Advertisements
Chapter 3 Reading HA'DI DAGA ALLAH Kaddarar So by Khadijah Al'Eeman BookTok Hausa Novels
Advertisements

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

HA'DI DAGA ALLAH Kaddarar So by Khadijah Al'Eeman

Author :  Khadijah Al'Eeman Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 10

6K to 9K   out of 29.9K words

Nasrin mai aikin abinci?,.....

Daddy yace ita,idon shi ya kad'a yayi ja sossai, yace "haba dan Allah a rasa wadda za'a had'a ni aure da ita sai 'yar aiki, 'yar talakawa, meyasa baza'a samu yarinyan mai kud'i a had'a ni da ita ba?, sai 'yar matsiyata haba dan Allah.......

Mommy ta ce koma yar mecece aikin gama ya gama, auren ne ba fashi, in kaga dama ka mutu, aure ne kamar anyi an gama, ya tashi zai fita, Daddy yace kafara shiri nan da two weeks zaka zama ango, ya juya ya fita ya nufi sasan shi, tunda ya zauna ba abinda kemai yawo akai, sai maganganun mommy da Daddy, yace "wallahi indai yarinyar nan ta yarda ta aureni sai ta gudu da 'kafanta, sai ta zama baiwa a gareni, daga haka wani wahalallen bacci mai cike da matsanan cin ciwon kai ya d'aukeshi.....

A 'bangaren gidan su Nasrin kuwa Ummah ta fad'a ma ta, hankalinta yayi mummunan tashi, Umma ta kira sunan ta tace "bawai na yarda da Auren bane saboda kud'insu ba, ban kuma amince ba saboda zaki aura mai kud'i ba, na yarda ne saboda hujojjin da Hajiya ta kawo min, Nasrin wannan Auren zakiyi shine saboda jahadi", kuma karki manta kina da lada har a wajen Allah, Nasrin ban yarda ko yaji kiyi ba bare kuma in ganki da takardan saki, ina son kimai biyayya yadda ya kamata, ki koya mai d'abi'a mai kyau, yanda zai rinka son mutane ya dinga tausayin talakawa, Nasrin na tabbata watarana zakizo kina murna kina dariya, kuma zakiji dad'in aurenki In shaa Allah, sanan karki yarda Hajiya ko Alhaji suyi kuka dake, domin sun yarda dakene sun kuma yarda da tarbiyanki, ina so kiba ma ma'kiyanki kunya, Dan Allah Nasrin......

Nasrin ta goge hawayenta tace ba komai, Ummah In shaa Allah sai kinyi alfahari dani, kuma na fahimce ki, na kuma ji dad'i sossai da Allah ya bani ke a matsayin mahaifiya, tayi murmushi tace Allah ya miki Albarka, Allah ya baki yara na gari, kuma Hajiya tace ki daina zuwa aiki, sannan zata turo mai gyaran jiki anjima, d'azun nima ta kirani take shaida min, tace Ummah Allah ya kaimu, tace ameen....

Yau aka kawo kayan sa rana, tare da akwatina set biyu, komai an saka a ciki sai kuma wani akwati daban shi kuma kayan event ne a Viki, tare da Invitation card na d'aurin auren dana event a ciki, kowanne an rubuta na randa zatasa, za'ayi kamar su "kamu (Indian Night), Dinner, arabian Night sai kuma walima" duk wanan aikin mommy ne da Na'ima su sukaje Dubai, suka had'o su, tare da furnitures da kayan kitchen da za'a zuba ma Nasrin a d'aki don sunce kar a kai mata komai, duk zasuyi.....

A 'bangaren Na'im ko hankalin shi duk a tashe ne, ko a bokanan sa sai dai Ahmad da Lukman suka kai musu kati, kullum yana d'aki, Na'ima ce ta shigo tace haba Yayanah wlh sands Mommy ta kirani take fad'a min murna nayi sossa, domin ko ba komai nasan halin Nasrin, wallahi kayi dacen mata, ya kalleta yace shiyasa kika je Dubai siyo mata kaya koh, saboda bakya sona yanxun kema koh, tace ba haka bane ana maka gata ne amma bazaka Sani ba sai nan gaba....

