Advertisements
Chapter 2 Reading HA'DI DAGA ALLAH Kaddarar So by Khadijah Al'Eeman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

HA'DI DAGA ALLAH Kaddarar So by Khadijah Al'Eeman

Author :  Khadijah Al'Eeman Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 10

3K to 6K   out of 29.9K words

da kud'i da kyar in iyayyenta zasu baka, yace saboda me?, tace irin wulakancin da Yaya Na'im yake mata, ai dole tace a'a.....

Yayi murmushi yace Yayanan naki bazai canja ba, ko yaushe zai daina abinda yakeyi oho, Allah ya sawake, sukace Ameen ya rabbi....

Na'im ya shiga Fallon Daddy da sallama, ya zauna, yace Daddy gani kayi kirana, yace Na'im, ya amsa da Na'am, ina son ka bani hakalinka anan, ya maganar da mukayi dakai kwanakin baya?,ya dukar da kai yayi shiru, yace toh na baka wata biyu idan har baka fito da mata ba zan aura maka Duk wadda naga dama....

Hankalinsa ne ya tashi, yace Daddy pls, ya dakatar da shi da hannu yace tashi ka tafi na gama magana.....

Ya fito zufa na keto masa ya shiga Fallon shi, ya zauna ya dafe kai, Na'ima ta taso da sauri tace Yayanah lpy?, meya faru?,....

Yace Na'ima Dady ya bani two months in fito da matar Aure idan ba haka ba zai bani wadda yaga dama, ni wlh banda Wanda nakeso kuma duk fad'in k.d banga wadda ta mun ba, inaga barin garin kawai zanyi ko kuma 'kasar ma gaba d'aya....

Tace a'a Yaya iyaye daban suke,kayi hakuri komai zai wuce In shaa Allah, zaka samu wadda kakeso, kaga before lokacin anyi bikin mu nida Ahmad, kila a friends d'ina kasamu wadda tayi maka, kayi hakuri....


Ahmad yace karka damu, zamu fara searching In shaa Allah zaka samu....

Lukman yace wanan gaskiya ne karka damu, kawai canja halinka zakayi ka koma normal kamar kowa, yace to dama ni abnormal ne?, yace kai wlh baza ka canja ba, Allah ya shiryeka....

Sai ga Nasrin ta shigo kwashe kayan da ta kawo ma su Ahmad abin motsa baki, ta dauka mistakely sai Cup ya fad'i a kasa ya fallatsa a kayan Na'im gasu white, yana tashi ya wanka mata wani lafiyayyen mari....

Yace ke jahillace, ko kuma makauniya, da bazaki iya d'aukar abu a hankali ba, dama halin yaran talakawan nan kenan wlh, jiki na rawa an'kosa aje a shanye sauran, banza kawai....


Na'ima tace haba Yaya Na'im dan ya fad'i bata Sani ba, gaskiya ka daina irin wanan...

Lukman baki bud'e yake kallonsa, Ahmad kuwa cewa yayi bansan randa zaka canja ba wlh, meye abin wulakantawa a talaka, da mai kud'i da talaka duk d'aya suke a wurin Allah.....

Ya juya yayi tsakiya shige d'aki ya bugo kofa...


*EDITED BY*
πŸ’Nusnim ( *TWIN SIS)πŸ’


πŸ“ *DEDICATED TO*πŸ“
Nafee Anker,Mm Shakur, Munay,Mamu,Afra and Rash kadam
Love u All😘
[1/25, 7:57 AM] β€ͺ+234 706 774 5996‬: πŸ‘« *HA'DI DAGA ALLAH*πŸ‘«

*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN

*21-25*
***********
✍🏻 Na'ima ta girgiza kai tazo ta kama Nasrin tace dan girman Allah kiyi hakuri, nasan zakice saboda anga baki da gata ne shiyasa, ba haka bane kina da gata, tunda Allah ya baki rai da lafiya, ki cigaba da hakurin da kikeyi nasan dole watarana Yaya Na'im zai nemeki, kuma zai baki hakuri, kiyi hakuri kinji, bata ce komai ba ta juya ta fita abinta....


"Lukman yace ma Ahmad ni wlh halinsa na bani mamaki, yarinyan da kwata kwata abin duniya be dameta ba, na tabbata da tanada inda zataje tayi aiki abiyata ta samu su rinka cin abinci zataje wlh....

