Author : Khadijah Al'Eeman Category : Complete Novels
ne, har yanxun kuna nan a haka lallai kam, taja hannun Nasrin tace muje d'akinki, Yayanah, Ahmad na fallon 'kasa yana jiranka, suka fice, ya rufa musu baya,.....
Sun shiga d'aki, Na'ima tace "haba Aunty Nasrin, meyasa kike biye mai kuna irin wanan abun, baki san yarda zakiyi kija hankalin Namiji bane?, tace "wallahi Na'ima nayi nayi har na gaji", tace "kash" ai ba'a gajiya, makaman ya'ki zaki nemo masu karamci da aminci, bari kiji kinsan yarda ake tarairayan new baby idan an Haifa?, toh haka zaki maida Yayanah, wallahi Aunty Nasrin "you can do it, karki bani kunya mana......
Nasrin tace "hmmm" naji ni bama wannan ba ina so ki ro'ki mommy ina son in koma makaranta, Na'ima tayi murmushi zaki koma school but da sharad'i, tace menene sharad'in?, tayi murmushi tace "sai kin canja min Yayanah, if you do that I promise you zaki koma any type of school of your choice", but now sai kinyi abinda ya dace,......
Tayi shiru idanuwanta sun kawo ruwa, Na'ima tace zaki iya Aunty Nasrin "promise me zaki canja Yayanah" and also you will love him with your heart and soul"?, tayi murmushi tace "In shaa Allah" zanyi 'ko'kari inga na shawo kan wanan matsalar, thank for your care, I really appreciate your efforts", nagode sossai.....
A nan ta 'kara mata wasu tips da zata bi domin shawo kansa, tace ina zuwa bari in d'auko bag d'ina nazo miki da wani tsaraba, ta fita bata dad'e ba ta dawo da jakanta, ta ciro humra tace "kinga wannan a gashi zaki rinka shafawa, ta 'kara ciro wani ta mika mata, wannan a jiki zaki rinka shafawa duk wani lungu da sa'ko na jikin ki, ta kara ciro wani kwalban turare tace wannan a jinkin kaya zaki rinka shafashi, sanan kwalliya ba kama hannun yaro duk wani shiga da zai rinka tasar mai da hankali ki rin'ka yi, and kuma nasan gobe zaki fara girki, a nan 'bangaren ba sai na miki bayaniba ke expert ce a nan wurin.....
Sanan gobe Yaya Na'im zai fara aiki, karki dinga barin mijinki da yunwa, kiji koh, Dan Allah Aunty Nasrin karki bani kunya, kiyi komai "for the sake of your marriage and also for the sake of our family",......
Tace "Karkiji komai zan baki mamaki ba d'an 'karami ba, daga yau ba sai gobe ba, ko dan son da kuke nuna min, zan faranta muku ni kuma da yardar Allah......
Na'ima tace mungode sossai, Allah ya bar 'kauna, school kuma "In shaa Allah" zaki koma.......
*EDITED BY*
π NUSNIM ( *TWIN SIS*)π
π *DEDICATED TO*π
Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you allπ
[1/25, 7:57 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*66 - 70*
**********
βπ»Gaba d'aya ya daburce, 'kamshin ya tada mai da hankali, 'karfin hali kawai yakeyi, ya gama sa mata kayan, ta kama hannunsa suka fita, shi dai binta kawai yakeyi tamkar raqumi da akala,......
Suna sauka Ahmad ya fara dariya, yana cewa Romeo and Juliet, irrin wanan soyayya haka, har ankawo abinci babyn mu nata kuka mu dai munci namu ko Nurrul Hayatee?, Na'ima tace wallahi kuwa baby, sun wani shige ciki, kamar su kad'ai ne a gidan......
Nasrin tayi murmushi suka gaisa da Ahmad, tace habebee muje muci abinci, ni wallahi yunwa nakeji, kuma kaima nasan kanajin yunwa, muje koh, ya bita kamar wani 'karamin yaro, ta juyo ta kalli Na'ima suka ma juna murmushi,.....
Suka zauna nan ma Nasrin tace ai ita dole a kan 'kafanshi zata zauna, yace ba ga kujera nan ba kija ki zauna mana, ta 'bata rai tace "wallahi indai bazan zauna a kan 'kafanka ba bazanci ba.......
