Author : Maman Teddy Category : Complete Novels
Kansa kiyi ta addu'a idan shi Alkhairi ne a cikin rayuwarki Allah ze kawo sanadin haduwarku ya Kuma saka soyayyarki a zuciyarsa kinji, ki share hawayen ki wane gata ne Allah baiyi Miki ba? Da har Zaki Bata hawayenki a banza idan so cuta ne ai hakuri magani ne".
Duk Jikin Insiyya Sai yayi sanyi tasan duk abinda salbiyyar ta fada Mata gaskiya ne gara tayi addu'ar idan da Alkhairi Ubangiji ya fita sanin ta inda connection din ze hadu.
Salbiyya ta Jima tana kwantarwa da Insiyya hankali, tare da kawo Mata misalai na yanayin rayuwa da zamantakewar aure da irin qalubalen da ake fuskanta a irin auren da take kokarin saka kanta a cikinsa, kafin su kwanta da yake ita ke hidimtawa Insiyyar a Nan.
Karfe hudu na asuba alarm din da mahmud ya saka ya fara Kara, a hankali ya Mika hannu ya dauko wayar ya kashe, bedside lamp ya kunna harkenta madaidaici ya haske su. Zahra na kwance a jikinsa tayi lif da ita tana sauke numfashi cikin salama, dabin su na jiya ya tuna da kyar ta yarda dashi akan babu abinda zeyi mata, Dan Saida ya riga ta barci ma sannna ta saki jiki tayi nata barcin.
Sai kusan biyu da rabi ya farka ya ganta ta shige jikinsa kamar yanda suke barcinsu normal,sleeping dress din ya Kama ya janye 'yar igiyar da ake daurewa ta sunce ya zare a Hankali suka Sami body contact ya saka blanket ya rufesu, Yana kunna wutar itama ta farka a mamakance take Masa wani kallo ganin ta ba yanda ta kwanta ba, da sauri ta rarumo blanket din tana kokarin rufe saman jikinta da yake bude muraran, wuf ya saka hannu ya rike Yana Mata kallon k'asa-k'asa. "wallahi kina tufewa labarin ze canza salo Bakisan "I will eager to show you...ba ki barni na samu relief mana."
Ya fada tana Kai hannunsa inda yasa ta wuntsila gefe ba shiri tana kankame jikinta, Dan ya shammace ta Bata taba zaton haka ba.
Dariya yayi ya mike Yana fadin "matsoraciya kawai duk saina cire wannan kunyar dai Naga alama bazata Bari a kularwa da Malam dansa yanda ya kamata ba, gara na rabaki da ita kowa ya huta,kema ki Fara aikin Lada". Binsa tayi da Ido tana mamakinsa Dan da gaske ta yarda maza kunyarsu ragaggiyace wallahi.
Toilet ya shige yabar Zahra tana rarraba idanu kamar na shege a rabon gado.
Harya fito Bata motsa daga inda take a kudundune ba.
Da alama wanka yayi, kusa da kanta yazo ya tsaya Yana mamakinta sosai. wani smile ya saki Yana ayyana shifa yana ganin gara ayita ta Kare kawai duk yanda yaso a samu sirrin yayi hating din abinda akeyi a duniyar Hausawa Wai dole a washe gari sai Baki sunzo gidan Amarya sunga kwakwaf, to amma shi hakurinsa da ya Kare duk yanda yaso ya Dan daga Mata kafa saboda jama'a abun nema yaje yaci tura. Dan jiyama Saida yasha magani, to gara yasan abunyi da wannan shagwababbar yarinyar, ya kamata tasan Allah Daya ne, duk da yasan itama tana bukatarsa a yanda yake gani a cikin idanunta, yasan kawai tana zulumin yanda abun ze kasance Wala Allah tana karanta irin novels din Nan tana Jin yanda take kayawa a irin wannan dareren shine dalilin da yake d'aga Mata hankali.
Jallabiya ya zura ya Zuba turarensa, sannan ya dawo ya Dan cire rufar daga fuskata. "Tashi kiyi sallah kada guri ya kure Zan wuce masallaci". Dan mirginawa tayi tana kokarin tashi Bata zata ba yayi Mata daukar jarirai ya nufi katafaren toilet din dakin da ita tana ta magiyar ya sauketa amma yayi Mata fumfurus Saida ya dangana da ita cikin bathtub wanda ya cika Mata da ruwa Mai maraifaicin zafi sannan ya dire ta, Ganin Yana kokarin cire jallabiyarsa yasa ta waro idanunta tana Masa duban rashin fashimta.
