Advertisements
Chapter 9 Reading HA'DI DAGA ALLAH Kaddarar So by Khadijah Al'Eeman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

HA'DI DAGA ALLAH Kaddarar So by Khadijah Al'Eeman

Author :  Khadijah Al'Eeman Category :  Complete Novels

Chapter   9 / 10

24K to 27K   out of 29.9K words

ta gani sai cewa tayi ya za'ayi a siyo mata kujeran dubu d'ari aiko na Fallon Nasrin dubu d'ari biyu da hamsin ne , ina laifin ya siyo mata na dubu d'ari biyar, sai kuma ta rufe baki kar ya jita, ba godi balle Nagode, shi halin Hidaya na bashi mamaki wlh, shiyasa yake bala'in son Nasrin, ta iya magana gata da biyayya, bata son taga ranshi a 'bace, shi be masan yadda akayi ya Aurota ba kuma da yayi yinkurin sakinta sai ya kasa ya rasa dalili ......

"Yau Hidaya ta amsa girki, haka ta saci hanya taje wurin boka, maganin da ya bata be mata aiki ba, na farkon ne kawai da akayi kafin ta shiga gidan ya kamashi, ya bata wani wai ta zuba mai a abinci amma karta bari yayi bismillah, ya k'ara bata wani turare ta fesa a jikinta da daddare,amma da sharad'i, shi turaren nan duk randa Nasrin ta Haihu ya ga baby ta zata haukace, ta tsorata da jin haka, tace toh aka she jaririn tun a ciki, yayi wani irin k'ara yace Maman a tsaye take tana adu'a sossai, kuma k'anwanshi da mahaifiyarsa suma a tsaye suke Dan haka bazai iya ba ta tashi ta tafi, ta zube mai kud'i ta bar wajen.....


Ta dawo tayi girkinta tsab tuwon semonvita da miyan kubewa d'anya tayi, ta barbad'e miyan ta juya sossai, ta shirya komai, a lokacin Nasrin ta fito tana bala'in jin yunwa ta Shiga kitchen domin dafa Macaroni dan shi take jin cin......

Sun fito sun zauna akan dining, tace ni bazanciba yau kwata kwata bakina ba dad'i wlh, yace toh zubamin ni yunwa nakeji, ta zuba mai zai kai baki kenan yayi bismillah sai ta dakatar dashi,yace menene sai tace ba komai,haka suka dinga yi har sau biyar, tsaki yayi ya ajiye abinci ya tashi, tana kiranshi ko sauraronta beyiba ya wuce kitchen, dama k'amshin abincin Nasrin ya cika mai hanci......

Ya sameta ta gama ta zuba wani a plate wani kuma a food warmer, tana wanke tukunyan, sai cewa yayi dan Allah a sammin ko kad'an ne yunwa nakeji, ta juyo ta kalleshi ai yau ba'a d'akina kake ba, ba Amarya tayi girki ba?

Ni dai idan zaki bani ki bani, tace idan bazan bada ba fa?

"Shikenan, toh bazan bada ba, ta d'aure fuska, aikuwa ya d'auki plate d'in da gudu ya fice ko kafin ta kai ga fita kitchen d'in har ya hau sama, tana kiranshi tana rik'on shi ko ya juyo, ta juya zata koma kitchen d'in taji anja tsaki sai a lokacin ta lura da Hidaya a wajen, murmushi tayi ta ce Amarsu sannu da hutawa, ta shige kitchen abinta, Hidaya kamar ta had'iye zuciya ta mutu.....

Da daddare ta shafa turaren nan a jiki lokacin kuma Na'im ya shigo, yana kallonta yaji kanshi ya fara sarawa....


*EDITED BY*
๐Ÿ’ NUSNIM ( *TWIN SIS*)๐Ÿ’


*DEDICATED TO*
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam
Love you all๐Ÿ˜˜
[1/25, 7:58 AM] โ€ช+234 706 774 5996โ€ฌ: ๐Ÿ‘ซ *HA'DI DAGA ALLAH*๐Ÿ‘ซ

*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN


*141 - 145*
*************
โœNasrin tun sanda Zainab ta bata shawara ta d'auka azkhar takeyi ba kama hannun yaro,sai dai ta kasa fad'a ma mommy halin da ake ciki,Na'ima ma inta tambayeta ya zamansu sai tace komai normal, in tace zatazo sai tace tana school ko ta zo bazata sameta ba....