Shi kuma yaji yana bukatar taci abincin, sai ya kama hannunta ya zaunar da ita kan 'kafarsa, ya zuba abincin ya fara bata a baki, tana 'koshi ta amsa spoon d'in ta fara bashi, Na'ima ta ta'ba Ahmd ta nuna mai su, ya saki baki yana kallonsu,....
Yace "baby yaushe suka fara wannan shirin haka?, tayi murmushi tace "ai ni dear dad'i naji wallahi, ta canja Yayanah, yanxun zai koma tamkar kowa, wallahi mommy sai taso Aunty Nasrin fiye da tunaninka, yayi murmushi yace "Allah ya 'kara had'a Kansu", tace "Ameen".......
Sai da Nasrin ta tabbatar ya kwoshi sanan ta kyaleshi haka, ta kwashe kayan ta kai kitchen, ta dawo ta samesu sunata hira, ta zauna kusa dashi, tace Aljananah yaushe zamuje gida gaida mommy?, yayi murmushi yace next week "In shaa Allah", tace toh Ubangiji Allah ya kaimu, dukansu suka amsa "Ameen".....
Ahmad yace toh masoya mu zamu tafi, mun gaisheku, Na'im yace "toh mungode", Ahmad yace Kasan mata da son gulma, zo muje waje abokina, Ku samemu a waje, suka fita abinsu......
Na'ima ta juya ta kalli Nasrin tace "wallahi har naji dad'i, ina ta sa miki Albarka, kinga yadda gaba d'aya hankalinsa ya koma kanki beda wani katabus, toh wallahi ki 'kara makaman ya'ki, kin dai ji abubuwan da na fad'a miki koh, ta d'aga kai, "In shaa Allah", I will try my best, tace toh shikenan muje,.....
A 'bangaren su Na'im kuwa Ahmad cewa yayi abokina wai meke faruwane?, irrin wannan soyayyar haka, Gaskiya kun birgeni, abokina kar kayi wasa wallahi, Allah ya 'kara dankon soyayya,......
Ahmad ya amsa da ameen, amma kasan menene?, yace sai ka fad'a, nan ya kwashe labarin komai ya fad'a masa,Ahmad yace kasan Allah wallahi karkayi wasa da damanka, kawai ka yarda kana sonta, menene a ciki,...
Na'im yayi murmushi, yace amma baka ganin ba zata rama abinda nayi mata ba kuwa?, Ahmad yayi murmushi yace "Nasrin nada hankali, tana da tarbiya ba abinda zata maka, ka yarda dani", yace toh shikenan za gwada, yauwa ko kaifa,.......
A dai dai nan suka 'karaso wurin su, suka musu sallama suka shiga mota suka kama hanya.....
*EDITED BY*
π *NUSNIM ( *TWIN SIS*)π
π *DEDICATED TO*π
Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you allπ
[1/25, 7:57 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*61 - 65*
***********
βπ»A lokacin Na'im ya shigo d'akin, yace toh ai sai a fito a d'aura mana girki koh, Nasrin tace "toh ba yanxun zamu fito ba kai wallahi heart ka cika son kwad'ayi, kai dai kace kayi missing d'in abincinah kawai", duk cikin shagwaba take kallonsa, ya tsaya shi kuma ya saki baki yana kallonta, sai kawai yaji tana burgeshi.........
Na'ima tayi gyaran murya tace toh ai yau daga gidan mommy za'a kawo koh, sai gobe zata fara girkin, su Yaya manya an'kwosa a fara cin girkin amarya, toh ai naga ka saba cin abincin ba yau ka fara ba koh, yayi murmushi yace "hmmm, baza Ku gane bane, Nasrin ta tashi da sauri taje ta kwanta a kan kafad'ansa tana bubbuga 'kafa dan Allah Aljannah nah ka d'an kaini bathroom mana inyi wanna, 'kafafuwana ciwo suke min yau wallahi, ya kasa ce mata komai, sai kallonta yakeyi, tace toh ka tsugunna in hau mana, "yace Nasrin kina da nauyi bazan iyaba", tace ni wallahi toh ka d'aukeni sai ka kaini, in yaso sai ka fito, ya kasa ce mata komai kawai ya sunkuceta yayi hanyar bathroom d'in, aikuwa ta juyo ta kalli Na'ima tana murmushi, Na'ima ta d'aga mata babban yatsanta alaman jinjina, a lokacin kuma suka shiga bathroom d'in......