Ahmad yace danma su mommy da sauran yaran gidan basa wulakantata, da wlh "she will run away" na tabbata, Allah ya kyauta ya shirya Na'im, sukace Ameen....


Yace mu zamu koma, Swt berry sai munyi waya koh, tace alright baby, "thanks for coming", ta rakasu har wajen mota suka kama hanya suka fita....

Yau ya kama Thursday, da daddare suna zaune dukan su a fallo, sai ga kiran Labiba ya shigo phone d'in mommy, ta dauka tace yakike ya school?, ta amsa lafiya lau, nan take fad'a ma mommy cewa next week Friday ne zasuyi send forth, mommy tace Ma shaa Allah zamuzo da izinin Allah, Allah yasa Albarka ta amsa, sukayi sallama ta kashe, ta juya wurin Dady, tace dadyn yara wai next week Friday send forth d'in su Nabila, yace toh fa na manta d'azun na je makarantan su shurem shima ranan Friday graduation d'in su.....

Mommy tace Shurem shine baka fad'a ba?, yace Allah mommy na manta ne,Na'im yace wawa kawai wata rana ma zaka manta da kanka ai, Na'ima kuma cewa tayi in an fad'a muku Abu a school kana dawowa ka fad'i kaji, yace toh Aunty Na'ima shiyasa nake sonki wlh amma shi Yaya Na'im d'inan sai masifa kawai ya sa ni, Dady yace a'a Shurem banda rashin kunya kajikoh, ya gyada kai, sai mommy tace to yanxun ya za'ayi Daddyn yara?, wa zaije ma Nabila?, .....

Yayi murmushi yace ina ganin Alhaji Tofiq da matarsa sai kuma Na'im, ya d'ago kai da sauri ya kalli Dady kamar zeyi magana sai kuma ya fasa, Alhaji Tofiq 'kanin Mahaifin Na'im ne su biyu ne kad'ai mahaifiyarsu ta haifa, daga kansu bata kara haihuwa ba har Allah ya mata rasuwa, ta rasu da shekara biyu Mahifinsu shima ya rasu, dangin mahaifinsu suna Libiya, mahaifiyarsu kuma danginta na kano, amma saboda basa son Auren shiyasa basu damu da a ina suke rayuwa ba, gashi mahaiginsu nada kud'i dai dai gwargwado, ya basu ilimi sossai kafin ya rasu, kuma dukansu suna da kud'i sossai, sai dai shi Alhaji Tofiq bai ta'ba haihuwa ba, wanan kenan....

Na'im ko aransa yace ni banzanje ba amma nasan Dady in har nace bazanje ba, zaisa ni zuwan dole, nasan abinda zanyi ai......

Haka rayuwa keta tafiya, kullum da muguntar da Na'im kema Nasrin, itako jar ta saba, da idan ya mata sai dai ta koma gefe tayita kuka Na'ima ke bata hakuri, amma yanxun ta daina, sai dai tsoron shi datakeyi haryanxun.....

'Bangaren gidansu Nasrin kuwa in ka cire ummanta ba Wanda yasan halin da take ciki, idan Inna Aisha ta tambayeta sai tace komai na tafiya daidai, mahaifiyarta kuwa kullum tana 'kara bata hakuri, tana ce mata ta rinka hakuri, takanyi murmushi tace Umma wlh baya damuna tunda dai ina samun abinda zamu rufama juna asiri, 'kannena na zuwa makaranta, muna samin abinda zamuci, kinga kome zemin ina 'karuwa dasu, kuma kowa na gidan na sona, Dan shi kad'ai yana hantarata bazai damena, ummanta ta ce Allah ya miki Albarka, tayi murmushi tace nagode ummanah.....

Yau ta kama an tashi anata girke girke da abubuwan da za'a kai makarantansu Nabila da kuma shurem, shiko goganaku ya kudundune a cikin blanket, Mommy ce taga har karfe takwas be fito ba kowa ya shirya har Alhaji Tofiq da matarsa sun zo, amma shi ko lekowa beyiba, ta shiga d'akinsa ta Ganshi a kwance tace Na'im lafiyanka kuwa naganka haryanxun baka fito ba, yace Mommy cikina ke ciwo sossai, tace subhanllah kasha magani kuwa?, yace eh nasha, kodai za'a kira Doctor ne, yace ai nasha magani zai sauka, tace toh Allah ya sawa'ke, ta fita ta fad'a musu, suka shigo suka mai sannu, suna fita ya fara tsalle yana murna, haka kawai a sa mutum zuwa wani B.U.K banzuwa....

