Advertisements
Chapter 14 Reading Auren Huce Haushi Book 3 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Auren Huce Haushi Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Complete Novels

Chapter   14 / 21

39K to 42K   out of 60.9K words

Haroon ya sauke su da abinci da gurin kwana Mai Rai da lafiya, lokacin Yana ambassadorn Niger a k'asar Rasha sunzo hutun karshen shekara ne suka baro Yamai suka shigo gaishe da dangi Allah ya hadasu, sunga karamci da kyautatawa mutane ne masu karki kamar me, Ishaq a gurinsa ya zauna suna ta Hira a Nan yasa su 'yan Nigeria ne, zainab da wata yarinya suka shigo musu da kayyayakin abinci, tunda ta shigo Abbie keta binta da kallo ita Kuma taqi yarda ta dago saboda taji yanda idanunsa suka yawo a jikinta, serving dinsu zata Fara Abbie yace ta Bari suje kawai saboda yaga yanda abokanen tafiyarsa biyun suke kallonta duk sai yaji ya damu,washe gari ma su suka kawo musu break fast sai kusan goma na Rana sannan masu gyaran suka kawo motar har gida,sunyiwa Alhaji Haroon godiya sosai Dan hanawa yayi su biya ko sisi na gyara sannan yasa akayi musu fulltank na petrol a motar.
Har ciki suka shiga suka gaishe da Hajiyar sun taso zasu tafi Hajjar ta Kira zainab tace tazo suyi sallama Kamar zata fasa kuka ta fito tana sadda Kai kasa da gaske mutumin Nan dodonta ne, daga gefe ta Dan tsuguna tana gaishe su.
Ya ishai ne ya dubeta Yana fadin kunyarwa takeji da take sadda Kai kasa kamar tana gaban sirikinta.
A haka su Abbie suka fice a waje sukayi musanyar number da Ishaq sannan ya karbi ta Alhaji Haroon Wanda suke Kira Abu.
Har suka koma sansaninsu Abbie na makale da tunanin zainab haka yayi ta fama da ita a cikin zuciyarsa har tsawon kwana uku Amma Kullum sai sunyi waya da Ishaq da Alhaji Haroon Ambassador a ranar cikon na hudu ne ya kasa daurewa ya dauko mota da ordily dinsa Daya suka biyo Sahara zuwa cikin gari.
Sam Alhajin Haroon baiyi mamakin ganin Muhammad ba Dan yasa da walakin goro Miya yanda yake kiransa da yanda yake tambayar su zainab yasa da wata a kasa, Yana zuwa baiya kwauron Baki ba ya fito da bukatarsa ta son Auren zainab inda Kuma ya fad'awa Abu shi Mai iyali ne har buyi a fada Mata idan ta amince zata iya aurensa a haka, Basu bar garinba Saida magana Mai karfi Dan ana tambayar zainab din ta rufe fuska, dariya Hajja tayi tasan za'a rina ita tun ranar da suka hadu a Sahara tasan akwai abinda Allah ya hada Dan taga yanda kowannensu ya nuna da suka had a Ido to abinne na zamani baka zakewa.
Cikin Kankanin lokaci sukayi wata irin shakuwa ta ban mamaki tamkar sun shekara suna soyayya sai yaji tamkar Bai tab'a son wata 'ya mace ba a rayuwarsa Dan yanda yake Jin zainab daban ne da yanda yaji a matansa na baya, kafin wani lokaci zainab sunyi sabo da Hajiya Inna ta waya Kuma kusan kowa a cikin family yasan Muhammad Dange zeyi Aure a Niger Dan tuni manya sun shiga maganar babu Bata lokaci akayi biki Daman ta hada karatunta tun shekarar data wuce, Shima suka dawo gida tunda an samu kwanciyar hankali a yankin da ake fama da tarzomar.
A lokacin ne Abbie ya Gama katafaren gidansa da Kuma wadan da ya ginawa 'yan uwansa duk da kowa ya Kama kasa a lokacin Amma samun ba Daya bane, da yawa Yan uwan Babansu Wanda suke uba Daya sun dawo sokoto kowa Kuma Allah ya saka Masa Albarka a cikin nemansa sai dai sa'id da yaransa sun Zama zakarun gwajin dafi a cikin Families din Dan babu Hadi ko alama tazarar da nisa tamkar Dangote a cikin zuri'ar Alasawan koki ta Kano haka misalin yake a zuri'ar DANGE da iyalan Alhaji sa'id din.
A lokacin Abbie ya dawo gida sokoto da aiki shine musabbabin da momin Kano ta dawo sokoton itama duk abin Jin dadin rayuwa an tanada a gidansa Nan Dan ko daga waje kalli gidan ka Kara kallon komai na furnitures ya zuba Amma dole yasa aka cire wasu Dan iyayen zainab sunce sai sun Mata nasu jeren an kawo Kaya na garari Wanda suka tada hankalin kishiyoyinta da farko ce musu akayi irin 'ya'yan buzayen Nan ne masu yawo suna neman sadaka ya gani a sansaninsu 'yan gudun hijira,Amma ganinta da 'yan uwan ta da irin dukiyar da aka Zubar sai Kuma jiki yayi sanyi Baki ya mutu tanadin wulakancin da akayi tanadi za'ayi ya kau.
Zamane aka Zubar na kishin mimmuge ba fada a zahiri Amma akwai 'yar kasa daga gurin babbar gidan wanda da wuya mutum ya gane lokaci daya, gashi Hajiya Inna da Alhaji sun dauki son duniya sun dorawa zainab, Shima Mai gidan wanda take Kira da general yake Mata wani mahaukacin so Wanda baya iya boyewa a gaban kowa gashi tayiwa sauran zarra a gurin komai na auratayya sai abun ya Zama biyu.
Ba laifi sunyi amarci sosai Dan Saida ta dauki kusan wata shida suna cin amarci sannan ciki ya bullo Mai wata irin fitinar son kasancewa da miji dole tasa ya dauketa ya tafi da ita wani course da zaya a South Africa abinda yaso ya tada hankali a gidan sai da yayi Jan Ido da kurarin duk wadda bazata zauna ba kofa a bude take sannan aka Samu zaman lafiya.
Ya fada Yana Dan Jan tsinin hancin Zahra "kinji yanda Muke muna ciki dan haka dole ki shirya tunda ba rago Kika aura ba tin a ciki ya Sami energy kinsan duk Inna tawa ta bani labarin nan?".
Rike Baki Zahra tayi "har wannan Kuma?." "A'a ba direct ta fada min ba fa cewa tayi Wai cikin rashin hakuri ya sakata, Saida na tambayi Hajiyar makwarari ta fada min kinsanta ita handsfree ce"..

