Author : Maman Teddy Category : Complete Novels
dakin Nan yanzu dai ba kyaleki zamuyi ba tunda babu idanun kunya".
Shigowa tayi tana fadin. "Alheri ya dawo Dani Mai gayya Mai aikin ne na rako dungurungun Dan haka kema tattarko ya naki ya naki Mai gurin yazo".
Wani irin Ras zahra taji, Ita fa abun Nan ya Fara Bata tsoro Wai me yasa a baya Bata jin haka ne Sai yanzu? turo kofar da yayi ita ta datse Mata tunanin data fada.
Shine Cikin shigar shadda sky blue sai walkiya take tamkar a matse Mai a jikinta ga wani ubansu kamshinsa na dindindin Daya kashe na kowa a dakin.idanunsa yana kanta wani irin azababben kyau tayi Masa Ganin ya shagala da kallonta kada a saki layi a gabansu sajeeda yasa tayi magana.
" Yallabai barka da dare, ya hidima? Allah ya Sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya da zuri'a d'ayyuba. To zamu tafi gata Nan Zan baka Amabarta a karo na biyu, kamar wancen karon, kaji tsoron Allah a Cikin zamantakewar ku ka tsare Mata mutuncinta a da Basu San waye Kai ba, Amma a yau ko baka fada Mana ba mun gani da idanunmu, nasan bestie zata iya fuskantar hari daga masu burin samun matsayi irin nata a gurinka, ko ba'a fada ba tunda a Dan kwaramniyar bikin Nan naji views din Mata da yawa a kanka. Gata Nan Bata da kowa a garin Nan daga Allah Daya halicceta sai Kai daka kawota,ka zamar Mata bangon da zata jingina dashi ka zamar Mata suturar da zata Kare Mata martabarta, kada ka cutar da ita Dan girman Allah Zahra marainiyar Allah ce duk da Bata rasa komai na gatan gidan duniyar Nan ba Amma tana bukatar samun nutsuwa tunda a can akwai 'yar kasan da ake soya Mata Aya a tafin hannuwanta ba tare da an ankare ba Saida tafiya tayi tafiya, Allah ya amintar dake bestie a Cikin gidan Aurenki ya Baki kariya irin wadda yake Kare bayinsa salihai da ita, ya amintar dake kamar yanda ya amintar da Annabinsa Ibrahim A.S daga wutar Namaruzu. Dan Allah kiyi Masa biyayya ki rufe masa sirrinsa kinji, Allah ya Baku zaman lafiya Mai dorewa ya kauda muku fitina"..
Sai Kuma muryarta ta Fara rawa, sai hawaye, da sauri ta nufi kofa ta fice. Zahrar ma share hawaye take haka Amatu itama idanunta sun cicciko da hawayen,Shima Dan gogan tunda yarinyar ta Fara magana yaji kamar ta Dora Masa bulo inci Tara a kansa, ya yarda kaunar precious da yarinyar Nan ta gaske ce babu algus a cikinta saboda yayi wani Abu Wanda ya gaskata hakan, Dan ranar Daya bijiro Mata da maganar soyyyarsa dan Karamin hauka sajeedar tayi Masa da kyar ya fahimtar da ita cewar gwaji ne yayi Mata ba Wai da gaske yake ba, duk da haka Saida ta nuna Masa kada ya karayi Mata irin haka za'a iya samun matsala.
A can main parlour kuwa abokan angone tare da kawayen Zahra sai wasu 'yan Mata na family din, tun a can ya fada musu Bai Hana zuwa sayen Baki ba Amma babu Mai shigar Masa dakin barci babu Kuma Mai Kara gane Masa Mata Ganin gurin dinner ma Ala amfana.
Yasha caccaka gurin friends dinsa yayi kunnen uwar shegu dasu shine dalilin Daya saka yayi amfani da kofar baya ya hauro stairs din shi kadai.
A Nan su sajeeda suka Sami su Khadija dasu Aneesah da sauran mutanen, Tajuddeen ne ya taso ya nufi Amatullah yana fadin. "Daman kina sama duk Kiran da nake Miki bakya amsawa?".
Dan bude hannunta tayi alamar babu waya a gurinta.
Jinjina Kai yayi suka nufi waje.
Addu'a sukayi aka shafa sannan kowa ya fito da wata Leda Mai shegen kyau a hannunta da alama kyautar girma ce daga bangaren anguna.
