Advertisements
Chapter 24 Reading Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   24 / 48

69K to 72K   out of 143.8K words

zo ba,shi ya sa na yanke shawarar na je gurin wannan Wan mara mutuncin komai zai tafi daidai."

Tsaki A.m ya yi ya ce da shi." Ai ko in ka ?ara gangancin zuwa ?ofar gidan nan ni ne ajalin ka,don na tsane ka tsana mai tsanani mugu kawai wanda ya kasa ri?e ?aran wan sa."
A.k ya kalli Baba Sani ya ce." To wai tsaya don Allah mene ne ba mu yi maka ba,za ka zo ka dami rayuwar mu?Kuma na gaya maka zan zo har gida aiki ne ya yi min yawa kai kuma mara ha?uri."

"Oho koma me zaku ce kuce amma ni ba ruwana gara ku tsaya ku ji mai yake tafe da ni ba wai ku tsaya SaSatu ba."

Ya ce ya na girgiza jikin shi har da ?ar wa?ar shi irin na cikakkun ?an bariki.

A.m ya watsa mishi mugun kallo ya na jin wani irin tsanar shi mai tsanani ta na zagaye duk ilahirin jikin sa ya ce.

" Ko ma me ya kawo ka ka Sace min a ?ofar gidana ko na kira ?an sadda su tafi da kai."

"Sojoji za ka kira ba ?an sanda ba kuma abin kunya a gare ka take,ka kulle surukin ka don ko banza na gama da kai tun da ?ar wana kake aure shi ya sha nono ya saki na kama."

Ya ba A.m amsa jin abin da ya faWa babu ko Wigon damuwa a zuciyar sa.
A.m ya yi ?uta ya ce." Allah ya tsare ni na haWa zuriya da kai dangin matsiyata,ai ko ba mata a duniya gara na zauna ban yi aure ba da na auri zuriyar ka jinin matsiyata dangin talauci."

Ya faWa cikin Sacin rai ya na jin kamar ya sha?o shi ya gama masa aiki,don ya ?ara masa ba?in cikin da ke cikin zuciyar sa.

" Ok to haka kace ko Wan ?aruna to sako min ?ar Wan'uwana wacce kuka yi auren kwangila da ita,dama na zo na tuna maka da yau saura wata biyu da kwana shirin da takwas da yini Waya,amma fa ban da kwana auren kwangila ya ?are ma'ana kuWin ka sun ?are shekara Waya ka iba,kuma waWannan watanni biyu da kwanaki suka rage sai a shirya sako min ?ata,don Juwairiya ba ta da uban da ya fini."

A tare suka buWe baki tsananin mamaki ya kama su ko kaWan ba su taSa tunanin haka zai faru ba,lallai Baba Sani ya cika tantiri Wan duniya ne wanda ya zama lamba Waya.

A.m cikin fushi ya taso kan sa ya na faWin." Baka da hankali matar ta wa kake maganar kwanakin rabuwarmu,kai za ka sake ta ni nake da ikon sakinta,kuma babu Wan iskan da ya isa ya sakin min mata.

Ya numfasa ya na jin wani irin tashin hankali da mamakin sa ya ci gaba da ce wa."Kuma da kake maganar haka auren ta na yi don ta haifa min yaro,ammma ko Satan wata ba ta taSa yi ba shi ne har za ka zo ka ce wa'adi ya cika?To na ga uban da ya isa ya sakin min mata."

" Allah ko Wan zamani hauka kake yi ka yi abu da ?uruciya ni kuma zan nuna maka da wanda ya riga ka shan iskar duniya,ya girme ka ko da da sakan ne.Bari kaji lokacin da ka zo nai man auren Juwairiya na bi dindigi na gane kai ko Wan waye da duk wani labarin ka,har da asalin matarka da komai na ta na sani zan iya zuwa gurin aikin ta na kai mata recording Win da na yi,lokacin da ka zo neman auren Juwairiya har ma da na Waurin auren ku."

