Author : Maman Teddy Category : Complete Novels
ta tafasa ban iya tofawa ba Dan bakin cikin dake ci min zuciya haka ya hakura ya tashi amsa Daya na bashi nace masa babu mutumin da ze iya yi Mana shari'a da duk Mai hannu a cikin Lamarin sai Allah.
Wurin goma Kiran Abbie ya riskeni banyi kasa a gwiwa ba na nufi part dinsa, Ina zuwa na samu Abbie ne da 'yan uwansa sai Safna da Aunty Sameera.
Ina shigowa Safna ta fara share hawaye, Abbie na fara gaishewa Wanda Ni dai da kunnena banji ya amsa ba, sai su Uncle Mustapha nayi musu gaisuwar Jimla.
Kamar jira ake Ina Zama aka Fara surfa min fada babu ji babu gani, Auncle Mustapha ne kawai ke supporting dina Yana fadin kowa ya lafa a tambayi ba'asin meya faru ne Amma babu Wanda ya saurare shi, duk yanda yaso ayi adalci a cikin Lamarin abin ya gagara, Dan har gaban Abbie mukaje zanyi Masa bayani Amma ya tashi ya bar gurin abinda ke daure min Kai yanda uncle saminu ya Zama shike bada Umarnin abinda za'ayi Dan yace aure nida Safna babu fashi haka aka tashi baran baran da uncle Mustapha inda ringa fada Yana fadin an fada musu mutane jahilai ne a tsaya ayi abinda ya kamata Mana sai a dauki son Rai a Dora ga gaskiya Amma ana neman taketa da gangan Dan wata manufa ta daban, a gaba uncle Mustapha ya sakani mukaji wurin Ammi Abu mafi bani tsoro Kinsan kallona Ammi batayi ba duk yanda uncle yayi Mata bayanin irin nasa hasashena wallahi Sam ta nuna Bata bukatar jin komai daga bakina haka muka fito Ina rangaji ga Abu goma da ashirin ya tare min inda nake tunanina Zan samu tallafi da tausaywa sai Kuma na Sami aka sin haka, Bari nayi Miki taku ta Mata a lokacin fa kakana Alhaji sa'id ya rasu, nasan da Yana Nan abun baze Kai haka ba.
Kiran sallar da aka kwalla shi ya tsayar da Mahmud da dogon labarin da yake bawa zahra, kallon fuskarta yayi sai ganin hawaye yayi suna bin kuncinta Bai hanata ba ya dai gyara Mata kwanciya a cikin jikinsa duk da lokacin sallah yayi.
AUREN HUCE HAUSHI.
Maman Fateemah.
09061432339
Or
08055362975
Page 94.
_______ "Pls previous ki daina kukan Mana, abun Nan fa wani past event ne ya Riga ya wuce kawai dai Ina fada Miki irin Qalubalen Dana fuskanta ne a rayuwa da Kuma irin yanda na koyi iya mu'amala da jama'a Kinsan masu iya magana na cewa na daka baiyi kallon waje ba, to Nima hakan ce ta kasance dani da ba'a Sami wannan matsalar ba da wata kila harna koma ga Allah bazan San wasu abubuwan ba na yanda wasu suke rayuwa, previous na koyi darasin rayuwa yanda bakina baze iya misalta Miki ba, tashi muyi haramar sallah idan Allah ya kaimu wani Daren saina karasa Miki sauran labarin dan nasan daga safe har zuwa dare babu lokacin Zama kinsan Hausawa sai a slow su da gidan Amarya".
Ya fada Yana dariya itama duk da zuciyarta babu Dadi Saida taurmusa.
Tare sukayi wanka ya wuce sallah itama ta Fara nafila kafin a tayar.
Har gari yayi haske Bai shigo ba itama azkar tayi da karatun Qur'an, tana kokarin cire abayar da tayi sallah ya shigo, a hankali ya tako har inda take tsaye Yana zuwa ya Ida cire Mata Yana Fadin. "Meya hanaki barci? dubi idanunki barci ne fal a cikinsu da gani".
Dan narke fuska tayi tana Masa wani kallo, dan smile yayi Wanda yake karawa kyakykyawar fuskarsa kyau.
