Author : Maman Teddy Category : Complete Novels
yiwa shocking.
"Kishiya Kuma? Har ka gaji Dani Nan da Nan haka? Daman abunda kake fada min ba gaske bane harka Gama Dani Kuma sai wata? Na shiga Tara, Dan Allah Dame na kasa maka ko ba irin type din da kakeso nake ba"..
Sai hawaye sharrrr.....
"Ya salam.! Previous meya hau kanki ne Wai tsakanin jiya da yau? Wace iriyar magana ce wannan marar dadin saurare, kece na gaji dake? koko ba irin type din da nakeso ba? Wallahil Azim ban tab'a son wata mace ba kamarki tunda Allah ya halicceni idan Kika cire uwata to ba'ayi ba Kuma Ina ganin har abada babu wata mace da zata samu matsayi irin naki a wannan zuciyar, kin Dade da mamayeta tun ban gama Zama mutum cikakke ba, maganar type Kuma ai ni har kin wuce sanina wato so kike na nuna Miki true colour dina a wannan fannin ko? Naga alama kema jirgi Daya ya dauko mu, Bari ki bani abinci mu gani daga Nan zuwa asuba ko mun Kai ga inda muka dosa inaga da tsarabar Lagos zamu koma SKT, da alamar ma Nan gaba kadan saina Fara service gaskiya".
Sunne Kai tayi a kirjinsa tana fad'in a'a wallahi bada fa wani Abu na fada ba cewa fa kayi Wai zaka kawo abokiyar Zama ai kowa yaji yasan banyi maka dai dai bane shi yasa zaka karo Aure".
"Ya salam! Previous yaushe Mika zama haka Dan Allah? To Bari na fada Miki kinyi min fiye da tunaninki wato Naga kin Zama sai a hankali ko? Kada fa na Fara guduwa da kafata kisa ace min ragon miji".
******Tunda su Ammah suka tafi Salma ke aikin kuka, bakin ciki goma da ashirin gana wannan wulakantaccen Auren gana Makarram ga Kuma uwarta Mai daure mata kugun itama tana wata uwa duniya da tata lalurar,ga mijin da aka Bata Wanda ta rainawa ajawalin shima ko kyeyarsa ma bataci arzikin gani ba har karfe Daya na dare ga unguwar irin sabuwar Nan ce wadda Bata da cikowar mutane, barci dai sai barawo Dan sai ana Kiran sallar asuba ta farka, haka ta wayi gari kamar mayya ita kadai a gida, sai wurin takwas taji ana buga gate din gidan da farko banza tayi Saida taji bugun Yana damunta sannan ta fito sai lokacin taga yanda gidan yake Dan Sam Bata fito ba, Data bude daga cikin kannensa ce mata, ba laifi ita da sauki Bata da halin sauran, murmushi ta yiwa Salma itama murmushin ta mayar Mata duk da zuciyar ta babu Dadi.
"Sannu da zuwa".
Salma ta fada tana Bata hanyar shiga.
"Yauwa sannu Aunty salma".
Kofar Salma ta rufe suka juyo cikin gidan ba laifi ya tsaru dai dai misali self content ne sai wani Dan karamin part Kamar boys quater.
Basket din hannunta ta aje ta zauna tana fad'in ga abincin break Nan inji Umma tace a gaisheki Kuma kada kiga Ya Anas baizo ba Aunty Bara'atu ce bata da lafiya tunda aka fada Mata Ya Anas din yayi Aure ta Kama Aljanu a kanta aka kwana yanzu ma zasu tafi gumau can Toro local government gurin mai Magani ance dai ko kwana akeyi a can din yace dai sai sun dawo ze shigo Nan gurinki yace na zauna na tayaki Zama zuwa dare".
Tunda Hafsa ta Fara rattabo Mata bayani taking wani tashin hankali ya rufeta sai gumin goshi takeyi, wulakanci dai ta tabbata a Nan ya Gama nunawa duniya ita ba komai bace ita da banza duk daya, Bata tab'a Jin tayi nadama ba sai yau, duniya tayi Mata juyin waina, ba haka ta shiryawa rayuwa ba taci buri kala-kala amma karshe ga yanda ta kare, Nan da Nan taji idanunta sun cicciko da hawaye Bata damu ba da Hafsa da take Zaune kuka ta fashe dashi tamkar wadda aka aikowa da sakon mutuwa, bare data tuna hotunan da magaji da mujiba suka Dora na bikin Zahra da irin gidajen da taga ana sabgar a ciki da Kuma gidan da majiba ta Dora hutunansu tana gani tasan shine gidan Zahra Dan taga magaji ma yayi hotuna a cikinsa.
