Advertisements
Chapter 15 Reading Auren Huce Haushi Book 3 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Auren Huce Haushi Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Complete Novels

Chapter   15 / 21

42K to 45K   out of 60.9K words

na shiga part din Abbie na sameshi shida uncle mustapha saboda tare muka shigo gidan, kiransa nayi muka fito tare kafin na kaiga yi masa bayanin komai uncle saminu ya nufomu afujajan yana fadain su dai an haifo musu masifa a cikin zuri'a daman duk namiji mai aure aure hakance ke faruwa to azo aga ga yarinya can a dakina na gama lalata da ita.
Wani wawan Mari uncle mustapha ya sauke masa yana fadin ban taba sanin kai mahassadi bane kuma masharranci sai Yau wallahi ka guji Fushun ubangiji a kanka yaushe ka zama haka haba ka rasa Wanda zaka ringa jifa da qazafin Zina sai dan zumunka kabar jaki kana dukan taiki, me yaron nan ne ya tsare maka? kullum idanunka da bakinka basa nufin alkhairi a kansa, to ka sake wata dabarar wannan batayi ba tun nagariba muke tare dashi a mabera sai yanzu muka rabu ya nufi nasu gurin Nina na shigo kiran da Alhajin yake mini,ko maganar bamu fara ba ya shigo ya kirani kafin ya kaiga fada min dalilin kiran kazo kana yiwa mutane shirme da girmanka da komai to kaddara ma abinda kake fadar gaskiya ne bazaka iya daukar matakin da saidai a wayi gari a ga ka dauka ba,amma ka zama jakadan yada munafurci da son hada husuma ka yiwa kanka fada wannan ba rayuwa bace,ka bawa shedan dama yana walagigi da kai haba meka nema ka rasa da har samun dan cikinka ze tsone maka idanu ne ayeh?.
Tunda uncle ya shara masa Mari ya dafe kunci bai kara dago da Kansa ba, bai kuma kara tofa wata ba yayi min wani kallon qasqanci yayi gaba, tsaki uncle mustaphan yayi yana fadin wahalallan banza Wanda hassada ke dawainiya dashi, gurina ya juyo yana fadin kayi hakuri Mahmud kaji babu wani Abu na batanci daze sameka in sha Allah, lokacin na fada masa safna Dana gani tana barci a bedroom dina, yayi mamaki kawai da gaske tare mukaje amma abun mamaki bata dakin ko alamar mutum ya kwanta a gadon babu, dan murmushi yayi kawai ya juya yana fadin take care.
Wallahi a Daren banyi barcin kirki ba saboda damuwa na rasa mena tsarewa uncle saminu ne yake bibiyata da irin wannan Abu na bacin suna? Sai kuma zargin da hadin bakin wani ake min wannan bita kullin.
Naso na fadawa Ammi amma saina share, amma naje har part din Aunty sameer, tana ganina ta tarbeni da murnarta asual muka gaisa kafin nayi korafin abinda ya kawoni Auntyn ta rigani da fadin kasan kuwa jiya mutuniyar a dakinka barci ya dauketa tana jiranka wai tayi maka coconut drink ta zauna zaman jiranka saida naga shirun tayi yawa na tura safara'u yarinyar da take min aiki ita ta taso ta, ai kuwa nayi mata fada sosai irin haka ai sai zargin wani Abu ya shiga dan haka nace ta saina shiga part din tunda duk maza ne, wallahi precious duk saita daureni da jijiyoyin jikina na rasa abin fada haka nan na fito daga part din nata.
A cikin satin tafiya ta samemu nida sameer muka tafi, a lokacin shares na saya a manyan kamfanin motocin duniya na zuba large share sosai a lokacin ne na canzawa kannena mata sabbin mitoci abinda ya ruda da yawa daga yara mata na family din mu 'ya'yan da iyayen sukayo min caaaa da kowa burinta ace muna tare da ita sai kuma safna ta fara fuskantar yan hamayya daga cikin dangin saboda ta saje da yaran gidan babu bambanci.
Lokacin da muka dawo ne aka fara magabar bikin Gambon mu Khadija wadda ke Germany.
Aishat ce ta bani bill na duk abinda suke bukata ni kuma na bawa sameer nace yaji dasu, sun kace raini a bikin nan dan komai unique Aishat ta sawo musu a Dubai da sukaje tunda dai kin ganta 'yar gayu ce ta bugawa a jarida kuma duk abinda ta sawo babu bambanci tare da safna tayo shi hatta da gold na mahakatan kudi saida aka sawo da ita.
A wannan bikin ne idanun safna suka bude fiye da dah, ta zama babbar yarinya tayi sabbin kawaye tunda ta shigo gari ga motor ta alfarma tana shiga ga suturu na kece raina ga 'ya'yan banki basa mata wahala.
A cikin wata hudu tayi wani irin fice a sokoto sai kuma lamarin ya zama marar tsabta ta shiga sabgar samari 'ya'yan Hutu, koda yaushe bata zaman gida ga yawan kawo samari gida barkatai, sabanin yaran gidan,dana samu Ammi da maganar ta takamin burki tace babu ruwana ai mai gidan da sauran yayuna suna gani, haka na zuba ido ina kallo amma bana jin dadin abun ko banza ina kaunar safn tunda zuciya tana son mai kyautata mata,amma dole na dauke idanuna nayi kamar bana gani mataki daya na dauka kawai na saina daina shiga sabgarta na daina tura mata kudin da nake tura mata special na daina mata komai hatta da tsaraba idan nayi tafiya na Dawo wadda sameer ke assasa ayowa yaran na fada masa a daina yi da ita, abun saiya dameta ya tada mata hankali duk yanda tasan zatayi mu hadu ma nayi blocking dinta.
Previous Ashe wannan matakin shine ze zaman mafarin faruwar Marsalar shine zaren da aka kulla kaddarar tawa dashi. Ashe shine sanadin da za'a samu sabani mai girma Wanda yasa mahaifiyata barin gidan aurenta na tsawon watanni ya dagula rayuka da yawa ya kawo sanadin da aure ya mutu murus.









