Advertisements
Chapter 3 Reading Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 48

6K to 9K   out of 143.8K words

sabgar ta ba ba zaka gane hakan ba.Zainab likita ta karanta a ?asar indiya.Mahaifinta ya na ji da ita don ita kaWai ya haifa,sukai hatsarin mota ya samu na?asa ba zai ?ara haihuwa ba.
Saboda haka yake ji da ita ba ya son ya ga Sacin ranta komai take so shi take yi,gara mahaifinta ya na Wan jan ido akan lamuran ta musamman shigar ta da ya tsana,amma mahaifiyar ta Hajiya Mariya ba ta barin ya tsawa ta mata a cewar ta in basu ba ta gata ba wa zasu ba.
Zainab mace?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ?ar ?walisa da gayu ga ?amshi a kwai son turare masu tsada da kamshi,ga son kwalliya ta na Sata lokacin ta akan kwalliya ita rayuwar ta tafi ba ta hamimmanci akan kwalliya da charting,sai ta wuni ta na kalle-kalle a waya ko Waukar hoto.Kullum rana na duniya Zainab ta yi wanka sai ta Wauki hoto ta yi posting Win shi ko da wankan kwanciya ta yi.Bayan kwalliya da take so a rayuwar ta sai waya ko da yaushe wayar ta ya na hannun ta.
Wani lokacin mahaifin ta ya na tonon ta ya na kiran ta suna mai aljanar hoto ta na son Waukar hoto ta tura a Social Media a yi mata comment da liking a na zuzuta kyawun ta,ko ta Wora a tiktok. Zainab mace ce mai son jiki da hutu duk da ba ta da ?iba sai dai jiki na mata,amma a kwai son jiki ko waya a kace ta Wauko sai tace wash!Ta mi?o ta na ya mutsa fuska ko alamar gajiya.
A ta?aice ba ta cas ko as Wakin ta kullum mai aiki za ta shi ga ta share,sannan mai wanki ta kwashi kayan ta hatta innerwears Winta,mai aiki take wanke wa ko al'ada ta yi sai dai mai aiki ta kwashe abin a bayi ta zubar sannna ta wanke.Ta na matu?ar alfahari da gatan da iyayen ta suka bata tare da yi musu addu'a.Mace sangartacciya mai son jiki da hutu da zallar wayewa mai ?anci wacce rayuwarta a cikin fararen fata ta yi.
Zainab ta na da kyua na nuna wa tare da mannata a hoton irin matan nanne waWanda ka na ganin su kaga hutu,ko kai mace in ka hansu sai ka yaba.Doguwa fara ga gashi da kyan diri sannan ta na ?ara zuzuta kyanta da mayuka na gyara gashi da fata da kuma sabulai masu tsada.Ita dai ta yadda ta bautawa jikinta ko da za ta karar da wunin ranar ne,shi yasa in ka kalleta dole ka ?ara.
Ta na da girman kai a gurin samari ga ta da farin jini,amma duk saurayin da yazo za tace bai yi mata ba.Mahaifinta ya na matu?ar son yaga ya yi mata aure don ta haifa mishi jikoki,shi yasa kullum yake lallashin ta akan ta fidda miji daga cikin yaran masu da shi da alhazawan da suke neman ta,amma ta?i ita ganin ta aure ta?urawa rayuwar tane.Tafi son rayuwar hutu da jin daWi sannan ba ta son ta?ura da shishshigi ga lamarin ta.
Abin da ?ara tsoratar da ita ganin ?awarta Nihal da ta yi aure shekara Waya da ya wuce.Ta na da kyau da gayu,amma tun da ta yi aure ta haihu ta zama ?atuwa ga tumbi da ta yi,sannan ?irjinta ya zube,kullum cikin aikin yara ko a gurin aiki ta rage ?okari,ga takurawa Wan tiktok Win da take yi mijinta ya hana.
Wannan dalilin yasa ta ?ara tsanar aure ta na gani kamar koma baya ne a rayuwar ta,ganin mahaifinta na da kuWi kuma ita ma ta tara kuWin da za ta Wauki nauyin kanta.Ta saka ma ranta ba za ta yi aure ba,in ma dole sai ta yi aure to ba za ta yadda ta haihu ba kawai za ta yi rayuwar hutu ne don gani take kamar tara yara wahala ce gata likita kuma bata son jikin ta ya canza.
Duk mazan da suke zuwa gun ta kullum cikin kushe su take yi ta na yi musu wulakanci,kuma in auren za ta yi tana son namji mai kyau wanda ya fita gayu da tsafta.Ba ta taSa jin soyayyar wani a cikin zuciyar ta ba,shi ya sa take wula?anta duk wanda ya zo gurin ta.
Kwasam!Ta haWu A.m a ranar wata daren alhamis da misalin ?arfe shidda saura kwata agogon birnin a ?asar London,ta raka yar gidan ?anwar mahaifiyar ta siyo kaya.Suna zaune a cikin jirgin za su dawo A.m ya shigo hannunsa ri?e da waya da cingam a bakinsa ya na taunawa a yangace.A.m na son cin cingam kamar mace hakan ya samo asali ga matar Alhaji Sama'ila da ta rike shi ta na son cin cingam.Hausawa sun ce zama da maWaukin ?anwa shi ke kawo farin kai.Aiko haka ta kasance A.m ya koya cin cingam a gurin ta duk lokacin da ya ci abinci ko ransa yake a Sace,sai ya huce a kan cingam Win.
Ran shi a Sace yake akan taron da suka yi da safe a companin su,sam yadda yaso taron ba haka ya kasance ba,wannna dalilin ya saka shi baro London bai kammalla abin da ya kawo shi ba.
Ya shigo cikin jirgin fuskar sa kamar an yi mishi mutuwa,bai kalli kowa ba sai kujerar sa da ya nufa ya na murza tafin hannun sa tare da tauna cingam Win da ?arfi saboda fushin sa ya ragu.
Wani irin kallo ya watsa mata ganin ta zauna masa a kujerar sa,da fari ya Wauka makauniya ce saboda kowa da numbar kujerar sa amma ganin ta na ri?e da waya sai ya daka mata tsawa da ?arfi yace."Za ki iya tashi a ?ujerata ki nemi ta?i tunna baki je makaranta balle kin san yadda ake irga numbobi."
A hatsale ta mi?e tare da faWin."What."Ita sai yanzu ta kula ba'a gurin ta ta zauna ba,saboda hankalin ta na kan wayar ta sanda ta shigo.Ranta ya Sace jin kalaman sa sai kawai ta Waga hannunta da nufin ta wanka ma mutumim da ya kira ta jahila mari,sai ya banbance waye ke da jahilcin atsakanin shi da tunna idanunsa sun kasa gane mishi wayayya mace mai a aji da class,wacce take tashe a tiktok.

