Advertisements
Chapter 7 Reading Auren Huce Haushi Book 3 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Auren Huce Haushi Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 21

18K to 21K   out of 60.9K words

Naga kema jirgi Daya ya dauko ku dashi, Kullum Kuna cikin wadannan kayan da aka daukewa Albarka yo ina dalili 'ya'ya kun dauki daba'ar Nasara kun yafa kunce shine gayu".
"Kinga tashina Daman zuwa nayi Naga yanda kuka waye".
Ya fada yana kokarin tashi daga kusa da ita "Dawo ka zauna ko lafiyar matar taka ai ban tambaya ba ka sakani surutu, to Yaya ita Fatimar ta tashi".
"Lfy kalau Alhamdulillahi, tace na gaisheki da kyau idan nazo"..
"To Masha Allah haka akeso Allah yayi Albarka a gaisheta ai zamu shiga muga daki kafin mu tafi da yau naso komawa Baban ku ya Hana yace saina kwana biyu na Dade banzo musu Nigeria ba".
"Au da tafiya zakiyi ban sallameki ba ai gidana Zan mayar dake sai kin zauna min kamar yanda na zauna Miki harna fadawa Uncle Ishaq ma tun ranar da kukazo ya Kuma amince Dan cewa yayi aike tawa ce duk yanda nayi yayi dai dai, Dan haka keda Hajiya Inna Zan hada ku mu zauna duk kowa ya ramawa kura aniyarta".