Sai dai Na'ima ta bisu suka tafi, shikuma Shurem su mommy suka je mai....

Gidan yayi shiru ba kowa sai ma'aikatan gidan, Nasrin ta kammala komai ta shirya zata tafi, Na'im ya kirata yace mata farfesun Kaza yake son ci yanxun nan, haka ta shiga kitchen d'in tayi mai, rabin kaza ta sa mai, tunda shi kad'ai ne a gidan, ta gama ta juye a bowl ta kaimai, yana bud'ewa yace yana ga kamar be kai kaza daya ba, ko kin sata ne zaki kai gidanku, zuciyanta na tafasa tace a'a rabi nasa saboda naga kai kad'ai ne......


Aikuwa ya d'aga ya watsa mata a jiki yace ki wuce kije ki yi wani, nan gidan ubanane kuma muna da komai enough, "dan haka sai kiyi min na kaza d'aya nake so, wawiya kazama kawai, 'bace min da gani karnayi 'kasa 'kasa dake a nan wurin,....

Ta juya ta tafi kitchen d'in ta had'a mishi wani ta kawo mai, ko kallonta beyiba, ta juya zata tafi yace ke, zonan, ta dawo tazo ta tsaya yace d'auka kije kisa a fridge na fasa ci, ko kuma ki zuba a leda ki kai gida, Dan na San kafin Ku samu irinshi sai anyi albashi ko kuma in daddy ya fitar da zakka, bata ce mishi komai ba, ta d'auka ta fita, ta kaiwa masu gadi, ta juya ta fita abinta.....


Angama su mommy sun dawo inda Labiba tazo da kyaututtuka, shi kuma Shurem shi a kaba "the best student" a school d'in.....

Akwana a tashi yau wata d'aya ya shud'e a cikin wata biyun da aka d'iban ma Na'im kuma yau ne aka d'aura Auren Ahmad da Na'ima, biki ne Wanda ya amsa sunansa, manyan masu kud'i sun halarcin d'aurin auren, Haka kuma amarya tayi kyau sossai, kawayenta sunzo har wa'inda sukayi school d'aya, An shirya dinner bayan ankai amarya, Lukman da Ahmad sunata nuna ma Na'im 'yan mata amma sai ya ta'be baki yace basu yi ba,a haka har a ka gama, washe gari kuma dangin ango suka had'a walima, can na hango Hauwa Usman da Hauwa Nuhu Shehu sunata kwasar girki LolπŸ˜‚....

A haka a ka kare amma fir Na'im yace bega wadda ta mishi ba, Ahmad yace mun maka Wanda zamu iya, Dady ya nema maka wadda ya ke so mu ba abinda ya damemu, da fad'a suka rabu ko rakiyan ango ma beje ba.....

Anyi sati biyu da bikin Na'ima, Dady ya kira Na'im yace masa kadai San yau saura kwanaki wata biyun dana d'iba maka ya cika koh, to wlh bazan sarara maka ba tunda kai ba kara min yaro bane, tashi kabani wuri.....

Yaje ya samu mommy a d'aki yana mata magiya, tace kaga Na'im ka fita a idona in rufe, aure ne sai kayi shi wlh, so kake mu zuba maka ido muyita kallonka ko menene, toh wlh baka isa ba dolenka kayi aure, shasha sha kawai, ta tashi ta fita ta barmai d'akin.....

*EDITED BY*
πŸ’Nusnim ( *TWIN SIS*)πŸ’

πŸ“ *DEDICATED TO*πŸ“
Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love u all😘
[1/25, 7:57 AM] β€ͺ+234 706 774 5996‬: πŸ‘« *HA'DI DAGA ALLAH*πŸ‘«

*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN

*26 27*
***********
✍🏻 Mommy na fita ya ri'ke kai yana salati, toh wai auren nan dole ne, a ina zan samu matar da zan aura daidai ni, ya Allah ka sa kada Dady yayi abinda yace zeyi, wlh bana son yin aure yanxu....

*BAYAN WATA 'DAYA*
Dady ne zaune shida mommy, Na'im yayi sallama ya shigo cikin fallon, suka amsa tare da kalonsa, ya nemi wuri a kan carpet ya zauna, yace Daddy ka kirani gani....