'Yauma kamar kullum tana zaune ta gama komai tasa karatun al'qur'ani tanaji, bata lura ba kawai taji ankashe,ta d'aga kanta da sauri Hidaya ta gani a tsaye da Haulat, sai hararanta sukeyi bata ce musu komai ba tsayawa tayi tana kallonsu taga ikon Allah....

Hidaya tace toh 'yar matsiyata anzo ansamu wuri an zauna har ana wani cikama mutane kunnuwa ba dama mutum ya d'an zauna a cikin gidan mijin shi sai an dameshi mtsw, toh ai ke kikayi sake har kika bar gadangare yake sha miki ruwa a tulu, wlh da nice da tuni nayi waje da 'yar iska, kawai tazo tana takura miki kinzuba mata ido kina kallo, horo ya kamata ki rinka bata mai tsanani wlh da kanta zata tattara inata inata tabar miki gida, ki zauna daga ke sai mijinki cewar Haulat......

Hidaya ta dafa ta tace kinsan talaka be iya samun wuri ba k'awata, tazo tayi bake bake amma gaskiyarki ne wlh nice nayi sake, ta juya ta kalla Nasrin tace sai a tattara a koma gidan tsohuwa a cigaba da tallan d'anwake kamar yarda aka saba, Nasrin dake zaune da murmushi a fuskanta ta juya tana waige waige, Hidaya tace cikin ihu ba dake nakeyi ba, ta juyo ta kalleta, dawa kikeyi ne? Haushi ya kamata "dake nakeyi dan iyayenki, Nasrin ta d'aure fuska ba dariya a fuskarta, ta mik'e tsaye tana kallonta sama da k'asa, ta nuna ta da yatsa tace "idan kinayi dani kiyi dani amma karki sake kisa iyayenah a ciki dan sunfi kowa daraja a gurina, wlh kika k'ara anbato iyayenah a maganarki sai na zubar miki da hakoran gaban bakinki, dan ni nasan darajar iyayenah da kuma na gaba dani......

Haulat tace "lallai yarinyar nan har kina da bakin fad'a ma mutane wannan maganar ke 'yar gidan uban wage? Kafin ta k'arasa taji kyakkyawan mari a fuska, Nasrin ni kika Mara an mareki idan kina da abinda zakiyi kiyi in gani, kuma karki k'ara sa mun baki dan ba dake nakeyi ba da matar gida nakeyi.....

Hidaya tace lallai Nasrin wuyanki yayi kauri ya isa yanka har kin isa ki maran mu k'awatah? Wacece ke a gidan nan? Murmushi tayi nice nan matar Na'im wadda ya Aura ta sanadiyan k'addara, kuma yake sona tamkar ransa, ina so kusan wani abu, banta'ba bin boka ko mallam ba dan Na'im ya Aureni bah, iyaye sune sanadiyar Aurenah tsakanina da shi kuma yake alfahari da Aurenah kamar yadda nima banta'ba dana Sanin Aurensa ba, yanxun ne ma na fara son Auren Na'im wlh, ba kuma Wanda ya isa ya rabani dashi ko mutum ko aljan sai dai Allah domin Aurenah dashi *Had'i daga Allah* ne........

Hidaya ta daga hannu zata mareta ta rik'e hannu ta wanketa da Marika guda biyu masu rai da lafiya, ta tafi kamar zata fad'i Haulat ta rik'o ta da Sauri, ni kika mara? Wlh sai kinyi dana Sanin marina! Auren nan sai ya zama bala'i a wurinki, sai kinyi nadaman Auren Na'im....

Ku fitan min a d'aki idan ba haka ba wlh sai na illataku, banzaye 'yan iska wa'inda basusan darajar Aure ba, and for your own Information idan na k'ara ganin k'azamen k'afafuwanku a 'bangarena wlh sai na nuns muku wacece Nasrin, dan naga har yanxun bakusan niba, ku fitan min a d'aki shaid'anu kawai, da sauri suka fita, tayi tsaki ta koma ta zauna ta cigaba da jin karatunta....