"Allah ya tsari gatari da Saran shuka ni naje gidanka na Mike kafa na Kama Zama tare da matarka ku ringa min dibar Albarkar da zata sakani na rasa Dan sauran Idona ko?".
Baki bude yake kallonta yayin da saura Yan uwa da suka rage a dakin tunda yawanci yaran sun fice.
"Meye kuke min wani kallo karya nayi? ko bakuga yanda yake cukumarta a gaban dubban mutane ba to Ina ga daga mu sai shi ai sai yanda ta yuwu Dan daudu a lahira".
Dafe Kai mahmud yayi Yana Kara kallon Hajjar ba tare daya iya furta Mata komai ba,wato Hali zanen Dutse halinta Yana Nan ita hands free ce babu abunda ya dameta Saida idan ta fad'a kayi yanda zakayi kawai.
"Allah ya bamu Alkhairi ki gaida gida Amma matata bazatazo Miki Niger ba tunda harda bita da kullin Wai zamu kashe Miki Ido". Yayi waje yana Jin tana kiransa yayi gaba, Bai haura sama gurin Ammin ba komawa yayi asalin part dinsa Daya zauna tunda Yana da Kaya a cikin tunda yawanci kayansa na biki a Nan Sameer ya ajesu.
Wani yadin filtex brown Mai kyau da tsada ya saka ya dauko agogonsa Omega ya daura ya zuba turarensa ya kafa hula shi kansa sai yaji yes hakan yayi masa daidai, Dan murmushinsa yayi Yana tuno maganar Hajja Wai kayansa kamar na roko. Ficewa yayi daga part din ya koma na Ammi Amma ta baya ya shiga inda ze sadashi da stairs din basai ya koma ta main entrance din ba.
Saman ba hayaniya kamar kasan, knocking yayi a kofar bedroom din Ammin Aishat ce ta bude Masa su uku ne a ciki mummy Badi'a ya Fara gaishewa tana tambayarsa Ina 'yarta, sai Amminsa ita kuma Aishat wani signing din da suke sukayiwa guna da👍 alamar jinjina wannan dabi'ar normal sun saba tun suna yara.
Wani Dadi ne ya rufe Ammi fuskarta sai annuri yake fita saboda yanda taga Hussein dinta ya Zama babban mutum ko ba'a fada ba kana ganinsa kasan ya samu kwanciyar Hankali.
Kan sofa ya zauna kusa da twins sister dinsa yana kallon yanda suka cika dakin da wasu jakunkuna masu hotonsu Shida zahra,. Yayin da Ammi ke hada wasu Kaya a cikin jaka daga gefe da alamar kowa sabgar gabansa yakeyi, rausayar da Kai yayi Yana kallon Ammi wadda itama rabin hankalinta Yana kansa.
"Ammi..na".
ya Kira sunanta abinda takeyi ta Bari ta bashi full attention dinta tana sauraren meze fada Mata.
Dan sosa Kai yayi kafin yace "munga sako jazakumullahu khairan Ammina, kuma naji kince Zaki turo Mata housemaid ko?".
"Eh haka nace duk da nasan akwai naka Wanda suke kula da gidan sai Naga ya kamata a Kara Mata wasu daga nan Kuma wannan kukun naka a canza Masa wani aikin ko Kuma ya koma kamfani yaci gaba da aikinsa a can Dan baze yuwu su zauna da ita ba, a yanda matarka take sai kana kula da irin abokanen ma da zaka ringa shigar dasu gidanka gaskiya".
"In Sha za'a kiyaye Daman kukun na mayar dashi kamfanin shinkafa dake can kebbi, Kuma inaga basai an Kai Mata Yara ba ki Bata binta kawai saiki taimaka ki kirawo Amminta ta bar Mana Aunty zilai wadda suka zauna a kano Naga Bata da matsala".
"Ok babu laifi saina kirata na gane matar itace wadda ta bawa sako ta kawo min Naga alamar kamar ma'aminciyar su ce".
Ya Jima a gurin Ammin kafin Aishat ta rakashi suka je suka gaisa da dangin zahrar Wanda suketa Shirin tafiya Dan kayansu ne su Aishat din suke hadawa su za'a bawa Basu Dade ba suka fito a hanyar da zata kaisu parking lot ne Aishat ke fadar
"Wai ya zahrar ne da fatan babu wata damuwa a tare da ita?".
"Lafiya kalau take kinsan gidan yau zuwa gobe sai a Hankali gidan yanzu na jama'a ne".
"Haka ne Kam ai daga Nan har wani lokaci mutane bazasu yanke a gidan Nan ba sai kayi hakuri bare Kai Mai jama'a ai sai abinda ka gani, ni addu'ata Daya kada 'yan matan dake haukar sonka su ringa je Mata gida da sunan kannenka kasan dai baza'a hanasu shiga ba".
Wani malalacin murmushi yayi yana kissima wani Abu a zuciyarsa.
"Naga kana murmushi ko ba gaskiya na fada ba?".
"Gaskiya ce mana amma inaga ba Sai muna garin ba za'a samu matsalar, nifa na takura mutum da gidansa da matarsa Amma ace ya fito yana teto a titi ai kamata yayi yanzu mutum na gida Yana hutawa".
"Ai maganinka kenan Dan sweet heart ma ba karamin bekenka ya gani ba, me ka zauna jira kaida matarka saboda wani dalili naka ka Zuba Mata ido kana kallo har tsawon wannan lokacin".
Girarsa ta dama ya dan dage Mata kadan "bazaki gane ba komai Yana da dalilin yinsa, we will talk later in Sha Allah, ai kece best friend dina tunda kin kular min da my previous, yanzu zanje muyi sallama da bakin da Sameer ya gayyato min Dan tsabar daukowa Kai jidali ya saka mutane barin harkokinsu suka taho har nan".

"Aini Wallahi yayi min dai dai wani ma Be taba zuwa 9ja din ba sai wannan sanadin".
Har gurin mota sukaje suna tattaunawa da 'yar uwarsa Saida ya shiga harya tashe ta Aishat tace Masa.
"Wai Ina mutanenka na ganka Kai kadai".
"Na Basu hutu amma fa kinsan duk da haka su zayyan suna waje Dan Ina fitowa suka dafa min baya nasan bazasu hakura ba".
Motar ya harba yayi gaba saida ya fice daga second gate sannna Aishar ta juya ta koma ciki zuciyarta fal farin ciki Dan uwanta ya dawo tare da wata irin haiba da kwarjini ga uwa uba cikar mutuntaka ta aure.

