Advertisements
Chapter 7 Reading HA'DI DAGA ALLAH Kaddarar So by Khadijah Al'Eeman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

HA'DI DAGA ALLAH Kaddarar So by Khadijah Al'Eeman

Author :  Khadijah Al'Eeman Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 10

18K to 21K   out of 29.9K words

'barin wata bata ta'ba yi ba?, ai mommy kema kyaso kiga jikokinki ta 'bangarenah!

"Gaban mommy neh ya fad'i har Na'im ne zai fara maganan haihuwa toh idan kuma rashin haihuwa daga wurin shine fah?, amma kuma abinda ya fad'a na cewar Allah ya bashi izinin ya k'ara aure har mata uku yanxun ba k'arya yayi bah! duk a zuciyar ta take fad'in haka.....

Ganin tayi shiru Daddy ya fara magana, Na'im kaje idan nayi shawara da d'an uwanah zan kiraka, Daddy dan Allah ina son a had'a da bikin Safiyya ne please Daddy",.....

Ba komai Na'im tashi kaje Allah ya za'ba mana abinda yafi alkhairi, Ameen! Ya tashi ya kama hanya ya tafi abinsa.....

Mommy ta juyo ta kalli Daddy tace nidai har ga Allah wannan aure be kwanta min a raiba, haba Mokmy yara kiyi mishi adu'a kuma kiyi mai fatan alkhairi, toh Allah ya za'ba abinda yafi alkhairi yace Ameen, ta mike bari inje in duba abinda akeyi a kitchen ta fita.......

"Washe gari Na'ima tazo gida dan tsara yadda bikin k'anwan nata zai kasance amma tana zuwa sai mommy ke fad'a mata abinda ke faruwa, sannan ta shaida mata cewar Daddynsu ya kira Alhaji Tofiq ya gaya masa kuma ya bada shawaran a barshi yayi tunda yace zai iya! Na'ima hankalinta ya tashi ta fad'a ma Mommy labarin Hidaya da Ahmad ya fad'a mata, Mommy tace subhanallah yanzun toh ya za muyi ne!

Karki damu zansa a mishi saukan al'qurani bayan bikin sannan kuma zamu tsananta adu'a, shima zanyi iya bak'in k'ok'arina inga ya rik'e azkar, sannan ita kuma Nasrin dama na siya mata form kin sani, nan da two weeks zasuje screening ita ba ma sai tayi wani Exams ba tunda Allah ya taimaka tana da JAMB, toh Admission ya fito kuma immediately zasu fara karatu kinga komai zaizo da sauk'i,.....

Na'ima tayi ajiyar zuciya shikenan Mommy Allah yasa haka shi yafi Alkhairi amma gaskiya Aunty Nasrin zata shiga wani hali wlh, ba komai Allah shi zai shige mana gaba cewar mommy! Ameen....

"Nasrin da taji Na'im zai k'ara aure har ta d'aga hankalinta amma mommy da Na'ima sun kwanatar mata da hankali, tayi adu'a Allah yasa haka shi yafi alkhairi,.....

"Haka rayuwa keta tafiya taje tayi screening d'in kuma Alhamdulillah ta wuce har sun fara lectures sun bata pure chemistry, gashi kuma abinka ga mai kwakwalwa tana fahimtar komai, tana zaune yauma kamar kullum wata tazo ta mika mata hannu tace Assalamu Allaikum, ta amsa mata cike da murmushi a fuskarta, sunana Zainab Abdullahi ina zaune a da mijinah a hayin banki amma gidan iyayenah na unguwar kanawa, kullum ina ganinki kuma course d'in mu d'aya dake please "can we be friends" in har ba damuwa tace "why not" ni sunana Nasrin k'asim muna zaune a isa kaita dake malali dat is gidan aurenah kenan! Amma gidan mu na Unguwar rimi....

"Zainab tayi murmushi Ma shaa Allah, Nasrin ta kalla agogo tace Zainab lokacin Sallah yayi muje muyi kafin time d'in lecture yayi, suka mik'e suka tafi tun daga ranan shakuwa mai k'arfi ya shiga tsakanin su....

"Alhaji Tofiq da Alhaji Haris Saif sunje sun sami 'yan uwan mahaifin Hidaya kuma a basu amma tun a lokacin Alhaji Haris Saif ya fahimci cewa akwai matsala amma ya zeyi tunda Na'im ya kafe dole sai anyi auren nan, yana hango akwai wani abu dake faruwa kamar yadda Mommy ta ke cewa koma menene Allah ya sa mudace.....