Sai suka zare ido jikin A.m ya yi sanyi matu?a har ya kasa magana don ya cika tantiri na gaske!

Ganin yadda maganar sa ta razana su sai ya yi dariya ya ciro wayar sa ya kunna recording Win suna ji,babu wanda ya iya ko tari a cikin su sai tsantsar razana da A.m ya ji musamman a ce ya kai ma Daddy kamar yadda ya yi ninya.

A.k ya gyara tsayuwar sa ya na jin wani wani irin tashin hankali ya na ziyartar sa,wani irin gumi yake ji?a shi don ko kaWan bai yi tunanin Baba Sani ya na da wannan wayon ba,lallai sun yi boko mai zurfi amma shi ya nuna musu aiki da shi.

" To kun shirya saurara ta ko na tafi don ni ba na son Sata lokaci."
A.m shiru ya yi ya Wauke kan sa ji yake kamar ya fisgo shi ya dan?ara wayar da ?asa.

A.k ya kalli A.m da ya kasa ce wa komai ya ce da shi." Ka shirya zama da Juwairiya a matsayin yadda ko wace mace take a gidan aurenta ko har yanzu ka na kan bakan ka ku...?"

" Allah ya kyauta na zauna na har abada da gaiyar tsiya ai in wannan mara mutuncin ya na raye ba zan taSa haWa zuriya da su ba,kuma mai zan yi da gayyar matsiyata ba na son Juwairiya yaro nake son ta haifa min na saketa,sannan ba zan yi asarar kuWina ba dole sai ta haifa min baby,wallahi ko dashe ne sai am mata don ba zan yi asarar kuWina ba."

A.m ya katse A.k da yake magana cikin zafi da kakkausar murya mai hargowa.
" KuWin ka ne zai tafi a banza ka maida matsiyata masu kuWi,dama ta hanyar wani Allah yake azurtawa Wan ?aruna,yanzu sai ka ?aro kuWi na shekarar ne ko shekara biyu,amma fa ka sani ba zan yadda Juwairiya ta zauna a cikin wannan daular ba,don haka sai ka shirya kawai ka je a farke mahaifarta ayi mata da she ta haihu kowa ma ya huta."

Ya ce ya na kallon A.m da jikin sa ya yi sanyi don yanzu yake nadama ashe tunanin halin sa ya wuce wannan.

Sannan ya Wora da ce wa "Mahaifiyar Juwairiya ta taso ni kan sauran lokacin da ya rage Juwairiya ta dawo aure za ta yi mata,sosai ta yi min bore har ta na barazanar kai ni kutu ?ila tare za a kai mu ko kuma ka ba ni kuWin da zan san yadda zan yi na kawar da idanunta kafin wa'adin ya cika."

Har zuwa lokacin shiru suka yi suna kallon juna da mamakon sa.

"A.m ka na jin abin da ya faWa na fara shakku an ya mutum ne shi ko aljani? Allah ba shi da imani karfa ya zo ya ruguza komai,zan ji kunya sosai domin ni Daddy zai fi ba ma laifi don ban kasance aboki na ?warai ba."

A.k ya ce ran shi a Sace ganin abin da suka yi cikin sirri ya na son ya fasu.

" Kyale matsiyaci ka ba shi kuWi kawai don ba zan iya sakin Juwairiya ba matu?ar ba ta haifa min yaro ba,don ina son jinina ya fito ta tsatson ta tabbas ubanta mutumim kirki ne don ya ba ?ar sa tarbiya na ?warai,amma na san kai yaranka sai dai su Wauki halin dabbobi don ba su yi dacen uba na ?warai ba."

Dariyar jin daWi ya saki ganin ya ci galaba a kan sa ya ce." Allah ya sa karuwai za ka kira su ni na san halin su,kuma na san irin tarbiyar da na basu in dai kawai na ji bayani wato kuWi abokan harka.In baka accourt numba ne ko cash za a bani."