*_ AUREN HUCE HAUSHI_*

_AISHAT ISAH MUSAH_

Maman Fateemah

Da sunan Allah mai Rahama Mai jinqai salati da Daukaka da Aminci su tabbata ga shugaban mu Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w.

Page 93.


_____ Precious wato Ranar wata talata 1/6 ranar da ta Zama baqar Rana a gareni da duk wani Mai kaunata, ranar da aka sak'a zaren mummunar kaddarata ranar data rikita Mana zaman lafiya ta Zama ranar da wani ko wasu suka dagula lissafin mahaifina ya Zama sai yanda akayi da shi dama duk wani Mai fada aji ya Zama soko marar katabus.
Tunda na tashi da misalin hudu da rabi na asuba yanda na Saba Sam najini a wani yanayi Sam banajin Dadin jikina ga faduwar gaba wadda da ita na tashi har nayi nafilolina na wuce masallaci gani Nan dai, sai da nayi karatun Qur'an sannan na samu relief na faduwar gaban, a ranar ko breakfast kasa fita nayi sai Sajjad autan momin Kano ya kawo min tunda Ammi Bata barin yaranta Mata shigowa part din mu ko Mai aiki Bata Bari su shigo gyaran part din ma maza ne keyi Kuma ko su zayyan basa shigowa gidan suna waje Bata hana suyi min aiki ba Amma Banda shigowa gida.
Haka na zauna Ina ta juye-juye a gado na rasa me yake min Dadi ga Sameer lokacin ana ta shirye-shiyen bikinsa a yanda mukayi ma a ranar Zan shiga Kano Dan na tura su naseer a sakawa gidan Dana Gina Masa furnitures tunda komai yazo, ban fito ba sai lokacin sallar Azzahar daga masallacin bangaren Ammi na wuce Ina Nan har la'asar tayi tambayar duniya akan meya sameni amsar Daya ce nake Bata ba komai, haka ta hakura ta kyaleni Amma itama sai Naga ta rage walwala.
Daga sallar la'asar ban dawo gidan ba Saina wuce mabera gidan Hajiya Inna a can na zauna nayi ta aikina har kusan Tara da rabi, nida zayyan ne kawai muka taho shiya tuk'o motar Sai goma muka shigo gidan saboda mun tsaya an sawo fruits saboda Dana shiga kitchen Naga sauran kadan Dan Apple da pear ma babu, ban shiga part din Ammi ba Amma na Kira su Batool nace suzo su shiga da kaya ciki.
Zayyan ya wuce Nima na shige ciki Dan har lokacin ji nake kamar Wanda aka yiwa duka, na gaji matuk'a.
Ina shigowa naji atmosphere din dakin ya canza daga daddad'an kamshin turarikan daki sai wani irin kauri marar dadin shaqa a dakin, ban zauna ba gudun A/C din parlour din na Kara na kunnu electric din da ake zuba masa turaren daki, tun a parlour na cire Kayan jikina wannan kuma normal d'abi'a tace ban fiye shiga bedroom da Kayan jikina ba idan na fita dasu Saida na cire na saka a washing machine ya Zama daga ni sai boxer short na wuce bedroom dina da niyyar nayi wanka na hada coffee na Sha tunda Ina da coffee maker a daki.
Ina shiga ba zato ba tsammani naji an rukungumeni gaba daya, sautin muryar Safna naji na fadin Dan Allah kayi hakuri,wallahi ka sakani a cikin mawuyacin Hali ka tausaya min idan ka fita a rayuwata mutuwa zanyi wallahi, Kai kadai nakeso nake muradi a rayuwata, kaji tausayi na, wallahi duk abinda kakeso Zan baka ko kaina Zan baka kaji dadi Dan nasan kana dasu da yawa Nima kazo wallahi kayi abinda kakeso Dani.
