Advertisements
Chapter 12 Reading Auren Huce Haushi Book 3 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Auren Huce Haushi Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Complete Novels

Chapter   12 / 21

33K to 36K   out of 60.9K words

yanzu Ashe ba angwancewar zanyi ba ai ruwa zata hana guru ko tace dakinku daya tasani a bakin duniya idan na hana kada ma kice mata ga India samu kiyi shiru da bakinki idan ba so kike na Dawo nayi dan wuya ba maimakon aga nayi free lamura sun karbeni".
Sunne kai tayi a kirjinsa "kai meu Amor kaida Hajiya fa bata baci ka manta lokacin da kace idan mun hadu zaka kai mata qarata akan abincin?".
Lakuce mata dan bakjnta yayi " ke bakya mantuwa ne Wai?"
"Eh da sauki ai unguwarma na fasa gaskiya ka manta duk ranar dana rakaka unguwa bama dawowa lafiya, haka kawai kaje ka hadani da abinda tafi su bar-bar tunda naga baka da ragi idan ta had'oka da mutane kaje ka Dawo kawai bana zuwa bansan ina zamu ba yauma ace ga mace an kawo maka naje na mutu a banza gara kaje kai kadai".
" kai!kai!kai! Ashe ni tsihon mai laifi ne ni wlh ni nama manta anyi wannan abun kice dole su little su taho gida tunda har kina kewarsu".
"A'a wallahi bana son ko ganinsu mutuwa ce kawai banyi ba a ranar, shi yasa nake ganin mutuncin zayyan shi yayi min alfarma aka dauke min su fa".
" kinsan Allah a ranar hankalina fa yana kanki dan abinda nayi niyyar yi din ma ji nayi bazan iya ba idan na tuna kina cikin wani yanayi kinsan daga ranar zayyan ya Kara samun wata daraja ta musamman a gurina? Kulawa fa da tausayi duka ya muna miki "

"Wai dan Allah me kayo a cikin gidan nan nifa har yanzu ban samu nutsuwa ba".
Tsinin hancinsa ya fara gogawa a kan nata hancinsa yana dan hura mata iskar hancinsa cikin nata.
" kizo muje ki rakani mana a can zakiji wannan amsar taki"

Dan rausayar da kanta tayi "gaskiya Ina shakkar binka tunda idan idonka ya rufe ba sauki kaje ka kaini inda Zan kwana Ina kuka ba Mai lallashina tunda idan kana fushi ba ruwanka Dani".
"Kai ai da Kennan Banda yanzu yaushe zanyi fushi ai nine a kwana da din ba bansa yanda abun yake bane kinsan ni kifin rjiya ne a wanna fannin.
*_AUREN HUCE HAUSH_*

AISHAT ISAH NUSAH

Maman Fateemah


Bismillahir Rahamanir Rahim.

Allah ka jikan iyayen mu kayi gafara da jinkai a garesu tare da sauran Alhummar musulmi da suka rigamu gidan gaskiya.


Ina gaishe da dukkan masoyana na kiss Dana nesa Allah yabar kauna da zumunci, nagode kwarai.

Gaisuwa ta musamman ga

1.Ramatu sunusu Ummi ( Mrs.Sani shehu kazaure )
2. Fauziyya lawal Ammanj sokoto.
3.Hajiya Zainab Bashir Aliyu ( Mrs Muhammad manga Taraba state.
Ina godiya Allah yabar zumunci da kauna.