Saida suka fito sannan salis ya Kira mahmud Yana fadin .
"To yallabai ango mu zamu wuce asuba ta gari".
Wani Abu mahmud din ya fada Masa ya fashe da dariya wadda ta janyo Hankalin da yawa daga mutanen gurin Yana fadin. "A'a kayi zamanka wasu har sun Fara ficewa daga cikin gidan ka duba time lokacin yaja da yawa".
Tun bayan fitar su Amatu zahra tayi tsilli-tsilli, sai taga yau ya Kara Mata wani kwarjin da girma gani tayi kamar ya cika dakin, numfashi ma neman tsaya Mata yayi wallahi wani irin Abu take gani a cikin idanunsa.
Yana sauke wayar daga kunnensa ya nufo zahrar Yana sakin tsadadden murmushi, ya Dan tsuguna a gabanta ya saka hannu ya dago fuskarta wadda hawaye ya bata.
"Ya salam!"
Ya fada Yana Zama kusa da ita, tafin hannunta Daya Sha lalle ya rike Yana Dan matsawa kada dayan hannunsa ya saka ya zare Alkyabbar daga kanta Yana karewa fuskarta kallo, be tab'a Jin ya gaji da kallonta ba shi dai ya yarda Allah ya jarabcesahi da wata irin soyyaya a kanta shifa ji yakeyi ko baze kusanceta ba ze iya rayuwa da ita har iya rayuwarsa.
Wani irin kanshi ne ke fita daga jikinta na musamman ba Wanda ya Zama constant ba a'a an samu Karin wani na musamman a Jikin.
"Welcome to Dange's house Mrs Mahmud Muhammad Dange, Alhamdulillahi bini'imatihi titummus salihat, Fateemah Allah yayi Miki Albarka yau gaki a gidan Mahmud Kuma gidanki da Zaki rayu a cikinsa ki dasa Mana bishiyar Zuri'armu a cikinsa ta girma ta yadu har asha inuwarta, Fateemah duk burina na duniyar Nan game da mace a kanki na ta'allaqa shi ki zamar min bargon daze lillib'eni ki hanani Jin sanyi sai dumin jikinki, ki daukemin duk wata kishirwar data addabeni akan diya mace kinji my princess, duk duniyar Nan da ke kadai na aminnta na bayyana Mata sirrina ciki da waje ke kadaice macen data tab'a gani ainishin waye ni tunda nayi Hankalin kaina, ki tallafeni kada ki Bari na shiga rubibi a hannun Mata kinji my previous, na baki amanar kaina da kaina tunda ni babu Wanda ya Baki Amana ta amma ke kowa fada min yake gaki Nan Amana na kula dake to nima ki kula Dani Dan tamkar marayan da bashi da uwa bashi da uba haka nake a gurinki ki bani dukkan kulawa kinji, kuma Dan Allah ki daina tsorona nifa babu abinda Zan Miki na cutarwa idan na cutar dake Nina cutar da kaina, duk wani burina nandora shi a kanki".
Ya fada Yana shigar da ita jikinsa Yana sauke ajiyar zuciya a jajjjere, lif tayi a jikinsa Amma fa yaji yanda heart dinta ke beating very fast. Lumshe ido yayi ya rasa meya canza Masa ita take irin wannan Jin tsoron nasa yasan ba dabi'arta bace hakan ko ranar Daya Fara fito Mata a mutum sak ba tayi irin wannan tsumar ba kawai dai ta Dan rikice Masa na dan lokaci Amma Daya saka Mata pressure dole ta nutsu tayi Masa abinda yake so a lokacin harya saida ya samu relief, Amma yanzu duk ta rikice Masa a Hankali yayi Mata magana a kunnenta.
"My previous me kike tsoro a tare dani, fada min kinji?".
Ya fada Yana Kara shigar da ita jikinsa yana kuma Dan shafa gashin kanta Daya Sha gyara na musamman, sanyi da salama da wata irin nutsuwa suna sauka a cikin zuciya da gangar jikin a lokaci daya.
Lif ta qarayi a jikinsa dan da gaske tana Jin wani irin Abu da ada Bata jinsa a tattare dashi, sai yanzu take jin da gaske fa auren ne a kanta sabanin da da take jinta dai gata nan.
