Author : Maman Teddy Category : Complete Novels
ciwon zuciya yaso yayi karfi a jikina Hajiya Dan yanzu haka zuciyar a kubure take Dan ma anyi Mata allurai Kuma Sameer yaje Abuja jiya ya kawo magunguna tunda mu a nan sun yanke mana, Kuma muna bukatarsu emergency, gaskiya ka zauna da ita a tambayeta me yake damunta da yayi cussing din irin wannan ciwon lokaci Daya Dan da alama da abinda ya tada Mata da hankali ba zato din, yanzu Shawara Daya ce akwai wani asibiti a Egypt suna da consultant cardiologist a can ya kamata a tarbi abun gaskiya".
Wani gumi ne ya tsaststafowa Hamza yasan duk abinda ya samu Mama Yana damfare da matsalar Salma sai Kuma abinda yake Mata fada a kansa ta daurawa Kai wahala akan Zahra bare Kuma da tazo taga irin daular da Allah yabawa yarinyar yasan harda wannan damuwar.
' Mun gode kwarai da gaske doctor,yanzu ka bamu address din asibitin kawai idan Allah ya yarda a cikin week din Nan sai muyi komai mu tafi"
Alhaji Jafar din ya fada cikin damuwa ya rasa me Rabi'a keso a wannan' rayuwar dai dai kwarkwado tana cikin rufin asirin Allah yasan ko banza bazata rasa kadara da zuzzurutun kudi sama da millions of naira ba tunda duk alherin daya samu matansa suna da kaso Mai tsoka a ciki.
"A'a Abba ai an Gama komai tun jiya yanzu visa muke jira naso na shiga Azaren yau sai Kuma Abdul Hakeem yace min Kuna Nan zuwa yau koma Mahmud ban fadawa ba zuwan nake saboda jiyan dare yayi".
"A'a doctor bani address maza yaushe za'ayi haka na Zama uban banza kenan,ni fatana a rike min uwata da mutumci bawai na Zama Mai idon cin naira bane, nagarta na duba naba shi bansan shi ba a lokacin duk da da wuya a fadi sunansa a fadin k'asar Nan ace ba'a San shi ba, hotunansa dake yawo da Kuma a social media da banbanci kwarar da gaske da yanayin da muka same a ciki shi babu Hadi ko Daya shi yasa bamu fashimta ba, kuyi hakuri mun gode da wannan hidimar da akayi ma ta wadatar Allah ya saka da Alkhairi".
Duk yanda Sameer yaso Abban ya fahimce shi ya nuna Sam baza"ayi hakan ba, doctor din ya Basu full address na asibitin da tsare-tsarensu duka sukayi godiya sosai suka fito Sameer yayi musu jagora zuwa dakin da aka kwantar da Mamar lokacin da suka shiga tana barki sai su Aunty Hassana da suka shigo su ganta ita da Inna mainuna su duba jikin nata kafin su tafi, sunyi mamakin ganin Abba dasu Hamza tunda ba Wanda suka fadawa sai Sameer duba da duka yaushe suka bar garin.
Gaban gadon Abban ya tsaya Yana warewa mamar kallo fuskarta da kafafunta sun kumbura harda hannuwanta, gurin sun Aunty Hassana
Abban ya juyo Yana gaishe da Inna mainuna ita Kuma ta jajanta Masa lalurar Mamar.
"Ina Hameeda da Salman suke ya jefawa Aunty Hassana tambayar dai dai lokacin da Aunty ladi ke shigowa yayar Mama.
Duk Saida daburce batayi zaton ganinsa a garin ba a irin wannan lokacin.
Cikin alamun rashin gaskiya ta Fara fadin "Alhaji kune a hanyar haka sannu da zuwa, Ina kwana?".
"Lafiy kalau ya Mai jikin?".
Jikinta da sauki gashi har tana iya barci".
Hameeda ce ta shigo da sallama da tea flasks da basket na abincin da aka kawo da dare jiya tasan ana daf da kawo na safe shi yasa ta tafi ta wanko kayan.
"Lah Abba sannu da zuwa Ina kwana?
"Lafiya kalau Hameeda ya Mai jikin kuma? Ina Salma take ku hada kayanku gida zamu tafi flight din karfe biyu zamu bi".
,Ya Abudul, ya Hamza Ina kwanan ku?".