Suna a haka Mommy ta shigo ta mika mai kaya tace yau da karfe shida za a fara Kamu (Indian night), su zaka sa, yace ni ba'inda zani, Mommy tace dole kaje kuma ka kuskura ka nuna ma mutane halin da ake ciki sai na 'bata maka rai wallahi, ta juya ta fita.......

Na'ima tace daurewa zakayi dan Allah Yaya, yace ba komai Na'ima, zanyi kokari inga nayi yadda take so tace yauwa, toh yanxun ka fito Ku gaggaisa da mutane, yace toh muje, haka nan yake daurewa yana dariyan 'karfin hali, amma zuciyan shi ba'kin'kirin take........

Itako bangaren Inna Aisha tana ta tsuma Nasrin, ji'ka wancan, sarki da wancan, wanka da wancan, ga gyaran jikin da ake mata, sai tayi bala'in kyau, kamar ba ita ba, 'kawayenta na School sunzo sai tsiya suke mata.........

Karfe shida naga kowa ya halarci Seventeen hotel, can na hango Ali jita a gefe yana jiran isowar ango da amarya, su bilkisu Ja'e da Aneelurv na hango a gaba gaba nace toh fa Lol......

Amarya da Ango na hango a tare sun shigo nace Ohmg wannan daga gani aikin Na'ima ne dan nasan halin Na'im sarai, Nasrin kuwa kanta a duke, shiko yana ta murmushi, hango mutanen da yayi ne yasa ya kamo hannun Nasrin ya rike, ita dai nata Ido, nan fa Ali jita ya fara wasa amarya da ango, can na hango tawagar gidan "Deejah's Kitchen" nata taka rawa nace lallai ma kowa ya gayyace su oho LolπŸ˜‚.....

*EDITED BY*
πŸ’NUSNIM ( *TWIN SIS*)πŸ’

πŸ“ *DEDICATED TO*πŸ“
Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you all😘
[1/25, 7:57 AM] β€ͺ+234 706 774 5996‬: πŸ‘« *HA'DI DAGA ALLAH*πŸ‘«

*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN

*31-35*
***********
Assalamu Allaikum
Masoyana ina mika godiya ta a gareku, na bada kulawa da kukeyi a gareni, na rashin lafiyan danakeyi, da wa'inda suka kirani da wa'inda suka min adu'a, nagode sossai Allah ya saka muku da aljannah, Allahumma AmeenπŸ‘

✍🏻 Rana bata karya sai dai uwar d'iya ta ji kinya, a yau ne d'inbin Al'umma suka shaida d'aurin auren *Na'im Alhaji Haris Saif da Nasrin 'Kasim* wanda aka d'aura a masallacin dake unguwan sarki wato Sultan bello, d'aurin aure ne daya tara manyan masu kud'i, yan jaridu, sarakai da sauran su, 'kanin mahifin Nasrin wato mallam shu'aibu shine waliyin Nasrin a inda gwamnan jahar Kaduna shine waliyin Na'im a kan sadaki naira dubu d'ari biyar.....

Anata d'aukan hoto da Na'im Wanda shikad'ai yasan abinda ke damun sa, amma a fili ya'ke kawai yakeyi, mahaifinsa yaji dad'in yadda ya sake, yana kuma rokon Allah yasa ya zarce a haka.....

A 'bangaren Nasrin kuwa jikinta ya mutu ta koma gefe d'aya ta zauna, tana tunanin ko wani irin zama zasuyi da Na'im oho, amma tasa ma ranta duk zaman daya ce suyi shi zasuyi, Ummantah ne ta dafa ta tace lafiya kuwa?, tayi murmushi tace ba komai Ummah, tayi murmishi tace Nasrin ai kindai ji fad'an da nayi miki kuma da fatan kin d'auka tace "In sha Allah" Umma, sai ga Inna Aisha da 'kanwar mahaifiyanta Aunty Amina sun shigo suna cewa ina amarya ta fito, nan Ummah ta kama ganin Nasrin tace Allah yayi miki albarka, Allah yasa ki gama da duniya lafiya, suka amsa da "ameen", ta mika ma Inna Aisha ita, nan fa Nasrin ta fara kuka tana turjiya da kyar a ka samu ta tafi aka kaita gidan kakaninta na wurin Uwa sukayi mata fad'a, aka kaita gidan 'kanen babanta tunda kakaninta na wurin baba sun rasu, Mallam barde da Mallam Shu'aibu sukayi mata nasiha, matayensu ma suka mata, a gidan Mallam Shuaibu aka barta har aka kawo motoci, suka kama hanyan gidan su Na'im da ke low cost, anje ankaita wurin Mommy ankuma bata amanarta ta amsa kuma tayi godiya.....