Yana ajiyeta ya juya zai tafi tayi saurin kamo mai hannu tana cewa "White man plss kayi min wankan duk jikina ciwo yakeyi", ya juyo da niyan mata masifa, sai kawai yaga tana mishi wanni kallon da bema san yadda zai fassara shi ba, duk jikin shi ya riga da ya mutu, ta 'ka'kalo murmushi yace "kinga muna da ba'ki a gidan nan, kar suga mun dad'e", tace toh shikenan sai na fito......
Bata jira mai zaice ba ta tu'be kayanta ta jefa a washing mashine,ta d'auko towel, da sauri ya juya ya fita, a lokacin kuma Na'ima ta fita, ya zauna ya dafe kai, yana tuna nin meke damunsa neh, yana jin wani abu ga me da Nasrin amma besan ko menene shi ba, ko dai ya fara son tah neh be sanibah, toh in dai hakane gaskiya akwai matsala,.......
Yayi tsaki ya nah 'karyata abinda zuciyarsa ke fad'a masa, anya da gaskene kuwa, bai ankara ba kawai yaji har ta bud'e kofar bathroom d'in ya mi'ke da Saudi zai fita, tayi saurin shan gabansa, tace haba Hubbynah, ka jirani mana in gama shiryawa ko gaida Ahmad banyi ba fa,.....
Be ce mata komai ba ya koma ya zauna, taje gaban dressing mirror d'in ta shafa mai, ta d'an dan gwala human da Na'ima ta bata na jiki ta shafa, ta shafa na gashin shima, ta gama kenan ta juyo zata je ta d'auko kayan da zata sa, taga yana Satan kallonta, tana kawowa daidai inda yake tayi saurin sakin towel d'in ta fad'a kanshi, tace "aush" tayi kamar ta yi tun tun'be, yayi saurin ri'kota yana cewa me ya faru, ta ri'ke 'kafa tana cewa na bige 'kafa ne, duk a cikin shagwa'ba takeyinsa,.....
Yace "sorry kinji, tashi kisa kaya, tace bazan iyaba ka d'auko min insa please, yayi kamar bazaijeba, sai kuma ya tashi ya d'auko mata jallabiya black da veil white,....
Tace saura bra da pant, yayi shiru yana tunanin ya zeyi ya d'auko, ta 'kara shagwa'be fuska tana kuka, yayi saurin cewa a ina suke ta nuna sight drawer, ya bud'e gasunan birjik a ciki, sai da ya 'kare musu kallo ya d'auko mai iri d'aya (pant da bra d'in) white and black colour ya kawo mata,.......
Tace toh kasa min mana, ya zaro ido yace "ni zansa miki?, ta gyad'a kai, yace "toh ai ban iyaba, tace zaka koya ai, ta nuna mai yadda akeyi da hannu, yasa yana wani runtse ido, ita kanta kunya takeji amma ya zatayi, dole ta ajiye kunya gefe, ta gyara mijinta.......
Yana sa mata tunda turaren humra nan ya biggi hancinsa duk ya fara da bircewa.......
*EDITED BY*
πNUSNIM ( *TWIN SIS*)π
π *DEDICATED TO*π
Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you allπ
[1/25, 7:58 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*71 - 75*
***********
βπ»Suna tafiya, Nasrin ta kamo hannun Na'im tace Aljanah nah muje ciki koh, ya bita suka shiga ciki,suka zauna a fallon 'kasa, sai kuma Nasrin tayi zunbur ta tashi, yace "Ina zakije?, tayi murmushi tace ina zuwa yanxun zan dawo, yayi murmushi yace ki sameni a Fallon sama ina jiranki, ta gyad'a kai ta wuce........