"Lfy kalau ya Mai jikin".
"Da sauki, Abba naji kana maganar Ina Aunty Salma ai batazo Nan ba".
Hamza Abban nasu ya kalla kallon tuhuma. Cikin kaushin murye yace.
"Shin abinda magaji ya fada min da gaske ne Rabi'a tasa ka fita da Salma da Asuba ta kofar baya tana kuka?"
*_ AUREN HUCE HAUSHI _*
AISHAT ISAH MUSAH.
Maman Fateemah.
09051432330
Or
08055362975
*Page 89.
_________Cikin kid'ima Hamza ya fara rantse-rantsen babu ruwansa ganin da sameer a dakin yasa inna maimuna yin magana.
"Dan Allah Alhaji a bar maganar nan sai an koma gida nan garin mutane ne ga mai lalura tayar da maganar a gabanta baze haifar da d'a mai ido ba, ayi hakuri abi komai a sannu sai Allah yayi magani ko menene".
Cikin wani irin bacin rai Alhajin yace " shi kenan inna Allah ya kaimu gidan lafiya".
"Yauwa Amin ai hakan yafi".
Zuru-zuru Aunty laran tayi tasan idan ta tashi ba karamin ruwa aka ballo mata ba.
Da sasarfa Abban ya wuce yabar dakin su sameer suka rufa masa baya, gefe sameer ya koma ya kira Mahmud Wanda lokacin suka tashi daga barci tun bayan idar da sallarsu ta asuba suka koma yana kara lallashinta da kasheta da kalaman soyayyarsa.
Zahra na jikinsa kiran sameer din ya shigo ita ta miko masa wayar.
Kiran ya daga yana fadin " ya akayi?".
"Abban madam ne ya shigo tun wurin ten shida su Abdul Hakeem da Hamza, Amma fa yace maganar fita da Hajiyar mubar zancen biya shi ze dauki nauyin komai abunda akayi a nan ma Ala amfana".
Tashi zahra tayi tunda taji duk taji abunda suke fada .
" meu amor wai Abban ne yazo garin nan bai nemeni ba? wallahi yanzu Abba ya yayeni baya yi dani".
Sai hawaye wasu na bin wasu, wayarta ta dauko ta shiga Neman Ya Abdul Hakeem cikin ikon Allah ta same shi yana dagawa ta fara masa kuka tana fadin "yanzu ya Abdul Hakeem har Abbna yazo garin nan Amma akaqi a fada min nazo na Ganshi tunda shi bazezo yaga inda nake ba kodan ni basu Hameeda bane..."? saita karasa sakin kukan sosai ta jefar da wayar a kan gado.
Janyota Mahmud yayi jikinsa yana fadin " Haba precious meye haka Mike fada akan Abbanki kada na qara jin magana mai kama da ita daga bakinki ai Abba bai cancanci haka ba gurin marar lafiya yazo keda ba cewa akayi yabar garin ba, idan ma baizo nan ba ina cewa shiya kaiki dakinki na Azare wancen ai shine farilla na nan kuwa ai tsabar bidi'a ce kawai tashi muje na gasaki da kyau kada muje gurin Abban kina ware kafa ya gane yarinyar tasa ta girma gara idan tukuicin ya fita kowa ya gani ko ba haka bane?"
Ya fada yana dauke tears din dake gangarowa da harshensa, jin ze saki layi yasa tayi saurin barin jikinsa tana cije lips dinta saboda zogin da takeji.
"Haba Ya Mahmud kaifa malami ne ina ruwanka da irin wannan sabgar karfa dan malam yaqi halin malam naga abun nake fa Yaya ba sauki wai ka manta nifa yarinya ce"
Dariya ta bashi wallahi yarinyar nan 'yar duniya ce tun Daren jiya ta Dame shi da wani Yayan shegantaka.
Tashi yayi shima suka shiga wanka saida ya qara hada mata ruwan zafi ta shiga sannan sukayi wankan suka fito yana maqale da ita, shiya shafeta da lotion yanayi yana mata dan abinda baza'a rasa ba, ya saka hand dryer ya busar mata da gashin kanta ya gyara shi tsab, ita mamaki yake bata idan taga ya zage yana irin wannan abun kamar ba shi ba.