Gira Daya ya dage Mata Yana murmushin data kasa tantance Kona menene "Ba.. ba.. masallaci zaka tafi ba Naga kana kokarin shigowa".
Girgiza Mata Kai yayi "na fasa fita yanzu wankan Zan sake kinsan bana gajiya da Wasan ruwa".
Bata San lokacin da dariya ta kubce Mata ba Jin yana fadin Wasan ruwa kamar wani small kid.
Ita dai batayi aune ba taji mutum a jikinta, duk iya magiyarta bai rabu da ita ba saida ya gamsu yanda yake so sannan sukayi wankan tare karshe shine yayi musu limanci a gida.
Sun jima suna Addu'oinsu sannan suka koma suka Kwanta Dan Shima barcin yakeji ba kadan ba.Amma Saida ya yamutsata iya yanda yake so Dan kirjinta Banda zogi babu abinda yakeyi da ba inda bakinsa Bai Kai ziyara ba Saida ya tabbatar ya Fara goge Mata hadda sannna ya saurara Mata ya sakata a jikansa kamar wata 'yar baby.
Wurin goma da rabi karar Kiran wayarsa ya tashi zahra, Mika hannunta tayi ta dauko wayar sai taga MY FIRST LOVE na yawo akan screen din wayar, wata faduwar gaba ce ta ziyarceta har wayar ta yanke bata dawo hayyacinta ba, wani Kiran ne ya sake shigowa cikin barci yaji special ringtone din Yana kadawa da sauri ya tashi sai yaga wayar a hannunta tana masa wani kallon tuhuma wayar ya saka hannu ya karba tana daf da sake katsewa ba tare Daya tanka Mata ba.
Yana daga Kiran ya tashi ya nufi kofa ya fice daga dakin. Baki a sake zahra tabi bayansa da kallo tana ayyana "wata sabuwa inji 'yan caca,wacece haka wadda har baza'a daga kiranta a gabanta ba? Harta koma ta kwanta sai kums ta tashi kamar wadda aka tsikara ta nufi kofar ta fice itama daga ita sai rigar barcin Wadda ta fito Mata da ilahirin surar jikinta muraran irin silk din nan ce kijinta ya fito muraran a ciki yayi irin cikar nan, wani yawu ya hadiye babu shiri..
*_AUREN HUCE HAUSHI_*
*AISHAT ISAH MUSAH*
(Maman Fateemah)
09061432330
Or
08055362975
Page. 84
.......".Good Morning Ammina". Abinda kunnenta ya Fara cin karo dashi kenan Yana fad'a lokacin data fito da azama idonta ya rufe da kishi ganin sunan da yake yawo a Kan screen din nasa, sai Kuma tayi turus taji wani irin sanyin Rahama Yana saukar Mata a cikin zuciyarta, dan ita kanta Bata San tana da irin wannan kishin ba sai yanzu da taga wasu kalmomi dake nuna mace aka alaqanta dasu, da sauri ta juya zata koma tunda babu wata tazara Mai yawa a tsakanin su, ita dai ba zato taji ya saka hannunsa Kan cikinta ta baya harga Allah batayi zaton ya ganta ba kuma Bataji tafiyarsa ko dan Valentino silifas din dake kafarsa masu irin laushin Nan ne, mannata yayi a jikinsa ta baya Yana cigaba da wayarsa ji tayi yana fadin. "Gata nan lafiayrta kalau Bari na Bata ku gaisa da 'yar taki Naga alamar Nan gaba duk tawaye zakuyi min tunda Naga kin damu da ita da yawa kamar an ce Miki Zan gutsiri Naman jikinta".
Wayar ya saka Mata a kunne Yana Kara kanainaye ta Yana shafa ruwan cikinta a Hankali.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, Ammy barka da Asuba".
Zahra ta fad'a cikin nutsuwa duk da jikinta yana karbar sakon da ake aika masa.
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, barkamu kadai diyata ya bakunta Ina fatan babu damuwa dai ko?".
