Advertisements
Chapter 5 Reading Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   5 / 48

12K to 15K   out of 143.8K words

yi matu?ar burge Mama wani ?arin burgewa ta baje akan tabarma har ta na cire hijabin ta da Wankwalinta.

Hakan ya yi matu?ar ?ara burge Mama sai ta ?ara jin ta saki jiki da ita tace."Bam ma sanki ba yarinya,amma da na ganki da Mariya ?ar ma?ocin mu na gane kece wacce aka yi maganar aiki da Juwairiya..."

"Ni ce Mama tabbas ni ce ina ta jiran ta ba ta zo ba,sai da ga ba ya Mariya ta zo tace min kin hana ta "Tace tare da ?atse Mama ba tare da ta kai aya ba.
"Haka ne gaskiya aikin nan ki nemi wata kawai."Mama tace ta Wan canza fuska kaWan,ganin haka sai jikin Anty Naja ya yi sanyi amma saboda ya ba hankalin da ta yi na Juwairiya ta kasa ha?uri tace."Don Allah Mama karki hana ta wallahi ba ni da matsala da ga ni har mijina,kuma in kina tunanin kwanan da za ta yi ne mijina ba zama yake ba wani lokacin ni kai na sai na yi bacci yake dawowa."

Ta matsa kusa da Mama tare da ri?e hannunta ta yi rau-rau tace."Don Allah Mama kar kice a'a ban Wauki Juwairiya a matsayin me aiki ba ?anwa ce a gareni,kuma duk ranar da kika ga wani abu ya faru mara daWi a tsakanin mu ki hana ta zuwa."

Ta yi shiru ko Mama za ta ce wani abu amma sai ta ga ta kauda kanta ta na tunanin wanda ba za ta iya cewa ta yanke ta barta ko a'a."Kin ji Mama ki amince don Allah!Na yi masu aiki da dama amma basa iya ri?e min amana,bayan haka sace-sace suke min."

Duk maganganun da take yi ba ta ce mata komai ba,aranta ta na tunanin karta amince a za a sami matsala da Baba Sani duk da shi ma ya na da laifi,in da ace ya na taimaka musu da ba za ta yi aiki ba.
'Ki na ji Mama da ban so na gaya miki wani sirrina ba,amma nuna amincewar ki ya zama dole na sanar miki domin ki taimakeni ki ceci aurena.Mai aikina mijina ya kama ta da yarana tana basu kirjinta suna tsotsa ita kuma ta na saka musu hannu a gabansu.Hankalinsa ya tashi ?warai ba yan ya mi?a ta ga hukuma ya kawo su asibitin da nake aiki,hankalina ya tashi ?warai na yi kuka kuma mun yi rikici da shi daga ba ya yace dole na bar aiki ko mu rabu.Ina son aikina saboda da shi nake taimaka iyayena,sannan ina son aurena na yi-na yi a dai na saka ni aikin kwana amma ba zai yiwu ba.

Mijina ya bani zaSin na bar aiki na kula mishi da yaransa ko ya rabu da ni,domin ya?i barin na ?ara Waukar me aiki.Mun yi rikici da shi sosai daga baya ya ha?ura na samu mai aiki amma daga wannan ya kama ta da wani matsala zai rabu da ni."Tace cikin hawaye ta ja numfashi sannan ta Wora da cewa.

"Mariya ita ta ja ra'ayina akan Juwairiya saboda ta gaya min ta na da hankali,da ?yar na ami???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nce da na ganta na yadda da maganar Mariya ki taimake ni Mama in har kika amince zan zama tamkar ?arki,zan taimaka ma rayuwar ku."

Jikin Mama ya yi sanyi sosai har ba ta san sanda ta amince ba jin aure na shirin mutuwa,duk da watarana ita ma aure za ta yi."Na amince Allah ya kyuata amma ?ar nan ya kamata ku din ga kiyaye wa,ni ma matsalar ba daga gareni ba ne a kwai ?anin mahaifinta ba lai-lai ba ne ya amince amma ta fara mu gani."

Sosai ta ji daWi ta buWe jakarta ta ciro dubu ishirin da biyar tace."Ga kuWin ta na wata biyu dubu ishirin sai ki fara koda sana'a ne,sannan dubu biyar na baki kyauta kuma gobe in Allah ya sa tazo za ta taho da tsa?o."

Mama ta ji daWin kuWin da ta bata ta na ta murna da saka mata albarka har ta yi mata sallama,ta kama hannun Juwairiya tace."Sis sai kin zo gobe ko?Don Allah ki zo da wuri ?anninki suna ta maganarki."Tace tare da shafa kanta.
"Gaskiya ta na da kirki sosai."Mama tace ta na juya kuWin da ta bata,sai kuma ta aje kuWin ta kalleta tace "Kin san me ba zan taSa kuWin nan ba sai mun ji me Baban ku Sani zai ce."Da sauri ta mi?e kawai ta na faWin."Ki ba ni naje na yo miki sare-sare ki fara sana'a ni fa ko me zai yi sana yi aikin nan,tunna shi ba taimakon mu yake yi ba don haka ba shi hurumin da zai hana mu."