Kina ji Saida sukayi wata uku suka dawo lokacin cikin watansa shida kuma tun a can a asibitin da take zuwa ante-natal clinic suka fada Mata twins ne mace da namiji Amma Tayi shiru ko Mai abun Bata fad'awa ba saboda abune cikin duhu kada ta fada yazo Kuma a samu akasin hakan, lokacin da suka dawo suka samu momin Kano ma tana fama da nata laulayin ciki wata ukau a watan da suka wuce ta Sami nata itama.
A Nan sokoton ma sun fada mata, da watan haihuwa ya Kama Hajiya Inna da kanta tazo ta saka zainab gaba lokacin baya Nan yaje wani aiki Lagos ai kuwa kwana biya da daukarta cikin dare nakuda ta tashi suka garzaya asibiti a cikin ikon Allah kafin asuba ta haifi yaranta biyu murna gurin Hajiya Inna Kamar ba'a tab'a haihuwa a gidanta ba, kafin gari yayi haske suka koma gida kafin wani lokaci gida ya cika da jama'a bare da abun shima uban gayyar yasha mamaki da Inna tace masa Yara biyu ne Sam cikin beyi wani girman azo a gani ba.
Ranar suna anyi hidima 'yan Niger sunzo tamkar a Niger mai jegon take yaran sunci sunan Aishat da Mahmud, sun Sami Alheri Kamar me Hajiya Inna ta Hana su Hajja zuwaira su tafi da zainab gida dole suka hakura suka tafi ita Kuma taci gaba da wanka a gidan innar har tsawon wata biyu,Saida Alhajin ya gaji yace Mata Wai bazaki mayar Masa da matarsa ba sai hakurinsa ya Kare kice yayi rashin kunya, ke ba bahaushiya bace ko wannan cika daren da yakeyi a gidan nan Bai isheki ki gane matarsa yake So ki bashi ba,dubi fa tamkar baya da wasu matan.
Inna Bata jaba tayi Mata abinda ya kamata ta mayar da ita.
Ranar data koma suka Bata girkinta Amma Saida Inna ta karo Mata da yarinya bayan masu aikinta.
Kafin wani lokaci yaran sunyi bulbul sunyi kyau Kamar ba twins ba, suna wata hudu momin Kano ta haifi Faruq .
Haka haihuwa ta budewa Ammi tayi gambon 'yan biyu Khadija Mai suna Inna ana ce Mata Nur wadda ke Aure a Germany wadda kukayi waya jiya tana kukan ba'a fada Mata ba Dan tana da tsohon ciki.
Sai Baool da suhailat kin sansu sai su Jamal da Auwam suna london secondary.
Mu dawo baya lokaci da za'a yaye mu Hajja ta dauke mu duka badan Inna taso ba ta hakura, da kyar Aishat tayi sati hudu aka dawo da ita saboda kuka takin cin abinci Kuma, Ni kuma naci gaba da Zama a can har na Kai minzalin sakawa a makaranta Abbie yaso na dawo Amma Alhaji Haroon ya Hana yace in dai makaranta ce za'a sakani wadda suke yin turancin ingila hakan Kuma akayi ban baro Niger ba Saida Zan tafi junior secondary school inda aka kaimu Nigerian Turkish a Abuja nida Aisha da Faruq.
A can na hadu da Sameer ajinmu Daya da farko fada mukayi dashi sai Kuma rashin lafiya ta kamani shi da Faruq sukayi jiyyata a sickbay, tun daga lokacin Kuma muka dinke dashi,sai lokacin muka Kara shakuwa da Faruq mutane suyi ta mamaki idan Yana ce min yaya Mahmud sabida suna ganin ya fini garin jiki ma.