*************

Tun bayan fitar mahmud zahra ke karbar Baki Dan ma Allah ya taimaka su Amatu da kannen Aunty safiya sun shigo,su suka ringa ba mutane kayan garar da aka kawo da sauran tarka na plates dasu jugs sai karamar blender ta hannu Mai aiki da batir Wanda ake Masa charge, sai kusan Sha biyu su sajeeda sukazo Ashe suna asibiti da Mama Hameeda ta kirawota tana kuka ta fad'a Mata ita tunda kuma ta Kira oga Sameer ta fad'a Masa shine ya Kira hotel din aka kaita asibiti da yake jiya Mamar saboda tsabar tashin Hankali wadanda aka saukesu a hotel tabi inda Allah ya taimaketa duk yawancinsu mutanensu ne 'yan Azare cikin dare ciwon kirji ya addabeta tamkar zata mutum.
Saida safe su Aunty Hasana suka sani abinda ya kawo musu tsaiko kenan a gurin tafiyarsu saboda jirgin karfe Sha Daya zasubi suda tawagar Ummee duk Sameer ne shida su Bashir suketa Kai kawo akan komai, dole sai su Ummeen ne dasu Hajiya kaltume suka nufi Bauchin da Alkawarin su Ummee zasu dawo sokoton kafin su wuce.
A gurguje sukayi sallama da zahrar saboda ya Abba da yazo tafiya dasu ita ummansu,zahra ta bawa su sajeeda Kaya da cosmetics kamar me tunda gasu Nan tamkar kamfanin ne a gidan ga wasu can a Azare har Kashi biyu duk na lefenta ne, suna kuka share share suka rabu sai yamma so sai su Aunty Rukayya da Aunty Fateeha suka tafi yayin da Hajiyar makwarari tace suje jikanta ya maidota Bata Gama abinda zatayi ba.
Zuwa magariba gidan ya Zama ba kowa daga Binta yarinyar da Ammi ta kawowa Zahra sai wasu yara da Hajiyar kadai.
Zahra Ammi ta Kira tace ta fadawa su Aunty zilai kada suyi komai zata aiko da abinci.
Bayan magariba kadan Aunty Aishat suka shigo da abincin lokacin Zahra na sama tayi wanka tana shiryawa, wata Riga ash colour ta saka irin ta mutanen Kuwait tayi rolling da veil din sai tayi wani irin kyau Dan yanzu ne kwarjiinin Amarcin yake bayyana a jikinta.
Saman Aishat ta haura tabar su Radeeya a kasa,sau Daya tayi knocking zahra ta bada Umarnin shigowa.
Suna arba da Aishat zahra ta rugo kamar yarinya ta shige jikinta tana fadin " Aunty Aishat nayi fushi idan ke bazaki zo ba ai saiki bada a kawo min Afnan Mana duk kewarta da dameni tana Ina ne dan Allah?".
Kan sofar dake dakin suka zauna Aishat din na fadin
"Afnan sunje Usman Dan fodio teaching Hospital dubiya, Inna Maimuna ce ta goyata kinsanta da son yawo".
"Su Inna kuma,to waye bashi da lafiya?"
"Naji dai suna cewa Mama kinsan ba sanin mutanen nayi ba".

