Author : Yusrah Musa Category : Complete Novels
tafi garinsu zanje na dawo da ita".
Zaro ido Auwal yai "ka dawo da ita kuma akan me sai kace wanda ka aureta".
Alpha bai tsaya sauraron sa ba fuuu ya d'ebi mota da mugun gudu ya fita a gidan kai Auwal ya jinjina yana shiga cikin gidan ganin mom dinsu tsaye yasa ya karasa zaiyi magana ta katse shi.
"zancen me kuke da Alpha ina zaije naji kana hana shi"? Zama Auwal yai yana sauke ajiyar zuciya yace "wai budurwarsa Lami ce zata koma garin ku shine zai bita bansan me zaiyo ba gaskiya Alpha ya zauce da yawa".
Kai mom ta girgiza tana cewa "to nikam me zance Alpha yayi nisa a son yarinyar nan fatana da addu'a ta kullum shine Allah yasa rabonsa ce idan ya rasa ta a rayuwa bansan wanne irin hali zai shiga ba".
Mi'kewa Auwal yai yana shirin fita a parlon yace "bari nabi bayansa ko a mashin ne" mom batai magana ba har ya fita samun guri tai tana zaman jiran dawowar su.
A tasha ya samu Alpha yana ta duba motoci duk ya had'a gumi karasawa yai yana cewa "ka gansu ne ko sun tafi"? Kai Alpha ya girgiza "a'a ban gansu inaga saidai naje mu tafi da Najat ta raka ni garin idan ban ganta ba hankali bazai ta'ba kwanciya ba" ya karasa maganar yana yin wajen inda yai parking da motar da sauri Auwal ya bishi yana rike shi yace.
"A'a Alpha kada kayi haka dan Allah mom bazata ji dad'i ba ka bari mu koma gida saika fada mata nima zanyi maka rakiyar ka nutsu" shiru Alpha yai ya kasa magana Auwal dake kallon shi yace "shiga muje" kaiya girgiza "bazan iya tu'ki ba" "ok bani key din shiga mu tafi" bashi yai yana shiga Auwal ya tada mota suka wuce zuwa gida.
Har lokacin mom tana zaune a gurin ganin sun shigo da yanayin da Alpha yake ciki yasa ta fahimci basu sameta ba zama sukai mom dake bin Alpha da kallo tace "baku samesu ba"? Kai Auwal ya d'aga "eh mom sun tafi da binsu zaiyi amma na hana nace ya bari mu dawo gida yaje daga baya" kai mom ta d'aga tana kallon alpha tace "kaga auta na kayi hakuri in Allah ya yarda wannan yarinyar zaka aureta bari Abbanku ya dawo zan sanar masa sai musan me za'ai" shidai Alpha yana shiru baice 'kala ba Auwal daya mi'ke yace "ai mom wannan soyayyar tasu irinta ake so kaso mutum tsakani da Allah Alpha yana burgeni nima inaso ya aureta domin ta kasance farin cikin sace Allah ya tabbatar da alkairi" Amin mom tace tana sake kallon fuskar Alpha wanda ya shiga mood altering kawai baya cikin hayyacin sa dan girgiza kai tayi tana masa addu'ar samun nutsuwa a zuciyarsa
Ramatu kam suna tafe tana zazzaga mata bala'i har suka hau mota bata daina kumfan baki ba kowa a motar sai mamaki yake
Lami tari da bai kamata ba batai ba har suka sauka kowa a garin kallon yake ana ta tsegumin Ramatu taje ta taho da 'yarta haka suka shigo gida Baffah na zaune kan tabarma a kofar d'akinsa gefen sa Habu ne da Sabi'u suna hira sai ganinta sukai kamar an jefota ga Lami a bayanta ko kallon inda suke batai ba ta wuce d'aki karasowa gaban su tai tana kallon Baffah zatai magana sai kuma tana fashe da kuka tare da durkusawa.
'Dagowa Baffah yayi yana kallon ta tausayi da damuwa fal a ransa yace "Lami kiyi hakuri da irin uwar da kika samu ki dau kaddara ki jure wata rana sai labari kuma duk abunda zatai miki ki bita mahaifiyar kice kada ki sa'bawa umarninta kinji insha Allahu zaki samu nasara" kai Lami ta d'aga tana mi'kewa tace "nagode Baffah na gode da samun ubah na gari irinka me share hawayen 'yarsa".
