ganin Nasrin a halin da take ciki, mommy tace ya kamata ka kira Tofiq su dawo shi da mallam, da sauri ya koma d'akin shi ya d'auko waya, ya kirashi ya sanar mai.....
Ba'a d'au lokaci mai tsawo ba sai gasu sun iso, aka fito mashi da ita, yana kallonta ya ganne meke damunta, ya fara mata Rukiyya amma shiru, ya dinga yi ya kai awa d'aya yana abi d'aya amma shiru kakeji, ya ce Alhaji bak'ak'en aljanu ne masu taurin kai, akwai wani magani da sai naje wani k'auye na nemoshi idan na kawo za'a had'a da garin habbatus sauda ayi mata hayak'i dashi da ikon Allah zasuyi magana zakuma musan Wanda ya aikata mata wannan aikin, kwana goma zanyi kafin nadawo, ga wanan idan kuka bud'e zaku gansu kala biyu ne a ciki da fari da kuma brown, farin zaku shak'a mata a hanci, brown d'in kuma a samata shi a ruwa a bata tasha, In shaa Allah ba abinda zasu mata har indawo sai dai suna nan a jikinta, sukayi godiya yayi sallama dasu Alhaji ya kawo kud'i ya bashi yayi Guziri, yayi godiya ya amsa ya kuma yi sallama da Alhaji Tofiq cewan daga nan garin zai tafi Neman maganin, yayi masa godiya sukayi musabaha ya juya ya tafi abinsa....
"Hidaya ce ita da Haulat a bayan gari sun ga wani dutse a wurin, shi kuma wani mutum ya hangosu sai ya la'be yana lekensu har suka gama suka wuce....
Yana ganin sun wuce ya fito, ya je wurin dutsen toh matanan me sukeyi ne a nan, sai da ya duba ba kowa sanan ya d'aga yaga layu ne kusan guda biyar a wurin, shi tsoro ma yaji yasa hannu ya d'auka ya bud'e su d'aya ansa "Na'im da Hidaya sai mutuwa! Na biyun ansa "Na'im da 'yan uwanshi har abada! Na ukun koh "Na'im da Nasrin rabuwa ta har abada! Na hud'in ansa "sai yadda Hidaya tayi da Na'im" na biyar d'in kuwa "duk inda Na'im yake zai baro ya dawo wurin Hidaya sai kuma wasu rubutu da bai san ko menene ba!.....
Saurayin nan ya girgiza kai yana mai adu'a a cikin ransa, duniya gaskiya ta lalace, ya tafi dashi har k'ofar gidansu ya d'auko ashana ya k'onasu, wannan kenan.......
"Yau kwanan mallam biyar da tafiya Nasrin sai dai abu mai ruwa ake riketa abata da kyar take sha, bata magana kwata kwata sai kuka, Na'im kuwa Alhamdulillah ya fara samin sauk'i amma har yanxun bai cika magana ba, baya kuma maganan Nasrin ko ya ganta sai dai yayi ta kallonta baya cewa komai....
Yau ne ake sa ran mallam zai dawo, kowa a family yana gidan, 'yan uwan Nasrin ma duk sunzo sun gaishesu sun tausaya mata kwarai da gaske, Mahaifiyarta kuwa da k'anenta kuka kawai sukeyi....
Ohh ni AL'EEMAN ko maganin zaiyi kuwaπ€ makaranta sai kusa Nasrin da Na'im a cikin adu'oinku... Nice dai *AL'EEMAN*
*EDITED BY*
π NUSNIM ( *TWIN*)π
*DEDICATED TO*
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam
Love you allπ
[1/25, 7:58 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*161 - 165*
*************
*d'inbin masoyanah ina godiya a bissa yadda kuke kirana kuna nuna damuwarki akan littafi. Had'i daga Allah ina sonki har cikin raina*
β"Hidaya taje ta cire abinda ta burne daga nan ta kama hanya zuwa gidan Surukanta tana tafiya tana kuka kamar mahaukaciya, kukanta ne ya tashi Nasrin da Na'im, sugunnawa tayi tana rokonsu akan abubuwan da ta musu, Na'im kasa cewa komai yayi domin komai daya faru ganin yakeyi kamar a mafarki....