" Ayya! haba shi yasa babu Wanda yazo gurina,Saida na gaji na Kira Aunty Hasana Amma kin fada min tayi sai cewa tayi zasuzo suna da wasu uzururruka ne Ashe Mamace jikin yaki Dadi Allah ya Bata lafiya".
"Allahumma Amin".
Aishat ta fad'a tana kallon zahra, kokonto ne ya darsu a zuciyar Aishat yanda taga zahra na Yan guje guje nan tasan ba'a gamu ba Amma saboda ta tabbatar saita cewa Zahrar.
"Dan Allah dauko min turarenki na gani Yana yi min Dadi sosai".
Tsam ta miqe Ras ta tafi ta dauko Mata su ta kawo Mata Aishat din ta dauka tana Kara shinshinawa tana kwarzanta kanshin su.
Handbag dinta ta dauki ta bude wasu kwalabe ta dauko tana murmushi sai wani kuma Karamin daurin magani a cikin irin ledar da ake zuba tablet a asibiti ta Mika Mata tana fadin "gasu Nan inji mummy Badi'a ta dauko wani turare Mai colour purple tace "Kinga wannna ki shiga toilet ki dan shafa a kirjinki da kasan mararki sai kuma wadannan guda biyun duka jikinki Zaki shafe dasu, wannann kuma ki zuba Madara ki Sha yau da gobe da jibi ya wadatar, Bari na dauko cups na hada Miki".
Zahra duk a kunyace take da Aunty Aishat din, ita mamaki take Bata tamkar ba dangin miji ba ita gani takeyi wallahi Kamar Aunty Hasanarta. Aunty Aishat ce ta tashi ta nufi kofa ta fice.
Bata Jima ba ta kawo cups da ruwa da farm fresh da Hollandis free mik, Aunty Aishat din da kanta ta hadawa zahra maganinta da Holladia ta Bata ta Shanye, Bata kayan tayi tace ta Adana kada ta Bari ko mahmud ya gani turaren na Mata ne kawai.
Kai ta gyada Mata tana Mata godiya, kasa suka sauko tare da Auntyn sai wurin 8:30 mahmud da Sameer suka shigo gidan, Sameer na ganin Hajiyar makwarari yayi turus Yana kallonta cikin madaukakin mamaki.
"Yanzu saboda Allah Baki bi su Rukayya ba Kika koma gida? to ko zaman daki zakiyi musu ne? Oh yau Naga ikon Allah gaskiya ko haihuwa tayi Allah bazan kowaki garin nan ba tunda baki iya cin Dan wake Mai yaji ba sai kin fantsama a ido, gaskiya gara da Allah yasa 'ya'yanki maza basa kusa dake da rawar gaban hantsi zaki Hana su wallahi, kawai kizo ki nemi guri ki zaunawa yarinya kina ganin shige da ficenta dan ki hanata watayawa kawai".
Tafi da sallallami Hajiyar ta dauka tana fad'in. "Yau Naga abinda ya isheni kaida ba gidanka naje ba ballentana kace nayi maka ba dai dai ba, su an fada maka irin kane zalamamme Wanda baya kauda Ido akan matarsa ai ban mance abinda kukayi min ba Ina zaune kuka kwakume juna kuna tsotse-tsotse ba kunya ba tsoron Allah saini na bar muku gurin, Amma kaga su da yake Allah yasa suna da ta Ido ko hannunta kaga ya rike a gaban mu eyeh?" . mahmud ne ya matso kusa da Hajiyar Yana fadin.
"Hajiya barka da dare, Dan Allah rabu da Sameer baya son zaman lafiya ai Nan dai gidana ne idan ma kin amince Zaki zauna har iya rayuwa kiyi zamanki daki ma sai Wanda Kika zaba zaki zauna".
"Allah yayi Albarka ko yanzu ka nuna min Kai cikakken d'ane na halak, Daman Kai nake jira ka mayar Dani yau can gidan ku Zan kwana ba gurin Hajiya Inna ba".
"Ok Bari na shirya sai muje na kaiki Nima ban shiga ba Nan nayo ya fada Yana nufar stairs da sauri yayin da Aishat tabi bayansa da sauri, Saida suka bacewa ganinsu Hajiyar ta kalli Zahra tana tabe Baki "ke Kuma miji ya dawo Kika nemi gurin Zama kamar wata kud'd'a marar wayo, baki ga ita 'yar uwar tasa ta bishi ba? Maza tashi ki bishi kinji ba'a sake da Lamarin miji".
Su Radeeya dai sai dariya suke musu suna daga d'ayan parlourn Dan da alama wannan har tace Hajja Bata iya ba.
"Yo ta Ina zata iya binsa kin kasa kin tsare kin hanata sakewa da mijinta".
Sameer ya fada a kule.
Shiru tayi masa Bata Kara tanka Masa ba.