Haulat ce da jaka a hannunta ta ke cewa k'awata wlh sai kinyi da gaske dan kishiyan nan taki watarana sai ta miki shegen duka, kisan abinda kikeyi wlh kinga yanxun kinsa ta daina kulata kuma kome kikace yayi zaiyi amma ni abinda ke ban haushi wai karkice ya saketa, kuma duk dalilin d'aya ne Auren su *Had'i daga Allah* ne, shine fa kawai dalilin, Hidaya tayi a jiyar zuciya tace dan Allah ki nemomin mafita mana, Haulat tace kawo kunenki kiji ta rad'a mata wani abu a kunne sukayi dariya suka tafa.........


*EDITED BY*
๐Ÿ’NUSNIM ( *TWIN SIS*)๐Ÿ’

*DEDICATED TO*
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam
Love you all๐Ÿ˜˜
[1/25, 7:58 AM] โ€ช+234 706 774 5996โ€ฌ: ๐Ÿ‘ซ *HA'DI DAGA ALLAH*๐Ÿ‘ซ

*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN

*146 - 150*
*************
โœ"Bayan Haulat ta tafi Hidaya ta zauna tana tunani a kan maganan da Haulat ta fad'a mata, tana nufin _Insa ma Nasrin maganin zubar da ciki a abincita_ toh tayaya hakan zai faru bata barin kitchen d'in sai ta gama dafa abincinta! Menene mafita zatayi anfani da Na'im ta samu abinda take so......

"A 'bangaren gidan su Na'im kuma mommy ne da Daddy a zaune suke tattaunawa, sai ga Na'ima ta shigo da twins d'inta suka ruga da gudu suka haye kan cinyan Daddy suna cewa oyoyo Grandpa cikin gwarancin maganan su, Mommy ne taja wo musu k'afa Ku saukan min karku 'balla min miji suna ta dariya, Mommy ta juya ta kalli Na'ima, wai in tambageki kuna waya da d'an uwan naki kuwa? Tace a'a rabona dashi tun randa muka rinka lallashin Shureim da yace bazai je India karatu ba, dan ko ranan dana kirashi ince mai yazo mu kaishi Airport Hidaya ce ta d'auka wai ya fita ya bar wayan, toh haryanxun ko na kira baya d'auka kuma be kirani ba! Na kira Nasrin nace mata zanzo cemin tayi tana school Na'im kuma na office, daman ni bama shiri da Hidaya shiyasa ma banje ba!

Daddy yayi ajiyar zuciya ni kaina ankawo min karar cewa baya zuwa office kullum kuma ko yazo baicika magana ba, Hidaya ke zuwa tayi komai na office d'in ta tafi, kuma ko na kirashi baya shiga, Mommy tace ba lafiya ba gaskiya, daman Daddyn yara sai da na fad'a maka kwata kwata hankalina bai kwanta da Auren nan ba! Ga yarinya da ciki kunsan tana wata bakwai yanxun, Allah kad'ai yasan wani hali take ciki a wannan gidan, kuma ko ankira antambaya sai tace komai lafiya, ni wlh banyarda da zaman su ba! Zanje ingani da idona, dan Allah ka mun uzuri inje in duba! Toh shikenan Ku shirya keda Na'ima sai kuje Allah ya kyauta, suka amsa suka tashi....

"Hidaya ne zaune take cema Na'im (da duk yayi bak'i ya rame kamar bashiba) ina son ka kira Nasrin ka mata magana ta taimaka ta koya min yadda ake kunun gyad'a tunda kana so sai in rink'a maka, ga ce toh kirata ta tashi ta fita tayi hanyar kitchen dan dama tasan yanxun tana kitchen, ta shiga da sallama Aunty Nasrin ina wuni ta juyo tana kallonta da alaman tambaya a fuskarta amma sai ta watsar ta amsa lafiya lau, kije Na'im ne ke kiranki, yana ina yana 'bangarena, ta ce toh!

Tana fita a kitchen d'in Hidaya da Sauri ta kwance gefen zaninta, ta ciro kullin maganin ta bud'e had'add'en jalouf d'in taliyan Hausa ne da yaji d'anyen kifi,sai da ta had'iye miyau amma da ta tuna abinda ya kawota tayi sauri ta zuba, ta gama ta rufe, ta kulle sauran maganin ta maida gefen zaninta....