Har muka Gama secondary muna tare da Sameer, lokacin da muka dawo gida gaba daya mun Gama makaranta lokacin muka Sami Abbie ya Kara Aure ya cike ta hudu, mace ce wayayya Aunty Sameera 'yar Minna ce Niger state bazawara ce da yaranta biyu na mijin baya Wanda ya rasu, sai kanwarta Sakina wadda ake Kira da Safna, lokacin bazata fi shekara Sha uku ba haka yarinya ce Mai saurin sabo Dan bamu fi sati biyu da dawowa ba muka shaku da ita sosai tamkar mun shekara Bata jin nauyin fada min komai saima Ina kwabarta gata da son kashe kudi Nan da Nan zata rokeni kudi, banajin komai saboda kirki Aunty Sameera Amma Ina ganin bekenta gurin tarbiyya gaskiya saboda ita'yar social life ce.
Lokacin Dana tashi zuwa Niger taso ta bini na hanata har gurin Abbie ta Kai karata nace masa bazanje fa da ita ba dole ta hakura.
A haka Muka share kusan wata hudu a gida ana ta processing na admission din mu inda Abbie ya hada harda Sameer ya Samar Mana a Oxford university ta London inda Aishat suka Bata physiology Ni Kuma business administration inda Sameer yayi Accounting, anan muka hadu da Mutuniyarki Dr Haseenah inda ita Kuma take medicine 'yar abokin Abbie ce tun haduwarmu ta farko ta ringa nuna min sign na soyayya Ni Kuma saina basar saboda Sam Bata cikin tsarin irin macen da nakeso, faruq sun bashi pharmacy haka mukayi ta karatu babu Kama hannun yaro ga Kuma Mr Johnson a gefe Yana kula damu, ba kowace semester ba Mike zuwa gida Muna level two hundred ne Akayi bikin Aishat Dan Kanwar Abbie na biyu Kinsan shi ya Abbas lokacin shima Yana PhD a Nan Auren Aishat ya taimaka Mana kwarai da gaske Dan abubuwa da yawa sunyi min sauki tunda Ina da gurin da inda zan aje abubuwana safe.
Idan anyi hutu ban fiye zuwa Nigeria ba sai idan Hajiya Inna ta matsa,a kwai zuwan da mukayi nida Sameer nayi mamakin girman Safna ta Zama budurwa sosai, lokacin hatta abincina ita take dafa min Bata gajiya da Yi min hidima Saidai idan ban bukata ba haka mukayi ta rayuwa idan na dawo mu dinke idan Ina can muna waya Idan na samu sarari, muna shekarar karshe ne munzo hutu lokacin na Dan Fara gwada business zamuje Istanbul ganin wasu Kaya da nayi magana da kamfanin ta website dinsu a ranar na Fara ganinki keda Abba kina Masa tabara da girmanki Wai Baki son seat din da kike kinfi son saitin window, kin tuna wani yazo yace Miki kije gurinsa ki zauna shiya zauna a naki gurin Yana sanye da facemask?".
Gyada Kai tayi alamar ta tuna "to nine".
Gyara Zama tayi tana kallonsa "shifa wancen yaro ne ba kamarka yake ba".
"Kin jini da yarinya to ke lokacin Yaya kike?"
Zan nuna Miki hoton ki gani, Kinsan a ranar Saida Sameer ya biku tunda yaji Abban na fadin Jordan zai kaiki hutu shi Kuma ya wuce saudia.
Sameer na biye daku har Saida ya tabbatar da inda kujene sannan ya dawo mukayi abinda zamuyi muka wuce London, haka muka ringa juyawa karatun da Dan kasuwanci.
Wani hutun da mukazo harda Aishat mukazo lokacin tana da cikin farko na yarinyar data Haifa ba rai.