*AUREN HUCE HAUSHI*
_AISHAT ISAH MUSAH
_*Maman Fateemah_*
08055362975
My
WhatsApps number.
*Page 83.
______Kara shigar da zahrar yayi jikinsa, nan da nan yaji labarin Yana neman canza salo shi Kuma harga Allah Yana bukatar privacy saboda matukar ya tab'a wannan shugwababbar 'yar raki sai abinda Hali yayi. Don yasan za'a Sha danger da ita ga mutanen biki suna Nan yasan da safe baza'a rasa masu zuwa suyi Mata sallama ba, yafi son sirri gaskiya. Amma dai zasuyi nafilar da Manzon Rahama yayi umarni da ma'aurata su yita.
"Cikin nasa salon da yasan Yana yin rinjaye a kanta ya Dan fara shafa cikinta a Hankali.
"Da yunwa a cikin Nan gaskiya, Bari na kawo Miki abinda zakiçi kada Nan gaba ayi min gorin ranar da akazo gidana ko abincin tarba babu Ina ta kurin sokoto aga nayi failing ko ba haka ba?".
Ita dai zahra shiru tayi masa shi ya kasa ganewa yau jinta take tamkar Bata taba wata kebewa tare dashi ba,taga sai wani rawar jiki yakeyi abinda ba halinsa ba, duk wannan kanewar ta nemi nata gurin wani sabon mahmud take gani ba Wanda ta sani ba.
Ya tambaya Yana kokarin zare Mata Alkyabbar gaba Daya daga jikinta wani fitinan kamshin ya mamaye shi, ga wani mahaukacin feeling da yaji Yana fusgarsa zuwa gareta, kankameta ya karayi a jikinsa da gaske ya shiga wani yanayi,ba Karamin yak'i yayi da zuciyarsa kafin ya sassauta Mata rikon da yayi mata Yana maida numfashi.
Alkyabbar ya aje gefen gadon ya Zama daga ita sai wata rigar atamfa wadda akayiwa wani fitinannan dinki Wanda ya fito Mata da ikahirin halittarta ta kirji zahiri, yabi shafaffen cikinta abinda ya Kara fallasa asirin kirjin nata kenan da suke a cike tsan-tsan, ai baisan lokacin Daya Kara mannata a jikinsa ba Yana fadin "Ashe wannan abar ba Karamin sitirtamin kayana tayi ba" Yana Kai hannunsa gurin.
Dan zabura tayi ta rike hannunsa ta shagwab'e Masa fuska tare da juya Masa sexy eyes dinta
"Please meu amorrr.....ba kyaufa ka Bari Dan Allah".
Saitin kunnenta yayi magana a hankali..
"Meye ba kyau din fada min abinda nayi Daya sabawa shari'a? Ina son Jin tempareture din jikinki ne naji kamar tayi high".
"A'a...ni lafiya ta qalau".
"Ok, to bari nazo".
Ya fada Yana gyara Mata zip din rigar, fuskarta ya dan shafa kadan tare da Bata wani light kiss a gefen wuyanta Wanda yasa tadan fitar da wani Karamin sound da yaso ya Hana shi fitar.
Babbar rigar ya cire ya aje a kusa da ita Yana nufar kofa ya fice, Dan kwanciya tayi a gefen gadon tana Jin wani Abu Yana circulating a cikin jinin jikinta.
Bai Jima ba ya dawo dauka da Leda Mai tambarin na Maru suya spots, da plates da sauran tarkacen su knife da cups da su forks, a kan Karamin Conner table ya Dara idanunsa na Kan Zahra wadda ta lumshe Ido tana sauke numfashi a hankali,wani special smile ya saki yana godewa sarki buwayi gagara misali da yayi Masa irin wannan kyautar, Saida ya aje komai sannan ya nufeta ya tsuguna dai dai saitin fuskarta Yana dan shafawa a hankali narkakkun idanunta ta bude tana kallonsa.
"Oya tashi kici abinci".
Ta lumshe idanun tayi. "I am ok fa, bana Jin yunwa barci nakeji".
Bai saurareta ba ya saka hannu ya dagota daga kwancen Yana fadin "Ni nagano yunwar a tare dake".