"Yaya ko da labari? Nasan jirana akeyi ko kuma gaisawa zamuyi ne?".
Kafada ta make irin yanda Yara masu kiwa sukeyi idan suna hannun iyayensu.
"Nifa Karatu nayi fa shi yasa ban kwanta ba gara na rabauta da Alkhairin dake cikin safiyar".
"Gaskiya ne sayyada". Ya fada Yana dariya, itama murmushi tayi, sunyi barci har kusan Sha biyu sannan suka tashi wanka suka shiga tare sun Jima sannan suka fito suka shirya ita cikin rigar material data Sha beads work shi Kuma cikin shada geezner boda style sai baza kanshinsu suke yi. Lokacin da suka sauko su Aunty zilai suna kitchen ita da binta suna girkin rana, fitowa sukayi suka gaisa sannan suka koma bakin aikinsu, bayan sun Gama break din ne suka dawo second parlour inda Mahmud ya dauki remote control ya canza Tasha daga Tauraruwa zuwa sport news inda ake highlight na kwallayen da akayi. Kasa hakuri Zahra tayi ta jefa Masa tambayar da take ci Mata tuwo a kwarya.
"Meu Amor Wai Dan Allah me kikeji idan kana kallon Ball din Nan?".
Dan kwantar da kansa yayi a gefen kafadarta Yana shaqar kamshinta Wanda yake sakar Masa da kasala.
"Yanda kukeji idan Kuma kallon series ko Kuna karanta novels Dan nasan daidaikun mata ne basa wannan sana'ar, Dan Batool har kwace wayarta na Sha yi lokacin tana secondary, to muma haka muke Jin Ball a cikin ran mu".
Jin jina Kai Zahra tayi tana farin "Na gane yanzu kam, ai karatun novel duniya ne Dan Idan book ya dauko Dadi wallahi bana kaunar abinda ze tasheni daga karatun".
Wata sinsina ya yiwa wuyanta tare da hura Mata iska ba kunne, hade jikinta tayi tana nuna Masa bangaren kitchen da Hannu.
Ido Daya ya kashe Mata. To Nima hakan nake Jin kwatankwacinsa akan Ball din".
Sun jima a gurin suna Hira har aka Gama labaran Ball din. Baki ne suka Fara zuwa danginsu na Dangen shuni Mama Bilkisu ce tazo Bata k'asar akayi bikin nasa, da gani sunyi saboda dashi sosai har yaranta, mace 'yar gayu ta ajin karshe ga sakin fuska Dan kamar ta goya Zahra sai fadin Masha Allah takeyi Nan da Nan aka cika gabansu da Kayan tarbar Baki Dan Aunty zilai expert ce a wanna fannin.
A cikin hirar da sukeyi ne Zahra ta gane suna k'asar Canada Latin America ita da yaranta inda mijinta yake ambassadorn Nigeria, Mahmud Bai samu fita ba sai lokacin sallar Azzuhar sannan ya samu ya shiga gari can family house nasu, Nan suka yini da Mama Bilkisu mace ce wadda tasan kanta Dan Mahmud na fita bayan sunyi sallah sunyi lunch taja zahra bedroom dinsu na kasa ta zaunar da ita ta ringa koya Mata dabarun yanda zata rike mijinta ita wani abun idan ta fada sai kunya ta rufe zahrar ita kuwa babu ruwanta sai dai tace ki dai Kade kunne ki kwashe a gaba ze amfane ki, sai kusan magariba suka tafi Zahra ta saka Aunty zilai ta hada musu Kayan biki masu yawa sannan ta bawa 'yan matanta designers din turarika da Dubai abaya tunda kamar gorinsu akayi a gurin kayansu, da kyar Mama Bilkisu ta yarda suka karbi Kayan Dan fur cewa tayi sunyi yawa sai an rage Saida Aunty zilai ta saka Baki ta barsu suka karba.
A nan falon sukaci gaba da Zama suna hira sai lokacin magariba su Aunty zilai suka wuce part din su ita Kuma Zahra ta koma sama, har akayi insha'i Mahmud Bai shigo ba, Zahra na Zaune ta tsula gayunta cikin English wears maroon Mai duhu tayi rolling da farin veil touching din dake jikin coat din sama ta saka maroon din lipstick a Dan bakinta Sai tayi wanu irin kyau kamar ka dauke ba b'oye tana fesa turare wayarta ta dauki kida Mai dadi da sauri ta nufi wayar Kiran na magaji ne, tunda ringtone dinsa shima daban.