Rudewa nayi gaba Daya na rasa in da Zan saka kaina, wani abune da bantab'a zaton faruwarsa ba ya sameni bagatatan, kokarin raba jikina da nata nake kokarin Yi Amma kamar Wanda akayiwa dabaibayi a hannunsa sai Kara shigewa jikina take ga ta hade kirjinmu sai goga min jikinta take cikin kukan dana kasa tantance wane iri ne, da kyar na iya kokartawa ba juyar da ita ta tafi zata fada Kan gadona banyi aune ba naji ta fizgoni gaba daya na fada saman kanta kafin nayi wani yunguri Dan tunda na shigo na shaki warin Nan na kara rasa kuzarina, naji an kwalla ihun kuka a saman kaina, abinda yayi saving din kenan daga rikon da Safna tayi min, da sauri na mirgina na tashi, sai lokacin na Farga da suturar dake jikinta, wata rigar barci ce marar Albarka duk breast dinta a waje. Ga hawaye bibiyu na bin fuskarta gashin kanta Mai Kama da hatsin bara ta barbaza shi.
Aunty Sameera na gani ta Dora hannu a ka sai kuruwa take yi, da gudu Safna ta tashi tana wani gunjin kuka tana fadin , wayyo Allah Aunty ki taimaka mini wallahi ba laifina bane barazana yake mini Koda yaushe ya lalata min rayuwata batun yau ba Aunty na shiga uku waye ze aureni a haka.
Cikin kuka itama aunty ta Fara fadin wallahi Mahmud kaci Amanarmu Dan kana da dukiyar da bazamu iya ja da Kai ko mahaifinka ba shine zaka ringa ketawa yarinya haddi, haba Ashe shi yasa taketa rama a tsaye,wallahi banyi zatonka a haka ba, aiko kana bin Mata Ina ga ka d'agawa yarinyar Nan kafa marainiyar Allah, Kuma inda mutumci ai zaman kanwarka take Dan haka wallahi dole ka aureta tunda Kai ka Fara saninta 'ya mace bazan yarda ba da wannan cin mutuncin da tozarci.
Tunda na samu kaina jikina keta faman tsuma ga wani uban jibi Daya rufeni duk kuwa da sanyin A/Cn da yake ratsa dakin, ni dai banga shigowa ko motsin uncle saminu ba sai ganinsa nayi a gabana jikinsa na tsuma baiyi wata -wata ba ya shareni da mari Yana fadin munafuki maci Amana,to yanzu ina masu cewa karya ake maka? Sai suzo suga ta'asar da kake aikatawa da idanunsu tunda suna ganin qazafi akeyi maka, Daman nasan idan zabuwa na yawo kere na yawo wata Rana zasu hadu, nasan za'a rina munafiki wallahi kaji kunya, Zina a cikin gidan ubanka wannan masifa har Ina Allah ya Kara Basu ne da Aure -Aure ba,kadan ma suka Fara gani.
Hannun Safna Aunty Sameera ta Kama tana sharbar kuka suka fice daga dakin, saida suka wuce uncle saminu yayi wata dariya Yana fadin. Yaro baisan huta ba in Bai taka ba, ba dai kace bazaka auri Asma'u ba kadan ma kenan sokoto Nan sai tafi karfin zamanka mu zuba kasa Ido wallahi saika Zama mujiya cikin tsintsaye duk kuwa da arzikin da kake yiwa mutane d'agawa dashi dariyar ya qarayi ya Sara ya fice daga dakin. Aunty Sameera na fita part din Ammi ta nufa ta shiga Danna bell ba k'ak'k'autawa Batool ce ta bude tunda itace ke kasa tana zuba Kayan dana kowa a fridge.