An tsaida rana lokaci d'aya da Safiyya, Tsakanin Nasrin da Na'im kuwa ba abinda ya canja yau yazo da farin ciki gobe kuma ya juya kamar bashi ba! Ita dai tasa ma sarautan Allah ido kuma bata ta'ba fad'a ma kowa ba in banda sanda ta fad'a ma Na'ima, kuma koda Ummanta taji labari ta kirata ta mata nasiha sossai akan ta zama mai hakuri tabi mijinta shiyasa ita kuma take shanye duk wani abu da zai rinka mata....

"Makaranta kuwa tana maida hankali sossai a tsakaninta da zainab sai mutuntawa da girmamawa kuma suna karatu sossai dan burinsu baifi ace sun fito da first class ba.....

Sai ince Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a....


*EDITED BY*
πŸ’ NUSNIM ( *TWIN SIS*)πŸ’

πŸ“ *DEDICATED TO*πŸ“
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Agra and Rash Kardam
Love you all😘
[1/25, 7:58 AM] β€ͺ+234 706 774 5996‬: πŸ‘« *HA'DI DAGA ALLAH*πŸ‘«

*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN


*96 - 100*
***********
✍"Nasrin na nan a zaune har Na'im ya shigo ta tashi ta amsa brief case a hannun sa tayi mai sannu da zuwa ya amsa ba yabo ba fallasa, suka haura sama yana Shiga ya fada toilet ya watsa ruwa, kafin ya fito ta ciro mai kayan da zaisa, ya fito ta d'auko mai zata shafa mai kamar yadda ta saba amma me sai ya dakatar da ita, ya shafa ya juya ya d'auko wasu kayan yasa ya ce muje yunwa nakeji.......

"Sun isa dining ya zauna ta fara zuzzuba mai abinci, sai cewa yayi cikin tsawa nace miki yunwa nakeji amma sai aiki kikeyi a hankali, ta d'aga kai ta kalleshi tace haba "hubby" yanxun duk saurin da nakeyi baka gani ba?, dan Allah waya 'bata maka rai? Ka shigo sai fushi kakeyi ni heart a 'yan kwanakin nan bansan meke damunka ba gaba d'aya ka canja na rasa gane kanka a 'yan kwana biyun nan......

Yace wai ke meyasa baki da hankali ne?, kisa min abinci kin tsaya kina min maganan banza, toh bud'e kunnenki da kyau kiji Aure zan k'ara very soon, abinci kuma na fasa ci, barin gidan zanyi inje inda za'abani ba tare da min wasu surutun banza ba, yaja tsaki ya tashi ya fita abinsa.....

"Nasrin kuwa abin mamaki ya bata toh ita bata san abinda tayi masa ba, gashi har yana ik'irarin zai k'ara aure, ita bata san abinda tayi masa ba, kuma a iya zamanta dashi bata ta'ba mai wani abu ba, kullum burinta shine taga ta kyautata mishi, kuma ba wai halinsa nada bane ya dawo dashi, tunda da halinsa ne nada bazaice zai k'ara Aure ba, duk da dai ance "mai hali bai fasa halinsa, koma dai menene Allah ya kyauta......

"Haka suke zaune yau ak'alla sun kai wata biyu kenan, wata rana zai zo da fara'a kamar bashi ba wata rana kuma akasin haka, yana abu kamar mai ta'bin hankali, tun bai damunta har yazo ya fara damunta, gashi tana son zuwa gida ya hanata zuwa, tana zaune a fallonta ta rasa abinyi can kuma ta d'aga waya ta kira Na'ima suka gaisa ta tambayi lafiyan twins, Na'ima tace Aunty Nasrin kamar akwai abinda ke damunki, muryanki yayi wani irri, mai ke faruwa ne?,.....

"Nasrin ta kwashe komai dake faruwa ta fad'a mata, Na'ima tace me yasa tuntuni baki sanar dani ba, tayi murmushin k'arfin hali tace da nayi tunanin wani laifi nayi masa k'ilan zan iya shawo kan abin, amma me sai naga abin natayin gaba, shiyasa na yanke hukuncin in kiraki sannan nayi nayi naje gida ke nama fita ko nan da can wlh ya hanani, tace karki damu ina zuwa, ta katse call d'in.....