Sallama tayi Masa Bai Sami damar Amsa sallamar ba ya Fara fadin.
"Allah ya sauwak'e wallahi idan mutum neman taimakon emergency yake a gurinki Allah Saiya mutu, bakiga missed calls dina ba sun kai dari ina ga, tunda zafin abun nake nemanki Amma ba amsa na Kira oga yace min tun Rana baya gida haba ki daina nesa da waya ai abokiyar Hira ce ko Dan kina tare da Aunty zilai ai kin Gama samun abokiyar hira".
Katse Masa zubar da yake tayi.
"Haba Dan Allah ayi mutum idan ya Fara magana ba comma ba Full stop. Ka fito a mutum sak ka fada min abinda zaka fada ba kayi ta Jan dogon labari ba".
"To yau dai ana idar da sallar la'sar Abba ya rangada daurin Auren Salma da Hameeda Dan yanzu haka Salma har sun dira a Miya, can Aka kaita wani tsohon saurayinta ne Ma'aikacin Nefa da yake yawan zuwa gaida Abba kusan duk sati duk da basa tare da ita shine yazo jiya suna bin gidaje raba bill din wuta, Abban yayi Masa tayin Auren salmar Amma fa Saida ya fada Masa gaskiya idan ze iya yace babu komai Yana so a haka. Yaje ya fad'awa magabatansa, daman an fadawa gidansu mai son Hameeda suzo da sadaki shine ya daura musu Auren yau yace a tafi da Salma gobe kayanta zasu biyota, taimakon da Allah yayi Mata Abba ya Basu gida a can Miya din tunda yana da gidajen haya a garin kuma kwanaki akayi modernizing dinsu. Ita Hameeda ce aka bashi hakuri zuwa wani satin ta tare tunda mijin baya Nan Yana kaduna gurin aiki, to kinji fa abinda Zan fesa Miki kike min surutu, yanzu haka Ammah dasu Aunty Hassana da Hajiya Turan gidan maji dadi suna can, ki Bari kawai saina shigo da labari wallahi buhu-buhu Zan shigo in zazzage Miki su ai anyi dai abun kunya wallahi Ashe duk lullubin biri aje yiwa mutane ai Ni Ya Mahmud ya Gama min komai kindsan bibiyar Salma yasa akeyi Masa Ina gida jiya ya kirani yace min sunyi magana da Abba Zan raka bilyan gidan malam Jos, Ashe asibitin da aka kwantar da Salma ya tura ya daukota Ni Kuma da nasan gari nayi masa jagora wallahi sanda ya kirani ya bani address din asibitin Nasha mamakin me zamuyo wannan asibitin ke........"
Wayar taji an zare daga kunnenta da sauri ta juya Dan kamshinsa ya fada Mata shine Amma koda Wasa bataji sanda ya shigo ba.
Wayar ya duba yaga magaji ne kunnensa ya Kai wayar Yana fadin "ka Adana sauran bayaninka zuwa safe".
Ai kafin ya Gama fada Magani ya kashe Kiran Yana rike bakin Al'ajabin Zahra Daman Yana Nan ya zage yana ta an tayo magana. Wayar ya aje yadan matsa baya Yana Kare Mata kallon ta burge shi matuk'a Dan ji yayi kamar ya sakata gaba yayi ta kallo, hannuwa ya bude Mata alamar ta shigo ya rungumeta, sun Jima a tsaye Saida yaji kamar kafafuwansa Bazasu iya daukarsa ba sannan ya Dan zameta suka zauna a gefen gadon, da kyar ya tashi ya shiga wanka Bai wani Dade ba ya fito ya saka Riga armless da wandonta three quater na Adidas dai tunda sune best kamfaninsa gurin sport wears, tana makake a jikinsa suka fito parlourn farko na sama In da aka aje musu dinner dinsu, sakwara ce da miyar Agushi sai black tea Mai Kayan hadin star anise a ciki, Saida sukaci abincin sannan suka dawo cikin parlour na biyu suka zauna duk ya kanainaye ta ya hanata sakat, nema yake ya ruda Mata lissafi ita Kuma Alla Alla take dare yayi ya karasa Mata labarinsa.