__Page 90.


____cikin abinda bai wuce minti goma ba Mahmud ya gama nasa shirin cikin suit Navy blue Goirgio Armani sai eyeglass daya saka mai azabar kyau yana daura agogo pateks a wrist dinsa, wani iri fitinannen kyau yayi mata ta kasa dauke idonta daga Kansa harya karaso inda take tsaye yana sakar mata da tsadadden murmushinsa mai shagaltar da ita, rumgumota yayi yana fadin
"Yaya dai 'yan mata? ko kin kyasa dan malam ne irin wannan kallon haka? Ko dai mu fasa fitar ne dan kina Neman hanani nutsuwa fa, wannan eyes din suna dauke da wani sirrin dake hanani nutsuwa matukar suna kallona,kina tuna abinda ya faru a soron gidan baba malam ranar da Mai mamana Mai sunan Ammi Bata da lafuya?Wlh bansan fa yanda akayi na jiki cikin jikina ba, kinsan abinda kuwa hakan ya jawo min a ranar?nayi Dana sani yafi sau shurin masaki precious, kinsan abinda ya daure min kai dake?".
Kai kawai ta iya girgiza masa.
" Da kika kasa ko daga ido ki kalleni ko naji mari kamar yards nayi tsammani, amma sai naji shiru kinyi lif kina dibar ni'ima ko?".
Sinne kanta tayi ji tayi kamar yanzu abin yake faruwa.
"Dan Allah abar zance nan bakaji abinda bature yace ba? Fast is fast present is continue".
"OK to shikenan ya wuce princess,zo muje".
Shi yake driving din motar su zayyan na biye dasu a hankali suke tafiya yana nuna Mata mahimman wurare a cikin garin bata San ina zasu ba saida taga signed board na Usman dan fodio teaching hospital.
Kenan gurin mama sukazo, to meya had'a tambayarta da zuwa gurinta ko kuma daga nan zasu wuce wani gurin ne.
A parking space suka tarar da Sameer, batayi mamakin ganinsa ba dan suna tafiya taji suna magana badai tasan koda waye ba.
Daga dan nesa da inda sukayi parking su zayyan suka Parker.
Shida sameer suna gaba zahra na bayansu bar suka shiga Aminity word na Bangaren retainer ship.
Dan knocking sameer yayi a kofar room four Aunty ladi ce ta bude kofar ganin sameer yasa ta matsaya tunda daga hanya tunda tun zuwanta shi yaketa fadi tashi da kai komo abisa 'yar uwarta, shiya turo mace ta zauna da Mama dazu lokacin da yasa a kaita immigration office.
Hanya ta bashi tana fadin "yallabai sannu da zuwa".
Kamar zatayi Kai kasa, Sam hankalinta Bai Kai Kan su Zahra ba, zaman glass dinsa Mahmud gyara sannan ya riko hannun Zahra suka shiga dakin.
Mamar na Zaune an jingina Mata pillow tana Shan wani Abu a cikin cup,tana kurba kafin ta Kai ga hadiyewa su Zahra suka shigo sunyi wata irin dacewa ta ban mamaki kana ganinsu kasan wasu irin couple ne da a cikin dubu da wuya a samu Kashi goma irinsu, basuyi aune ba suka tsinkayo tarin kwarewar ruwa ya sarke Mama babu k'ak'k'autawa Nan da Nan idanunta suka firfito abinka da Mai idanu a warwaje da sauri Aunty laran ta natsa kusa da ita ta karbe kofin tana fadin "sannu Rabi'a kibi a hankali tunda an samu tarin ya lafa".
Da kyar ya lafa Mata tana ta faman haki.
Daki ne madaidaici Wanda ya hada ababen more rayuwa sosai tamkar gida.
Duk yanda Zahra taso Mahmud ya saki hanunta yayi biris da ita.
"Sannu Mama ya jikin naki?"
Cikin raunin murya ta amsa da gani tana Jin jiki, "yauwa Zahra na gode kwarai da gaske kuyi min godiya gurin mijinki na gode Allah ya saka da Alkhari".
"Amin" Zahra dasu Sameer suka amsa shi Dan gogan ko tari Bai kubce masa ba tunda ya shigo sai wani kallo yake bin mamar dashi, ji yayi ya Fadi nauyi yayi faduwar sanho a rairaiyi, shi ashe ganin tsoro yake Mata a Dan ganin da yayi mata, sai yaji duk abinda yayi niyyar ya sauke mata yaji baze iya ba ya barta da wannan kaddarar ciwon data sameta kawai ta isheta musiba.
Tun ganin da Mama tayi musu Bata Kara dogo da kanta ta kallesu ba Dan wani irin kunya da nauyi ne suka rufeta yau ga Zahra a gabanta tare da Wanda suka dauka kaskantacce marar galihu a baya Wanda aka dunga fad'a musu da wani haske a tare dashi da yafi na sauran manemanta na baya amma tayi biris da maganar, gata gasu cikin wani irin yanayin da yafi duk wani tunaninta da hangenta.
Sai da ya bushi iska sannan yasa hannunsa na hagu ya zare glass din dake idonsa ya yiwa Mama kallon Kai tsaya cikin muryar data saka zuciyarta kadawa ya furta.
"Hajiya Rabi'aaaa..!!!".