Hakuri Hafsa da dinga bawa salma Dan ko ita abun yayi touching din ta Dan ance ciwon 'ya mace na 'ya mace ne.
Abincin dai kasa cinsa tayi Dan dankalin Hausa ne sai kunun tsamiya da jallof din taliya, abunci dai gashi nan tasan da gangan akayi Mata shi Dan kada ace ba'a kawo Mata ba.
Har dare ya kawo jiki ba Ango ba labarinsa ko Kiran wayarsa babu, Amma dai zuwan Hafsa sai yasa Salma ta Dan ware suna Hira da Hafsa din tare suka dafa abincin Rana tunda babu Abinda Abba baisa anyi Mata ba haka Ammah ma tayi nmijin kokarin hada Mata duk Abinda uwa takeyi, ganin dare ta Fara yasa Hafsa tafiya a tabar salma ita kadai.
Zahra a ranar ta karbi kidan general Dan ta gane shayi ruwa ne Lipton kadai ke canza Masa kala, Dan babu daga kafa Saida yaga da gaske ta gaji sannan ya kyaleta, Amma dai ya yaba mata Dan ta shayar dashi ruwan mamaki ta haddace karatun tas har Kari aka samu, Saida sukayi sallar asuba suka kwanta, Dan migonowa yayi jikinta ya rungumota jikinsa ya furta.
"Previous.. wallahi kin gama min komai, Allah ya sakawa Ammah da Alkhairi data Baki tarbiyyar da tasa aka dunga Adana mun kayana, kin fa bani mamaki, ilove the way you..,kiss, licked my ears,look at me as you blew me.... Pls tell me who can teached you how to do this special making love?".
Wata kunya taji ta rufeta sunne kanta tayi wallahi ya Sanya jin kunyarsa ba kad'an ba.
Ganin ta qudundu ne kanta a kirjinsa ganin hakan yasa ya Kai bakinsa kusa da kunnenta Yana hura Mata iska a hankali.
"Please precious tell me what should i do to prepare you for second round?".
"Ya ilahiy! Shike nan ta tarowa kanta match wallahi".
"Ok let's talk about what we can do differently next timeeee..." Ya karasa fada Yana Kara hadeta da jikinsa.
"Dan Allah ka Bari wallahi nifa kunyarka nakeji".
Wata dariya yayi a hankali.
"Amma yarinyar nan, kin sakani a daki kinata sarrafani kamar zan zauce na haukace shine Zaki wani rufe Ido kice kina Jin kunya ta tab da kunya ta Kare a duniya".
Saida ya huta yanda ransa keso sannan sukayi wanka, sukayi breakfast sannan ya jata suka fita Sai lokacin ta karewa gidan kallo ba karya ya hadu iya haduwa Kai da gani kasan gidan ya lashe mak'udan kudi Dan karshen gayu dai an tanada a cikinsa sun zagaya ya nuna Mata yanda komai yake sai lokacin taga she ba wani irin Babban Nan bane Dan gidan sokoto ma ya fishi girma sai dai wannan din ma yaji ababen more rayuwa, da yamma suka fita beach anan taga yanda Mata ke yawo cikin tubarriji ba kunya ko tsoron mahalicci dole ta matsa Masa suka nufi irin gurin da ake hutawa, suna Zaune suna Hira duk Wanda ya kallesu Saiya qara kallo, daga gefensu Zahra kaji ance "Jadida".
Da sauri ta juya tasan ko wacece tare sukayi F.G.G.C KAZAURE da ita Dan yawanci 'yan class dinsu ke fada Mata sunan wani teacher dinsu Muhammad Naseer mutumin Sudan ya saka Mata suna a washe garin da aka kaita makarantar yake tambayar ta Ana jadida? Saboda ya ganta Balarabiya, ai kuwa sai 'yan class suka dauka wasu ma cewa suke Zahra jadida kawai.
Ai kuwa tana juyawa sukayi arba da zainab murtala Aliyu 'yar Jos ce amma mazauna Lagos babanta Dan canji ne.