"Mommy ce ta bashi labarin abubuwan da suka faru, rik'e kai yayi ya rasa mai zaice, ya d'ago idanuwan shi da sukayi ja kamar garwashi ya nuna Hidaya da yatsa yace bazance miki komai ba amma kije duniya ce ta isa kowa riga da wando, ya dukar da kai yana hawaye abubuwan da tayi mai suke k'ara dawo masa babu abinda yafi mai ciwo kamar yadda ya rinka share Nasrin, da ta bashi da Nasrin yana ganin zai iya yafemata amma tunda ta rabashi da Nasrin a lokacin da take da bukatar kulawanshi gaskiya bazai iya yafe mata ta cutar da ita ba d'ankaramin cutarwa ba, mik'ewa yayi yace Hidaya bazan ta'ba yafe mikiba wlh na tsaneki, kije kuma na sakeki saki Uku.....
Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi ta bishi ta kama kafafuwanshi dan girman Allah kayi hakuri wlh sharrin shaid'an ne da kuma k'awa dake zugani, dan Allah ka yafemi, tureta yayi ya haye sama abinshi.....
Juyawa tayi ta kalli Mommy da Daddy ta na rok'onsu, Daddy kasa cewa komai yayi sai kallo da yake binta dashi, ita koh mommy cewa tayi dama ni saida nayi zargin wani Abu, haka kawai Na'im bazai zo da maganar Aure ba, Ashe kece kika k'ulla mugun abu, da kika shigo gidan ma maimakon ki zauna lafiya ki barshi da matar shi kuyi zaman lafiya a'a wannan ma bai isheki ba harda yink'urin kisa, gaskiya kiyi wawta amma kuma kanki kika cuta ba kowa ba Allah ya shiryeki ya kuma yafe miki.....
Ta juya wurin Nasrin wadda in banda kuka ba abinda takeyi, ta tsugunna tana rokonta ta yafe mata ta kuma tayata rokon Na'im da ya yafe mata, murmushi tayi hawaye na zuba a fuskarta tace indai nice na yafemiki sai ki rok'i Allah shima ya yafemiki, maganar Na'im kuma kisa a ranki ya yafe miki dan zan mai magana kuma nasan zai saurareni, dan haka kije ba komai, Allah ya yafe mana gaba d'aya, ta mik'e tana fad'in nagode Allah yasaka da alkhairi ta juya tana kuka ta fita.....
Nasrin ta mik'e ta haura sama zuwa 'bangaren Na'im na da, ta sameshi a tsaye sai kuka yakeyi tasa hannunta ta zagaye shi ta kwantar da kanta a kafad'ar shi, wani irin shock yaji, tace haba Namijin gaske, bansan ka da rik'o ba karka manta Manzon Allah (S.A.W) ya hanne mu da rik'o ya kuma umurce mu da mu zama masu yafiya, ina son kayi hakuri ka yafemata bagashi ya zama tarihi yanxun ba, a koda yaushe *Ina tare dakai*(littafin Miemie bee), kuma mun zama *jini d'aya*( na Aneelurv), kaga ba Wanda ya isa ya rabu sai Allah ni dakai *Had'i daga Allah* ne, Dan haka kayi hakuri ka yafe mata, muma muna ma Allah laifi ya kuma yafe mana, ya juyo ya rungumeta sossai na yafe mata Dearnah amma kisani ta cutar dani ba d'an kad'an ba, Allah kad'ai zai iya yimun sakayya tsakanina da ita amma tunda kince in yafe mata na yafe mata komai ya wuce.....
Yauwa nagode sossai Allah ya k'ara tsaremu daga Sharrin aljani da mutune, ya amsa da Ameen.....
"A 'bangaren Hidaya kuwa tana fita wani mai mota ya yanko da gudu ya kwasheta ta fad'i, daya juya yaga ba kowa ya gudu abinsa, sai wani bawan Allah ne yazo zai wuce ya ganta a kwance a wurin ta rik'e k'afa sai kuka takeyi ya karfi wayarta ya kira mahaifiyarta ya gaya mata zai kaita asibitin dutse taje ta sameta a can, ya d'auketa ya kaita, mahaifiyarta taje ta sameta, likita kuma ya gaya musu saidai a yanke k'afar, tayi kuka kamar zata mutu ta kuma yi data Sani ba d'an kad'an ba, Rayuwa kenan.....