Ya tashi, ya haura sama shima, ya shiga bathroom dan ya watsa ruwa, ya gama watsa ruwan ya fito ya shafa mai yasa riga "short sleep white da three quarter wando white", ya fesa turaren white men, ya dawo fallon ya zauna yana jiranta.........
A 'bangaren Nasrin kuwa, ta cire wannan kayan da ya sa mata, ta d'auko wata riga iya kirjinta kawai ta ke rufewa, ko cibiya bata kai ba, ta dauko wando skin tied iya cinya tasa, ta shafe ko ina da wa'inan turarukan, sanan ta d'auko turaren down hill ta fesa a jikinta, ta raba gashinta gida biyu rabi ta kama da ribbon pink kallan skin tied d'in, kasanshi tasa pin na kama gashi colour sa blue, colour d'in rigan kenan, d'ayan kuma gefen ta 'kara taje shi ta barshi a baje, ta d'auko d'an kunne d'an 'karami pink colour tasa, sanan ta d'auko wani hill d'in takalmi blue colour tasa shi, gashi simple make-up tayi, abin ba acewa komai, tayi kyau sossai, ta kalli kanta a madubi sai kuma ta fara jin kunya, sai kuma ta tuna da maganan Na'ima, nan da nan taji wani 'karfi yazo mata, ta kama hanya ta fita........
Na'im na zaune ya d'an kishin gid'a ya rufe ido don bacci be isheshi ba, ya ji ana hura mai fuska, a hankali ya bud'e ido, ya 'kara rufewa ya bud'e, ya tashi zaune ya 'kare ma Nasrin kallo, yace "tsarki ya tabbata ga mahallincin wannan sura", ya had'iye miyau da kyar.......
Be san sanda ya jawo Nasrin ba, ta fad'a jikinsa, ya kai bakinsa kan nata wani irrin laushi yaji, ga wani 'kamshi dake fitowa daga bakinta,......
Saida ya tsose bakinta sossai, da kyar Nasrin ta kwace kanta zata gudu, ya 'kara fisgota ta fad'a kan jikinsa, yanata wani shinshinata, duk ya birkice,da kyar ya saita kansa,.......
Yana kallonta, ita kuma ta dukar da kai sai ya d'agota suka koma kan carpet, yace "Nasrin", sunan har kwakwalwar kanta taji shi, don be ta'ba kiranta dashi ba, yayi masifar dad'i a bakinsa, ta amsa a hankali........
Yace ban san da wani ido zan kalleki ba, bansan da bakin da zan ro'ke kibah, dan girman Allah kiyi hakuri ki yafe min duk abubuwan da nayi miki a baya, wallahi bansan me yasa nakeda wannan halin bah, but zama dake da kuma wa'azin da kike min, tare da taimakon Na'ima yasa na fahimci ya rayuwa yake, don girman Allah ki yafe min.......
Wallahi ina sonki tamkar raina, ina son muyi zama dake na aminci da karamci tare da mutunta junah, Nasrin zuciya baza ta ta'ba samun natsuwa da kwanciyan hankali ba, matsawar bakice kin yafe min ba, kuma ina so ki furta kina sona kamar yadda nake sanki, inajin ki har cikin raina, ina kuma alfahari dake a matsayinki na matata......
"Nasrin" kuka yaci 'karfinsa, ya kasa magana......
Ta d'ago kanta tana kallonsa ita ma tana hawaye, ta goge mai hawayen fuskarsa tana jijjigashi, tamkar karamin yaro tace "nagode ma Allah daya nuna min wanan ranan, na dad'e ina jiran wanan lokacin sai gashi Allah ya nuna min yau"........
Naji dad'i sossai da Allah ya fahimtar da kai gaskiya, yadda rayuwa take, na yafe maka mijinah domin ni ba jahila bace bare ince bazan yafe maka ba, domin ko Allah muna masa laifi ya yafe mana, toh in haka ne, ni wacece da za'amin abu ince bazan yafe bah......
Assalima yanxun Kaine keda aljannah tah, idan na bika tayi min kyau in ban bika ba kuwa, na gama ta'bewa duniya da Lahira, toh dan me bazan yafe maka bah,.......