"Karki damu Allah ya miki albarka" Amin Baffah Lami ta fad'a tana wucewa da kallo suka bita duk su ukun tsaki Habu yayi yana cewa "Wai dan Allah Baffah yanzu haka zamu zuba ido mu bar yarinyar nan tana cin ba'kar wahala kamar ba a gurin uwarta take ba gaskiya nifa babah Ramatu ta kaini bango zan dau mataki akanta".
Gyara zama Sabi'u yai "eh kayi gaskiya Habu dole mu gyara zaman gidan kamar ba mafad'i Baffah koda ace baka raye iyakaci kenan balle kana nan gamu amma ace gida ya lalace dole mu canza al'amarin gidan nan zamu zauna gabadaya yau da dare mu ji matsalar kowa mu gyara zaman mu kaji Baffah".
Kai Baffah ya d'aga "to naji zancen ku kuma na amince domin nima ina son hakan ina kaunar ganin ahlina cikin farin ciki ina son naga suna walwala musamman yarinyar nan Lami ina jin tausayin ta a raina har bansan yadda zan kwatanta muku ba na amince kuyi komai kun cancanta ku 'ya'ya ne na gari".
Kai Habu ya d'aga "shikenan Baffah idan anyi sallar isha zamu samu zama dukkan mu don magance damuwar gidan nan kowa ya fad'i abinda ke ransa".
"Kwarai Habu kayi gaskiya haka za'ai Allah ya kaimu daren" Sabi'u yayi maganar yana mi'kewa yace "lokacin dawo da dabbobi gida yayi Habu taso muje" tashi habu yai suna fita yayin da Baffah ya bisu da kyakkyawar addu'a cikin jin dad'in samun su dayai matsayin 'ya'yansa nagartattu.
Bayan sallar isha kamar yadda suka tsaya haka suka shigo suna shimfida manyan tabarma guda biyu Baffah ya zaune suma suka zauna ga Salamatu da Ramatu Lami na gefe kad'an da Baffah saida suka nutsu kowa yai shiru Baffah yace Sabi'u ya bud'e musu taro da addu'a.
Duk hannu suka d'aga Sabi'u yana jero addu'o'i suna Amin Amin harya gama suka shafa sannan Baffah yace.
"Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu".
Duk amsawa sukai "Amin alaika salam wa rahmatullahi wa barakatuhu".
Kafin Baffah yace Ramatu tayi farat tace "nifa na gaji bacci nake ji, meye ne na tara mu haka abinda ban ta'ba gani ba sai yau ko wata sabuwar tsirfarce ta samu"?.
Ba wanda ya kula Baffah dake kallon sauran yace "to alhamdulillahi ina godiya ga Allah daya nuna min wannan rana duk da banyi tunani ba na sani zakuyi mamaki zakuyi ta tambayar zuciyar ku meya faru akai kiranku ba komai bane dama na tara kune akan naji meke faruwa meke damunku kowa ya fad'i matsalar abinda ke ransa ina sauraron ku Salamatu mu fara daga kanki domin kece uwar gida kece babba"?.
'Dan shiru Salamatu tai tana tunani na 'yan mituna kafin ta d'ago tana kallon kowa tace "eh to gaskiya nikam ta bangare na babu komai ina wa kowa kallon kima da mutunci yara kuma na rikesu daya bana bambantawa ina yabawa da nagartarsu da kyakkyawar tarbiyyar da suka samu a gurin malam bani da bakin godiya gareka saidai nace Allah ya saka da alkairi kayi mana komai matsayin ka na me gida baka ta'ba gajiyawa damu ba ta bangaren abinci sutura harda kud'in kashewa na ihsani ka biya dukkan komai nauye nauyen dake kanka ka sauke ka karemu mu da karfinka da jarumtar Allah fatana a koda yaushe Allah ya kyautata ka kamar yadda ka kyautata mana" ta karasa maganar tana share hawaye.
"Amin nagode sosai Salamatu da shedar arziki da kikai min ina da ya'kinin cewa ko bayan raina zan samu yabo a gareki" juyawa yai saitin Ramatu yana cewa "Ramatu saura ke na dawo gareki kema meke damunki me yake faruwa akwai abinda ake miki wanda bakya jin dad'in sa".