Zainab ta sauke hannunta a hankali jikinta ya yi sanyi matu?a ganin matashin saurayin da ya kafa mata manyan idanunsa ya na kallonta,cikin zafin rai a yadda idanun sa suka nuna jira yake ta mare shi ?ila ball zai yi da ita yadda ya haWe fuska.
Ta shiga in ina ta na ?o?arin matsawa daga gurin ya tureta ya na faWin."Matsalar ?an matan bahaushe kenan daga sunga sun fita waje su dinga nuna isa.Da kin mare ni wallahi sai na yanke duk yatsun ki na kai ma karan gidan mu nan gaba sai na ga da wane hannun zaki yi mari."Ya ja tsaki tare da zama ya ma?ala earpis a kunninsa tare da harWe hannun sa duka a ?irji,zuwa can ya cire earpis Win ya lumshe idanunsa.


Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi na huWu dan har yanzu shinfiWa ne har ba'a fara ba.Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ?ofa a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA HU?U*

Jiki a sanyaye ta koma kujera ta zauna ta na jin wani shauki ya na ratsa bargon jikinta,hannu ta sa ta share zufan goshin ta tare da jingina kan ta da bayan kujera ta na kallon sa cikin wani irin yanayi.Ganin halin da ta shiga Imsal ya matso dai-dai kunninta tace."Gaskiya gayen ya na da kyau sosai."
Zainab ta ?ara lumshe idanunta ta na kallon shi ba tare da tace mata komai ba,amma ta na jin wani girmar lamari a tare da shi,zuciyar ta ta na bugawa da sauri-sauri haka bugun ?irjinta.
A lokacin da jirgin ya fara tafiya Zainab ji take kamar ta je gurin sa ta yi mishi magana,ji take komai na ta ya sukurkuce,amma ganin yadda ya Waure fuska idanunsa na rufe ya sa taji karayar zuciya.
Wayarta ta ciro ba tare da ya sani ba ta dinga Waukar sa hoto,ta na turawa ma ?awayen ta da ta yi saurayi.Ko da suka iso Nigeria bai kalli in da take ba,ya na janye da troley Win sa hankalin sa na kan A.k da yazo Waukar sa.
Da sauri ta ?arasa gurin sa tare da shan gabansa saura kaWan ta faWi,amma ba ta kula ba ta tsaya ta na mishi murmushi mai Waukar hankali.
A.m ya juya bayan sa ya na kallo a tunanin sa wani take ma murmushi a bayan sa,don shi sam ba yarinyar ba ta yi mishi ba,saboda tsiwarta sannan shi a wannan lokacin babu so a tsarinsa,bai shirya aure ba duk da burin iyayen sa kenan.
Kallo ya bita da shi tun daga saman ta har ?asa ta na da kyau shi ma ya san haka,amma hakan bai wani dame shi ba kasancewar ya sha haWuwa da mata kala-kala.
Wani ?arin murmushi ta ?ara saka mishi tare da bin sa da sauri ganin ya fara tafiya."Don Allah ka tsaya ina son magana da kai,in ba damuwa ina son mu ?ulla abota."Ta faWa tare da mi?a masa hannunta .
Wani ban zan kallo ya yi mata mai kama da ya ga kashi yaci gaba da tafiyar sa ba tare da yace mata uffan ba.Jikinta ya yi sanyi ta na tsaye ta na kallon shi har ya shige cikin motarsa,wanda A.k ya tu?o don ya Wauke sa.Da idanunta da suka canza kamar za ta zubda ?walla ta kalli bayan motar.
TURAKI FAMILY
Abin da taga an rubuta keman a bayan motar wani irin farin ciki ta ji ganin A.m ko Wan waye,sai murna ya kama ta sosai tasha jin mahaifin ta na waya da wani daga cikin family Win.Ba ta son wulakanci sannan ta sha wula?anta maneman ta,amma wannan karan ta na ji ranta sa samu kalan mijin da take so.