Yayi ajiyan zuciya yace Na'im ban ta'ba tunanin in nasa maka doka bazaka biba sai a wanan lokacin, na baka ilimi, tarbiya, soyayya ta d'a da mahaifi, kome zanyi sai na fara tuntu'banka kafin nakeyinsa, amma kai baka gani, Ashe ban isa ince ina son wani abuba kayi shi cikin gaggawa har sai raina ya 'baci, toh shikenan tunda na lala'baka, na nuna maka, na nuna 'bacin raina, amma still baka canja ba, ka 'ki bin dokata, kwata kwata, toh ka sani na 'baka za'bi ka'ki bi, this time around ni zan aura maka duk wadda naga dama....

Yace daddy pls ka saurareni, "Daddy yace Na'im bana magana biyu" tashi ka bani wuri, ya juya wurin mommy yace yanxun mommy kina kallo za'amin haka, ta daka mai tsawa tace Na'im you are very stupid, kana tunanin zamu zauna da kai a haka ne ba aure, toh ina son ka Sani kaima ta dalilin aure kazo duniya, don haka u most do it, tashi ka fita ka ba mutane wuri.....

Yana fita ta juya ta kalla Daddy tace toh yanxun ta ina zamu fara, yace bari Tofiq yazo muji yadda za'ayi, kinsan shi shawara yana da dad'i ko ya kika gani, tace wanan gaskiya ne, ya d'aga waya ya kirashi, yace gashinan a hanya dama gidan zaizo....

Ba afi minti talatin ba sai gashi, nan daddy ya fad'a masa duk halin da ake ciki, Alhaji Tofiq yace Yaya da an d'an kara bashi lokaci, Daddy yace kasan na bashi lokuta sossai, tun yaushe nake mai magana ya'ki saurarata yaushe zan zauna ina kallon shi, Na'im yafi so ayi mai duk abinda yake so, toh kuma ni abinda nake so ya gane mu muka haifeshi, mune iyayen shi, dole ya bimu.....

Alhaji Tofiq yace wanan haka yake, sai dai wani hanzari ba guduba kuna ganin haka ze yiwu tunda fa kowa yasan irin tsanar da yake ma Nasrin, Mommy tace In shaa Allah babu wata damuwa, kubar min komai a hannu na, ya kuma cewa toh iyayenta fa?, Mommy tayi murmushi tace abu mai sau'ki gobe In shaa Allah zanje in samesu kuma da izinin Allah komai zai daidaita, yace toh shikenan Allah yasa Albarka, suka ce ameen....

'Bangaren Na'eem kuma hankalin shi ya tashi sossai, yaje har gida ya samu Na'ima ya fad'a mata komai, tace kaima Yaya Na'im nasha fad'a maka cewan ka daure ma xuciyarka ga 'yan mata nan kala kala a gari wasu har kawo Kansu sukeyi wajenka amma kwata kwata baka kulasu, kai ba Aljanu gareka ba kai ba wani matsala kake dashi ba, rayuwar nan da kake gani bata da tabbas, mutuwa akeyi, so kake idan ka rasu ya zama baka da gata, ba ka da mai cewa Allah ya ji'kan baban mu, ya kamata gaskiya kama kanka fad'a, ni dai a matsayina na 'yar uwarka na baka shawara.....

Ya tashi tsaye yana kallonta idanuwansa sunyi ja sossai, yace gaskiya Na'ima bazan iyaba, barin 'kasar zanyi gaba d'aya, in na tafi sai inga wa za'a yiwa auren dole, Na'ima tace "haba Yayanah", iyaye daban suke komai zasu maka dole sai kayi hakuri, kuma kayi biyayya, sai kaga komai na tafiya dai dai yadda ya kamata.....

Yaya Na'im komai kace daddy ya maka yana maka, haka mommy tana maka, toh meyasa wanan karan bazaka musu suma abinda suke so ba, Albarka yayita binka har karshen rayuwarka?,.....

Gaskiya Yayanah ka zauna kayi tuna ni, kama Lanka fad'a, ni na rabu dasu lafiya, kai kuma d'an uwana ne rana d'aya, lokaci d'aya aka haife mu, sai dai kai ka rigani fito wa ne toh dan Allah kaima ka samu ka rabu dasu lafiya, ka roki Allah, Allah yasa shine mafi alkhairi a rayuwaka....