Gyara zama Ramatu tai "nikwa ni akewa abinda raina baya so dan duk gidan nan babu wanda aka rainawa hankali kamar ni Kowacce bola aka d'ebo ni za'a lodawa saboda an tsane ni bansan me nai maka ba gara daka za'bi a zauna aji matsalar kowa sannan Ilyah ma yana da matsala domin munafikan yaran ka Sabi'u da Habu sun ware shi suna nuna masa 'yan ubanci komai su biyu suke babu ruwan su dashi".
Wani kallo Habu yaiwa Ilyah yana cewa "shine yace miki ba ruwan mu dashi sau nawa muna binsa yana zamewa ko abinci da kike ganin muna ci mu biyu ga Ilyan nan ki tambaye shi har gobe idan zamuci sai mun masa magana amma yace Allah ya sauwake to ya kike so muyi iya so muna nuna masa baya gani kema bakya gani bari kiji wata magana daga yau baza mu sake...........................
Katse shi Baffah yai "Habubakar bari kayi shiru haka Ramatu uwa ce gareka".
"Ah dole malam ka gama 'kwarkwance su cewa su wulakanta ni kuma yanzu dan kar nace da hannunka shine harda wani kayi shiru ni uwarsa ce tab Allah ya suturu bu'kwui inji kishiyar 'konanna nikam ban haifeshi ba yaje can kabari ya nemi uwarsa na haifi wanda na haifa".
Kowa kallon Ramatu yake da mamaki duk da dama ba ba'kuwarsu bace amma cewar Habu ba d'anta bane yaje ya nemi uwarsa a kabari bai kamata ba bata kyauta ba.
Baffah yaji zafin hakan da tace amma ya share cikin kaiwa zuciyarsa nesa yace "Ramatu wannan shine abinda yake damunki sun ware Ilyasu a cikin su babu ruwan su dashi haka ne"?.
"Eh haka ne basa kaunarsa kuma idan sharri na musu ko suna ganin na musu karya ka tambaye su basa kaunar Ilyah sam".
Kai Baffah ya jinjina "shikenan naji matsalar ki bari nayi magana dasu" kallon Sabi'u yayi yana cewa "Sabi'u meye matsalar ka matsayinka na babba cikin 'ya'yana kaine jagoran gida".
Fara magana Sabi'u yayi "ni Baffah damuwa ta rashin biyayyar da Ilyah yake maka da zama cikin samari yan shaye shaye da yake bugu da 'kari kullum idan muka ce yazo muci abinci ko kallon arziki baya mana matsayin mu na 'yan uwansa baida kamar mu a duk fadin duniya ko me zaiyi saiya yi shawara damu Baffah ka fahimtar dashi ka farkar dashi ka tuna masa matsayin mu a gunsa".
Yana rufe baki Ramatu ta wurga masa harara tana cewa "dama har wani matsayi kuke dashi a gurinsa in kuna tunanin kuna da mahimmanci ku daina Ilyah ba sa'an shirmenku bane abinci kuma bazai ci daku ba wannan doka tace dana kafa masa har abada".
Cikin 'bacin rai habu yace "to saime dan kin hana shi hakan bazai rage mu da komai b.....................
"HABUBAKAR kayi shiru dan Allah ka bari Ramatu uwace a gunka" Salamatu ta fad'a tana d'aga masa hannu huci Habu keyi ransa duk babu dad'i amma sakamakon Salamatu tayi masa magana yasa dole yai shiru bai amayar abinda ke cin ransa ba.
Baffah baice 'kala ba ya kalli Ilyah dake gefe kamar ba babu shi a gun yace "saura kai Ilyasu muna sauraron ka meye matsalar ka".
'Dan tsaki Ilyah yaja yana kau dakai kamar bazai magana sai kuma yace "ni bani da matsala kalau nake rayuwa ta idan akan haka ka tara mu ni zan fita dan ina da gurin zuwa daya fi min wannan zaman".
Kaiii duk kallon sa sukai a hasale Habu yace "Allah ya wadaran ka Ilyah wallahi kaji kunya kayi asara wannan d'abi'ar daka dauko sam babu inda zata kai ka sai halaka tun wuri ka gyara kafin lokaci ya'kure maka".