Takaici ya hana A.m magana sai A.k ne ya kalli A.m ya dafa kafaWar sa ya na faWin "Ka koma ciki kawai zan ji da shi."

Kamar ?aramin yaro ya juya ya shiga ciki da ?yar yake Waga ?afafun sa ya na shiga falo ya zauna shaSar, ya na jin wani ?unci a ran sa abu ya haWu ya tarun masa goma da ashirin.

Juwairiya ta fito daga kicin jin shigowar sa wanda ta Wan ji hayaniya sama-sama,amma ba ta sheda abin da yake faruwa ba,asalima komawa kicin ta yi ta ci gaba da aikin ta don babu kyau laSe.

Hannu ya mi?a mata ta iso gare shi janyo ta ya yi ta faWa ?irjin shi tare da matse ta da ?arfi har sai da ta yi ?ara ya ce." Juwairiya ina cikin damuwa sosai abu ya yi min yawa.Zainab ba ta son farin cikina wai dama haka ne abin da kake so shi yake wahalar da kai?Tana amfani da son da nake mata ta na azabtar da zuciyata,ga Baba Sani ya zo ya ?ara min zafi."

" Baba Sani ya zo gidan nan na shiga uku."

Ta ce tare da zare jikinta daga gare shi ta zare idanunta don ta san zuwan shi ba alkhairi ba ne.

Kan sa ya Waga masa ya ri?e hannunta sosai." Yanzu ta tafi."Ya kwashe duk yadda suka yi ya gaya mata cikin rauni yake maganar.


Juwairiya ta yi shiru ta na kallon sa sai ya ba ta tausayi sosai juya mishi baya ta yi da nufin ta ce mishi ya bayyana auren su kawai,don ta gama kamar ya fara son ta da irin kashe ta da shaukin kala-kala da yake yi,amma sai ta ji muryar sa ya na faWin.

"Juwairiya don kawai ina kwaWayin na ga ?waina a duniya kuma ke ce mace ta biyu bayan Zainab da na ji zan iya rayuwar auren wucin gadi da ita,da ace zan iya zama da wata ba yan ke da zan rabu dake ne kawai saboda tantirin ?anin mahaifin ki sam ba shi da mutunci,sai dai kamar yadda ba zan iya rabuwa da Zainab ba domin an halicci zuciyata don ita haka ba zan iya rayuwar auren wucin gadi da wata mace ba in ba ke ba."

Tasowa ya yi ya rungume ta ta baya kamar yadada Juwairiya take hawayen jin ya na faWin zai iya rabuwa da ita hak shi ma ya fara hawayen rashin Wa.

Juyo da ita ya yi suka fuskanci juna dukkannin su hawaye na zuba fuskar su ya ce."Kin san na yi miki ?o?ari Juwairaah don Allah ko da nine ba na haihuwa ki yadda na zuba kuWaWena ayi miki dashen mahaifa kin ga Zainab ita an yanke mata mahaifar."

Da yadda yake magana ya ba ta matu?ar tausayi sosai ta ?ara sautin kukan ta ta na ganin an ya ta yi masa halacci kuwa,duba ga irin abin da ya yi mata kuma sai da ta yi masa al?awari karo na farko ta ji ba ta kyauta masa ba,don har ciki ta zubar wanda bayan ta sha lemun tsamin,amma har wata biyu bai zoba sai da zai zo ta ji ciwo sosai,sai dai shima bai yi ma zuciyarta adalci ba saboda ta na son shi ko idanunta ya isa ya isar mishi da tsa?on hakan,amma ya yi biris da ita ko tunanin shi bai gane son shi take ba."

A tare suka fara tafiya kowannen su ya shige Waki domin samawa junan su maslaha daga halin ?uncin da suke ciki.