Clotset suka shiga ta saka Riga abaya 'yar dubai shi yayi mata rolling shi kuma ya saka wani wagambari fari tas, lokacin da suka fito har breakfast yazo daga gidan Ammi tunda ta Hana ayi musu a nan duk da jiya binta ta Dawo da gamma tunda bayan sun wuce da dare yayi waya da laminu daya daga cikin masu gadin gidan ya fadawa Tanimu ya kai yarinyar gida tunda 'yar gari ce washe gari da gamma sai ya koma ya daukota.
Suna saukowa Abincin ya zama ready yarinyar da alama ta horu da iya aiki, abinci ne kusan kala hudu sai ruwan tea mai hadin su na'a na'a dasu lemon grass da kayan kamshi. A plate daya ta zuba musu cheeps din sai kuma pepper soup din zabbi da fattira ta zuba musu black tea din.
******
Tunda Abdul Hakeem ya fara waya hankalin Abban ke Kansa saida ya sauke wayar Abban yaga yana bata rai ne ya tambaye shi.
"Me Uwar ta fada maka daya bata maka rai nan da nan haka?"
"Rabu da ita kawai Abba, shirme zata yiwa mutane wai fa kuka ta kama dan an fada mata ka shigo garin, duka da yaushe mukazo da zata fara yiwa mutane halin nata ita batasan ta gima ba, abu kad'an kuka kamar wata baby, ai yanzu kuma sai dai yaranta suyi wannan abun".
Dan murmushi Abban yayi. " yi hakuri Abdul maza kirawo min ita ".
Tana ganin kiran Ya Abdul Hakeem din tayi saurin dauka tana fadin.
" Ya Abdul Hakeem zakuzo dan Allah ".
" Ba Abdul bane uwata nine ki kwantar da hankalinki gamu nan, bawa mijinki wayar na fada masa".
"To Abbana na gode".
Ta mikawa Mahmud wayar,da kallo ya bita sam bata jira taji me zasu fada ba ta nufi kitchen taga me zata yiwa Abban nata mai sauki kuma favourite dinsa.
Suna gama waya da Abban Mahmud ya kira zayyan yace yaje ya dauko masa Hajiya Inna
Kitchen din yabi zahra ya samu tana ta kokarin hada abinci dan ma da alama wasu abubuwan an dafa su irin su nama haka nan da nan gidan ya dauki kamshi, taya ta wasu kanaun abubuwan yayi nan da nan suka gama suka hada table sannan suka koma sama sake watsa ruwa sukayi zahra na fesa turare taji wayar Mahmud ta dauki slow music Sameer ne.
Dauka yayi taji yana fadar " OK ganu nan".
"Sun karaso?".
Kai ya gyada mata ya nufo In da take tsaye.
" oya! Muje mana sun shigo ciki fa".
Hannuwansa ta rike duka biyun "nifa kunyar Abban kuma nakeji wallahi sai naga idan ya kalleni kawai ze gane".
Ai Mahmud bai San lokacin daya fashe da dariya ba saboda da iya gaskiyar ta tayi maganar.
"Wai daga jiya zuwa Yau meya hau kanji wannan yarinyar? Yanzu fa kika gama matse yan hawaye akan baizo ba kuma yazo zaki dauki kinibibin kina jin kunyarsa, yaushe ze wani gane ai ba Wanda ze dauka ba karbi sadakina ba har mukazo nan ki share kawai".
Ba zato ya janyo ta gaba daya saida tayi dan kara " oh sorry ke dince sai a hankali".
Gaba tayi ta fice daga dakin a hankali take tafiyar cikin nutsuwa dan bata fatan kowa daga cikinsu ya gane ta.
Suna parlourn farko, tunda suka dosa gidan Abba ke Hamdala ga Allah s.w.a ko yanzu ubangiji ya fitar dashi daga zargin mutane akan auren da yayiwa yarinyar nan.
Kafin ta karasa shigowa Mahmud ya sameta a hanya.
Tare suka shiga, tana ganin Abban wani farin ciki ya rufeta da dan sauri ta karasa inda yake zauna shima fara'a fal a fuskarsa fadi yake "Masha Allah uwata"
A gabansa ta tsuguna tana gaishe shi, shima Mahmud din kusa da ita ya zauna yana gaishe da Abba hannu ya miki masa sukayi musabaha dashi sannan su Abdul Hakeem ma suka taso suka gaisa, duk yanda Abban yaso Mahmud din ya tashi bai tashin ba itama zahrar da gaske nauyin Abban nata tajeji Yau Kamar wani sirikinta.