Da sauri ta bude Jin kukan dake tashi daga wajen, dai dai da shigowar Ammi cikin parlourn tunda itama taji Karan door bell din da akeyi ba sassuci.
Da sauri Ammi ta karasa shigowa tana tambayar Aunty Sameera me yake fatuwa? Cikin kuka riris Aunty Sameera ta bude bakinta da kyar ta Fara fadin . Ammin Batool Mahmud ya lalatawa Safna rayuwa wallahi a gado na samesu shida ita tana ta rusa kuka da magiyar ya barta Amma abun yaci turn Ashe Daman haka yake Mata ta kasa fada sai Rama take a tsaye na shiga uku Yaya zanyi da wannan abun kunyar? Kasa ko motsi Ammi tayi haka batool ita abun Daya fi daure Mata Kai duka yaushe hakan ta faru kamar a cikin Shirin film to da yaushe ya shigo gidan da har wannan dogon labarin ze wakana har haka, Amma saboda tarbiyyar da akayi Mata yasa Bata tofa ba ta zubawa sarautar Allah Ido Amma ta yiwa abun question mark.
Innailaihi wa innailaihi raji'un, abinda Ammi ta dinga maimaitawa kenan ta kasa furta ko kalma Daya tamkar an saka padlock an rufa bakin da zatayi wani sharshi.
Uncle Saminu ne suka shigo shi da Abbie sai Momin Kano wadda ranar girkinta ne Dan a can part dinsa na bangarenta ya iske shi shine ta biyo su ganin hankalinsu a tashe.
Da ganin yanda Abbie ya shigo hankalinsa ba a karamin tashe yake ba Fadi yake Ina safnar take maza a Kira doctor innailaihi wa innailaihi ilaihi raji'un , wannan wace irin musibace ta shigo gidana?.Dan cikina ya aikata irin wannan rashin Albarka a cikin gidana, Ina Mahmud din take? Ita Ammi rasa abin cewa tayi ji tayi kamar an Dora Mata bulo inci Tara a kanta ga kirjinta yayi Mata nauyi, sahal ne ya nufi kofar fita da sauri saboda gaba daya suka fito Jin kuka a part dinsu Suma abin ya Basu mamaki Dan a gaban Sajjad na wuce Yana waya, Amma a cikin abinda Bai wuce mintina goma ba wannan kurar ta tashi, tun daga parlour har bedroom suna bude Amma bana ciki dole Sajjad ya koma ya fadawa Abbie bana nan, abunda ya Kara tada kura kenan uncle saminu ne yayi tsagal ya Fara fadin to Daman ta Ina ze tsaya yanda yayi wannan abun kunyar Zina har cikin gida duk wadda ake a waje Bata wadatar ba sai an yiwa yaran cikin gida fyade.
Nan da Nan Abbie ya Kara tunzira ya shiga fada sunce yayi fadan da Basu tab'a gani yayi ba Fadi yake wallahi babu shi babu ni ya cireni daga cikin y
'ya'yansa tunda na fita zakka naje ya sallamani gani ga duniyar Nan idan giyar kudi ke rudata Ina Dan k'aruna yake.
Jin furucin Abbie yasa uncle saminu tarar numfashinsa Yana fadin idan ya tafi ai yaci bulus a Nemo shi yazo ya aureta dole, idan aka barta a haka ai an zalunceta gaskiya saboda an fita gata, ai tun faruwar wancan abun nace maka ga Asma'u Nan na bashi Amma lokacin saika nuna ba haka ba in da anyi Masa Auren Aida hakan Bata faru ba, da ba'ayi maka halin Dan akuya a gida ba, idan kayi sake sai an Fara shigo da shegu ma cikin gidan Nan.