Saida ya mila ya mile Dan kansa ya Dan ragewa kansa zafi sannan ya fara fadin "Bari muci gaba ko" Kai ta gyada Masa Dan ita kam ba baka sai kunne.
"Wato precious Naga gararin rayuwa kowa fa juya min baya yayi babu Mai saurarena sai uncle Mustapha da Batool kawai, abin baqin cikin Wai a tsaya nayi bayani ma abun ya faskara ta ko Ina babu sauki a haka Muka kwana uku idan Kika ganni lokacin Zaki tausaya min a lokacin dukiya ta dai batayi min amfanin ba tunda Bata Hana an wulakqanta ba, a ranar na hudun na tsunci maganar Wai a ranar za'a daura mini Aure da Safna abunda ya yamutsa min lissafi kenan cikin tashin hankali na shiga wurin Ammi wallahi precious Ina shiga Ammi ta Mike tabar parlourn da sauri nabi bayanta Ina hadata da Allah akan ta tsaya taji gaskiyar abinda ya faru Amma kinsan me tace min?
Wai fa cewa tayi inje inyi abinda nake so tunda karana yakai tsaiko gani ga rayuwar Nan tunda fasadi na zaba duniya tafi Dan bagaruwa jima, wallahi a lokacin ji nayi kamar na mutu na huta nakeji,ga wani irin Abu da nake jinsa a jikina, precious wallahi Addu'oin da nake na azkar lokacin da kyar nake yinsu,Dana fito mabera na nufa naje yau dai na fada mata halin Dana tsinci kaina a ciki tunda nasan Bata San wainar da ake toyawa ba, Amma kinsan abun mamakin da tashin hankali itama sammankal duk abun iri Daya ya Zama Bata saurareni ba karshe ma maganganu ta yarfa min masu zafi ga shi Daman wani Abu na min sukuwar sallah a cikin kaina, Nan da Nan naji wani bacin Raina ya qaru ban baro gidan ba Saida naci alwashin saina Bata mamaki kuma kozan mutu saina nemoki duk inda kike a duniya Kuma a dakinta a gadonta Zan Fara saninki 'ya mace, kadafa kice Wai bani da masaniyar inda kike hummmm a'a ana bibiyar min ke ciki da waje, kinga lokacin Dana fito daga parlourn Hajiya Inna ko takalmi kafata babu banbi takan motar Dana shigo ba na Fara tafiya a kasa wani Abu Daya bani mamaki a lokacin precious wallahi Ina ganin kamar mutane basa ganina tunda konaje kusa da mutane bana ganin alamar sun San da mutum a kusa dasu gani ba boyayyan mutum ba, haka na dosa wata irin tafiya tamkar kad'ani akeyi kuma tafiyar wata iri ce Mai cin dogon zango a cikin lokaci k'alilan a cikin abinda Bai wuce minti arba'in ba ni dai sai ganina nayi a talatar mafara na fuskanci mutane suna ganina a lokacin Tunda Ina wuce Ina Jin ana fadar bawan Allah ko daga Ina? haka na dinga tafiya wlh ko gajiya banayi Dana baro cikin gari naji kamar Ina Jin barci na kwanta a wurin wata bishiya, to Ni dai daga lokacin bansan kuma Yaya akayi ba ni dai nasan na farka na ganni a asibiti ta tare da Abubakar wlh nayi zaton ko sokoto na dawo sai Kuma Naga bakin fuska su Malam Abu mafi daure Kai ganin Abbanku da nayi sai Lamarin yafi karfin Dan karamin tunanina na wancen lokacin Dan nasan wannan abun wani connection ne daga Allah Daya hadani dasu yasan abinda nake rokonsa dare da Rana, precious nayi dawafi a dakin Allah na Kai mutane suyi min Addu'a akan wani Abu da nake nema duk a kanki Dan Ubangijina kadai yasan yanda ya jarabci wannan zuciyar da soyayarki tun Baki San meye soyayyar bs, Kinsan Kuma shi maji rokon bayinsa ne Kuma mafi tausayin masu tausayi mafi jinqan