Advertisements
Chapter 46 Reading Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   46 / 48

135K to 138K   out of 143.8K words

da ke kike da cikin nan in da ana yi ma mutum numfashi to zan sauwa?e miki yin sa,don haka duk abin da nake yi mata saboda baby ne,kuma da zarar ya fita shikenan."


Ya ce mata da murya sanyayya yana kallon Juwairiya a wula?ance.

" Gaskiya dole ka yi magana da Abba ta koma gidanku na yarda,ko miliyan nawa zan ba da in har za a kula da ita amma ta bar mini gidana."

Ta faWa masa cikin karayar zuci saboda ganin yadda ta koma ya firgita ta.

Tsaki ta saki ta kalle su duka ta ce." Kan ku ake ji ni kaina na ?osa na bar wannan gidan da baku san ha??in kowa ba sai kanku."Ta juya ta koma falo.

"Yanzu da gaske girkin za ka ka yi mata da wannan daren?"Kawai sai ta saka kuka ganin yana saka doguwar riga.

"Yarona zan yi wa girki karki damu cikinta ya shiga na wata huWu, kin ga mun kusa yarda ?wallon mangwaro mu huta da ?uda."Ya ce da muryar rarrashi.

A lokacin da ya fita kifa kanta ta yi ta din ga kuka sosai ba?in ciki cushe a zuciyarta,tana jin wani Waci na ganin ta a gidan,wasu irin abu da suka faru dama waWanda ba su faru ba ta rin?a hasasowa,sai ta ?ara sakin wani kukan tana buga kanta da gini.

Da ga ?arshe kasa zama ta yi ganin uku har ta gota ta sauko ?asan,sai ta ga a wannan lokacin A.m ya kammala Wanwaken ya kawo mata,amma saboda muguntar da ta saba ta ce sai ya jira ta ta gama.

Da takaici ya ishe ta komawa Waki ta yi tana ta kuka sosai a yadda ta ga Juwairiya, daga yau ta ije aiki har sai ta haihu ta bar musu gidan,don ba za ta iya barin ta da shi ba a cikin gidan.


Kamar yadda suka saba kwana a falo haka ta kasance yau ita Juwairiya ba ta yi bacci ba,sai shi da yake ta gyangyaWi daga ?arshe bacci ya kwashe shi.

Ta gyara zamanta ta ci gaba da kallo tana karanta lintafin Hausa novel mai suna(Burin duniya na Jamila Lawal Zango Jamcy)Wanda Hamdiya ta tura mata saboda ya rage mata kaWaici.Sai dai tsoro da tashin hankalin da yake cikin lintafin da tausayin Khairi da kuma takaicin doctor Garkuwa ya sa ta ije lintafin, da tsananin tsoro ta kashe wayar gabaki Waya.


A.m da ya ji kiran salla zubbur ya mi?e ya kalle ta wadda tsoro ya sa ta baccin dole.


Ji ya yi kamar ya sha?eta da sauri ya haye sama ko tashin ta bai yi ba,saboda takaicin gani girkin da ya yi mata ko guda uku ba ta ci ba.

Ya tura Wakin ya shiga har yanzu bacci take yi saboda bayan kukan da ta sha bacci ya Wauke ta ba don ta so ba.

" Zainab ki tashi kiyi sallah."

Sai ta yi tsuru tana kallon sa yayin da hawaye yake bin gefen fuskarta.

" Na rasa ta yadda zan fito na yi miki bayani ki yarda da ni Zainab."Ya faWa muryar kaukausa domin shi yana ganin bai kamata ta Waga hankali a kan yarinyar da baya jin sonta a cikin ransa ba.

" Na gaya miki ba so a cikin auren nan na yi shi ne don kawai mu samu Wa,kuma na yi miki al?awarin da zarar ta haihu zan cika miki al?awarin da na Waukar ma ki ba ta saki uku."


" Zuciya ce take War-War amma tun da haka ka ce shikenan ka yi ma Abba magana ta koma gidanku."Ta ce mishi lokacin da ta yi hanyar bayi.

" Wannan ba zai yiwu ba domin Abba ya ce dole sai na zauna da ita,amma ni ba zan iya zama da wata mace ba bayan ke,ki yi ha?uri har ta haihu sai mu bar garin bayan na saketa mu koma London sai mun Wauki tsawon shekaru kowa ya manta mu dawo."

Rungume shi ta yi tare da manna mi shi kis ta ce."Na yadda da kai mijina na san duk wannan matsalar ni na kawo shi,domin da ban biye wa son zuciya ta ba,da son gayu da ?yal?yali na haihu ko da Waya ne, da baka janyo Juwairiya cikin rayuwarmu ba,na yi takaici sosai ban san cewa kana son yara haka ba,sannan ba za ka iya rayuwa dole sai ka so ka ga Wanka."