A.k da Baba Sani ya sasha fama kafin Baba Sani ya amince ya karSi kuWin da ya ba shi,amma ya rantse in har lokaci ya ?are zai zo ya ?ara karSar wani kuWi,kuma A.m ya sa a ran shi dole ya saki Juwairiya ko da ba ya so.

A.k ya yi shiru kawai ya na kallon sa har ya gama zuba mishi rashin mutunci ya tafi,a ran sa takaicin A.m yake yi sosai don shi ya jawo musi wannnan tashin hankalin,haba!A ce kana auren mace wani yazo ya yi maka iko da ita sai ka ce ya na zaman dadiro.

Ai dama duk abin da aka yi tare da son zuciya a kwai nadama a cikin sa dole mutum ya yi nadama, yanzu in da duniya ta san matar sa ne har wani banza ya zo ya maida su A.t.m Win sa,to koma mene ne ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ka doka.


Sati biyu da Zainab ba ta nan Juwairiya ta yi amfani da damar ta koya mishi wani kalar kulawarta,wanda shi kan shi mamakin ta yake don yanzu ta cire kunya ta na son ta saka mishi soyayyarta a ciki zuciyar shi,don haka duk abin da ta san zai faranta mishi rai kuma matar sa ta kasa da shi Juwairiya ta cika gurbin sa,shi kan sa mamakin yadda ya saki da ita yake yi.


Sai dai ya kan tuna Juwairiya ba macen da namiji zai iya wula?antawa ba ne ko da kuwa ba ya son ta,don Allah ya yi mata abubuwa da dama ga tsananin kula da ibada sosai,sam ba ta wasa da ibada wanda hakan ya na matu?ar ?ara masa ?imarta a idanun sa.

In ka gan su a gidan zaka Wauka wasu masoya ne ko da yake ya sha gaya mata shi kan sa bai san ya aikai ya sake da ita da yawa ba,amma kawai su rayu tamkar ma'auratan da suka yi auren soyayaya domin ya na jin zai iya mata komai a zaman su in dai zai faranta mata.

A.m ya kai da komai ba ya iya yi sai dai ta yi masa hatta abinci a baki take ba, gabaki Waya ya shagwabe ya koma kamar wani ?aramin yaro ya na fatan ina ma ace Zainab Win shi take da wannan hali na kula da shi lailai da ya more.

Juwairiya ta dage sosai ta saka wata irin sha?uwa a zuciyar A.m ba tare da ya san haka ba,shi ya na danganta hakan da irin kular da take ba shi shi ya sa in ya ji kewarta sai ya Wauka jikinta da yake matu?ar so yake sa shi jin kewarta.

Amma take zai nemi waya ya kirata su shi hira sosai,ya kuma Sata lokacin sa ya na waya da ita.

Duk irin kular da take ba shi ta mai da kanta tamkar baiwa a gare shi ta na jiran ta ji ranar da zai rungumeta ya ce mata ina son ki!


Amma bai taSa faWin haka ba sai kalaman da suke sakata kuka yake faWi irin su,kina da wata irin baiwa da ba ko wace mace take da shi ba,in kika ri?e al?ur'ani ki na karatu wani irin ?arin ?ima kike samu a idanuna,domin Allah ya jarabce ni da son mace mai kula da ibada.


"Juwairiya duk ranar da muka rabu zan yi fama da kewar ki ina kishin mijin da zaki aura nan gaba domin ya yi dacen mace ta gari da baiwar kyau da sura.

Alokacin da nake kallon ki cikin hijabi sai nake jin tsanar ki kamar ba ki waye ba,ashe Juwairaah mata masu saka hijabi wata baiwa suke da shi na kyawun sura kike Soyewa.Surar ki abin sha'awa ce ga kowa.

Har lau ina faWa miki zuciya ta da gangar jikina za su yi kewar ki,amma ba komai zan mai da kula ta akan Wan ki sai ya zama wani abu a rayuwa,Allah ya sa ki haifa min baby mai kamar ki."