Ba ita daya ambaci sunanta ba su Zahra ma Saida sukaji tasu zuciyar ta kada, Dan Zahra zata iya rantsewa da girman Allah Bata tab'a Jin muryarsa da gautsi irin haka ba.
"Ga Zahra nan ki dubeta ki K'ara kinso ki daqile Mata rayuwa ki Hana ta Kai inda ubangiji ya nufa taje kinyi ta kulle-kulle ki dan kada ta cimma rabonta na rayuwa da Allah ya hukunta a kanta, kin manta tun mutum na cikin mahaifiyarsa yake rubuta duk al'amuransa na duniya daga arzikinsa ajalinsa Dan wuta ko Dan Aljanna, an riga an rubuta alkalamin ya karya tawadar ta bushe, alkawarin Allah gaskiya ne baya tashi,gata Nan KAINUWA ce dashen Allah. Kuma duk kullin da kikeyi Allah ya nuna Miki iyakarki naso da lafiyarki da sai kinyi Dana sanin zuwa garin Nan to Amma sai gashi Abu kadan ya Hana zuciyarsa ta zauna lafiya tana neman bugawa a banza, abinda Kika so ya Sami Zahra sai gashi tun ba'aje ko Ina ba ya Sami yarinyarki, kinso Zahra ta lalace sai Kuma ta Zama Dan tsiron da Allah keso ko babu ruwa Saiya rayu,an Bata Almajiri marar galihu Maimakon tausayawa maraicinta a'a sai Kika gano tunda da Dan rufin asiri ba yanda Kika zata ba kina.cewa sai dai kyau ya qare a banza inda sai dai a kare a yawon kakksbar raba, duk da haka sai Kika dauri aniyar wargaza Mata rayuwar Aure saboda naki yaran Basu samu kamar nata almajirin ba, kin manta ayar da Allah subahanahu wata'ala yace cewa wamakaru "wamakarallah wallahi khairul makirin" Bari na maido Miki da abubuwan da kikayi ta fafutukar su zamar Miki tsanin daze ruguza duniyar gidan aurenta naji garin yayi min zafi na manta da ita har abada sai dai Wanda suka hada su gaji su kwance auren ko?" Ya jefa Mata tambayar duk jikinta rawa dake ga gumi ya tsatstsafo Mata a goshi har diga yake, duk tsiyar da kuke k'ullawa Asabe yarinyarki ta fada min komai har garuwan da Kike aikenta neman tsubbace tsubbacen ku, kinci daraja Daya wadda tasa na kyaleki na Kuma kyale 'yan koren naki, shi yasa na raba yarinyar taki da garin Dan matukar tana kusa zanyi Mata abinda asirin ki ze tonu abinda bazan so ace iyalin Abba itace ja Baga a cikin tafiyar, ko Mai gadin gidansa bazan iya keta masa rigar mutunci ba bare matar da yake aure ance ko a lahira wani Yana cin arzikin wani, Wallahil Azim da sai kunyi Dana sanin Baku santa ba a rayuwarku,Kinga zaman lafiya a kiyaye shigia eighteen dinta Amma duk Wanda ya kuskura ya k'ara gigin saka kansa a cikin lamarinta tofa maganar ba irin wannan za'ayi ba, zakuje asibiti na dauki nauyinki da duk Wanda yake tare dake a tafiyar saboda kinzo rako min princess ne ciwon ya tashi tunda dama da akwai shi,to gara ki Fara sheda wutsiyar ragumi tayi nesa da kasa, idan kin raba kanki da ciwon hassada idan Allah ya taimakeki ki samu waraka idan Kuma Yana Nan tofa Saida ya zamar Miki sanadin komawa ga Allah tunda ita dai wannan dai da aka dunga kokarin daqileta kada ta Kai inda ubangiji ya nufa tifa tayi Miki tazarar da za'a iya cewa tamkar tsakanin sama ne da kasa".
Wayarsa ya mikawa Sameer.
'Kira zayyan ka fada Masa ya shigo da sakon Nan".
Glass dinsa ya mayar a idonsa.
Tunda ya Fara zazzaga maganganunsa wuta da daukewa duk wani mahaluki dake cikin dakin Dan wannan dabi'ar ba kowa ne yasan Yana da ita ba, Idan ka tabo shi saiya rama tun Yana yaro haka yake.
Ba'afi minti uku da gama wayar ba zayyan ya shigo da ledoji guda biyu a hannunsa ya dan risina Yana fadin "gasu sir".
"Ba kowace ta ta".
Nan da Nan ya cika Umarnin uban gidan nasa, ya aje Kayan da asabe ta kawo na turarikan wuta a gaban Mama sai Wanda aka karba a gurin asaben dai Wanda ya Zama sanadin da tabar garin da Kuma tatsar bayanai daga gurinta.
Gasu Nan idan Kuna da bukarsu a gaba saiyi muku amfani, ke Kuma Idan mun fita saiki nuna Mata wadanda bata kaiga ganinsu ba, Kuma yanzu haka Salma ta sauka a Azare zata amsa tambayoyin Abba tunda kinqi fad'a masa irin tarbiyyar da kike bawa yaransa".
Bai Kara tofa komai ba ya janyo Zahra suka nufi kofa su zayyan suna take musu baya, suna Daf da barin dakin suka jiyo kukan Aunty larai tana Fadi "na shiga uku Rabi'a ki tashi"