Da sauri ta karaso ganin da gasken itace ta fada ne Dan tabbatarwa ne kawai rungume juna sukayi cikin farin cikin ganin juna babu zato,Saida suka Gama murnar su sannan Zahra ta gabatar da zainab gurin Mahmud suka gaisa tace Mata maigidanta ne, ta gabatarwa da Mahmud zainab kawarta tun suna secondary Nan suka koma gefe Hirar yaushe gabo ta balle anan zainab ke fada Mata itama tayi aure shekara Daya da rabi kenan harta haihu Dan ba rai sai yanzu take da wani cikin sun shagala da Hira sukaji magana daga bayansu ana fad'in.
"My beauty wato Hira Kika samu Kika manta Dani ko?".
"Wayyo my love wallahi na gamu da friend dina ce, rabon damu hadu tun secondary kaga kuwa ai mun gaisa mu tuna baya ko?".
Haka Nan Zahra taji kamar tasan muryar dake magana a bayanta.
"Zahra ga my love Mubeen ku gaisa".
Dan juyowa tayi tana fadin.
"Barka da yamma".
Ido cikin Ido sukayi dashi Amma saita dake tayi kamar Nan duniya Bata tab'a ganin Mai Kama dashi bama, Amma shi saida ya Dan so ya rude Dan da kyar ya iya fad'in "lafiya kalau".
Zainab Zahra ta kallo tana fad'in "sai munyi way kenan? Bari na wuce sai anjima ku gaida gida".
Ta juya ta koma gurin da Mahmud din yake Zaune Yana faman daddanna wayar hannunsa, da kallo Muneeb din ya bita sai kuma idonsa ya sauka akan Mahmud. Da sauri ya nufi inda yake zaune yana karasowa ya Fara fad'in .
"Wa nake gani kamar Mahmud Dange a gurin Nan?".
"Nine Mana muneeb sale,daman talaka na ganinku?".
"Tuba nake yallabai wane ni ai ku ganinku sai Mai sa'ar gaske Nima tsintuwa nayi Allah ya tsaga da rabona a yau, Daman kana kasar nan watannin baya akace min kana uk can ka koma da zama".
"A'a gani kuma a Nigeria,kawai dai nayi tafiya ne wadda na jima shine ake cewa nabar k'asar'.
Zahra dai Batasan inda suka San juna ba Amma da gani sun yiwa juna farin sani.
Zahra Bata San Abinda Mahmud ya bawa Muneeb ba taji dai Yana godiya kamar ba gobe Saida suka tafi Mahmud ya kalli Zahra.
"Gafa ex-boy friend dinki Wanda ze min shigar sauri".
"Daman kasan shi ne? Naga the way yanda kuke magana da sanayya sosai a tsakani".
"Zomu tafi wannan Kuma sirrine".
Sai dare suka karaso gida saboda go slown garin, sati daya sukayi a Lagos suka dawo sokoto, sun dasa wata irin soyyaya Mai tarihi a Lagos Dan ba karya sun gane juna yanda ya kamata, da gani kasan suna cikin ganiyar kuruciyarsu ga wadatar arziki sai abun yayi musu wani irin kyawu na ban mamaki, satinsu Daya da dawowa Ammah tazo sokoto, ai tun daga gate din gidan Alhaji Muhammad Dange Ammah ta Fara tasbihi ga Allah s. w. a Dan ko makaho ya shafa yasan da abun Wai an Rana nik'a da Akuya.
Ammi ta yiwa Ammah tarba ta girmamawa kamar ta goya Ammah sun Dade suna Hira tamkar Aminai Ammi tayi godiyar karamcin kyautar 'ya sumutum da akayiwa Mahmud ba tare da la'akari ko shi waye ba, an Kai Ammah gidan Hajiya Inna sun gaisa sun aje Mata tata tsarabar da sakon Abba Daya bada a kawo Mata, ai Ammah Bata k'ara tsinkewa da Lamarin ba Saida ta shiga gidan Zahra tasbihi kawai take ga Allah Dan wani garin yafi gaban kunu, Ashe Bataga komai ba Saida idanunta suka nuna mata.
Tana kasa suna Hira da Mahmud suka shigo tun kafin su taso magaji ya Kira shi ya fada Masa gasu nan tare da Ammah Amma tace kada a fadawa zahra bazata kwantar da hankalinta ba idan tasan zasu shigo gari, ya dai ce Mata ayi special girki zasuyi Baki,suna zune aka Danna door bell baiyi amfani da remote control ba yace ta tashi ta bude, ba musu ta tashi tana tafiyarta kamar tana tsoron taka kasa ta bude kofar, ai ita dai Zahra Batasan lokacin da tayi wani uban tsalle ba ta fada jikin Ammah sai kuka tana fadin.