"Ban sako dakai ba Habu kada na sake jin bakinka yace min wani abu idan ba haka ba ran kowa da yake nan saiya 'baci" Ilyah ya fad'a tare da mi'kewa ya kalli Baffah dake binsa da kallo kafin yace.
"Kaja masa kunne ya fita harkata kafin ayi 'batacciya sai nayi abinda kowa zaiyi danasani".
"Yau d'an halak haka nake son ji karka ragawa kowa" Ramatu ta fad'a tana hararar Habu.
'Diban takalmansa Ilyah yai zai fita Baffah ya dakatar dashi "kada ka fita Ilyasu bamu gama magana ba ka zauna ban baka izinin tafiya ba".
Batare da Ilyah ya juyo ko ya dakata daga tafiyar da yake yace "dama umarnin ka nake nema saika sani abu zanyi basan zauna ba na fita zaka iya sawa a taro ni".
Da kallo suka bishi yana fita Baffah da gabadaya zuciyar sa ke masa zafi take masa shiru yayi ya rasa me zaiwa Ilyah ya dawo kan hanya addu'ar nan kullum yi yake ba fashi amma abun na Ilyah gaba yake saidai bazai 'kosa ba zaici gaba da nema masa shiriya...................
"To nima dai zan tashi dan na gaji bacci nake ji" Ramatu ta fad'a tana mikewa ta shige d'aki tare da rufo kofa.
Har lokacin Baffah yana shiru ganin yanayin yasa Sabi'u cewa "kayi hakuri Baffah mun 'bata maka rai ka yafe mu na dauka idan muka samu zama zamu fahimci juna ashe saidai mu fahimci damuwa munyi kuskure bansan me zamuyi yanzu ba na kasa gane komai".
"Me zamuyi kuwa daya wuce hakuri da addu'a dan Allah Baffah kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka insha Allahu komai zai setu" Habu yai maganar.
Ganin dai jiya iyau Baffah baice komai yasa Sabi'u cewa "BAFFAH ka gafarce mu dan Allah idan mun saka a wani hali".
'Dagowa Baffah yayi yana kallon su tare da girgiza kai yace "Sabi'u Habu Allah ya muku albarka baku ta'ba 'bata min ku farin ciki nane ina alfahari da samunku ina fata ku kasance cikin farin ciki har abada Allah ya tsare min ku ya shiga al'amarin ku ya baku 'ya'ya da matan aure na gari yasa ku gama da duniya lafiya duk abinda kuka san zaisa naji dad'i kuna kokarin yi min Allah yasa kuma ku samu masu yi muku".
"Amin Baffah mun gode sosai".
"Karku damu kuje ku kwanta" mi'kewa sukai suna masa saida safe ya rage daga shi sai Salamatu da Lami kallon Lami yai yana cewa "kiyi hakuri ke ba'a tambayi taki damuwar ba ko"? Kai Lami ta girgiza tana share hawaye cikin takaicin abinda taga Ilyah ya masa tace "ka gafarce ni Baffah ka yafewa yaya Ilyah abinda yake maka ka bishi da addu'a ka masa fatan gamawa da duniya lafiya shine fata na".
Kallonta Baffah keyi yarinyar nan za'a tona kafin a samu irinta zai wahala shiyasa koda yaushe yake farin ciki da samunta matsayin 'ya gareshi sake kallonta yayi yana cewa "kada ki damu indai wannan shine burinki zan cika miki tashi kije ki kwanta" mi'kewa tayi tana masa saida safe ta tafi, numfasawa Salamatu tai tana kallon Baffah tace.
"Malam na sani kana cikin damuwa a gidan nan mun gaza gyara zamantakewar mu badan bazamu iya ba sai rarrabuwar kai nayi tunanin a yau zamu magance matsalar mu amma sai naga abun yaci tura dan Allah malam kayi hakuri" kai Baffah ya girgiza "babu komai Salamatu tashi kije Allah ya mana sutura" Amin tace tana mikewa itama ta shiga d'akinta aka bar iya Baffah a tsakar gida yana sa'ka da warwara ya dad'e kafin ya mi'ke yana daukar buta yai alwala ya shiga d'akinsa ya fara nafila yana rokon daidaituwar al'amari a tsakanin zaman zuriyar gidan sa.