Sai kuma ta sake shi ta sa kuka ta ci gaba da cewa." Kaicona da na bi ruWin duniya na ?i bari na haihu ko sau Waya ne,ina ma matan da suke shan maganin hana haihuwa don wani buri na su,ko mazan suka umurce su za su daina duba ga irin yadda na tsinci kaina cikin nadama.Don Allah A.m karka karya al?awarin da ka yi mini,saboda kishin ka zan ije aikina har Juwairiya ta haihu na ?osa ta fita daga cikin rayuwarmu ba zan iya barin ka kai da ita ba,wallahi jiya da na gan ta hauka ne kawai ban yi ba,saboda duk kyan da na ke da shi na tsorata da ganinta.Ashe haka mata suke canzawa in suna da ciki."


Ri?e ta gam ya yi har cikin ran sa yana jin tausayinta don in ya kalli cikin Juwairiya ji yake yi kamar zai sume,to ina ga ranar da ya fito duniya ya ga Wan mutum ace na shi.

" Na yi miki wannan al?awarin ba ki da matsala."

Duk wani abun da A.m zai yi ya kwantar da hankalin Zainab yana yi,abu Waya ne ya ji sam ba zai iya ba yadda ta hana shi ko da kallon Juwairiya,domin ko motsi ya yi idanunta na kan sa.

Gabaki Waya ta ije duk wani yawonta da take nadamar yin sa da ta yi,tana zaman gida sai ta yi kwanaki ba ta fito ba.

Duk sadda ta ga cikin Juwairiya da ya?e ?ara girma, sai ta shiga Waki ta yi kuka ta yi kuka har ta ji babu daWi,watarana sai ta yi ta buga kanta a bango tana nadamar ri?on sakainar kashin da ta yi masa.

Ba ta ?ara shiga tashin hankali ba sai da Juwairiya ta fara kubburi duk da alokacin cikinta wata shidda da sati biyu,hankalinsa ya yi dubu ya tashi kamar zai yi hauka,wanda Zainab ta ka sa gane akan baby yake yi ko uwar baby.

Da suka je asibiti likita ya ?ara tura su scanning sannan jini za a ?ara mata,saboda jininta ya yi ?asa,take A.m ya ce a iba na shi a saka mata.

Zainab ta tada hankalinta matu?a tsiya sosai suka yi akan ya siya jini a saka.

Sai dai ba ta yi nasara a kan sa ba, don kwana biyu ya yi ana iban jinin sa wanda aka sakawa Juwairiya,da yanzu ta fara raina kanta ganin yadda take komawa har kammanninta sun fara canzawa,ga ?afafuwanta da suke kubbura.


Bayan an saka mata jini suka dawo gida Allah ya Wauki wani irin tausayin Juwairiya ya saka a zuciyar A.m,wanda ko juya idanunta ta yi sai ya ji wani madarar tausayinta a cikin ransa.

In yana gida sam ba ya iya zama a ko ina sai falon ?asa,daga baya ?arya ya yi wa Zainab cewa Momi ta ba shi umurnin ta koma sama,in ya so a ba ta Waki Waya ta zauna madadin zaman ta a ?asa.


Zainab hankalinta ya ?ara tashi saboda tun da ta dawo ta ga duk sun canza mata suna wani nan-nan da ita.


Kullum suna sintiri gurin kawo mata abinci na ?waWayi,haka Momi da Abba kullum sai sun kirata sun ji lafiyarta.

Ta raina kanta matu?ar gaske kullum cikin nadamar abin da ta aikata take.Ga tarin dukiyar da take buri ta samu ta samu don yanzu ?asar ingila take son ta haWa hannu da asibinta,kuWi kam ba ta da matsalar su amma babu kwanciyar hankali,saboda ta lura yanzu sam hankalin A.m ba shi a jikinsa,da ta yi masa magana ya ce zuwan baby ne.


A.m da Zainab suka shirya zuwa waje suka yo siyaryar kayan baby,wanda ita kanta Zainab ba ta san iya yawan kuWin da ta kashe ba.

A.m sai haWa tarin dukiya yake yi ma Juwairiya har da wasu share Win sa na waje yake son ya bar mata,saboda kar in suka rabuya rage mata jin zafin rabuwa da baby.

Ita kanta Zainab ta yi masa al?awarin za ta ba ta dukiya masu yawa, ita dai burin ta ta bar mata A.m da babyn da yanzu take jin ta fara son sa a cikin ranta,don son da za ta nuna masa shi kawai zai ?wato mata martabarta a gurinsa.

Bayan Juwairiya ta dawo sama wata ?aryar ya shirga ma Zainab akan dole yanzu ya rin?a kwana da ita saboda cikinta da ya shiga wata na bakwai.