Ko da ta isa gida tunanin wannan kyakykyawan saurayin ya tsaya mata a zuci,da ta rufe idanunta kyakykyawar fuskarsa take hangowa.Tun kafin Abban ta ya dawo ta kira tare da bashi labarin saurayin da ta haWu da shi,kuma ya tafi da imanin ta.
Dariya ya yi sosai kin yadda ta ruWe akan shi ta na mishi shagwaba da ?yar ya samu ya lallasheta,ta kashe wayar ta bayan ya yi mata al?awarin gane ko waye daga cikin family Turaki saboda ya san Alhaji Sama'ila abokin cinikayyar sa ne.
Ko da ya dawo gida haka ta sa shi a gaba ta na ta yi mi shi magiya,har ya gaji da ?orafin ta ya kira Alhaji Sama'ila.
Bayan ya gaya mi shi dalilin kiran sa dariya sosai tare da farin ciki ya yi,a ransa ya na ro?on Allah ya sa A.m ya so Zainab ko ba komai ya yi dacen mace,sannan zumuncin kasueancin su zai ?ara ?arfi.
Duk yadda Abba ya yi da ita kan ta ha?ura da numbar A.m da ta kafe sai an turo mata,amma taki daga ?arshe kan dole ya ?ara kiran Alhaji Sama'ila ya turo mi mi shi da numbar.
Da gudu ta ruga cikin Wakin ta da wayar ta a hannunta bayan ta kwashe numbar a wayarta.Kan gadon ta ta faWa ta na ajiyar zuciya mai ?arfin gaske ,tare da ?an?ame filo a ?irjinta.
Ran ta ya fara Saci ganin ta yi kira ya kai sau biyar ba'a Waga wayar ba,da ga ?arshe sai ta ji an kashe wayar jifa ta yi da wayar ta ta zauna akan gadon ranta a jagule.
Ko da Alhaji Sama'ila ya tare shi da zancen yarinyar da suka haWu a jirgi,nuna ya yi bai gane ba in ma ya haWu da ita ya manta.Ganin kauce-kaucen da yake mi shi sai ya yi masa umurni da yaje ya ganta ya na son ya nemi aurem ta.
Babu yadda A.m zai yi ba tare da ya so ba ya amince duk da a wannan lokacin ya fara tunanin lokaci ya yi, da zai yi aure ya huta da damun da iyayen sa suke mi shi a kan ya yi aure sannan ya na bu?a?ar ya ga yaransa ga ?aninsa ya na da biyu.
Da wannan tunanin A.m ya amince ya je gidan su Zainab tamkar za ta yi hauka haka take ji a ranta,da ta gan shi ruWewa don Allah ya saka mata son shi a birnin zuciyar ta.
Tun ya na share ta har ya bada kai bori ya hau.Zainab ba ta a cikin matan da namiji zai wula?anta ita kanta ta na alfahari da hakan.Haka suke shan soyayyar su kullum suna ma?ale da waya ana ga ya ma juna kalamai so.
A hankali A.m ya fara jin tsanar wasu daga cikin halayan Zainab,musamman yanayin shigar ta da tsabon son jikinta,sannan shi namiji ne mai son mace wacce ta iya girki amma tunkafin su yi aure ta gaya mi shi ita ko ?afar kicin ba ta shiga.
Dariya ya yi kawai don ya yi tunanin tsokanar shi take yi ganin ta wayayya mai aji,ya san babu yadda za'a ta bari ?ar aiki na yi mi shi girki,ko a gidan su Amminsa take mi shi abinci.
Haka dai aka dinga cin soyayya har Allah ya kai si ga aure.Bayan an gama shagali amarya ta tare a Wakin mijinta.Shi kaWai ya shigo bai nemi rakiyar kowa ba,ko A.k daga kofar gida ya tafi ya na ta mishi dariya.
Da gudu ta taso ta rungumshi ya janye ta jikinsa,kasancewa wannan ne karon farko da mace ta rungume shi,idanunsa ya kafa mata duk rashin kunyar ta sai ta ji ta kasa haWa ido da shi ta sunkuyar da kanta.