A kunyace zahra tace Mata "babu komai Ammy na gode".
"To Masha Allah haka ake so, Allah yayi Albarka".
A zuciyarta ta Amsa da "Ameen".
Wayar ya mayar kunnensa yaci gaba da magana da Ammin nasa inda taji tana fada masa ga masu kawo musu break nan.
Taso ta zare hannunsa daga kan ruwan cikin nata Amma yaki Bata wannan damar falon saman ya shigo dasu ya zauna kan two seater ya dorata a cinyarta yayi Mata irin rungumar Yara har ya Gama wayarsa da Ammi dinsa.
Kallonsa tayi tana dan marairaicewa "pls ka barni nayi wanka kaga Ammy tace Baki sun taho kar ace min kazama fa"
Bakinta ya saka yatsarsa ya Dan zageye lips din Yana fadin "waye zece Miki kazama ai ke ko Zaki shekara bakiyi wanka ba babu Wanda zega kazantarki kinsa kuwa baiwar da Allah yayi Miki?".
Dan far tayi Masa da fararen sexy eyes dinta tana Masa wani kallon da yake susuta shi tana kokari barin Jikin nasa, tashi yayi tsam da ita Bai koma bedroom din da suka kwana ba, wani taga ya nufa da ita, ita fa sai yanzu taga yanda tsarin sama ma yake tamkar wata fada.
Bedroom din da suka shiga tsaruwarsa ta Kai matuka tamkar a gidan duniyar za'a dauwama, bakin katafaren gadon ya zaunar da ita yana fad'in "Ga master bedroom dinki Nan Idan munyi break zamu zagaya kiga gidan naki ki duba kiga ko da abinda beyi Miki ba Sai a canza ko".
Security dinsa na gidan ya Kira kafin su shiga wankan ya fada musu idan yaran da zasu kawo abinci sunzo a fada musu su aje a dining room.
Sun Bata lokaci gurin wankan Dan da gaske mahmud so yake ya budewa 'yar gidan nasa Ido kafin a shiga daga other room.
Dan Saida ya yamutsata yanda yake so sannna ya saurara mata dan harta saddaqar ita Kuma a toilet abun ze risketa sai taga ya basar ya rufe idonsa, yana sauke numfashi da sauri da sauri, ya rigata fitowa Dan da gaske ji tayi wani irin nauyinsa ya mamayeta yanda ya sawa idanunsa toka tasan ranar da Mai abkuwar zata afku sai gyarawa Allah Dan Bata hango abin da sauki ba.
Daure da Dan madaidaicin towel pink ta fito Bata gansa ba a dakin sai kamshinsa da dakin yake zubawa, lotion din Aveeno ta dauko ta Fara shafawa tana mamakin wasu abubuwan da yake ajewa da suka danganci cosmetics kusan saita samu abinda take amfani dashi ba kamar perfumes dinta wannan ko kuskure babu.
Wani ubansun lace ta saka marar nauyi kalar peach Mai shegen kyau tsada riga ce T bubu da straight siket, ta hade gashin tasa Masa band sannna ta kafa daurin da 'yan Mata ke yayinsa, Sam Bata Saba da yinsa ba shi yasa da tayi yayi Mata wani irin kyau ba kadan ba, bedroom din ya shigo tana cikin saka Karamar sarka a wuyanta, karasowa yayi ya karba Yana saka mata Yana sanye da T-shirt Fara tas da sai Dan karamin tambarin bakin zare da gefen hago saitin zuciyarsa da bakin trouser na kamfanin Herme's yana Zuba mayataccen kamshinsa na ibada, Kansa ya kwantar a gefen wuyanta Yana shakar Wani fitinanan kamshi dake fita a bayan kunnenta da wuyanta.
"Previousss..."
Ya fada Yana saka hannunsa cikin rigarta Yana shafa shafaffen cikinta, dif wuta ya dauke Mata wuta maimaita Kiran sunanta yayi a saitin kunnenta Yana Dan busa Mata iska a ciki.
"Umhumm".
Ta amsa Masa a takaice.
"Zo muje kina da Baki 'yan uwan Ammi ne Wai yanzu zasu koma akwai masu komawa makaranta".