Ta yi maza ta fice daga Wakin kafin Mama tace komai sam ba ta jin tsoron abin da zai ce in dai ba kasheta zai yi ba ta rantse sai ta yi aikin.

Kamar yadda ta gaya mata mijinta ba mazauni bane haka kuwa ta gani,don tun da ta fara aiki ba ta gan shi ba sai tan?amemen hoton su da yake manne a falon wanda tun da taje ranar da Mariya ta kaita ta gan shi a hoto,wannan dalilin ya sa hankalin ta ya kwanta ko da ta ga Baba me aiki aikin ta take yi ta tafi ba ta kwana.

Ta na aikin ta cikin kwanciyar hankali ga abinci da take ci kullum taci mai kyau ta sha mai kyau,don Anty Naja ba ta da rowa ko nama taci sai ta rage mata saboda yadda Juwairiya take kula da yaranta ga ta da tsafta ko ina na gidanta tsaf ya na tashin ?amshi.

Kusan sati biyu ta na aiki cikin jin daWi kuma har zuwa wannan lokacin Baba Sani be dawo ba,kullum in dai za ta dawo Anty Naja na sawa a yi girki da su ta saka mata a kula kuma da yawa,don haka ba sa matsalar abinci ga Wanye da take badawa a kai ma Mama in dai za ta yi aikin kwana.

Ranar Juma'a da safe bayan ta gama aikin ta ta shirya musu abincin karyawa ta ibi nasu kamar yadda ta yi mata umurni,kasancewar ta gama aikin kwana za ta yi hutu har ta bawa Juwairiya hutun kwana biyu.

A hanya Juwariya ta na tafe ta na ta yi mata addu'a don tsakanin su Allah ne kawai zai biya ta,saboda irin kyautata mata da take yi fara aikin ta ta bata kaya masu kyau sosai da abin alheri ko hijabi kala biyar ta bata,sannan ko ba?i ta yi bata ce mata me aiki sai dai tace ?ar'uwanta ta na da matu?ar kirki sam bata nuna wani abu ko rashin mutunci.

A dai-dai ?ofar gidan su ta tsaya cikin firgici ganin Baba Sani ya Ware kan motar sa ya na ri?e da ?atuwar bulala,sai juya ta yake ya na zare ido ransa a Sace da ga ganin yadda ya Waure fuska alamun ba mutunci.



Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi na bakwai.Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ?ofa a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE)

Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*



*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA BAKWAI*



Tsananin mamaki ya kama shi ganin yadda Juwairiya ta gan shi amma sai ta yi tsaye ta na kallon shi, ba tare da nuna wani tashin hankali a fuskar ta ba ko tsoro.

Ya Wan ?are mata kallo cikin mugun nufin sa amma sai ya ga duk da ramar da ta yi,ta ?ara mishi kyau Wan tafiyar da ya yi.

Juwairiya da tsaya ko zai ce wani abu amma ganin ya yi shiru,ya sa ta nufi hanyar shiga ?ofar gida za ta shige.Da dauri ya sha gaban ta a ransa ya na mamakin dai na tsoron shi da ta yi,tun ranar da ya nemi haWa jiki da ita.
"Da ga gidan uban wa kike?"
Ya tambayeta da fuskar shanu y na zare mata idanunsa da suka kaWa suka yi ja,saboda tsabar fitina da ya saka ma kansa.Ta Wan ja ta tsaya tare da matsawa nesa da shi ganin yadda ya matso daf da ita.

"Ba na hanaki yawon maula ba,shi ne don kin ga ba na nan kika mai da shi sana'ar ki?"Ya tambayeta tamkar zai kai mata bugu.

"Ni ba maula naje yi ba,aikatau na samu nake yi domin na ciyar da kammu."Ta faWa mishi ba tare da jin tsoro ko shakku a ranta ba.

Wani irin azababben mari ya wanka mata wanda ya sa ta yi taga-taga za ta faWi,amma ta dake duk da azabar da ta ji kamar za tai fitsari a tsaye sai ba ta nuna mishi ba,don a shirye take ta shirya tsaf!Ko kasheta zai yi.

Matu?ar mamaki ya kama shi wai yaushe ya yi sake har ta raina shi haka,amma sai ya ?ara Waure fuska yace."Na ga kwana biyu kin raina ni Juwairiya saboda na nuna miki manufa ta a kanki,to wallahi har yanzu ina kan baka na saina cika muradina gara ma ki amince ki sami maslaha a rayuwarki."
A wannan lokacin ta ji wasu tagwayen hawaye sun cika mata fuska,zuciyarta ta amince da lai-lai shi ba mutum bane don ta yi tunanin rasuwar mahaifinta zai saka ya ha?ura da ?udirin sa.