Bayan sun yi sallah sun ci kayan daWi da ya siyo musu,suka tsunduma kogin soyayya.Wani irin tarairayan juna suke yi ma junansu A.m bai san ya kamu da soyayar Zainab ba sai da ya aure ta yake jinta a zuciyar sa.Koda yaushe suna ma?ale da juna in ba shi a gida suna kan waya.Ya na matu?ar ji da ita ba ya son Sacin ranta.
Abu Waya da ya fara kawo musu cikas yadda Zainab take son jiki komai suka yi amfani da shi,a nan za ta barshi sai in shi ya Wauke da fari abin bai dame shi ba,amma daga bisani sai ya ji ya na taSa zuciyar sa.
Kusan shi yake Wan wasu aikace-aikace na gidan.Sati biyu da auren su mahaifiyarta ta kawo mata masu aiki mata guda biyu.Da fari A.m ya?i amincewa amma daga kan dole ya ha?ura,saboda yadda sha?ar numfashin gidan yake son ya fi ?arfin sa.Hankalinta kwance ta ci tasha ta tafi gurin aiki.Hakan bai wani dame shi ba saboda ya na matu?ar sonta.
Kamar yadda Zainab ta tsara ba tare da ya tsani ba take shan maganin ha na Waukar ciki a Soye,ba ta damu da mai zai faru ba duk da ta san illar sa musamman da take likita,amma yadda A.m yake yaba halintar ta ya sa take shan maganin don ba ta son canjin jikinta.Kuma mafiyawancin family Win su suna da ?iba.
Tsaye yake a gaban madubi ransa a jagule ya na kallon kansa a madubi,zuciyar sa babu daWi.Matu?ar yunwa yake damun shi amma ba ya son cin abincin masu aiki,saboda daWin shi bai kai na amminsa ba ya na jin kunyar zuwa ?arSo musu abinci,wanda ita Ammin da kanta tace ya kama ta su fara girki saboda ta gama kawo musu na amarci,in bai manta ba rabonsa da abinci tun daren jiya da ya ci a gidan A.k.
Ya Wauki kum cikin Sacin rai ya na tunanin bayan ya na matu?ar kiahin Zainab,sannan ita ba ta da kiahin kanta don ko masu aikinta mata yadda take fito musu kamar tsirara ya na bashi haushi amma ita ko a jikinta.Da namiji zai Wauko kuku ya dinga mishi girki.
A hankali ya ji an turo ?ofa an shigo wani Wan murmushi dole ya yi mata ya na jiran ta ?araso,amma sai ya ji an yi shuru kamar ba'a shigo ba idanunsa ya Waga da nufin ya kalleta yau yangar ce ta motsa.
Sai ya ga mai aikin su wacce bai ma san sunan ta ba tsaye ta na kallon ?irjinsa ta na lashe baki,idanunsa ya kai kan jikinsa tare da jin kunya don daga shi sai Wan tawul iya gwiwarsa."Ke!Uban me kike kallo ?azama kawai?"Yace da ita ran shi a Sace ganin yadda take kallonsa kamar wata mayya.
Da sauri ta matsa cikin tsoro muryar ta na rawa tace."Madam ce ta bani umurnin na shigo na share Wakin."Ta ba shi amsa tana jin wani lamari dangane da shi.
"Tunna kin ga da mutum ba sai ki fita ba,banza mayya kawai."Yace da ita bayan ya ?ara daka mata wani tsawan,da sauri ta fice har ta na buge kanta da ?ofa.
Ya zama dole na Wauki mataki ba zan lamun ce da waWannan ?azaman arna suna shigo mim Waki ba,gajerun wandunan sa ya kwashe ya saka a sif Win sa ya na takaici don ya san masu aiki suka wanke.


Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi na huWu dan har yanzu shinfiWa ne har ba'a fara ba.Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*






*SAKACINA KO HALIN

3 / 48