masu jinkai Naga Ijaba, bana inkari da lamarinsa Amma na Kara samun yakin Dan Rahamarsa ce ta lullubeni ya kawo Habib ya ganni a wancen lokacin, ga wata sabuwa Ina Jin maganar mutane Amma Ni Kuma bana iya magana, lokacin na shiga tashin hankali ba kadan ba Dan ji nayi na koma mutummutumi, asibiti sunyi iya abinda zasu iya suka sallameni Baba malam da Abban ki su suka dunga Fadi tashi akan lafiyata Dan abun babu dadin ji na shiga wata irin rayuwa lokacin na Kara gane mahimmancin lafiya da tasirin Addu'a, su Habib su sukayi jiyyata a dakin soro na gidan malam har Allah ya bani lafiya, lokacin ne Abubakar ya fada min ai aikin da yake komai na tafiya dai dai, dan dai lokacin kina syprus to Nima ganin nesa tazo kusa saina nemi gurin Zama naje Bauchi nayi duk abinda ya kamata akan layikan waya da dasu system da credit card na bank da duk abinda ya kamata banyi kasa a gwiwa ba na Kira Sameer da Bilyaminu muka zauna dasu a dakin Dana Kama a hotel, Abu na farko Dana Fara shine kad'a musu warning akan inda nake kada naji kada na gani duk da Sameer ya fada min hankali fa ya tashi na barina gida gashi uncle saminu ya assasa daura min Aure da Safna, banji komai ba nasan suda ganina ba Nan kusa ba ko zan waiwayesu ba lokacin ba, aiki na bawa Sameer na Nemo ma'aikatan wata ngo's suzo mu zauna Ina son muyi aiki dasu a zahiri Amma ba sune zasu ringa harkar kudi ba, kinsan k'asar mu indai Zaki bada budi to kome kike nema kin samu Nan da Nan suka shigo muka Fara aiki Ni Ina gefe Sameer ne oga, ba Saina Baki labari ba Kinga yanda makarantar Baba malam ta Zama, ke kuma a can syprus din bamu barki sakaka ba sai Dana tura Omer ya shiga jikinki a can ya Zama idanuna ya Kuma yi Miki tayin soyayya sai akayi Dace kince Masa a'a sai dai kuna mutuncin da ta Kai ko siyyaya kikayi shi yake biya koba haka bane? Kuma 'yan Nigeria sai ake Baku wasu kudin scholarship daga wata kungiya MMD anyi haka? Ke naki yana ninka na sauran kunyi bincike kun rasa gano meyasa hakan yake faruwa haka ne? Kai kawai Zahra ta gyada Masa Dan ya kasheta da mamakinsa, cheeks dinta ya shafa a hankali Yana Mata smile har dimful dinsa ya Dan lotsa kadan Kinsan Allah da ban Aureki ba ina ga hummm.... Allah dai ya kyauta da dai Kam.. za'a Sami matsala Dan inaga maza biyu Zaki aura Dan Ni dai bazan hakura ba to sai Ubangijin Daya dasa soyayarki a zuciyar ya ta kaita al'amuran, Kinsan Muneeb Dan yayar mummy Badi"a ne?".
Wani kallon warrr tayi Masa na nuna mamaki, ban gane ba kasan shi kenan?.
Bar wannan maganar ta wuce sirrina ne bazakiji yanda aka haihu a ragaya ba, Sameer ne ya Zama Dan leken asirina duk yanda kaso aji wani Abu Sameer yaki fadin komai shima nunawa yake Yana zuwa ne Koda hasken da ake samu a Kan tafiyar tawa, Kuma duk abinda nake yiwa Hajiya Inna nace ya Dora Dan a Dan tsakanin jininta Saida yayi mahaukacin Hawa har Egypt sukaje da Uncle Mustapha da Mama mainuna surukar Aishat Ina da masaniyar komai Dan hatta bill dinsu na Asibitin Ina daga can nayi komai abinda ya darsa zargin Sameer yasan inda nake a zuciyar uncle Mustapha.
Sameer ne ya kawo min labarin Ashe lokacin Dana bar gida Batool rikicewa tayi a gidan ta Hana kowa zaman lafiya ta Fadi