Author : Yusrah Musa Category : Complete Novels
gabadaya tare da fara tunani da nazarin yan uwan nata da abinda yake faruwa to meke damunsu ace ubansu d'aya suna son mutum d'aya akansa suna neman jefa fitana fad'a da 'kiyayya a zuciyarsu wanda ta tabbata Asad zata iya rantsuwa da Allah tayi masa farin sani basa gabansa babu wacce zaiso a cikonsu bawai tanai musu fata bane amma bata ji a jikinta cewa akwai matar Asad a tsakanin Khimiyyah da Makiyyah kawai haukan su suke sauke numfashi tai tana sake jan bargo ta rufe har kanta tayi shiru tun tana tunani har barci ya d'auketa.
MRS AL-AMEEN AHMAD CE 馃槝馃ぉ.
Thanks for ur support馃挀馃挴馃挀馃挴馃 I really appreciate it 馃尮馃挀馃挆馃挒 Allah yabar 'kauna yan uwa insha Allahu gobe xakuji ta yadda aka samo asalin tushe ta wannan 'kungiya da farkon wanda ya samar da ita da had'arin da take dashi馃懝馃懣鈽狅笍馃拃.
Typing馃摬 sun jun 9/24 yr Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty 馃拑馃馃馃檵馃し.
Mai tambarin yma dutse Jigawa new world 馃尮馃 new life and new style sabuwar duniya kuzo kuyi kallo dad'i yana Jigawa 馃槣 garin ilimi garin addini zaman lafiya Jigawa 鉀帮笍馃彏锔忦煑.
Ranar muce masoya maza karda muyi sanya muyu rausaya yan uwa mu taho da baya baya mune muke shagali馃拑馃拑 ranar mu tayi haske 馃寖.
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 馃挮 HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY GIDAN KAR'BAR MUTANE HANNU BIYU DA ZAMAN LAFIYA ANNURI HASKE LEKA GIDAN KOWA KODA MAKIYA NA KALLON KA RAMIN KURA SAI YAYANTA HAKA TAKEN MU YAKE 馃尮鉁岋笍.
STORY AND WRITTEN
鉁嶏笍YUSRAHMS ABUBAKAR 馃尮馃 MRS SIR馃憣 YALLA'BAI馃檱 MAI GIRMA馃檯 MAI NASARA馃 MAI D'AUKAKA馃 BABBA馃 KAFIN ALLAH ALHAJI馃憢 KAINE GATANA馃 AL'AMEEN NA YUSRAH KAKE MALAMINA馃槏 OGANA馃檲 MAI GIDANA馃し LIMAMINA馃し SUPERSTAR猸愷煂狆煂 D'INA SIR AL-AMEEN AHMAD馃槝馃槝馃槝馃檱馃檯.
Wannan page din naka ne dan uwa rabin jiki NURA SANI ABBAN MUHAMMAD AND SHUKHRAH FATAN ALKAIRIN ALLAH YAKAI MAKA DUK INDA KAKE BROS馃挴 NA YABA DA KYAWUN HALAYENKA馃憣馃憤馃挀馃挴.
#Vote
#share
#fallow.
yusrahmusa65@gmail.com 馃檯.
__________________________________
37~AL-KABIR
The Great
38~AL-HAFIZ
The preserver.
18~Allahumma salli wa ala sayyidina muhammadin sayyidil Hafizinah.
馃寗WITCHERY ND SUDDENLY馃寗
Episode 37&38.
A cikin wani 'bakin kumburarran mummunan fusataccen daji na tsafi masu duhuwa ababen tsoro da mugayen manya bishiyoyi a tsaye d'ima d'ima kamar tsaunuka masu wasu irin ganyaye da rassa abin tsoro kallon su kad'ai zai iya tashar maka da hankali lokaci guda ka fita hayyacinka musamman in suna kad'awa maimakon subada iska mai dad'i saidai su hankad'o wani turnu'kakken ba'kin zafi kamar ana watso tafashasshan ruwan zafi babu wanda yasan da zaman dajin balle har a samu wani mai 'kwarin gwiwar iya zuwa har yace zai binciki wani abu da kuwa ranar za'ai babu shi saidai uwarsa ta haifi 'kaninsa dan zai tafi lahira kai tsaye babu wani jinkiri ko kwano-kwano dajin ya kasance dajine na tsafi ba kowa yake ganinsa ba asalinsa na wasu baka'ken munanan aljanu 馃懝馃懝馃懟 ne horarru wajen iya tsari da sarrafa mugunta babu d'igon imani a tattare dasu basu da tausayi basa d'aga 'kafa basa uziri ko a jariri ne mutum mai gaskiya kuwa basu da ma'kiyin daya kaishi zasuyi fad'a dashi su ya'ke shi akan yabar hanyar 'kwarai d'ai dai ne masu tsallewa tarkonsu ta wannan hanyar suke bi suka halaka mutane da yawa suka rijayo mutane da yawa sukai musu mubaya'a sun kasance anan tsahon shekaru suna rayuwa a ciki tare da wata had'ararriyar shahararriyar bokanya matsafiya abar tsoro mai tsoratarwa asalinta mutum ce kuma ta kasance a cikin mutane daga baya ta za'bi ba'kar rayuwa ta za'bi ta zama masifa da fitina a cikin mutane ta hana su zaman lafiya.馃懝馃懝.