"Ka sani ko mutuwa zan yi ba zan lamunce ka biya bu?atar ka a kaina ba!Ina matu?ar kaico a rayuwata da ka fito a matsayin ?anin mahaifina.Ko mutuwa zan yi sai dai na mutu."Tace mishi ta na ?o?arin shigewa gida.

Sororo ya yi lai-lai ya yi sake tunna har taga wallar shi ta na faWa mishi mugayen kalamai,masu tsauri a cikin idanunsa ba tare da shakku ko shakkar sa ba.

"Tun da kika ce haka mu zuba ni dake,bari na tuna miki akan ki zan iya komai tun da kika girma na Wora kwaWayina akanki Ki kuka da kanki zan iya komai don na cimma manufata."

Ta buWe baki za ta yi magana wani irin takaici ya to?are mata ma?ogaro,sai hawaye da suka fara turereniya a fuskarta da ta tuna ?anin mahaifinta yake mata wannnan halin,sai ta ruga a guje ta shige cikin gida ta na kuka.

Mama dake ?o?arin hura wuta a murhun gawayi idanunta duk sun yi ja, suna zubar hawaye saboda wutar ta?i kamawa sai saka leda take yi.Sai ganin ta ta yi ta shigo da kuka ta shige cikin Waki ta buWe baki da nufin ta yi magana,duk da cewa ta san dalilin kukan saboda ta ji dirin motar sa sanda ya dawo sai kuma ga shi ya shigo.

"Saboda ba na nan shi yasa kika saka ta ta na yawon maula ta samo muku abinci ko?Na rasa wani hali kike so ki koya mata shi yasa na tsaneki saboda mugun halinki."
Ta yi shiru ba tace komai ba dama Wabi'ar ta kenan duk sanda zai yi mata rashin mutunci ba za ta tanka ba,haka ma yanzu mutuwar Yayan sa bai saka ta canza ba.
Har ya gama bambamin sa ya fice bata ce ?ala ba,amma ta na jin gara su ha?ura kawai da tashin hankalin da zai jawo musu.Bayan ta gama kukan ta ta share kamar kullum don Mama ba za ta taSa lallashinta ba.

"Juwairiya ina ganin a ha?ura da aikin nan kawai."Tace cikin ?unar zuciya ta na kallon ta."Gaskiya Mama sai dai kiyi ha?uri,amma ba zan ha?ura tunna shi ba taimaka ma na yake ba."

"Amma kina ganin tijarar da yake mana ko?Kin san halin shi ba shi da kirki,ni fa bana son tashin hankali ya dinga jibgar ki a banza."
Juwairiya shiru kawai ta yi a ranta ta saka komai zai faru sai dai ya faru,amma aikin Anty Naja yanzu ta fara.Hankalin Mama ya tashi da safen ranar da ta gama hutun ta bayan Juwairiya ta yi sallah ta tafi aikin ta,ba ta kula da kiran da Mama take ?wala mata ba.

Da yamma da ta dawo Baba Sani ya shigo da bulalarsa ya yi mata duka,har bata iya tashi amma ba hana washegari ta koma aikin ta ba.Ganin irin dukan da yake mata Mama ta hana ta aikin,sai dai wannan karan ta bijire ma umurnin ta don ta rantse ko kashe ta zai yi ba za ta bar aikin ba.

Tsakanin ta da mijin Anty Naja ba ruwanta da shi tun da ta fara aikin so uku ta gan shi,duk sanda ya shigo ya ga yaran a kusa da ita sai ya fara musu faWa ya kora su cikin Waki ya na harararta ya na mazurai,a yadda yake mata ta lura ya matu?ar tsorata da halin masu aiki.

Ganin haka ta ?ara kame kanta ta na mamakin yaran duk da suna zuwa islamiya amma ba su wani iya karatu ba,don ko babban dake da shekaru tara ko alhamdu bai iya cikakka bare ya damu da sallah ba,sai kallon catoon da suke yi kullum ba ?au?autawa,ganin haka ta dage da koya musu da saka su su yi salla,abin da ya ?ara saka Anty Naja son ta a cikin zuciyar ta.

Ganin ?an canjin da yaransa suke samu abin ya burge shi har yake amsa gaisuwar ta a sake,wani lokacin har kyauta yake mata na kuWi yace ta kaiwa mahaifiyarta don Anty Naja ta gaya mishi mahaifinta ya mutu.