A hutun ne Ubangiji ya bude min kofar nawa arzikin Dan Ina sokoto uncle Ishaq ya kirani a waya yace min ga condensed milk Nan wani abokinsa yayi order dinta Kuma kafin ya Kai kasuwa wasu Kayan nasa da sukafita mahimmanci suka shigo shine yake son ya sayar dasu a tsaye shine ya bani rancen kudin idan an sayar na maida masa da kudin.
Kamar wasa aka kawo Madarar da Sameer muka shiga kasuwa muna yiwa mutane talla kafin sati Daya gaba Daya ta kare sai Kuma costumes ta ko Ina ana booking dink Kayan nan da nan uncle Ishaq din yayi magana da kamfanin suka saya lokacin harda powder milk yayi order shi yazo har Nan sokoton ya Kama min store sai daga baya Alhaji kakana yayi ta fadan Dan me za'a Kama hayar store Alhalin gasu Nan kamar banza hakuri uncle Ishaq din ya bashi yace saboda kada abun ya Zama fitina shi yasa Amma idan kudin sun kare ba za'a sake ba.
Kafin wani lokacin abubuwa sun bungasa Kota Ina kudi shigowa suke Nan da Nan jari yayi karfi na ban mamaki, da kyar muka koma london saboda kasuwa ta kankama.
Cikin ikon Allah muka Gama jarabawar lafiya muka tattaro muka dawo aka Dora daga inda aka tsaya, lokacin su Aishat suka koma India da zama.zuwa lokacin munyi wata irin shakuwa da Safna komai ta nema take zanyi Mata tunda kudi dai Allah ya hore,da taimakon uncle Ishaq muka dunga fita kasashen duniya sawo Kaya da bada aiki a kamfanoni.
Kafin shekara biyu Ni kaina bazace ga abinda na mallaka ba lokaci Daya saida muka bude kamfanoni a cikin gida da manya manyan stores na Kayan abinci yawanci a states din mu na arewa muka Fara muke diban yaran mu na gida muke Kaiwa suna aiki sayar da Kayan mukayi musu tsarin kamar makaranta Dan harda Mai gadi idan suka dawo daga sallar insha'i Kuma ba Mai fita Saida lalura saboda yanda zamani ya Zama abinda ya Zama.
A cikin shekara ta hudu ne komai ya fito Dan lokacin ne aka bude kamfanin riguna abaya a Dubai da materials da laces na garari aka bude na jewelry a India sai wasu Kuma a China wallahi precious Ni kaina bansan ta ina na samu wannan dukiyar ba nasan dai condensed ce sanadin.
Kinsan har lokacin Sameer Yana bibiyar min ke duk inda kikayi makaranta Ina da masaniya ke har korar masu son Aurenki gaskiya mune Abu daya ne bamu da Hannu na yaron Nan Dan uwan momin Kano shi ne dai bansan inda aka haihu a tagayar ba.
Wata zabura Zahra tayi, janyo yayi jikinsa.
Wata ranar lahadi Ina Zaune a gurin da aka tanada Dan hutawa Ina ta faman aiki saiga Safna ta nufo inda nake da system a hannunta, tayi kwalliya sosai tunda Ni kaina nasan Ina Mata hidima Dan duk abinda na bawa kannena to tare nake Basu da ita Dan irinsu kudi ma saina Bata sau biyar ban Basu sau Daya ba.
Sannu Tayi min tana zama daf Dani har breast dinta Yana Dan tabani, ta tashi daga gurin nace Mata saita shagwab'e fuska tana fadin Dan Allah na barta ta zauna kusa Dani wani Abu Zan nuna Mata, kamar rufin Baki saina kasa musa Mata cikin Jin Dadi ta furta Thank you dear.
Wani website ta shiga ta Fara nuna min wasu tsala-tsalan sarkoki na gold masu Azabar kyau tana fadin na tayata zabe Wai Aunty Sameera ce zata saya Mata Wanda zata saka tanar bikin kawarta 'yar ministern Albarkatun kasa, ba zato mukaji salati daga bayanmu da sauri na juya sai Naga kawu saminu Yana tafa hannu Yana fadin wane irin rashin mutumci ne haka da yammacin Allah wata'ala na shigewa yarinyar daba muharramata ba irin haka Ashe Nima lalataccen ne.
Saboda bakin ciki ko kallonsa banyi ba na dauki wayoyina nayi gaba, ko akan wani bana son a jefe shi da kalmar Nan bare Ni a kaina.
Ina gurin Ammi sai gashi ya biyoni Nan muna Zaune ya shigo Yana huci Yana fadin har yaushe nayi arzikin da Zan wulakantashi Yana min magana kada na lalata yarinya tunda giyar nera na dibata shine nayi tahowata na barshi ga banza.
Hakuri Ammi ta bashi ya juya ya fice Yana kananun maganganu.
Fada sosai Ammi tayi min lokacin tace kada ta Kara Jin makamanciyar irin wannan magqnar a gidan Nan idan son yarinyar nake ayi magana ita Bata son kananun maganganu, na fada Mata babu wata soyayya a tsakaninmu da safna.
Abu kamar ya wuce da dare saiga Kira daga Abbie a waya naje Yana nemana.