Kai ta gyada Masa tana Dan zame jikinta daga jikinsa ta dauko madaidaicin gyale ta Dan rufa, sai tayi masa wani irin kyau na musamman, Kara matsota Yayi ya saka hannunsa ya zagayeta a jikinsa Yana hade bakinsu.
Saida yaji tsayuwar na neman gagarsu sannna ya saurara mata ji yake tamkar ya hadiyeta Dan soyayyarta da take zalzala a zuciyarsa, a Kan sofa ta zube tana mayar da numfashi, Dan ita lamarinsa na yau Yana neman yafi karfin Dan karamin tunaninta, Shima da kyar ya saisaita kansa dan da gaske in dai zasu wuni tare tofa da ranar Allah ze iya bude aiki.
Saida suka dawo cikin hayyacinsu sannan suka nufo kasan Dan Lamarin nasa sai kallo ya badawa idanunsa kwallin rashin kunya duk ya hanata rawar gaban hantsi Ina wallahi ada idan akace zeyi haka zata iya rantsewa da Allah bazeyi ba saboda yanda take ganinsa ba ruwansa Dan bawan Allah Ashe dai a wannan fannin ba mumini,kowane kurtu ma duma ne, ga wani tsare gida da taga Yana yinsa a cikin gidansu taga har manya suna shakkarsa.
A hankali suka ringa saukowa Yana rike da hannunta Yana Dan murzawa kadan kadan duk yanda taso ta zame hannunsa yaki sakin nata Kamar wadda zata guje Masa, ita ta rasa wace irin fitina ce ke dawainiya dashi yau yi yake kamar ze hadiye ta
*_ AUREN HUCE HAUSHI_*
AISHAT ISAH MUSAH
(Maman Fateemah)
09061432330
08055362975
Page 85.
............. A haka suka jero suna tafiya sunyi wata irin dacewa ta ban mamaki Dan kyaune ke dukan kyau kwarjini ke dukan kwarjini, suna nufo down stairs din ta ringa jiyo maganar jama'a da alama suna da Dan yawa, a haka suka ratsa parlours biyu suka nufi na farko, sai Dan satar kallon gidan zahra takeyi Dan da gaske gidan ya razanata a yanzu sabida Bata taba kawo da ire irensu a cikin kasar ma Baki Daya, suna dosar parlourn ta hangi harda manyan mata, taso ta kwace hannunta Amma dan tahalikin nan yayi mirsisi ya doje har suka shiga, a qalla sun Kai mutum bakwai harda wadda sukaje Azare da ita.
Direct gurinta ya nufa Yana amsa gaisuwar da Yan matan ke Masa, kusa da Hajiya zuwaira yaso zaunar da zahrar Amma ta noke ta zauna daga kasa Kan carpet tana gaishe da manyan yayin da sauran kamar sa'anninta da wadanda ta girma suka gaisheta. Radeeya ce ta dan matso tana fadin. "Aunty zahra Ammi tace a fada Miki idan an jina za'a turo Miki da house maid dinki".
Kaita kyada Mata kafin tace "na gode madallah kiyi min godiya'.
Sun yi musu nasiha sosai kafin su tashi Daya daga cikin matan na fadin "Mahmoud yaushe za'a kawowa su Alhaji ita su ganta".
Dan shafa Kai yayi Yana Dan murmushi kasa kasa.
"Zamu zo in Sha Allah idan mun dawo daga tafiya".
Dago Kai zahra tayi Jin ya ambaci tafiya, wai shi baya gajiya da yawo ne saboda Allah.
Har gurin mota suka rakasu suna musu fatan sauka lafiya, sai da suka fice daga gidan sannna suka juya Yana mak'ale da ita, directly dining room suka nufa wasu mahaukatan food warmers ne kusan guda biyar sai tea flasks biyu da saura cas musu kyau. Tashi mahmud din yayi yana fadin "taso muje ki nuna abinda zamu dauko a kitchen".
A yangace ta tashi hannunta ya sarkafo cikin nasa Yana Dan sinsinar wuyanta suka nufi kitchen din, duk abinda ake bukata ta dauko shi da kansa ya wanke su a sink Yana Mata hirar tare zasu ringa abinci saboda baya son abinci masu aiki.