Shi dai Bai juya ba ya dai nunawa su Sameer akan su koma.
A hanyar su ta komawa ne suka hadu da doctor zainab ta fito daga Gyne emergency.
"A'a wa nake gani kamar 'yata? Yallabai lafiya na ganku da daren nan haka a asibiti daba sai a kirani ba".
Gaishe da ita sukayi Zahra sadda Kai qasa Dan ji tayi duk kunya ta rufeta, Mahmud ne yace.
"Ba komai doctor munzo gaishe da marar lafiya ne".
"A to Allah ya qara sauki, 'yata ya jikin naki?"

A kunyace tace "jiki da sauki mummy".
",To Masha Allah, Dan Allah ki kiyaye shanye shqnyen magungunan Nan badan jikinki Mai kyau bane da an samu matsala sosai" .godiya sukayi Mata sannan Sukayi sallama,ta wuce Suma suka wuce, har sukaje gurin mota babu Wanda ya tofa ko kalma Daya a tsakaninsu Dan ita Zahra ji tayi tana wata shakkarsa Bata taba zaton ze iya shafawa idanunsa toka yayi irin wannan rashin kirkin haka ba.
*_ AUREN HUCE HAUSHI_*


AISHAT ISAH MUSAH
(Maman Fateemah)
09061432330
08055362975


Page 91


_________ Tunda suka dauki hanya yake sharara gudu sabanin dazu da suke tafiya a slow, taso tayi Masa magana to ganin Yana yinsa yasa tayi shiru ta zubawa hanya idanu, zuciyar ta fal da mamakin rashin kirkinsa Daman haka yake?.
Har suka shigo rukunin gine-ginen unguwarsu Bai tanka Mata ba Saida sukazo dai dai wani gida Mai farin fenti da ash colour sannan ya Dan juyo ya dubeta, "Kinga gidansu dodanniyarki Nan".
"Wacece Kuma dodanniyar tawa a garinku nida ko one week ban cika ba a garin da har zanji tsoron wata".
"Dr Haseenah ba dodanniyar ki bace?".
"Allah ya sauwak'e wallahi meye abin tsoro a tare da wannan Mai siffara mazan, mace ba gaba ba baya, Kace 'yar garinku?".
Ba zato taji ya fashe da wata dariya Yana duka sitiyarin motar da hannunsa.
"Amma wallahi kin cuceta, tana ganinta Mai zafi Amma ke kina siffantata da maza".
Hannu ya Kai ya Dan shafi gefen cinyarta "ba wannan ko?".
Dan zumburo Baki tayi tana matsawa "to karya naji Kai idonka baya gani, wallahi har naji bana son unguwar".
"Kai! Kuji mu da yarinya haka kike da kishi? Kince kin tsani Kano Kuma my home city din ma sai Kice Bai Miki ba saboda kishi,to Yaya zamuyi dake idan Zan kawo miki 'yar buzuwata diyar Mama filani, Dan ta kirani mun zauna tace idan kin kwana biyu kin Zama 'yar gari ta bani Insiyya in Kara da ita Wai Daya tayi min kadan".
Wani irin kallo ya zuba Masa da sexy eyes dinta.
"Ki rufa Mana asiri mu karasa gida lafiya,kada kisa a tashi damu a social media ace Amare sabbin Aure sun rigamu gidan gaskiya a sanadin hadarin mota suna tsaka da cin amarci".
"To Ni menayi,?".
Ta qara kada Masa idanun tayi, wani smile yayi.
"Naga alama wannan kin wuce tunanina Bari muje gida kiyi min bayani da yaren da zanfi ganewa tunda kin Fara Zama 'yar hannu".
"Meye kuma 'yar hannu?".
Dariya ya qara yi "kije ki tambayi hausawa".
Ya fad'a Yana saka signal na shiga wata kwanar.
"Ina Kuma zamu? Naga ka shigo wani gurin nifa barci nakeji".
",Fadi gaskiya dai yarinya, ko dai...?.
Rufe fuska tayi da tafukan fararen Sol din hannuwanta Wanda suka Sha lalle.
Wani irin kyau tayi Masa ba kadan ba.
"Kunyar wa kikeji a Nan?".
Dai dai lokacin da taji ya Danna horn Sau biyu abinda ya tilasta ta bude idon ta kenan.
Budewar idanunta da bude gate din sai suka Zama kusan lokaci daya.
Hannu kawai ya dagawa securities din yayi gaba, wasu gine-gine ta gani masu azabar kyau ga titi Nan dodar sai haske kamar Rana ga flowers Nan masu kyau an qawata gidan dasu, Bata ankare da Ina bane Saida taga sun karaso main ginin da aka kawota ciki, Bata tab'a zaton girman gidan da Hajiya Inna take fad'a ya Kai irin haka ba,to ai wannan sai a dafa mutum a cinye na wancan gate din ma basujin ko labarin ba, parking lot na motocin gidan Wanda suke tamkar kamfanin siyar da motoci ya nufa da alama ba 'yan milkin bane a kansa Dan tana ganin yawanci sai dai a shigar da Masa da ita ciki.
Kallonsa take galala Kamar wata 'yar kauye.
"Lafiya irin wannan kallon haka? Duk gidanki ne gate uku gareki dayan sai kin kwana biyu kin warke tas mu zagaya kiga inda yake, gasu Nan compartment compartment sai inda kikeso Zaki zauna".
"Ko dai zamu zauna ai Ni Kuma na Gama shiga taitayina nasan wannan gidan mace hudu ne wata kila harda kwarkwara ma tunda da abun".
Bai tanka Mata ba ya bude ya fito, itama ta fito tana Kara waiwayen hanyar da suka biyo sai yanzu ta Kara karewa gidan kallo, ita abin yafi karfin sannin ta gaskiya da data ambaci tsoro Ashe ba tsoron takeji ba sai yanzu.
"Oya let's go".
Ya fad'a Yana janyota jikinsa "Wai tunanin me kike ne haka Kona Dr.din ne?.
"Dan Allah ka daina fada min sunanta".
"Tona daina muje kiyi min wanka kiyi min tausa yanda zanji Dadi Baki labarin nawa wata Kila mu gama zuwa asuba".