"Yanzu a kasa fada min gakunan a hanyar zuwa, wallahi magaji mun Bata da kai na fasa rik'on wallahi tunda kaci amanata".
"A'a ki tuhumi Ammarki da mijinki sune Basu fada Miki ba,Ni Dan Rakiya da sai yanda akayi Dani".
Har suka shigo zahra na jikin Ammah tare suka zauna kamar zata shige cikinta sai dariya magaji yake musu Dan itama Ammar idanunta kamar ruwan hawayen ne, sun gaisa da Mahmud sosai sannan Zahra ta Kira Aunty zilai a waya tace tazo ga Ammah, sai gata da gani harda gudu ta hado, dan Sai daga bayanta sannan Binta ta shigo, murna kamar me sai dariya take yi Mahmud fita yayi magaji ya bishi tunda ya cika cikinsa a gidan Ammi.
Bayan fitar Mahmud Zahra ta tashi ita Aunty zalai suka shiga fito da kayan abinci dasu drinks tamkar mutum goma ne zasuci sai da Ammar ta tsawatar musu tana fadin.
"Ke Zahra duk waye kuke kawowa wannan abincin haka? Nifa na koshi naci na surukarki mace Mai kirki ga nagarta".
Zilai ce ta karbe zancen "wallahi kuwa Ammah kirkinta ya Isa gashi kamar ta goya uwar dakina Dan so da kauna wallahi Ammah ranar Nan Ina mofin a wancen parlourn naji Yana fadin "wallahi Ammi Ina son Zahra ki tayini sonta". Bansan dai Abinda ta fada masa ba naji dai Yana jera Mata godiya".
Babu laifi Ammar taci abincin,Saida ta Gama suka haura sama tayi sallah, ta shishshiga ko Ina ta gani tana godewa Allah Daya bawa marainiyar ta gidan da ko cikin mafarki Basu tab'a zato ba.
A Nan zahra ta zazzagewa Ammah yanda Mahmud yaje asibiti yayiwa Mama tatas, abun ya bawa Ammah mamaki kenan shi harya gano abunda ta kasa ganewa shekara da shekaru, sannan Ammah ta fada Mata Mahmud ne yasa aka dawo da Salma daga Jos da duk abinda ya faru har tarewar Hameeda wancen satin, duk sai tausayinsu ya Kama Zahra ganin ita 'yar riko ma Abba ya zage dantse yayi abun azo a gani na shidimar daurin Aure to bare Kuma na 'yayan cikinsa wadanda daga su ba saura 'ya mace a gidan Kuma Amma ace abun yazo haka a hagunce babu Dadi duk da ance yayi musu komai Amma dai ba haka akaso ba.
Sai karfe hudu da minti goma su Mahmud da magaji suka shigo gidan, a gurguje saboda lokaci jirgin hudu da rabi zasu bi zuwa Bauchi.
Mahmud da kansa ya Kai Ammah airport tare da zahra sukaje lokacin da zasu shiga jirgi rike Ammah Zahra tayi tana kuka da kyar Ammah ta lallabata ta wuce lokacin da zata shige ta juyo sai taga Mahmud ya rungumeta da gani lallashinta yake yi.
Bayan sati Daya visa dinsu ta fito inda zasu Fara shiga India gurin Baba malam tunda an sallamesu suna gidan Mahmud din, tare suka juya da Aunty Aishat saboda hutun su Abulkhairi ya kusa karewa.
Tun daga airport kowa yayi nasa gurin ita Aishat Ya Abbas yazo suka wuce, su Kuma Mr salahuddeen yazo ya daukesu.
Sun samu jikin Baba malam yayi sauki sosai Dan Yana tafiya da kafafunsa sai Dan abunda baza'a rasa ba Kuma sunce sai a hankali komai ze zama normal, murna da farin ciki ba magana kamar malam ya hadiyesu Dan farin ciki Dan yanda ya gansu yasan suna cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Da dare ne Mahmud suka zauna da Malam ya warware masa zare da abawar Abinda ya faru dashi Wanda ya sabbaba fitowarsa daga gida, sannan ya juya ya kalli Habib da yake Zaune Yana saurarensu.