Abinci ne kusan kala biyar funkaso yace ta zuba musu tare da kunun gyada Wanda yaji kwakwa da Madara, sunci sun koshi sannan suka tashi ya Taya ta suka kwashe kayan da sukayi amfani dasu. Da suka koma parlourn Basu zauna ba lungu da sako na gidan ya shiga nuna Mata ba karamin mamaki zahra tayi ba Dan ko a mafarki Bata taba tunanin rayuwa zata kaita irin wannan gurin ba, kallon mamaki take binsa dashi Amma ya fuske ya nuna kamar baisan abinda take nufi ba, dakin da suka shiga ne yayi muguwar tafiya da imaninta, dakin Yara ne akayi Masa wani decorations masu kyau da daukar hankali ga wasu irin Turkish furnitures child size masu azabar kyau hatta shelves din dake cikin wani kamar Dan dakin glass a bangaren da katayi Dan karatu child size ne, ga colours din purple da pink ne sai ya bada wani yanayi Mai kyau a dakin, Kara shigar da ita Yayi jikinsa yana da shafar abinda yake tsone Masa ido a Hankali.
"Yaya me za'a Kara ko a rage banji kinyi comment ba fa tunda muka Fara zagaya gidan naki ko Bai Miki ba a canza Miki wani? Ga Kuma dakin babies dinmu fa yayi ko a canza musu tsarin?".
Kasa magana tayi Dan hannunsa ba karamin dagula Mata lissafi yakeyi ba ga Wani numfashi da yake sauke Mata a gefen wuyanta.
"Pls talk to meeeee..zMana kinyi shiru,Bai Miki ba ko?".
A kasalance ta furta "komai yayi fa Allah ya Kara budi ni amma fa gidan Nan tsoro yake bani yayi min yawa".
Wata shafa ya yiwa saman cinyarta Yana fadin "Ai kuwa Saida kiyi hakuri duk gidajenki haka suke wasu ma sun fishi girma so nake ku wataya keda yaran mu a Hankali Zaki Saba Kuma me kike tsoro gani gaki ai ta maganar tsoro ta wuce Kuma".
A Nan ma Saida ya tsotseta tas sannan suka fito yana rike da hannunta, suna dawowa kasa Baki suka Kara zuwa 'yan uwan momin Kano ne da su Aneesa dole tasa yabar gidan bayan sun gaisa da bakin.
Direct gidan Ammi ya wuce a gurin Abbie ya yada zango sun Jima suna Hira kafin ya nufi bangaren Momin Kano suka gaisa sannna ya shiga gurin Hajiya Babba itama ya gaisheta taso ta tsare shi da surutu sai Allah ya taimake shi aka Kira wayarsa ya fice da sauri.
Bangaren Amminsa ya nufa Yana shiga parlourn farko yaci karo da su Batool sun Shirya Wai zasu gidansa suka gaishesa Suka wuce, shi Kuma ya shige Yana gaisawa da jama'ar da suke cikin sauran parlours din.
Bedroom din Ammi na kasa ya shiga Bata nan sai Hajja da jama'arta wasu nata Shirin tafiya bare yaran cikinsu saboda makaranta da sallama ya shigo,da wani malalacin kallo Hajjar tabi shi Yana gaisawa da Hajja karima 'yar uwar kakansa uwa Daya uba Daya tana Dan tsokanarsa irin na jika da kaka.
"Kai kuma me Zan gani haka daka fito gari da wadannan kayan Wai bakasan yanzu ka manyanta bane ba?".
Wata dariya ce ta kwace Masa Yana Zama kusa da Hajjar tare da riko hannunta. "kikace menene? To meye laifi Dan na fito a haka su wadannan ba kaya bane?".
Harara ta watsa Masa "Dan Allah rufe min Baki Ina wasu Kayan mutunci a Nan gida cike da jama'a Dan ma surukan naka suna can sabon gininka da kayiwa tawaye kaki zama, Dan Allah kaje ka sake wasu kayan kada ka shigar musu a haka da wannan Kayan kamar ka roko".
Wata yarinya ce kamar sa'ar su zahrar jikar Hajja karima tace "Haba Hajji ai hakan shine gayu kinsan kudin kayan da suke jikinsa kuwa wallahi saisu saye duk kayan cikin trolley dinki" .
"Karbi Nan sa'ada ai