"Na'ima ta kira shi tace haba yayanah two dayz ka shareni kwata kwata ka daina ji dani, sannan ga Amir da Amira suma sunata missing d'inka and u refuise to come why, ko min maka wani laifin ne?, ......

Yayi maurmushi ko d'aya my sister abubuwa ne suka min yawa a office, tace toh yayanah Allah ya bada Sa'a, ya amsa da Ameen, tace ya gida ina Aunty Nasrin?, itama kwana biyu Shiru kakeji, yace kedai bari ni yanxun ma wlh haushi take bani sannan kuma ni yanxun Aure ma nake son yi wlh, gaban Na'ima ne ya fad'i tace Yayanah Aure kuma?, Aunty Nasrin d'in yaushe yaushe ka Aure tah?, yau fa Aurenku 8 months fa kwata kwata, me ye dalilin son k'ara Aurenka?, Aunty Nasrin d'in toh me takeyi maka, bata kulaka ne?, ko kuma bata yimaka abinda kake so ne da zaka k'ara Aure?......

"Na'im yayi ajiyar zuciya yace babu ko d'aya nidai haushi take bani kawai, kuma har yanxun bata da ciki, ni kuma haihuwa nakeson yi a yanxun, toh shikenan Yayanah naji, wacece Auntyn nawa?, yayi murmushi ko keh fa, sunanta Hidaya, kuma tare muke aiki a office amma ni ina gaba da itane, tace toh shikenan Allah yasa alkhairi a cikinsa, yace Ameen nagode sai nazo ganin yaranah, sukayi sallama ta ajiye wayan amma tana tunanin ta ina zata 'bullo ma wannan al'amarin abin ne akwai rikitarwa wlh....

"Tana wannan tunanin taji andafata ta juyo da Saudi, Ahmad ne takagani, yace haba dear, meke faruwane tun dazun nake sallama amma baki amsa ba, menene fad'a min,....

"Tace Habibi kai dai bari wani al'amari ne ke faruwa wlh me wuyan fassaruwa, na rasa ta inda zan fara, yazo ya zauna yace menene fad'a min, kafin na fad'a maka bari in tambayeka, Habibi kasan wata wai a office d'insu Yaya Na'im mai suna Hidaya?,....

Ya d'ago da sauri ya kalleta yace dear me ya had'aki da Hidaya?, a ina kika Santa?, kinsan kuwa wacece "Hidaya"?, ta girgiza kai tace bansaniba amma dan Allah ka fad'a min wacece ita......

Yace toh Hidaya itace.........


*EDITED BY*
πŸ’ NUSNIM ( *TWIN SIS*)πŸ’

πŸ“ *DEDCATED TO*πŸ“
Nafee Anker,Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you all😘
[1/25, 7:58 AM] β€ͺ+234 706 774 5996‬: πŸ‘« *HA'DI DAGA ALLAH*πŸ‘«

*WRITTEN BY*
KHAFIJAH AL'EEMAN


*111 - 115*
*************
✍"yau ta kama juma'a kuma yaune d'inbin Al'ummah suka shaida d'aura Auren *LUKMAN MUHAMMAD* da amaryarsa *SAFIYYA HARIS SAIF* da kuma *NA'IM HARIS SAIF* da amaryarsa *HIDAYA HASHIM* an daura lafiya sai dai mommy ta hana yin ko wani event ta dalilin aure Na'im da bata so, Na'ima tayi tayi mommy ta bari ko dinner ce ayi amma fir tak'i yadda, shiko Lukman cewa yayi ana kai mai amaryarsa zai had'a dinner shi da abokanan sa.......

"A 'bangaren Nasrin kuwa ba Wanda ta gayyata sai 'yan uwanta da suka zo, 'yan uwan mahaifinta kuwa tasha habaici a wurin su wai ta kasa rike mijinta gashi nan zai mata kishiya, sai dai tayi murmushi kawai abinta, ......


"Mommy ta kira Na'ima tace mata yanxun xa'a kawo amarya kuma daga nan za'a wuce da ita malali a 'bangaren Na'im zata zauna kafin ya kammala d'aya gininsa na Kinshasha, ki shirya kije ki taya Nasrin aiki Ku gyara ko ina ki tabbatar tayi kwalliya ba wata matsala, tunda kinga an riga an tafi da Safiyya ba wanni aiki....