Duk lokacin da ya faWi haka Juwairiya ringume shi take ta saka kuka iya ?arfin ta shi kuma ya Suge ya yi ta aikin rararrashi.

A haka dai suke zaman su cikin kulawa da juna da girmama juna don in Juwairiya na mishi magana,gabaki Waya hankalin sa yake ba ta ko tari ba ya yi sai ta gama ya na matu?ar girmama lamarin ta,don ita ma ta na ba shi kulawa har ya na kawai ya ?yale Zainab ta tafi duk in da yake so tun da ya na da wanda take kusam makwafin ta kawai Juwairiya ce baya jin ta a zuciyar ta amma komai na ta ya yi masa.

Ranar wata alhamis Juwairiya ta dage ta shirya ma A.m abincin da yafi so wanda duk sai da ta zauna ta tambaye shi,ta kuma saka su a cikin ranta don kullum sai ta tambaye shi abin da yafi ?auna a cikin rayuwar sa,kuma duk ya gaya mata.

?arar shigowar mota ta ji da sauri ta mi?e daga sallayar da take zaune bayan ta idar da salla,ta na karatun alkur'ani ta rage zaman jiran dhi don ta ?agu ya dawo musamman da ya kirata ya ce mata a kwai labari mai daWi.

A ranta tunani take ko zai zo ya faWa mata ya na sonta shi ya sa ta Wauko kur'ani ta na karantawa,saboda ta za?u matu?a da ya shigo.


?aga labulen ke da wuya ta le?a kawai sai ta ga Zainab ta fito janye da akwati,wani irin tashin hankali ya ziyarce ta ta saki wata ?ar ?ara na rashin jin daWin dawowar ta ta zauna jaSar!

Sai kuma ta yi zubbur ta mi?e da ta kalli kanta a madubi sai da gabanta ya buga ta yi kyau matu?a ga ?arin haske da ta yi,da jikinta bai da haske amma yanzu wani irin ja ta yi sosai jikinta kamar ka losa jini ya fito.

Falo ta fito amma lokacin har Zainab ta shige ciki sai ta koma Waki ta yi kiran A.m tare da yi mishi albishir da Zainab ta dawo.

Zubbur ya mi?e ya tattara komai ya taho gida don ya ganta saboda ya yi mising Winta sosai.

Ya na shigowa Wakin ya same ta a zaune ta na Waki waya take yi ganin sa sai ta kashe wayar ta mi?e ta na zare ido,tare da dafe ?uncinta a tunanin ta mari zai kai mata kamar na farko.

Amma sai ya ba ta mamaki sosai ya ganin ya harare ta ya saki tsaki ya nemi guri kusa da ita ya zauna.
Abin sai ya ba ta mamaki ta kalle shi ta ce." Habibi i miss you zuc.."

Wata uwar harar ya daka mata tare da taSe bakin sa.
"Rufe min baki shashasha kawai ni za ki yaudara duk abin da kika ga dama ki je ki yi ta yi na zuba miki ido duniya ce,tunna ?an'uwan ki dabbobi ne ba su san a kwai Allah ba bare annabi ya faku."

Ya mi?e ya sauko ?asa don ya ci abinci ita ma sai ta biyo shi dama wanka ta yi ta na son ta sauko ?asa ta ci abinci,sai aka kira ta ganin kiran na kuWi ne don wata Hajiya ce take son ta yi mata oder kayan Waki za ta aurar da yara biyu.

Biyo shi ta yi da sauri suka sauko ?asa duk yadda take ta mishi hira bai tanka ba don ya so ace Juwairiya na gefen sa yake cin abincin ya yi ta mata sanni ,ita kuma ta yi ta murmushi dimple Winta ya na lotsawa shi kuma ya yi ta saka hannu a gurin don ya na burge shi,sai ya ciro wayar sa ya tura mata da tsa?on

24 / 48