*********Tunda su Abba suka sauka a Bauchi yake Kiran wayar magaji Amma amsar Daya ce not available, malam Bala ne yaje dauko su tare suka taho dasu Aunty Hassana da Inna mainuna da Hameeda. Dan daga gidan zahrar airport suka wuce inda suka samu su Aunty Hassanar, tunda su Abba suka baro gidan Zahra Bai Kara kallon Hamza ba Dan idan ya dube shi ji yake zuciyarsa tana wata irin tafasa, Bai tab'a zaton haka daga gare shi ba, yayi zaton hankalinsa da tunani sun wuce haka kenan da hadin bakinsa aka munafurce shi anyi masa lullubin biri.
Karfe biyar saura suka shiga cikin garin Azaren katagum.
Gidan shuru kamar babu mutane a cikinsa su Aunty Hassanar suka shigo, parlourn Ammah ba kowa sai kamshin turaren daki Dana girki Daya cika shi.
Saida Aunty Hassanar tayi sallama sau biyu sannan Alawiyya ta fito daga kitchen tana amsa sallamar tare da fadin
"Lah Aunty, Inna sannaunku da zuwa mutanen sokoto ya hanya?".
"Hanya Alhamdulillahi mun dawo lafiya, ya muka sameku?".
Inna maimuna ta fad'a tana zama a Kan two seater.
"Lfy kalau Inna ya aka baro Amarya? mu ai mun tsufa a gida, Ashe Mama bataji Dadi ba a can?".
"Wallahi kuwa jiki kam babu Dadi tunda har za'a fita da ita can misira".
"Allah ya Bata lafiya, sannu Hameeda ya Mai jikin?".
"Jiki da sauki Alawiyya nagode".
Ammah ce ta fito daga cikin corridor din bedroom dinta.
"A'a Masha Allah! Inna sannunku da hanya, ai tun dazu nake zaman jiranku da naji shiru Baku karaso ba na shiga daki gurin wayata da ake Kira".
Abinci Alawiyya ta kawo musu da drinks.
"Waini Hajiya Ina su Hanifa ne naji gidan shiru alhalin an bar Miki 'ya 'yan Amana".
'yar dariya tayi "suna gurin Babansu tun safe dayazo gurin Abba suka tattara suka bishi".
Aunty Hassana

12 / 21