Kusan kullum Juwairiya ta dawo sai taci na jaki a gurin Baba Sani jikin ta duk shatin duka ne,amma hakan bai saka ta karaya ba ta ci gaba da aiki don yanzu suna ci ga Mama dake sana'ar ta rayuwar su ta na tafiya cikin rufin asirin Allah sai dai takurawar da Baba Sani yake mata,wanda hakan ya na damin Mama ga shi ta?i ta dai na aikin.
A haka rayuwa take gara musu yau fari gobe tsumma,yayin da kullum burin Baba Sani ya cika burinsa amma Allah bai ba shi damar ida mugun nufin sa a kanta ba.Ganin haka sai ya Sullo mata da nuna mata kuWi ya na jan ra'ayin ta akan ta amince mishi ko sau Waya ne,amma ta?i duk ta gan shi sai ta nemi tsari da sharrin sa don ganin sa take kamar wani sheWani.

Ta Wauki tsawon shekaru biyu ta na aiki a gidan Anty Naja,a lokacin ta girma ta ?ara wayewa ga hankali da natsuwa kullum cikin hijabi take bata cirewa sai in mutanen gidan ba sa nan,ko ita Anty Naja ba za ta ce ga yanayin jikin ta ba,don tun kafin takai haka da Baba Sani ya saka mata ido ta yi tunanin ko jikinta yake ruWarsa,bare yaanzu da ta zama ?an mata ta cika ta batse ga Anty Naja da take ba ta kaya masu kyau kuma ta ba cin me kyau,har mai na shafawa da na wanke kai take siyar mata.
Maza da dama sun sha bayyana soyaryarsu gurin ta wasu kuma suje gurin Baba Sani,amma sai ya ta?ar?are yace Juwairiya ?ar mace ce sannan ba ta da kamun kai har kwana take a waje.Ya faWi mugun abu da ba ta mata suna ya gaya musu,wasu suna jin haka za su tafi wasu in suka nace ya yi musu korar kare don ya rantse,in har ba ta amince mishi ba to ita da aure sai dai ta ga ana yi ko kuma in ya mutu.

Juwariya yarinya mai kimanin shekaru sha tara.Ta na da haske amma ba can ba,fuskarta mai kyau irin zagayayen fuska gareta,da dogon hancin ta ha?oran ta masu kyau ga ?ar wushiryar ta a tsakiya,wanda in ta yi dariya yake ?ara ma kyau matu?a!Da dimful Winta.Bata da jiki amma a kwai shafe sannan doguwa ce ba can ba,amma ta na da tsawo wanda yake ?ara mata kyau.

?irar jikinta me kyau ne ko ita ta na alfahari da hakan wato irin jikin nan ne mai Waukar hankali waWanda ko wane namiji yake burin samu mace mai irin sa.Wannan dalilin ya sa kullum take cikin hijabi do ko ?awayenta suka shigo suka gan ta ba hijabi,sai su yi ta zuzuta ta su na yaba kyawun jikinta.

A wata ranar litinin da safe bayan mutanen gidan sun gama karyawa suka wuce gun aiki,kasancewar da garin a kwai zafi sannan Anty Naja ta tura mata da tsako a cikin wayarta me botira da ta siyar mata,don ta din ga kiran ta ko kuma in ta tafi aiki da wuri ta gaya mata abin da za ayi,don yanzu girkin su ya dawo hannunta saboda Baban Abnaj yafi son girkinta.
Waina da miyan karas za'a yi da farfesun rago,ganin ta na da aiki ya sa ta zage damtse ta na yi tun ta na cikin hijabi har ta cire ta na ta aikin ta,ta kunna wayarta ta na sauraron karatun kur'ani cikin suratul ma'ida.Ta shafa'a ta na ta aikin ta sai ?anwar Abnaj mai suna Ibtihal ta danna remote ta Sata saitin tibin,Abnaj Wan shagwaba ya saka kuka ya zo ya na sanar da Juwairiya akan ta zo ta gyara musu.

Hannunsa ta kama suka nufi falon da nufin ta gyara mishi,ta na tsaye a gaban tibi ta na ta ?o?arin yadda za ta gyara amma ta kasa gashi ita ba ta san yadda ake yi ba,sannan gashi har sun fara kuka akan a gyara musu.
A hankali ya buWe ?ofar ya shigo da sallama a bakinsa,Juwairiya da hankalin ta ke kan tibi ba ta san ya shigo ba,ko in ce dukan su sai bayan ya Wauki tsawon lokaci ya na kallonta cikin mamaki a ransa ya na mamakin dama a kwai wannan halittar a gidan sa?Don shi zai rantse bai taSa mata kallo ko na sakan bane ya san dai ta na da kyau a fuska.

"Oyoyo Daddy!"Abin da yaran suka ce kenan wanda ya Wauki hankalinta ta mi?e a razane ta yi diri-diri,tamkar za ta shige cikin ?asa yayin da wani irin

5 / 48