Nama ne Wanda ita dai bazata ce ga yanda aka sarrafa shi ba, ya gyara hannun rigarsa ya Fara Bata tana mitar ita ta koshi Amma Bai barta ba Saida ya tabbatar da ta koshi sannan ya dauko Mata mutuniyar farm fresh ta strawberry ya cika cup ya kafa Mata a Baki ta Sha rabi ta kawar da Kai kamar yanda yaran goye sukeyi idan suka koshi da Abu.
"Pls precious ki shanye mana farm fresh ce fa, ko kin daina yayinta ne? Naga tunda mukazo kabi nema ba alhalin an cika Miki store da ita".
A shagwab'e ta dago sexy eyes din ta tana Masa wani kallon Daya nemi jefa shi a wata nahiyar.
"Nifa na koshi kamar na cikin mafa ze dawo nakeji".
"Ok. Shike Nan Bari na dauke kayan sai ki shiga kiyo Alwala kafin na dawo".
Har ya kai kofa ya tsinkayo maganarta tana fadar "pls naga zaka mayar Kai bakaci komai ba".
Kafeta yayi da Ido Yana nazarinta "Da kina son naci ai da kin bani, amma Baki bani ba tunda na dauke kuma sai wani jikon Wanda kikaci shikenan is enough for us, koba haka ba?".
Ya dage Mata gira ya fice.
Tsam tayi da ranta tana hasaso mezeje yazo, ita fa duk lamuransa sun tsaya Mata a Rai yanda ya downgrade din kansa a Azare da yanda ya ringa mu'amalantar Almajiran malam, a yayin zamansa a can, ita fa gani take wallahi yanzu yafi karfin ajinta nesa ba kusa ba duk da tasan itama yes ba karya Ubangiji ya Gama Mata gata ya dauke Mata iyaye Amma cikin Rahamaniyya tasa saiya saukake Mata duk wani tsananin rayiwa, duk da Tasha badaqala a baya sai gashi ya zama tariihi.
Allah be Bata ikon tashi ba har ya dawo, ruwan dake hannunsa na laimar alwala ya Dan yarfa Mata sai tayi figigit tana sauke ajiyar zuciya.
Gaba yayi ya nufi kofar da take tunanin toilet ne, ta Mike a hankali tabi bayansa hanya ya matsa ya Bata tare da fadin "shiga kiyo Alwala Ina jiranki".
Ya juya ya fice daga dakin, brush ta bude sabo ya wanke bakinta sannan tayi alwalar gurin mirror ta nufa ta karewa kanta kallo, wallahi tausayin kanta da kanta takeyi tasan sai yanda hali yayi Dan ita kadai tasan me take hangowa a cikin idanunsa.
Tana tsaya taji alamun za'a bude kofar tayi saurin barin gurin, Yana budewa tana zuwa bakin kofar jallabiya ce sabuwa fara Kar a jikinsa sai Zuba kamshinsa nan nasa na musamman yakeyi, hannu ya Miko Mata yana sakin murmushi Yana fadin "inye 'yan matan gidan mahmud Dange, yarinyar Nan kina yanda kike so da Dan malam din Nan wallahi sai cika kike kina batsewa irin kada a kawo Miki wargi din nan ko?".
Kauda Kai tayi tana sakin murmushin ta Mai shagaltar dashi "Ni wallahi ka Bari idan wani yaji saiya dauka haka ne fa".
Hannu ya rike ta fito daga toilet din.
"To da karya na fada ba cikar kike kina batsewa ba kawai Dan ki Sara min allo ki hanani rawar gaban hantsi ni da halaliyata za'a hanani dama daddawata da moda".
Ya fada Yana kafeta da tsumammun idanunsa, sadda kanta tayi kasa Dan abinda take gani a can baya ta gani yau muraran a idanun nasa ta rasa wane irin abu ne da yake sakata a rudu haka.
"Muje muyi sallar".
Hijab taga ya dauko Mata fari sol dashi Mai laushi irin na mutanen Indonesia din nan ya zura Mata,Yana janye da hannunta suka nufi wani guri kamar space din da ake saka dining table suna zuwa taga an yi gurin ne domin ibada kawai ba Bata lokaci ya shige gaba yaja musu sallah, raka'a biyu yayi musu yayi sallama ya Jima Yana musu Addu'oi da harshen larabci Wanda har Saida zahra ta dago da kanta ta Zuba Masa idanu tamkar shine Dan mun gada din, a hankali ya matso inda take saune ya dafa kanta ya ringa kwararo Addu'a, Nan da Nan jikinta ya hau tsuma sai kuka Dan Allah ji tayi tamkar tafi kowace mace sa'ar samun miji Mai addini Dan Bata taba tunanin iliminsa ya Kai haka ba tun a wancen lokacin bare kuma yanzu da taga ra'ayal ainiy.