Aka kaita wani d'aki a gidan ita da 'kawayenta,kafin time d'in Arabian night yayi.....

A 'bangaren ango kuwa ya nuna kamar ba abinda ke damun shi, har su Ahmad na mamakinsa, amma kuma sun ayyanah a ransu akwai abinda ya shirya, amma koma menene Allah yasa alkhairi ne.....

'Karfe hud'u aka shirya arebian Night, Na'ima bata a 'bangaren ango bata a 'bangaren amarya, sai da taga komai ya tafi daidai, sanan hakalinta ya kwanta.....

Anyi arebian night lafiya, kowa yaci yasha, anyi hamdala, can na hango su *Fatima Malunfashi, Aneelurv, Stylish, Autar Hajiya, Fiddo Sodangi,JJ, Real Amani, Amra, Nafee Anka, sunci sun sha sunata selfie LolπŸ˜›.......

Antashi lafiya kowa yana ta sa albarka, anfara shirin kai amarya, Matar Alhaji Tofiq ne Ta kama hanun Nasrin, ta kaita wurin daddy da Alhaji Tofiq, aka kira Na'im shima yaje, Mommy ta shiga itama, aka musu nasiha sossai, Mommy tace Na'im ba saki a tsakanin ka da Nasrin, ba duka, duk randa ka d'aga hannu ka duketa ban yafe maka ba, ya d'aga kai da sauri ya kalleta, Hajiya Hawwa matan Alhaji Tofiq tace haba Hajiya, don Allah ki janye wanan kudirin naki, tace a'a Hawwa nasan halin Na'im, gwara in mishi gargad'i tun yanxun, tace Allah yasa mu dace, Allah yayi muku Albarka, Hajiya hawwa ta maida Narin d'akin shi kuma ya tafi wurin abokanansa, a ka fara shirin dinner......

Happy Sallah to you all, may Allah continue to guide and protect Muslim Ummah Ameen... Takabalallahu minna wa minkum

*EDITED BY*
πŸ’NUSNIM ( *TWIN SIS*)πŸ’

πŸ“ *DEDICATED TO*πŸ“
Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam
Love you all😘
[1/25, 7:57 AM] β€ͺ+234 706 774 5996‬: πŸ‘« *HA'DI DAGA ALLAH*πŸ‘«

*WRITTEN BY*
KHADIJAH AL'EEMAN

*36 - 40*
***********
✍🏻Anje wurin dinner, nan ma anci ansha, kowa ya sha kaya white, can na hango 'yan Party, Fatima Malunfashi, BLG,Anee, stylish, Autar Hajiya sai shugaba kwatakwata Nafee Anka, ansha white gowns anata kai naman kaza baki LolπŸ˜‚.....

Akace Ango zai ciyar da Amaryarsa, haka ma Amarya zata ciyar da Angonta, Na'ima suka had'a ido da Na'im, ta nuna mai hannu alaman yayi yadda akeso, ya kad'a mata kai alamar bazai iyaba, ta kara rokonsa, ganin kar ya nuna ma mutane halin da ake ciki ya kama hanun ta suka yanka cake d'in, ya ciro yasa a bakinsa ya kamo ha'barta ya kai bakin shi kan nata, yasa mata cake d'in a bakinta yayi fuska abinsa, ita ko Nasrin kamar 'kasa ya tsage ta shiga don kunya, mutane kuwa sai shewa sukeyi suna ihu, aka ce saura Amarya ta rasa yarda zatayi tasa hannu ta d'auka ta kaimai baki ya bud'e ya amsa, wuri ya kaure da tafi, Na'ima tace ma Ahmad wallahi Yaya d'an duniya ne
, ji shi kamar bashiba, Ahmad yace ke dai bari wallahi ni kaina mamaki yake bani, Allah yasa a d'aure a haka tace "ameen Hubby".........