Tashi tayi ta nufi kitchen lokacin suna hira da Mahmud dasu ya Abdul Hakeem.
Binta ta tarar tana wanke kayan da sukayi aiki dasu gaishe da zahra tayi tana fadin "wlh Aunty barci ne ya daukeni bayan ma gama gyaran falukan na shigo da abincin da Baba Haruna ya kawo".
" OK babu damuwa ke kinci abincin?"
"Eh nayi mana tunda da safe nida security din kofa haka Ammi tace na ringa yi tunda na iya sosai race Amman ke Aunty zilai ce zatana yi miki".
Ok. Ga saura can na Wanda aka kawo din ki diba sauran ki fitar musu dashi, yanzu zoki tayani dauka muje can babban parlour Abbana ne yazo ganina".
" to Aunty muje" zahra ta dauka itama ta dauka suka nufi can parlourn.
"Haba uwata danmi kika wahalar da kanki haka?"..
Binta ce ta tsuguna tana gaishe Abban sannan ta gaishe da sauran ta koma dauko sauran.
" Abba abinda kakeso fa nayi maka tunda na duba naga da fresh milk ta shanu".
Ya Abdul Hakeem ne yace "to kaji Abba Biryqni rice tayi maka kaga kuwa tayi abinda bazakaqi ci ba, kinyi masa mutumin?".
Kaita gyada Masa.
Table mat Binta ta shimfida guda biyu daya Abba dayan su ya Abdul Hakeem.
Saida ta zubawa Abbanta komai sannan ta zuba musu ba karya ta tabbata rainon Ammah abinci tayi dadi iya dadi ga gas meat din Abba shima yayi dan kin cin pepper soup din sukayi sai nasan sukaci Mahmud bai wani ci abin kirki ba tunda basu Dade da yin breakfast ba kawai da dan kada taki ci ne ba dadi.
Suna gamawa zayyan ya Karaso da Hajiya inna afujajan dan cewa ba lafiya ba tunda jiya suka bar gidan kuma Yau a tura daukota.
Saida ta shiga ne kuma ta samu Salama tunda taga zahra lfy sai hira sukeyi da jama'a.
Zahra ce ta tashi tana fadin "sannu da zuwa Hajiya daga ina haka?".
" O'o daga gida mana mijinki ya tura a daukoni babu shiri wallahi nayi zaton wani danyan aikin yayi yake nemana"
Rufe ido sameer yayi tana ayyana "wlh duk jirgi daya ya kwasosu ba saiti kina sisin kwabo".
Sameer din ne ya tashi ya nufi Inda suke dan kada ta kira musu ruwa da bakinsu da babu saiti.
" Sannu da zuwa Hajiya ki karaso baki garemu saiku gaisa ko".
"To muje din ai hakan zumunci ne".
Saida ta shigo sosai taga Alhaji Jafar sai kuma ta fara fadin "ikon Allah yo ai nasan wannan Alhajin ba kai bane ka sauko dani daga kan dutsen Arfa dana hau bara waccen lokacin dasu Mustapha suka bace min?".
Dariya Abba yayi saboda ya tuno drama da suka sha a lokacin.
" nine mana Hajiya Ashe bazaki manta in ba".."
"Kai Haba shege ke mance Alheri ai nayi takaicin rashin tambayarka kai na Ina ne lokacin yo a gigice nake daka rakani gurin ma'aikatan sokoto kuma nayi gaba naga na gida a she da sauran haduwa kaima sana'ar ce ta hadaku da wannan miskilin?".
" Dan Allah ki zauna Ku gaisa sai ayi miki bayaninsa".
Sameer ya fada.
"Kai tafi can lokacin daya taimaka min kuna can kuma taku sabgar ba sai daga baya kika sani ba, shiya yasa bara nace bana zuwa ina jimamin rashin dan tagwaye tunda shine me biya min nida 'yan uwana muje,gara muje umara tunda Allah ya fito min dashi".
" Dan Allah ki zauna ku gaisa tukunna sai ayi labarin" su dai dariya kawai sukeyi tsohuwar warka ce bazake ce itace mahaifiayar milliners ba kuma kakar billionaire it's very simple and funny.