Sai da ya Gama Mata Addu'oin sannan ya daukota cak ya rungume abarsa Yana fadin " pls precious kinsan bana son kukan naki ko? Ki daina kuka babu abinda Zan Miki ki saki jikinki Dani kinji, Nima na gaji sosai babu abinda nakeso sai nayi barci na huta ai kin gane".
Kai ta gyada masa tana Kara lafewa a jikinsa tamkar mage, ya yarda yayi amanna itace weakness din da gaske Dan ji yake baze iya matsamata ba gurin sex Dan ya fuskanci tana zulumin abin ba kadan ze da raka da ita ta Kara sakewa yasan duk runtsi ba za'a dauki lokacin da sukayi a baya ba.
*****Kuka take tamkar wadda akayi mata babban rashi irin na iyaye,duk iya ban baki Salbiyya babbar hadimar Fulani tayi Mata Amma kamar tana Kara tunzira ta, dan tayi masifar kwallafa ranta a Kan mahmud, guyn yayi Mata karshe taci burirrika masu yawa a Kansa,tun bayan dasu Ammi suka dan tattauna a kan yuwuwar hadasu aure bayan samun matsalar data kusan rusa farin cikin da yawa daga family din nasu mahmud.
Tashi Salbiyyar tayi tana fadin "Bari na Kira Giwar Mai martaba tazo taga halin da kike ciki kada ciwonki ya tashi mu shiga uku"
Ta dauko wayar ta tana kokarin Kiran Fulani, da sauri Insiyya ta rik'e hannunta tana girgiza Mata kai saboda kukan da yaci karfinta.
Fasa Kiran tayi itama barazana ce saboda lokacin kusan Daya da minti goma, daren ya Fara nisa bazaso ta daga Hankalin uwar gijiyar tata ba.
"To ya kike son naji Miki ranki shi dade? sai Abu Daya kikeyi tun dawowar mu daga gidan Amaryar Nan Kika birkice min kink'i ki fada min damuwarki ko ina da abinda Zan taimaka Miki dashi".
Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Haura'ul insiyya bata damu data gogesu ba.
"Ina sonsa,son da bansan ta Yaya na Fara shi ba,batun yanzu nake jinsa a Raina ba sai dai Ganin babu fuska yasa na hakura , sai kuma Mama ta fada min sunyi magana da Ammi zasu had'amu aure tun bayan da aka samu matsalar da tasa yabar gida aka rasa Ina ya shiga a cikin duniya, na gansu a India Shida wannan matar tasa, tun a lokacin naji Ina masifar kishinta, saboda Ina Ganin indai tana gabansa babu wata mace da ze daga Ido ya kalla Wallahi".
Ta fada tana share wasu sabbin hawayen da suka ciko Mata idanu.
"Haba ranki shi dade har kina tunanin akwai namijin da zece baya sonki? Ai sai dai Idan ba'a bashi ba, ki gafarceni abunda Zan fada, ni bana Miki fatan ki shiga gidan Aurenki a mace ta biyu, fatana ki shimfida rayuwar ki keda mijinki da 'ya'yanki ki juya abinki yanda kikeso, Ina shi yaron da kuke karatu dashi a can Rasha din Dan nan Nigeria Wanda iyayensa sukazo suka gana da takawa ba naji ance Shima jinin sarauta bane? Kinsan dai da wuya Mai martaba yayi magana biyu ki yiwa kanki Qiyamul laili ki Zubar da wannan batun Kinga dai yanda baiji kunyar kowa ba a gurin dinner game da matarsa, haka naji wasu na fada har suna cewa ai a can gurin wayonsa ya samota, to kinga ko kin shiga ba wata daraja zakiyi ba tunda ba shine yace Yana sonki ba, mazan yanzu sun ganki sunce suna so ma Yaya aka k'are ballentana kin Zama matar shige? Babu abunda Zaki tsinta a gidan sai zaman hakuri, ki cire ranki daga