Toh mommy yanxun kuwa In shaa Allah, ta tashi ta shirya ta bar ma Mommy twins ta tafi, taje ta samu sun Riga sunyi komai har abincin da zasu tari 'yan kai amarya, Na'ima tace Aunty Nasrin ya kamata a kunna turaren wuta, tayi murmushi wlh Na'ima bansan meyasa ba kwata kwata bana son k'anshin turaren wuta sai dai asa na tsinke da kuma room freshener, Na'ima ta tsaya kallonta tana nazarinta sossai, idan baku manta ba Na'ima likitar mata ce, taja hannun ta suka Shiga d'aki, Aunty Nasrin yaushe rabon da kiga period d'inki, yau wata biyu kenan wani abune?....

Na'ima tayi hamdala Aunty Nasrin kina da ciki naga alamomi da yawa a tare dake na mai ciki, murna Nasrin keyi sossai, Na'ima tace kinsan me za'ayi bana son kowa yasan da cikin nan ina son ki 'boye ma kowa amma banda Mommy zan gaya mata da kaina.....

Nasrin ta yi shiru toh saboda me, ina ce abin farin ciki ne da ya kamata ko kowa bejiba Na'im ya Sani, Na'ima murmushi tayi toh ai ni ba Wanda ma nafi so kar yaji irin Yaya Na'im, toh me yasa bakyaso yaji? cewar Nasrin, Na'ima tace saboda wani dalilin da daga ni sai Mommy muka Sani, kiyi hakuri Dan Allah kada kowa yaji, In shaa Allah na miki na miki alk'awarin ba Wanda zaiji cewar Nasrin tana d'an goge guntun hawayenta......

A 'bangaren Mommy kuwa ankai mata amarya ta amsheta ba yabo ba tafallasa ta d'an mata nasiha daga nan suka wuce malali.....

Sunje Nasrin da Na'ima sun amshe su hannu bibbiyu sunci sun sha daga nan aka watse aka bar amarya da k'awayenta, Hidaya ta tashi tana juyi ta dubi k'awayenta tace ya kuka gani Hidaya matan Na'im, suka sa shewa tace yanxun saura abu d'aya ya rage min ko dai in fitar da waccan Mayyan ko kuma in hana ta sukuni a gidan nan, suka kara sa shewa....

"Kunsan wani abu kuwa bata haihuwa juya ce niko a nan ba Wanda be san na ta'ba zubar da ciki ba kunga kuwa ni nasan ina haihuwa, suka k'ara shewa harda tafawa, tace dan haka Na'im sai Hidaya, Hidaya sai Na'im, zama daram dam ko ya kuka ce suka fara dariya suna cewa sossai ma kuwa, .....

Abinda basu sani ba shine Nasrin zata shiga 'bangaren zata ce musu idan suna da bukatar wani abu suyi magana sai dai me ta gama jin komai da suke fad'i salati kawai takeyi tana me furta _Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un_ shine kawai abinda take cewa,.....

Yanxun ne ta gane dalilin da yasa Na'ima tace kar ta fad'a ma kowa, amma ta d'au ma kanta alkawarin zata bita duk yadda take so kuma zata dage da adu'oi , ai tasan mai hakuri baya ta'ba ta'bewa ta juya ta koma abinta......

Ango ya shigo da abokanan sa sunyi adu'an alkhairi sun kwashe kawayenta sun maida su gida, dama ita Nasrin kowa ya tafi ta 'bangarenta......

Ya kura su dukansu ya musu nasiha yace idan da mai magana yayi Nasrin tace bata da abin cewa, Hidaya kuwa ta ce nidai a bi ahankali a zauna dani lafiya, idan ba haka ba za'a ga ba dai dai ba, kuma ni ba zan zauna inyi ma kowa girki ba kowa yayi nashi sannan kuma ba za'a rinka shiga sabga nah ba idan ba haka ba wlh za'a ga ba daidai ba na gama magana.....

Maganan ta ya bala'in k'ona ma Na'im rai, amma besan meyasa baya iya yi mata magana ba, ya rasa meke damunsa, Nasrin kuwa tashi tayi tace Ango da Amarya asuba ta gari, bata jira cewar su ba ta haye sama abinta......