Kuyi hakuri yau sai ahankali sai kujira next typing Wanda may be shine last episode......
Nice dai *AL'EEMAN*π
*EDITED BY*
πNUSNIM ( *TWIN SIS*)π
*DEDICATED TO*
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam
Love you all
[1/25, 7:58 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*165 - 170*
**************
β"Hidaya ta shiga matsanancin rayuwa, ga kud'in suna dashi amma ba k'afa, mai aiki aka samo take mata komai, tunda abin ya faru Haulat batazo ta dubata ba, data kirata ma cewa tayi bata garin, alhalin tana nan, ita kanta Haulat d'in tana cikin mawuyacin hali domin ta fara rashin lafiya data je asibiti aka gano tana da HIV Aids, tayi itama nadama da dana sani ba d'an kad'an ba......
"Na'im da Nasrin kuwa sun koma gidan su, babin soyayya sabuwa suka bud'e, data ce wash ko mai yakeyi zai bari ya maida hankalinsa a kanta, gashi yanxun wani shagwa'ba takeyi ya rasa a ina ta koyon wannan shagwa'ban domin gaba d'aya rikita shi take (ni AL'EEMAN nace aikin Zainab ce, duk ita ke koya mata wani kussa da kisisinah), gashi ta k'ara cika ta zama babbar mace.....
"Yau cikin Nasrin Nine months, three weaks, suna kwance kamar yadda suka saba, tana mak'ale a jikinsa, ta fara jin bayanta na sarawa, amma ta cigaba da daurewa, can kuma sai mara ya d'auka tun tana iya daurewa har ta fara hawaye, gashi Na'im na bacci bata son ta tasheshi, a hankali ta ja jikinta ta sauka daga gaddon amma kuma sai dai ta turkushe a wurin, kafin kice me har paya ta fashe amma still tak'i tashin Na'im, sai ta fara nishi da k'arfi aikuwa cikin hukuncin Allah baby ya fad'o, sai kuma ta k'ara wani nishi sai ga wani babyn ya k'ara fad'owa,kamar ance sun had'a baki suka fara kuka a tare.....
Na'im kamar a cikin mafarki ya fara jin kukan jarirai, bud'e idon da zeyi yaji da gaske ne fa kuma a d'akin yakeji ya sauka ya kunna haske kawai suka had'a Ido da Nasrin da duk ta had'a zufan wahala, ga kuma babies har buyu a gabanta, mamakine da al'ajabi suka cika shi, ya matso ya dafata yana mata sannu, cikin dashashiyar murya tace ya kira mata Na'ima tazo ta yanke cibin tunda harta mahaifa ta fad'o, da Sauri ya duba agogo k'arfe hud'u da rabi, ha daga waya ha kira Ahmad, Ahmad na ganin shine da Sauri ya d'aga ya ce lafiya? Ya gaya mai halin da ake ciki, ya kalla Ni'ima dake kwance a kirjinsa ya tadata da sauri ya fad'a mata, da sauri suka mik'e suka sa kaya ta lek'a ta tashi ido tace idan su Amir sun tashi ki kula dasu zamuje mu dawo, cikin sauri suka fita a gidan......
"Sun isa Na'ima da sauri ta shiga d'akin ta yanke cibin, ta tambayi Nasrin wanda ta fara haihuwa ta nuna mata, ta duba taga mace ne, ta duba d'ayan itama macece, gasu adentical twins ne, da kyar ta gane cewan babban ta d'anfi fad'in fuska akan k'aramar, nan da nan ta had'a ruwa ta gasa Nasrin da kyau da towel sukayi anfani, sannan ta fito tama yaran ta gyara ko ina, ta bud'e gidan da turare.....
"Alhamdulillah Nasrin ta sauka lafiya kuma kowa yayi murna ba ma kamar uban gayyar wato Na'im jinshi yake kamar ya had'iye maman da yaran....
Ranan suna Yara sunci sunan Mommy da Umman Nasrin, ana kiransu da Hanam da Hanan, suna ne da aka narka kud'in gaske, kaya kuwa ba'a maga suko su Amir da Amira dad'i sukeji sunyi k'anne, bayan suna da kwana d'aya Mommy tazo zata d'auka Nasrin a nan fa aka shiga daru da Na'im, shi wlh a bar mai matarshi, mommy tace bai isa ba wlh sai ta tafi da ita, yanaji yana gani aka tafi da ita shima ya had'a kayanshi yabi bayansu, yaje 'bangaren shi dake gidan mommy tace kayi ka gama.....