A cikin hasala momin Kano tacewa uncle saminu haba wace irin magana kake fada haka Bai Dace ba Dan zumunka meze Hana abi abun a hankali ita safnar yarinya ce karama da za'ayi ta babatu tayiwa mutane bayanin abinda ya faru Mana. Dan me za'ayi ta dorawa mutum Daya laifi ita meya kaita part dinsu a irin wannan lokacin ayeh?.
Cikin tashin hankali uncle saminun ya taso Mata kamar ze daketa Yana fadin.
To kice da hadin bakinki yake ketawa yaran mutane haddi kenan, Dan munafurci bazaki Bari ayi Masa hukunci ba tunda Yana kawo Miki abin duniya idan ya lalace Baki da asara Dan kishiya ne ko?.
Momi Bata barin ta kwana ta zaburo zata gaggaya Masa magana Abbie yayi Mata Karan tsaye, kofar fita ya nuna Mata alamar ta fice, zata bude baki tayi magana Ammi ta girgiza alamar tayi shiru kawai.
Ammin ma juyawa tayi zata bar gurin cikin kaushin murya wadda tunda suke Bai tabayi Mata magana da makamanciyarta ba.
Ki fad'awa danki duk inda ya shiga ya fito yazo Ina nemansa idan Kuma ba haka ba wallahi da kaina Zan Mika case din Nan human right kinji na rantse.
Yanda Bata tofa ba lokacin da suke babatun yanzun ma wucewa kawai tayi tana jiyo yanda Abbie din ke kwantarwa da Aunty Sameera murya Yana Bata hakuri ita Kuma tana daga murya, Batool ma barin gurin tayi.
Hummm previous Ashe kuka Rahama ne bansan haka ba sai a ranar, Dan naso ace Zan iya yinsa konaji sassuci Amma Ina Idanuna sun soye babu alamar hawaye sai zafin zuciya kawai nakeyi.
Tunda suka fice daga dakin Nima na zura jallabiya na dauki key nayi waje tunda na fita na rasa Ina Zan nufa nayi ta yawo a cikin gari har sha biyu da kusan minti arba'in da biyar, Dana gaji da yawo na shiga wata primary na yiwa Mai gadin gurin bayani Ina son na yada zango ni matafiyi ne, wallahi haka na kwana ko gyangyadi Bai kamani ba, ban taba tunanin haka akeji idan an yiwa mutum k'azafi ba sai da yazo kaina, ban taba tunanin Alkhairi Yana Zama mugunta ba sai a kaina da Safna ban taba hasasota a haka ba ko cikin mafarki, shi yasa hausawa ke fadin idan kaga mutum a Rana barshi a ranarsa da hikimar da tasa aka aje shi a ranar.
Bayan nayi sallar Asuba gida na nufo ban shiga gurin Ammi ba part din mu na nufa Ina zuwa dakin naji wani irin tashin hankali kamar lokacin abin yake faruwa, a parlour na zauna Ina sakawa da kwancewa na rasa tudun dafawa, wurin bakwai da rabi naji ana tab'a kofa ban motsa ba ban Kuma bada izinin shigowa ba, Faruq ne shida saif kanin Ya Abbas ne suka shigo Ina Zaune Ina dafe da goshina kaina na matukar Sara min, daga kallon farko da nayi musu ban sake daga idona na kallesu ba.
Cikin nuna damuwa Faruq ya tambayeni Wai meya faru ne jiya shi Yana barci baisan wainar da aka Toya ba, Saida Asuba sahal ke fada Masa abinda ya faru,

15 / 21