Aishat Bata Jima ba ta sauko tana fadin "Sameer Bari mu wuce mukam Saida safe".
Tsam Hajiyar ta Mike muje ki tafi dani kada wannan Mai dacin ran ya kifar Dani a hanya yanda yake cika Yana batsewa baza'a haifi da Mai Ido ba".
Har gurin mota Zahrar ta rakasu tana rike da babbar jakar data hadawa Hajiya nata kayan harda na makotanta ta Bata Wanda take ta Kira ana yiwa zahra Allah Sanya Alkhairi, Saida suka wuce ta dawo.
Tana dosar kofar Sameer da shi suka fito,Sameer din rike da wasu files a hannunsa shi Kuma Dan gogan yana waya da wani yare Wanda Bata San ko wane yare bane. Rab'awa tayi zata wuce yayi ram da hannunta Yana binta da wani mayen kallo, marairaice Masa tayi tana Masa nuni da oga Sameer Amma ya fuske saima k'ok'arin mannata a jikinsa da yakeyi.
Wani killer smile Sameer yayi ya Kara gaba Dan yaga alamar ogan nasa sai a Hankali yau wuni yayi sakarwa kansa ruwa, Saida ya Kare wayar sannan Sameer ya dawo da laptop a hannunsa Mika Masa hannunsa dayan yayi ya saka Masa ita ya juya Yana fadin. "Good night".
Motarsa ya fada Yana sakin murmushi, a fili yace "wallahi ka shiga cikin tsarin dai sai yarinyar Nan ta goge maka hadda tas kazo kana sakin layi a gaban mu, Mata! Mata! Hummm ayi dai mu gani".
Ya figi motar ya fice daga gidan ai Kamar jiran ya fice mahmud yake yi ya wani juyo da ita Yana faman shinshina jikinta wani irin kamshi yakeji Yana fita daga jikinta Wanda yake bijoro Masa da wani irin feeling na tashin Hankali, hannunsa ko Ina yawo yakeyi a jikinta da kyar ya saurara mata suka shige ciki a daddafe sukaci cus-cus da vegetable soup sai wani nama Mai ruwa-ruwa da yaji spices da seasoning sai tashin kamshi yakeyi, kwanukan da suka Bata ta dauke ta shigar dasu kitchen sannna suka haura sama Yana rungume da abarsa suna shiga ya wuce toilet yayi wanka duk da kafin ya tafi sallar magariba Saida yayi wankan, tana zaune ya fito daure da towel fari sol a kugunsa Yana goge jikinsa da karamin Shima fari ne.
Lotion kawai ya shafa ya nufi clothset dinsu ya sako t-shirt Navy blue da trouser milk Mai haske na kamfanin Armani ya nufota Yana zuba kamshinsa na gado, hannu kawai ya Mika Mata ta Kama ta Mike Bai wani Bata lokaci ba ya kashe wutar dakin suka fito ya daddanna wasu numbers suka mufo down stairs. Wani Dan Abu ya Danna Kamar switch din kunna wuta sai gurin ya bude keys ne a gurin masu yawa Daya taga ya dauko har ze kashe wutar kitchen ya juyo motsin mutum sai lokacin suka tuna da yarinyar da Ammi tasa aka kawowa Zahra ita Kuma Aunty zilai su Aishat tabi tace sai an kwana biyu zata dawo duk da haka ta fadawa Ammi bazata ke kwana a can ba.
Ita dai ikon Allah take kallo ta kofar Baya suka fice parking lot ya nufa Yana rike da ita har suka karasa gurin motocin tamkar company sayar da motocin ne a gurin wata BMW ya bude saida ya sakata a front seat sannan ya koma ya zagayo ya zauna a seat din driver yayi Bismillah ya tuka suka nufi gate, tun kafin su karaso securityn dake Zaune bude musu gate din horn kawai yayi musu ya fice daga gidan, Saida yayi balance a Kan titi sannan ya Dan juyo Yana kallonta duk kanshinta da Kuma wani fitinanan kamshi duk sun cika motar. A Hankali ya Dora hannunsa a Kan cinyarta Yana shafawa a Hankali Yana kallon fuskarta sama yayo da hannunsa ta Dan zabura tana rike Masa hannu.
"Wai bazaki tambayi Ina zamu bane kikayi min shiru kina kallona?".
Juya Masa idanunta tayi masu saka shi cikin wani yanayi.
"Nasan duk inda zamu gida ne tunda baka da gefe a Nan garin".
"Good lallai yarinyar Nan kin Fara sanin DANGEN naki kenan".
A Hankali yake tafiyar har suka shigo mabera, Dan kallonsa tayi.
"Kaman gidan Hajiya Iya ko?".
"Inye lallai kin zama 'yar gari irin wannan saurin fashimta haka? Wato kin gane daga zuwa Daya kawai, Naga alama kwana kadan Zaki Fara nuna min gari nan".
Dan murmusawa tayi kawai Horn Daya yayi aka bude Masa ya shige Yana musu fitila sabanin da da yake tsayawa yanzu saboda zahra yasa ya shige kawai.
Har kusan Yan madaidaitan steps din kofar shiga part din ya Kai motar, gidan shiru Kamar ba jama'a duk bakin sun wuce Daman yawancin su danginta ne 'yan kwantagora suka sauka a gidan Dan ma ya saka Faruq ya samarwa da wasu dakuna a hotel, to yau kuma ya bada motar DANGE transport ta kwashesu tare da Sha Tara ta arziki ta mayar dasu. Kwantar da kujerarsa yayi yana bin wakar Daya saka ta wata tsohuwar mawakiya 'yar America Brandy a cikin wakarta ta awanna be down, baya

7 / 21