*EDITED BY*
πŸ’NUSNIM ( *TWIN SIS*)πŸ’


πŸ“ *DEDICATED TO*πŸ“
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you all😘
[1/25, 7:58 AM] β€ͺ+234 706 774 5996‬: πŸ‘« *HA'DI DAGA ALLAH*πŸ‘«

*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN

Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.A),ina mika godiya gareku masoyana kan adu'oin ku akan rashin lafiyan Mahaifiyata ina alfahari da ku, Allah ya bar zumunci, nagode sossai wa'inda basu da lafiya Dana gida Dana asibiti Allah ya basu lafiya, AmeenπŸ‘........

Wa'inda suka rigamu gidan gaskiya tunda ga zamanin annabi Adam har zuwa yanxun Allah ya jik'ansu ya yafe musu, mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani, Allahumma Ameen..πŸ‘

*116 - 120*
*************
✍ "Ango ya kwana d'akin Amarya, sai dai duk magungu nan da Hidaya tayi anfani dashi bashi ya hana Na'im gane cewar ita ba budurwa bace, amma abin takaicin shine ya kasa yi mata magana, sai dai abin na k'asan ranshi......

Nasrin kuwa da ta tashi ta gyara ko ina ta had'a break fast ta cika cikinta, ta koma 'bangarenta ta rufo kofa, da suka Na'im yace "Hidaya yunwa nake ji please ki had'a mana break fast tsaya tayi ta na kalonsa galala, tace wlh bazan yiba daga zuwa ko amarcin ban gama ci ba amma zaka wani ce min in shiga kitchen?, mtsw ta ja tsaki, sai dai tashi yayi ya shiga kitchen d'in da kanshi ba dan yaso ba, saboda dama Mommy bason Auren nan takeyi ba, yasan bazata ta'ba kawo musu abinci ba......

Biyo shi kitchen d'in tayi, Swt hrt why not ka kira Nasrin ko ita zata iya, bana son ka wahala, yayi shiru sai kuma yace ina zuwa ya haura sama sai tabi bayansa, yaje ya samu k'ofan a rufe ya knocking tace waye ne?, ya amsa ta, ta bud'e k'ofan ta gansu a tsaye tace "lafiya?, Lafiya lau dan Allah break fast nake son ki had'a mana, saboda me yasa zan had'a muku break fast kai da kanka kace ka yarda kowa yayi girkin ta, yanxun kuma kana cewa inyi maka break fast?,......

Murmushi yayi kiyi hakuri please ki had'a mana, kinsan amarci muke ci ba mu gama ba ai be kamata in shiga kitchen yanxun ba cewar Hidaya, Nasrin ta kalleta galala tayi wani shu'umin murmushi bakomai "Mine, me kake so kaci?, komai kika min inaso zanci, toh shikenan ba matsala, ta kai mai light kiss a saman lips, ta juya ta wuce ta bar Hidaya da bak'in ciki.....

Ta dafa ruwan zafi da ruwan citta da kanun fari, ta dafa white doya ta zuba a food warmer, ta nik'a kayan miya ta soya ta kad'a k'wai ta d'aura egg source da yaji curry da albasa sai k'amshi yake yi, ta na cikin juyawa Hidaya ta shigo tace "kiyi sauri yunwa nakeji" ta d'ago kanta tana kalonta lallai Hidaya wlh ba dan mijina ba ke baki isa in kalleki ba, amma ni nasan darajar Aure kuma ina son mijinah tsakani da Allah, sanan kuma ina Neman ladan da Annabina Muhammad (S.A.W), yake kwad'aitar damu akan aure, ta juye a cikin small bowl ta d'auka zata fita ta juyo tace kinsan ni nayi ilimin Addini kuma nasan darajar Aure ta juya ta fita abinta......

"Hidaya ta fito ta fara masifa tana zage zage wai tace mata bata da ilimi ita jahila ce, Na'im yazo yana cewa wai me kukeyi ne haka?, dan Allah bana son hayaniya, kuzo Ku zauna muyi break fast please yana Jan kujeran dining ya zauna,Nasrin tace ni na riga da na yi nawa ta juya ta haura sama abinta......

Sun zauna suna cin abinci, Hidaya tace "ni wlh abincin nan ba dad'i kwata kwata ci kawai nakeyi, ya d'aga kanshi ya kalleta, "ke" wacece bata iya abincin ba toh har makaranta koyan abinci tayi, sannan kuma

7 / 10