Daga nan aka wuce da Amarya gidanta da ke malali kan titin Isa Kaita, gidan ya had'u sossai, a 'kasan akwai d'akuna hud'u ko wanne da toilet da bathroom a ciki, sai kitchen katon gaske a cikinsa akwai store komai da komai akwai, colour d'in Fallon blue and golden.....

Sai in ka haura sama, saman 'bangare biyu ne d'ayan komai nasa white ne dayan kuma Orange and lemon green, wanan kad'ai ya isa mutum ya banbance 'bangaren Na'im da Nasrin, in ka shiga falonta akwai d'akuna guda uku kowanne an 'kaya tashi da kayan alfarma, daya colour d'insa pink ne, d'ayan kuma peach colour ne, na ukun kuma lemon green ne........

'Bangaren Na'im kuwa shima three bedroom ne, d'aya white and orange ne, na biyun white and peach, na ukun kuwa white and pink ne......

Gida kam ya had'u sai Sam barka, kowa ya musu fatan Alkhairi, an tafi an bar Nasrin da Na'ima kawai a gidan, bayan sun kimtsa Na'ima tasa Nasrin ta 'kara yin wanka, tayi kwaliya tasha gown d'inta white and orange........

Na'ima ta kama hanunta suka zauna, tace Anty Nasrin kinga yanxun kin zama matar aure,Ina son duk wani tsoron Yaya Na'im ki ajiyeshi a gefe, ki fuskanci auren kai tsaye, nasan kin fi kowa sanin halin Yaya Na'im daga 'bangaren good sight d'insa da kuma bad sight d'insa, yanxun ya'ki zakiyi ba d'an karami ba, canja Na'im Anty Nasrin ba abu bane mai wahala, sai kinyi hakuri, kin kuma daure, na yarda dake na kuma yarda da tarbiyanki, kiyi abinda dangin mijinki zasu 'kara sonki za kuma suyi alfahari dake......

Aunty Nasrin ina nan duk wani abinda zai shige miki duhu ki gaya minshi, ina son in zama abokiyar shawaranki, bana so ki rinka fad'a ma kowa sirrinki ki zama mai 'boye sirrin gidanki, Allah yama Auren nan naku albarka tace "ameen".....

A daidai lokacin sukaji an bud'e kofa, Na'im ne ya shigo da sallama suka amsa, yace Ku fito fallo, ya juya ya fita, suka rufa mai baya........

Sunje fallon sun sami Lukman, Ahmad sai Na'im, suka nemi wuri suka zauna, a nan Lukman yayi musu nasiha mai ratsa jiki, sukayi adu'a suka kama hanya Na'im ya raka su, itako Nasrin ta rike Na'ima tana cewa karki tafi dan Allah ki kwana a nan.....

Tace Aunty Nasrin gobe zan dawo In shaa Allah, tace "to ina jiranki" ta juya ta tafi, Na'im ya dawo ya taradda bata a wurin ya d'auka ledar dasu Lukman suka sa ya siya, ya haura sama ya shiga 'bangaren ta, bata fallo ya shiga d'akinta, ya sameta a zaune ya wurga mata ledar a fuska, yace gashi nan mayya nasan abinda kika zo ci kenan, kin matsa dole sai kin aure ni toh wallahi sai kin gwammaci zama a gidan Ku akan wanan auren da kika yarda aka yishi, wawiya kwai, mtsw banza ya juya ya fita, ita ko bata ce mai komai ba har ya fita......

*EDITED BY*
πŸ’ *NUSNIM ( *TWIN SIS*)πŸ’

*41 - 50*
***********
✍🏻Nasrin tayi murmushi tace duk abinda ka min zan jure Na'im, amma wallahi sai ka durkusa kana rokona in soka, kuma wallahi zama a cikin gidan nan yanxun na fara, har sai na cika wa iyayenka

3 / 10