*BAYAN SHEKARA BIYAR*
"Abubuwa sun faru da yawa ciki harda kammala karatun Nasrin, Nabeela ma ta haifa baby girl ansa mata suna Fatima ana kiranta da ikram, k'annenta ma sun dage sunyi karatu sossai yanxun Haka ma maganar auren biyu daga cikinsu akeyi, "yan uwan babanta yanxun ji da ita sukeyi tamkar kwai, Mommy ma yanxun Shureim kad'ai ya rage mata ta aurar, su Nasrin yanxun hankali ya kwanta gashi kud'i na shigowa ta ko ina, Na'im yayi kiba abinshi yayi kyau, gashi yana Samun kulawa sossai a wurin Nasrin, jinsu sukeyi kamar zasu cinye junan su......
"Nasrin ne a zaune tana duba wani file da zatayi submitting gobe da safe, sai ga wani yaro d'an shekara biyu yana gudu yazo bayanta yana cewa mommy kinga Hanan koh! Ga Hanan a tsaye tana haki, ta kalleta tace meya faru me yayi miki? Toh mommy bashi bane chocolate d'in da Daddy ya siyo mana jiya ni ban cinye nawa ba ya d'auke ya cinye min, toh kiyi hakuri ba k'anin ki bane zan siya miki wani kinji koh! Ta gyad'a kai, sai ga Hanam ta fito tana cewa nima hardani koh mommy? Tace kwarai ma kuwa harda ke suka fara tsalle suna murna, sai ga Na'im ya shigo rige rige sukeyi daga su har Maman su, dariya yakeyi saida ya rungume Nasrin kafin ya fara d'aga yaran d'aya bayan d'aya suna dariya,....
Yace toh kuzo muyi selfie ya ciro wayansa nima na matso ta gefe na shiga Ashe Nasrin ta ganni ta galla min harara tace mallama sai ki kama hanya ki wuce leken asirin ya ishe mu haka nan, na juya jiki a salu'be na fita a gidan, ina jinta har tana saka key dan kar inkoma.......
Toh nima anan zan tsaya da abin rubutuna sai kun sake jina acikin sabon littafina mai suna *MA'AURATAH*
Godiya ta tabbata ga Alla (S.W.A) mai kowa mai komai Wanda shine ya hallici sammai da k'asai da abubuwan da ke cikinsa, shine ya bani baseerar da kuma ikon rubuta wannan littafi, ya Allah ka k'are mu da lafiya wa'inda basu da lafiya Allah ka k'aresu da lafiya,ka jik'an wa'inda suka rasu muma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani Allahumameenπ
*GODIYA TA MUSAMMAN A GAREKU*
π Excellent writers
π Pharty novels
π Aneelurv Novels
π Nafee Anker novels
π Faxy fashion novels
π Matan kwarai group
π All dostis of Nusfulhayat
πDaga marubuta group
π Stylish Housa novel
π Home of Hausa novels
π Eshart tsafe novel
π Taskar 'ya'ya mata
Kai dama Wanda ban anbata ba Dan wlh kuna da yawa, da badan Ku ba da ban kai matsayin da nake a yanxun ba Dukan ku *AL'EEMAN* na sonku
*KUNFI KOWA SON WANNAN NOVEL 'DIN*
π Deejah's kitchen groupπ
*AL'EEMAN* na alfahari daku
Ina missing d'inku masoyanah na gaskiya
π Fatima Ahmad magayaki
πAisha Sani d'anladi πZainab Aliyu buratai π Maryam Umar d'an Fulani (Allah ya jik'anki)
π Bar'atu Rabi'u sulaiman
π Baraka Lawal garba
Kai wlh kuna da yawa Allah ya bar k'auna
Ban manta dake ba aminiyar kwarai *ANEELURV*
*Wannan littafin sadaukarwa ne a gareku*
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshrt, Mamu, Afra sai kuma Rash kardam
*Khadijah* na sonki
*EDITTED BY*
πNUSNIM (TWIN SIS)π
Sannu da kokari Allah ya bar zumunci
Taku a koda yaushe
*KHADIJAH AL'EEMAN*π