MRS AL'AMEEN AHMAD CE 馃槝 MAI TAMBARIN YMA DUTSE 馃彏锔忦煆旓笍 JIGAWA STATE.
TYPING 馃摬 SAT, MAR 23/24 Yusrah Musa Abubakar 馃挒馃尮 maman little Zaran aunty.
馃挮 ANNURI WRITER'S ASS馃挮 HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY GIDAN KARBAR MUTANE HANNU BIYU 馃尮馃 DA ZAMAN LAFIYA ANNURI HASKE LEKA GIDAN KOWA KODA MAKIYA NA KALLON KA RAMIN KURA SAI 'YA'YAN TA KIRARIN MU KENAN.
Ya mai nasiha ga alumma muso juna mu rike gaskiya amana dan gudun kuna mu raya zuminci hanya ne na aljannah makiyin zumunci baya kusanci ceto ba ga wassu baitukan soyayya maula na daga masoyiyar ka Yusrah ta dumus yar Musa.
_______________________
Allahu dan isar bawan nan da ka Aiko shine Muhammad rasulullah daya sauko me sansa ka fad'i ba shakka zai karko albarcinsa bani basira me fad'i ka bani hikkimar sarrafa waka alhadi idan nayita bata ga buri aji dad'i a kara kankame soyayyar manzo na.
馃拫YUSRAH MS ABUBAKAR MUHAMMAD馃拫.
23~AR-RAFI'U
The exalter
24~AL-MU'IZZ
The giver of honour
12~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Khaidinah.
馃寗THREAT ND TREASON馃寗
Episode 23 nd 24
Bayan kwana biyar da faruwar haka Tanko ya dawo daga d'an yawon shashancin daya je ko hutawa baiyi ba Mudi ya munafirta masa cewa Lami fa ta dawo ya kamata suje su lallameta kafin wannan d'an birnin ya biyota idan sukai sa'a ta amince zata aure shi yarda yai da shawarar Mudi yace gobe zasuje.
Washe gari da magriba suka je kofar gidan Baffah suka sa aka yiyo musu magana da Lami tayi mamakin ganin Tanko har mamakin nata ya'ki boyuwa ranta a'bace tuna wulakancin dayai mata a dandali kwanan baya tace "meye ya kawo ka Tanko ko 'batan kai kayi tun wuri ka saitawa kan ka hanya".
Tanko na shirin yin magana Mudi yai gyaran murya yana cewa "haba Lami kamar baki le'ka birni ba zaki mana wulakanci sannan baki tsaya kinji abinda zan fad'a miki ba kawai kika yanke hukunci".
A fusace Lami tace "baka da wani abu da zaka fad'a min wanda zaisa na saurari Tanko kamar yadda ya tozarta ni a gaban kowa nima tun daga ranar na zubar dashi a rayuwa dan haka ka barni dan Allah naje nayi rayuwa ta".
Zata juya Tanko ya katse ta "haba Lami ki tsaya ki fahimce ni muyi maganar gaskiya nasan na aikata miki kuskure banyi dadai amma kiyi hakuri kinsan ina son ki".
"Na sani kuma na gode da soyayyarka gare ni saidai ka sani ka makara domin na riga na hakura dakai Tanko dan haka ka kyale ni nayi rayuwa ta".
"Bazan rabu dake ba Lami har sai kince zaki aure ni kin rabu da wancan shashashan tsigalallan birni".
"Kada ka sake zagin sa".
A hasale Tanko yace "na sake shi dambun uban sa wato kinje ya zuzzuga ki shine zaki min rashin mutunci" "ba rashin mutunci nayi maka ba Tanko kawai na nuna maka gaskiya ne kayi hakuri bazan iya aurenka ba na riga na hakura dakai dan Allah ka fahimta ka rabu dani".
Kai Tanko ya jinjina "shikenan na barki har abada kuwa jeki abinki" yana rufe baki Lami ta fad'a gida da sauri kai Tanko ya jinjina yana jan tsaki yace "lallai yarinyar nan ta kira ruwa saina gwada mata rashin imani na dan ko yayanta Ilyah bai isa