Da fari ?in amincewa ta yi amma daga baya sai ta yarda akan za su dun ga kwana dukansu tare.

Sai dai A.m ya?i mata ya Wan nuna mata hakan ba zai yiwu ba ta amince,don ta san yanzu in dai ba rashin tausayi ba bazai kalle ta ya bu?aci wani abu daga gareta ba,duba ga yadda ta koma.


Juwairiya na WanWana kuWarta duk wani wahala da take ba ma mutanen gidan,da tsiwa kan dole ta watsar domin yanzu ta kanta take yi,kusan kullum cikin wahala take domin cikin na matu?ar ba ta wahala sosai,kamar za ta mutu ko nishi ta yi sai ta ji wani azaba,ita kam ta sheda mutuwa za ta yi,shi ya sa kullum take kuka sosai akan ya kai ta gurin Mama,saboda ta san mutuwa za ta yi.

Ranar wata daren Alhamis A.m hankalin sa ya tashi matu?a ganin yadda take sauke numfashi sama-sama.

A lokacin cikin wata takwas ya shiga amma duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata,saboda ta yi wata irin ?atuwa a yadda kamanninta suka canza ina tunanin ko Mama ta ganta sai ta yi da gaske za ta gane ta.


A.m hankalin sa ya tashi ?warai tun da ya fara kwana da ita ya shiga tashin hankali,ganin irin wahalar da take ji sam ba ta samun bacci.

Hannunsa ya sa da nufin ya kamata cikin tausaya,amma sai ta ture shi ta ri?e kwankwasonta tare da rintse idanunta,tana jin wani irin azabar raWaWin mutuwa yana shigar ta.

" Wayyo Allah na!Mama ki yafe mini dama haka kika ji kika haife ni! Wayyo Mama ba laifina ba ne halin da kike ciki ya sa na amince da abin da mugu azzalimi ya zo mini da ita.Baba Sani Allah sai ya saka wa mahaifina sam baka ri?e maraicin da mahaifinmu ya baka amana ba."

Sai ta cige baki ta mi?e da nufin ta tashi,amma ta kasa da sauri ta koma ta zauna, tare da jingina kanta a kan gadon don ji take kamar Wan dake cikinta zai fito ta bakinta.

A.m da yake jin wani tashin hankali kusan haka suke kwana duk da sun je asibiti,amma sai a ce musu lokaci bai yi ba,sannan (E.D.D)Winta bai yi ba balle ayi mata aiki,don haka su jira lokaci.

Duk iya juriyar sa in ya ganta cikin wannan tashin hankalin sai ya ji hawaye da nadama na shigar sa.

Bai san cewa ya sha?u da ita ba musamamman lokacin da ta fara masa tsiwa, tana nuna ba ta son sa da tsoron sa.

Hunnunsa ta kama ta ri?e ta kalle shi da fararan idanunta wanda yanzu suka koma suka rine saboda ruwan azabar da take kwankwaWa.

" Bazan yafe maka ba kai da Baba Sani, kai harma da A.k duk da na san ka tilasta shi ne,amma wata?ila da ya jajirce bai amsa ba da ba ku zo gurina tun da kana jin maganar sa b...."

" Juwairiya ki yi shiru za ki haihu lafiya ki koma gurin Mama in sha Allahu Mama za ta ?ara tozal..."

Katse shi da ?arfi ta yi." Ka yi shiru don Allah mutuwa zan yi! Jikina ya ba ni bazan ?ara ganin Mama ba a rayuwata,ka raba ni da Mama don kawai burinka na ka samu Wa.Ka tuna ni ma ?a ce wacce uwa ta haifa take sonta, kamar yadda kake son Wan da za ka haifa,saboda burinka na haihu ka ba wa matarka ka nisanta ni da Mama A.m ba ka yi mini adalci ba,na tsane ka bana sonka.Dubi irin wahalar da nake sha amma fatan ka na haihu ka rabani da Wana,saboda ka faranta ma matarka.Wai shin ita ce mace kaWai a duni..."

Wani irin hajijiya da take yi ya hana ta ?arashe maganar sai da ta Wauki tsawon lokaci ta ce a wahale.

" Wayyo Mama na ?ara girmama lamarin uwa a raina,na san ha??in ki yake bibiyata tur da irin ?a kamata wacce za ta aikata wani abu ba tare da sanin mahaifiyarta ba!Tur da ni kaicona da na yi miki butulci na yi aure ba tare da sanin ki ba.
A m ka Wauki kukana ka tura ma Mama ta yafe mini ko na samu salama a makwancina."Ta ce yayin da idanunta ke rufewa muryarta na ?asa-?asa.

" Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un!"A.m ya faWa cikin tsananin tashin hankali yana jijjigata.
" Da gaske mutuwa za ki yi Juwairiya! Don Allah kar ki mutu wallahi ban aure ki don na kashe ki ba,ki buWe idanunki Juwairiya ki tashi don Allah mai kike so na ce ma Mama da take zaman jiran ki?"


A.m ya ruWe sosai jijjigata yake amma tamkar babu rai a jikinta.
Hawaye yake yi cikin tashin hankali a ransa yana tunanin dama haka mata ke haihuwa.


Yana tsaye a kanta yana jijjigata ya rasa na yi zuwa can sai ta buWe idanunta, tana wani irin jijjiga kamar wacce ta kamu da tsin?a-tsin?a,sai jini ya fara zuba sosai kamar an buWe famfo.

A.m ya mi?e daga jikinta tare da sakin wani iri ?ara ya ce.

" Juwairaaaaah!"

Kawai ya zube ?asa babu numfashi.





TO MASU KARATU KU DAI BIYO NI KU JI YADDA ZA TA KAYA A TSAKANIN SU YAU BAN YI TYPIND DA YAWA BA,SABODA BA NA JIN DA?I KU YI HA?URI DA WANNAN ANA TARE.


KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



SAKACINA KO HALIN MAZA


TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY




TALLAH!TALLAH!!TALLAH!!!

INA ?AN MATA DA MATAN AUREN DA SUKA SHAYAR SUKE SON MARTAR ?IRJIN SU YA DAWO?

INA MATAN DA SUKE FAMA DA RASHIN ?IBA KO INA A ?AME?

MAZA GARZAYO KI SIYA INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO DA ?IBA,MAGANIN AN RIGA AN GWADA KUMA YA NA DA AKYAU ?WARAI.BARI IN GAYA MIKI YAR'UWA DUK WADDA TA CE MIKI MARTABAR ?IRJINKI,ZAI DAWO MATU?AR JIKINKI BAI MURJE BA,TO GASKIYA KU?IN KI KAWAI ZA TA CI.

IN HAR KINA SON MAGANIN YA YI AIKI A JIKIN KI SAI KIN DAURE,KIN SHA SAFE DA YAMMA.SANNAN MUNA AIKAWA KO INA SIYAN NAGARI MAIDA KU?I GIDA.

MAGANIN AKAN FARASHI MAI TSAU?I IN KINA SO MAZA GARZAYO KI KIRA WANAN NUMBAR ( 07088268243) KO (08144072423)

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ?ofa a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




COMMENT,READ FOLLOW AND COMMENT.






SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*


*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 37*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


Zainab da ke kwance ta mi?e cikin tashin hankali jin ?arar A.m ta ruga Wakin da gudu.Abin ta gani ya yi matu?ar razana ta,Wora hannunta ta yi aka tare da sakin ihu,saboda ta rasa me za ta yi.

Girgiza sa ta fara yi tana faWin." A.m ka tashi don Allah kar ka mutu ka bar ni!Ka san ba zan iya rayuwa babu kai ba."


Ta kalli Juwairiya da take cikin wani hali gani ta yi kamar babu rai a jikinta,sai jikinta ya kama rawa ta rasa ba?in ciki za ta yi?Ko akasin hakan.


Dabara ta faWo mata ta ruga da sauri ta ibo ruwa ta watsa masa.

BuWe idanunsa ya yi da sauri tare da mi?ewa ya kamata kamar zai Sallata ya ce." Ina Juwairaaah ta mutu ko?"

Zainab da ta kasa magana idanunta ta kai gurin da take kwance rai kwakwai mutu kwakai.

Da sauri ya bi in da ta kalla da idanunsa sai ya mi?e zubbur ya nufe ta ya Wauke ta zai fita da ita.

" A.m dare ya yi fa yanzu ina zaka kai ta?"


Ta yi masa tambayar da ko kallonta bai yi ba ya fice,ba ta ankara ba sai jin tashin motarsa ta ji ya fice da ga gidan.

A.m da yake tu?i cikin tashin hankali Allah ne kawai ya kai shi asibitin.

Ba tare da Sata lokaci ba likitoci suka rufu a kanta,wacce ba ta san halin da take ciki ba.

Jikinsa har rawa yake yi wani irin tashin hankali ya ziyarce shi,ji yake kamar zai yi hauka,domin ya rasa asarar babyn Winsa ne bai so ya yi,ko halin da take ciki ya saka shi cikin wannan halin.

Wayarsa ya zaro a cikin daren ya kira A.k ya fi sau goma sai dai bai Waga ba,sannan ya kira iyayensa ya sanar musu.

Ya yi shiru yana tsaye a gurin Wakin da aka kwantar da ita sai le?e ta windo yake yi,amma duk iya ?o?arin da likitocin suke yi

46 / 48