Alhaji Jafar ne yace "rabu dasu Hajiya sannu da zuwa ya akaji da jama'a?".
"Alhamdulillahi Yaya bayan rqbuwa kuma Ashe addu'ata ta karbu ai a gurin d'awafin bankwana saida nace Allah ya had'a fuskokin mu ko a daras salam ne Ashe a nan ma zamu hadu".
Zarha ce ta matso suka gaisa da Hajiyar wannan sauran suka gaishe ta.
" kai kuma haka ake sai kayi min aike haka wuta wuta duk a tada hankalina".
"Kiyi hakuri to daman kiranki nayi ki tayani rokon Abban zahra akan marar lafiyar da kukaje dubawa da Hajiyar maru itace za'a fitar zuwa Egypt to har an gama komai kawai visa ake jira sai yace a'a a bari shine nake son a bashi hakuri ya bari mu ida ladarmu, ayi hakuri Abba ba qararka na kawo ba".
" wai kana nufin shine baban zahara'u taka?".
Kai ya gyada mata "Ikon Allah kace ta gida ce ka auro yo ai ni tun ranar daya taimaka min ya zama Dana,kuje kuci gaba da aikin ladarku ni nayi izini ai Dana ne ake yiwa wasu ma bare shi ai kujerun makka na wajena duka a kaisu Azare badan babu ba a'a kyauta ce a bawa hadimai da dangi da makota kafin nazo naga guri duk da daman nayi niyyar zuwa naga masu karancin nan da suka bawa dan tagwaye mata irin wannan ga jijyarsa da kukayi bamu da abinda zamu Baku sai dai Allah ya biyaku da mafificin alkhairinsa".
" Allahumma Amin Hajiya nagode kwarai da gaske yanda kikace haka za'ayi".
Sameer ne yadan risina tana da sadda kai "to min gode Abba kenan basai kun tafi da ita ba ayi hakuri jibi ne zamu wuce sai kuma idan wani ze bimu daga baya Amma nida yayar Hajiyar zamu wuce in sha Allah"..
" kai kuje kuyi shirin Ku a banza ma dawa ake yiwa ruwa bare kuma a karkara"..
"To mun gode Allah yaja kwana".
Hira ce ta balle tsaanin Abba da Hajiyar duk yanda yaso ya yakice hirar yabar gidan taki saida suka fita sallah ne yace a fada mata zeyi mata zuwa na musamman ya bada dubu Dari uku a bata,ko zahra basuyi sallama ba sai ta waya ya kirata ya fada mata dalilinsa.
Sai dare aka mayar da Hajiya inna wuni tayi tana fadin " haba shi yasa naji kin kwanta min zahra'u Ashe da walakin goro a miya,kin taso gidan masu nagarta da saninin ya kamata".
****
Tunda Mahmud ya fita maida Hajiya bai shigo ba sai gurin Tara tunda har lokacin ya rike su sails bai bari sun koma Azare ba.
Tana shafa' da wuturi ya shigo da alama a gajiye yake sosai,wanka ya fada bai jima ba ya fito lokacin tana ninke hijabin ta fito daga gurin sallar.
Hannunsa ya bude mata ta taho a hankali ta fada kirjinsa yayi mata murfi da hannuwansa,ajiyar zuciya ta sauke jin sanyin ruwan yana ratsata.
Shirya ki rakani unguwa duk da a gajiye nake Amma gara muje kawai gobe in sha Allah babu inda zan fita so nake na zauna dake na fada miki waye ni,da dalilin daya fitar dani daga gida da duk komai nawa tunda naga alamar ko zamu shekara Dari ba tambayata zakiyi ba".
Lif tayi tana jin dadin sanyin jikinsa.
"Preciousss"..
Ya kira sunanta yana dan yawo da hannunsa a jikinta.
" Na'am meu amorrr..."
"Fada min ina kike son muyi honeymoon din mu kinga ummee tabamu ticket na qasashe uku".
Dan Jim tayi kafin tace "nafi son Qasashen middle East gaskiya bana son European countries idan so samu ne mu fara da Saudi Arabia muje Ku ziyarki Qabarin Annabin Rahama muje muyi umara kuma kaga saimu tafi da Hajiya inna ko tunda naji tana fadin zataje".
" Tab Allah ya kiyaye na tafi da ita