AUREN HUCE HAUSHI

AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateenah

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Page 92.






_______Ba bata lokaci na shigo mota ni da Abubakar muka nufo gidan ban shiga dakin kai tsaye ba tunda naga kusan takalman mutum biyar, ina nan tsaye saiga uncle mustapha ya fito yana waya saida ya gama ya karaso inda nake tsaye yake tambayata meya farau tsakanina da safna ban rufe masa komai ba na fada masa duk abinda ya faru, girgiza kai yayi kawai cikin bacin rai yace na koma kawai ba saina shiga ba, haka na juya ba musu na nufi mota muka fice daga gidan, ni dai bansan yanda suka kaya ba tun daga lokacin wata magana bata kara tashi ba amma na janyewa safna sosai sai abinda baza'a rasa ba, amma dai ban fasa yi mata hidima ba duk abinda zanyiwa su yaran gidan babu bambanci da ita wani abun ma sai nayi mata ban yiwa su Batool ba tunda Aunty sameera samunta bai kaina su Ammi ba tunda suna business sosai ita da momin kano.
Wani sabon salon da safna ta dauko kuma na zuwa part dinmu wai zatayi min gyara ko kuma ta dafa abinda tasan shine favourite dina ta dauko ta kawo min, nayi nayi ta bari amma saita ringa min magiya akan ita bada wata manufa ba takeyi, wannan yawan shige min din da tajeyi saiya kara mana shakuwa da kusanci sosai har ya kasance wata rana Dana dawo da dare na sameta tana barci a dakina sai abin ya daure min kai na juya na futa daga dakin

14 / 21