"Habib".
Mahmud ya kirawo sunansa.
"Na'am" ya amsa.
"Wadannan shugunan na kayan motoci Daman da sunanka nayi komai ai ka sani lokacin har kana korafin ya za'ayi haka nace ka barshi duk Daya ne, anyi hakan?".
Kaiya gyada kafin yace "Tabbas anyi haka".
"To Alhamdulillahi, Daman nayi ne da sunanka lokacin bani da bakin fadar hakan shine dalilin, sai Kuma shagunan da aka zuba Atamfofi da su laces da materials Dana kayan Yara, ina ga shida ne ko?".
"Eh haka suke".
"Ok.to na Ammah ne Kai na wakilta kaje ka kaimata takardun shugunan da duka lissafin daka turo min ka mayar dasu cikin Account dinta, Sai Kuma sauran kantin Nan guda hudu na shaddoji da sauran kayqn maza da sabuwar plazar Nan Mai sunnan malam wadda aka bude a katagum road duka na malam ne, gidan kusa da Malam sani Mai wankin hula duk da dai bakasan anyi gininba to na Ashiru mai shayi ne, Shima yayi abin a yaba Masa ya bani shayi ba adadi nayi nayi ya karbi kudin yace a'a Kuma na fadawa Sameer a bashi jarin sana'a bayan shayi badan ya manyanta ba da Kano Zan kawa shi kamfani to nauyin iyali sunndanne shi, ka karbi takardun gidan suna hannun Bilyaminu sai kaba Baba malam ya bashi ayi min godiya kafin na shigo garin".
Tunda Mahmud ya fara bayani malam ke jinjina Kai yasan za'ayi haka Dan yayi istihara yafi sau shurin masaki Amma babu canji wata irin daukaka yake gani tare da yaron.
"Allah yayi maka Albarka ya shiga cikin dukkan lamuranka yanda ka kyautatawa bayin Allah Ubangiji ya kyautata lamuranka na duniya da lahira yayi maka tukuici da gidan Aljanna ya baka zuri'a dayyiba ya Kare gabanka da bayanka ya Kara arziki Mai Albarka, lallai Ubangiyi maji rokon bawayinsa ne nayi Addu'a tun Ina da kuruciyata Ashe sai girma ya kamani Allah ze tabbatar Mana da abun, sannu mahmudu kaji mun gode! Mun gode!! Ubangiji yayi jagora".
Saiya sadda kansa kasa sai Jin shashshekar kukansa sukaji.
Nan da Nan Mahmud ya rude Yana tambayarsa menene? Sai da yayi Mai isarsa sannan ya shafe hawayen.
"Mahmudu wani Alherin sai kayi hawaye, wallahi yafi gaban dariya me Zan cewa Ubangiji banda nayi ta tahamidi ga sarki rabbil Izzati. Alhamdulillah!. Alhamdulillahi!! Alhamdulillahi,!!! Alakulli halin.
Fitowa su Mahmud sukayi Nan compound din gidan shida Habib, suna Ida fitowa Shima Habib ya Fara nasa matse hawayen Yana fadin "wallahi bani da bakin yi maka godiya kayin min gata na gidan duniyar Nan kayi min Abinda bani da halin yinsa akan yayan mahaifita Allah yayi maka sakayya da Aljanna madaukakiya".
Kafadarsa Mahmud ya Dan doka kadan.
"My man kana bada maza fa gurin yawan kuka nan ai namijin duniya baya kuka duk wuya duk dadi, haba! Be strong Mana Dole ka baro gida ka shiga duniya kaga yanda maza ke yin kwakawrmaya, Zan fadawa Baba malam dole a cikin uku ka zabi Daya ko Nan India ko Dubai ko Kuma China,amma saina hadoka da Ubaidat yanda aikin ze tafi yanda nake son ganinka, zamanta kusa da Kai ze Kara maka support ba kadan ba, tunda Nima ban samu nutsuwa ba Saida kuka bani Kanwar ku, Zan fadawa malam ayi maganar biki a kusan Nan ku tattraro ku taho".
Ya fada Yana Masa murmushi, Shima Habib murmushin yayi kafin yace.
"Ai Ubaidat an kasani ta samu Mai kudi a Itas gadau Amma mazaunin Abuja har anyi biki wata Daya Daya