Wallahi na yafe duniya da Lahira, kuma zan maka biyayya dai dai gwar gwadon iya wata, sai dai kaima ina rokonka don girman Allah ka canja d'abi'unka, kaso talakawa ka taimaka musu, iyayenka ka rinka yi musu biyayya, tsakaninka da kowa ya zama sai dai Sallama kawai, toh rayuwa zatayi kyau kuma kaima zakaji dadi, sannan zanyi alfahari da kai a matsayin miji please........
Yayi saurin sa ma ta hannu a baki alamar tayi shiru, yace "In shaa Allah, zaki sameni mai yin duk wani abu da zai faranta ran kowa, kuma yanxun zan amsa sunana na "white man", domin komai nawa zai zama fari harda zuciyatah......
*EDITED BY*
π NUSNIM ( *TWIN SIS*)π
π *DEDICATED TO*π
Nafee Anker, Mm Shakur, munay, Mamu, Afra and Rash kardam
Love you allπ
[1/25, 7:58 AM] βͺ+234 706 774 5996β¬: π« *HA'DI DAGA ALLAH*π«
*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN
*76 - 80*
***********
βπ»Nasrin tayi murmushi, tace "Alhamdulillah", yau ina mai matuk'ar farin ciki, Allah ya amsa adu'o'i nah, gashi Mommy da Daddy ba 'karamin dad'i zasu ji bah,.........
Yayi murmushi yace gobe nake so muje gidan, amma su Shureim ba sa nan, tace ina suka je?, yace "sunje gidan Dady Tofiq dukan su" kai gidan bazai min dad'i ba, amma tunda Mommy na nan ba matsa, yayi murmushi yayi 'yar gidan mommy,........
Dare nayi tayi wankanta kamar yadda ta saba, tasha white Night gown d'inta ta kwanta, ba ta dad'e da kwanciyya ba ya shigo d'akin, ya yaye blanket d'in, yace mata "waya gaya miki yanxun ke kad'ai zaki rinka bacci?, ai yanxun mu biyu zamu rinka bacci........
Ta shagwa'be mai fuska tace toh ai ni na fara jin bacci, yayi murmushi yace "mallama tashi zakiyi mu tafi 'bangarenah", ta rufe ido kamar tana bacci, aikuwa bata ankara ba taji ya d'auketa chak, be direta a ko ina ba sai saman gado, ya hau shima, yasa kansa a 'kirjinta nan da nan wannan turaren humra ya daki hancinsa, ya sauke nufashi da sauri, yace "Mine" ina da tambaya, tace "yi tambayarka ina jinka", yace dan Allah menene sirrin wannan turaren, tunda nake ban ta'ba jin turare mai 'kamshin dad'in wannan ba wallahi,......
Tayi murmushi kai dear, turare ne kawai ba wani abu ba, sai yayi murmushi yace tashi muyi sallah, tace "toh ai ni nayi sallah" yace raka'a biyu zamuyi mu gode ma Allah, taji gabanta ya fad'i, don ita wallahi ba abinda take tsoro irrin wannan Daren........
Yace mata tashi mana, ni gashi har nayi ke kina zaune, ta tashi tayo alwala, ta fito, tayi hanyar 'kofa, yayi saurin shan gabanta, yace ina zakije?, tayi murmushi tace hijabi zan d'auko, yace koma in d'auko miki, ta koma ta zauna, ya juya ya fita yana murmushi, a ranshi yace "yarinya duk ki gama wani jin tsoronki"......
Ya kawo mata hijabin, tasa, suka tada sallah, sun idar, yayi mata tambayoyi kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, ta kuma bashi amsa yadda ta dace, tana mamakin addini irrin na white man, nan ya kama kanta yayi mata adu'a, daga nan suka mike yaja hannun ta suka koma saman gado..........
Daga nan labari ya fara canjawa, naso inga ko me zai faru, ashe Anee Luv na biye dani tana kallona, daga nan ta jawoni waje tace toh ya isa haka sai a barsu su sha amarcin su, dole ne sai kin d'auko komai ne?,..........
Nace toh Anee Luv da safe na koma, masu karatu nima zan ajiye littafina da abin rubutu, zanje in huta sai gari ya waye da safe na dawo,........
Sai Ince Nasrin da Na'im asuba ta gari.......
*EDITED BY*