Juyo Wanda zatayi Nasrin ne a tsaye ta hard'e hannayeta tana kallonta, jikinta ne ya fara rawa, tayi murmushi Hidaya kenan ta fincikota ta rink'a janta har saida suka kai fallo, sannan ta saketa lallai Hidaya angaya miki kowa jahili ne kamarki, duk wayanki wlh ni Nasrin na fiki, ke ga munafuka tunda kin assirce Na'im ya kama shi nima bari ki nuna min naki hatsabibanci koh? To bari kiji ni Allah na rik'e ba tsafi da tsubace tsubace ba, karkiga na bakki da Na'im kinata abinda kika ga dama bawai tsoron ki nakeji ba, ba kuma bani da mafita bane na barki da mallaminah ne yadda zaiji dad'in damkeki idan ya tashi wato Allahu (S.W.A), karkiyi tunanin kina cutar damu ne wlh kanki kike cuta bari in gaya miki kiji duk wayyan da kikayi da Mahaifiyarki da kike gaya mata shawaran da Haulat ta baki toh duk a kunnenah, najiki sarai, kinsan shi Allah ba azalimin bawansa bane, duk abinda zaki min wlh na rik'e Allah da mazonsa.....

"Hidaya ce ta harareta toh me zaki iyayi, Na'im ya riga ya zama nawa ba Wanda ya isa ya rabani dashi, sai ni nan sukaji ana fad'a, Mommy ce ke fad'in haka ga Na'ima a bayanta, ta wanke Hidaya da lafiyayyen mari, dama sai da na fad'a ma Na'im bana son Auren nan Amma naga ya dage sai yayi, ni nasan baki barshi haka ba wlh, sannan kuma yanxun jikan nawa da za'a haifo min daga tsatsa mai kyau zaki kashe min?

Lallai Hidaya kin tabbatar min da ke mahaukaciyya ce, ta juya ta kalli Nasrin wadda idan ba ka lura da kyau ba bazaka gane tana da ciki ba, dan cikinta 'boyayyene, ina Na'im ta ce yana sama mommy, ta haura saman da sauri, ta shiga ko ina kazanta kamar ba mutum ke zama ba gashi yayi bak'i ya rame, yana zaune a k'asa, mommy ta dafa shi yana d'ago kai ya kalli mommy, tace Na'im me ke damunka ne ka koma haka, da kyar ya bud'e baki yana cewa nima bansani ba! ya fara kuka ya k'ank'ame mommy, itama sai hawaye, ta goge mai hawayen, tace ina ka ajiye kadarorinka da suke nan gidan yace yana hannun Hidaya...

Da sauri mommy ta shiga bedroom d'in tana dubawa, can kamar ance mata ta duba k'asan gado ta gansu a jakarsu ta d'auko ta fito, ta rik'e mai hannu suka sauko tace ma Nasrin d'auko duk wani Abu da zaki buk'ata ki rufe 'bangarenki kizo mu tafi, Na'ima rakata Ku sameni a waje, Hidaya na gefe duk tayi wani irin ta zazzaro idanuwa, suka d'auko suka bi gefenta suka wuce tana ganin sun fita ta d'auko mayafinta ta shige mota ta kira Haulat su had'u a kan titin Sultan road yanxun nan ta kashe wayar.....

Sun had'u ta gaya mata komai da ya faru sai cewa tayi Nasrin d'in nan ta zama mana ciwon ido wlh, zama be ganmu ba muje mu sami boka muyi mai bayanin komai daya faru, suka kama hanyar wurin bokan su...


*EDITED BY*
๐Ÿ’NUSNIM ( *TWIN SIS*)๐Ÿ’


*DEDICATED TO*
Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam
Love you all๐Ÿ˜˜
[1/25, 7:58 AM] โ€ช+234 706 774 5996โ€ฌ: ๐Ÿ‘ซ *HA'DI DAGA ALLAH*๐Ÿ‘ซ

*WRITTEN BY*
KHADIJA AL'EEMAN


*156 - 160*
*************
โœ"K'arfe hud'u na yamma kenan amma haryanxun mallam shiru be dawo ba, Alhaji Tofiq adu'a kawai yakeyi Allah yasa ba wani abu bane ya faru domin ko number shi ya kira baya shiga, gashi jikin Nasrin yayi tsanani sossai, na dai Na'im ne Alhamdulillah yana jin sauki.....