Jikin shi yayi sanyi, yace shikenan Na'ima zanyi yarda kika ce, kuma In shaa Allah bazan basu kunya ba, tace toh shikenan Allah ya bada Sa'a, yace "ameen" shiyasa nake sonki sis, akwai hankali, Allah ya baki masu miki yadda kike yima 'yan uwanki har iyayenki, sukaji ance Ameen, ba kowa bane illah Ahmad, ya karaso da murmushi a fuskansa ya d'aga ta, yana cewa lallai matanah yar aljannah ce, dukan su sukayi dariya, Na'im yace kunga tafiya ta nima na kusa auren nan in huta da abinda kukeyi min, Na'ima tace Yaya kazo kuci abinci, yace na 'koshi zanje gida inci, ya tafi abinsa...

Mommy taje gidansu farko ta fara samun Inna Aisha da maganar, tace toh Hajiya ban'ki ta taki ba, kuma ba wai ban isa in baki ita ba, na fi son mu samu mahaifiyarta domin tana da hakki akanta, kar taga kamar an ma ta ba dai dai ba, har sauran 'yan uwan mahaifinta bama ita kad'ai ba, tace wanan haka yake, Inna Aisha ta d'aga waya ta kira Mallam Shu'aibu da Mallam Barde, tace suzo tana nemansu, saboda itace babba, duk ta girme musu, basu 'bata lokaci ba suka zo, aka kira itama umman Nasrin d'in tazo ta zauna,....

A nan Inna ta zayyane musu komai da ake ciki, hankalin Umma ya tashi tace Hajiya kina sane da irrin abubuwan da ke Shiga tsakanin Na'im da Nasrin, kinsan a duniya ba Wanda Na'im ya tsana kamar Nasrin koh, kuma sanan yanxun ace da shi za'a had'ata Aure, gaskiya bazai yuwu ba kiyi hakuri Hajiya, Mommy tace kiyi hakuri dan Allah, Fatima ki bani hankalinki a nan ki saurara da kyau kiji, Na'im nada wani d'abi'a na wulakanta mutane nida mahifinsa munyi munyi ya daina abu ya gagara, sai dai daga baya mun gane cewan aure ne kawai zaisa ya natsu, toh auren ma ya gagara, ya'ki fitowa da wadda yake so, munyi lallashin, abu ya gagara, toh ta wannan hanyan ne kawai za mu samu ya koma kamar kowa, kuma ta hanyan had'a shi aure da Nasrin ne kad'ai zaisa ya janja, domin Nasrin itace yarinyar da muka yarda da tarbiyanta, Fatimah, Nasrin na tabbata zata maida mana da gidan mu abin alfahari, zamuyi alfahari da ita, ki taimaka mana dan Allah.....

Ummah tayi a jiyar zuciya, tace Hajiya na fahimce ki, kuma In shaa Allah zan 'karfafa ma Nasrin gwiwa, zan kuma fahimtar da ita yadda zata game, Allah yasa muce gwamma da akayi, kowa yace "Ameen"....

Inna Aisha ta ce Alhamdulillah, naji dad'i sossai Fatima, Allah ya sa a dace, suka ce "Ameen"..

Suko su mallam Shu'aibu da mallam barde a ransu dad'i sukeji, don sunsan Nasrin zata sha wuya, amma a filli sun nuna suna farin ciki da abin, Mommy ta musu godiya tayi musu sallama, tace sai anzo neman auren Nasrin, ta tafi abinta....

*EDITED BY*
πŸ’NUSNIM ( *TWIN SIS*)πŸ’


πŸ“ *DEDICATED TO*πŸ“
Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you all😘
[1/25, 7:57 AM] β€ͺ+234 706 774 5996‬: πŸ‘« *HA'DI DAGA ALLAH*πŸ‘«

*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN

*28 -30*
**********
✍🏻 Mommy ta isa gida lafiya, kuma ta fad'a ma Daddy yadda sukayi, Daddy yayi farin ciki kuma yaji dad'i sossai, yace Mommyn yara kira min Na'im d'in, ta d'aga waya ta kira shi, tace kazo ka samemu a Fallon 'kasa, bata jira abinda zaice ba ta katse wayan, cikin minti uku sai gashi yazo, yayi sallama ya shigo ya nemi wuri ya zauna.......

Dady yace Na'im mun yake had'aka aure da Nasrin, ya d'ago da Saudi, cikin tashin hankali yace wata Nasrin d'in?, Mommy tace Nasrin dai ta nan gidan, yace mommy Nasrin d'in nan gidan kokuwa

2 / 10