"A 'bangaren Hidaya kuwa tun bayan dawowan su daga wurin boka tsula tsiyarta kawai takeyi, ta kawo waccan namijin ta kawo wannan, amma sai dai ta farayin wani mugun mafarki, sai taga ana binta za'a kasheta, ko kuma a dinga ja mata kunne ta je ta cire abinda ta birne Wanda ta sanadiyar shine Na'im ya aureta dan a duniya ba wadda ya tsana ada irrinta amma tunda taje nijar wurin wani bokanta ya bata wannan abin ta birne shikenan......

Yauma tana zaune abin duniya ya dameta saboda ko a zaune take sai taji ana k'ara ja mata kunne, amma na yau yafi don har ta'bata taji anayi, sai tsorata tah akeyi! Ba Arziki ta tashi ta d'auko mayafi ta kama hanya ta fita, ko mata baza ta iya tuk'awa ba mai a daidaita ta samu ta hau, tayi mai kwatancen wurin, sai fad'a sukeyi da shi, dan ta dameshi da yayi sauri, shi kuma gani yakeyi India baso takeyi ya tashi sama ba to iya gudu kam yanayin shi, da ya gaji da ihunta ya sauketa yace mata kuma tunda sunyi rabi sai ta bada kud'in rabin idan ba haka ba wlh zai tara mata jama'a, ta dinga masifa tana cewa da gatanta da ta hau wannan shegen adaidaitan zai wulak'antata, suna cikin haka sai ga k'awarta mai suna Rashida .m. Zarma ta kalleta wanake gani kamar Hidaya? Nice Rashida Ya kwana biyu? Lafiya lau, ya naga kunata sa'insa da mai adaidaita lafiya? Wlh cewa nayi ya kaini wani waje shine ya ajiyeni a nan kuma sai na biyashi ko ya tara min jama'a, Rashida tayi murmushi kinga irin rayuwar da nake jiye miki koh! "Hidaya ina baki shawara ta gari bakya d'auka ina gamawa sai Haulat ta hure miki kunne ke kuma a bi yarima a sha kid'a, shed'an yayi zigi sai ki bita duk inda tayi, wlh Hidaya alhakin Na'im da Nasrin ne ya fara kamaki tun a duniya ma kenan, kina da gata da komai amma mai adaidaita ya rinka Neman tozartaki yana ci miki mutunci wlh idan baki daina abubuwan da kikeyi ba kin koma ga Allah kinje kin rok'esu yafiya sun yafe miki ba wlh a duniya baki ga komai ba, yanxun kika fara fuskantar matsalili wlh, ni shawara na baki kafin babbar k'awarki tazo ta hure miki kunne, tace "nagode sissai Rashida zanyi anfani da shawaranki In shaa Allah, Allah yasa Hidaya tace ameen, toh yanxun ki bashi kud'insa kizo muje mu rage miki hanya nida babynah neh! Tayi murmushi karki damu zan hau wani adaidatan nagode da kulawarki, toh shikenan sai anjima, ta wuce ita kuma ta biyashi ta hau wani mai adaidata d'in......

*6:45 pm*
Exactly time a agogon Nigeria, kuma adaidai lokacin ne mallam yayi sallama a fallon Alhaji Haris Saif, kowa sai farin ciki a fuskarsa aka tareshi cikin mutunci da jin dad'i, a lokacin kuma ake kiran sallah yace Ku tashi mu gabatar da Sallah tukunna daga nan sai muyi abinda yadace muyi, suka mik'e gaba d'ayansu sukayi alwala akayi sallah.....

Bayan sunci abinci sun natsu mallam ke basu labarin wahalar da yasha a hanya, Yace "Alhaji wannan matsafin ba k'aramin matsafi bane, bina ya rink'ayi yana son ya kashe da Allah ya taimakeni inayin azkhar sossai daya ga ba sarki sai Allah ya gaji sai ya tafi ya barni, Alhaji Tofiq yace "Allah ya k'ara tsarewa ya kuma kiyaye dukansu suka amsa da ameen, ya d'auko magani ya basu yace a rink'a yi mata hayak'i ana samata a ruwan wanka da ikon Allah zata warke ko me akayi mata ya umurcesu da su fito da ita .....

Bayan anfito da ita, ya bud'e maganin da ya d'ebo ya had'a da garin habbatus sauda, yace akawo mishi garwashi ya zuba nan da nan ta fara gurnani shi kanshi Na'im dayake kwance a kan kujera wani irin atishawa yakeyi ma Wuyan fassaruwa, sai aljani da ke jikin Nasrin ya fara magana _cewan

9 / 10