Shiru dajin yake tsit baka jin komai sai dariyarta zaune take a wani ba'kin kogo ta tan'kwashe kafafunta da manya manyan wasu darukan tsafi a gabanta sai sautikan kuka ne ke fita a ciki abubuwa ne 'kanana saika lura zaka gane mutane ne tayi musu tsafi suka zama wadannan yan kananun kamar teddyn roba ta wasan yara ta d'aga kanta sama sai dariya take hannuwanta a bud'e ha'koranta na tsiyayar jini idanuwanta ma haka kayan jikinta duk jini ne a jiki ga takubba馃棥锔忊殧锔忦煆 da wu'ka'ke a gefenta da yawa.
Daina dariyar tai tare da sauke kanta kasa tana kallon darukan muryarta kamar zai fashe tace "kuma ku zama jini domin baku da amfani" ta karasa maganar tana zuba musu wani ruwan tsafi akan a take suka narke jini ya balle ya fara bubbuga nan da nan ya cika gurin tanjan kamar kogi tashi tsaye tai ta fara zagawa da wani sandar tsafi a hannunta ta nuna jinin tana cewa.
"Wannan jinin kaine zaka zama jigon wannan 'kungiya kaine masifa da fitana saika zama bala'i ga duk wanda yaso gano asirin mu saiya hallaka dakai zamuyi amfani wajen kare kanmu da kungiyarmu kaine asirin mu kaine tanadinmu nayi alkawarin saina hallakar da mutane masu tarin yawa dakai" ta karasa maganar tana busa wani abu a take jinin ya 'bace ya zama gurin ya gyaru kamar dai babu abinda ya faru kira ta fara da wasu irin sunaye marasa dad'in ji nan take wasu 'bakaken aljanu 馃懝馃懟 suka fara dira a gabanta masu siffa abin tsora.
Cikin bada umarni tace "ku zama mutane ku bazu kubar dajinnan ku shiga gari gari kasa kasa ku fara aikin dana saku babu tausayi har jariri tsohuwa ko bazata iya tashi ba ku had'o da ita ina so naga na hana kowa jin dad'i da sukuni ina so na tarwatsa farin ciki kuje na baku umarni" nan take suka fara baza fuka fukansu suna tashi suka tarwatse suka watsu ko'ina bayan sun fita daga asalin dajin tsafin suka fara sauka kasa suna zamowa mutane kallon kansu aljanun sukai bayan su komo mutanen sukace wannan siffar akwai kyau dole ne ma muyi aure da mutane muje zuwa kowa ya kama gabansa" nan take kowa yai inda yasa gaba suka bazu d'ai d'ai kamar wasu matunen arziki.
Zaune wani hamsha'kin mutum yake a office dinsa ya jingina bayansa da kujera yana juyawa a hankali idonsa a rufe AC na seseta shi saidai da alama baya cikin yanayin jin dad'i ba wata walwala akan fuskarsa yayi matukar zurfi a tunanin da yake knocking akai masa batare daya bud'e ido ba yace "yes waye? zaka iya shigowa".
Bud'e kofa yai yana shigowa kansa a sunkuye cikin sanyin jiki ya tsaya tare da gaidashi sai lokacin ya d'ago daga jingine a kujerar da yake tare da cewa "lafiya na ganka a haka miya faru"? Kasa magana Safyan yai saboda tunanin abinda zai faru idan ya masa bayanin mutanen da suka bar nan yanzu domin basu bukaci had'uwa dashi ko su samu tattaunawa ba basa bukatar jin komai daga bakinsa saidai ya girbi abinda ya dad'e yana shukawa.....................
"Kai Safyanu magana fa nake maka da akwai wani abu ne"?.
Kai Safyan ya d'aga yana mi'ka masa takardar hannunsa yace "eh yalla'bai gashi sa'ko daga commissioner daga can sama yace a kawo maka" jiki na 'bari yasa hannu ya kar'ba da sauri ya bud'e yana karantawa ganin abinda ke ciki an dakatar dashi aiki sam ba suspect ba balle yasa ran dawowa ba wani abu dazai samu nan gaba takardarsa bazata sake masa wani amfani ba saidai yai kasuwanci yasa ya mi'ke tsaye gumi na tsatstsafo masa yana kallon takardar idonsa yayi ja ransa a mugun'bace yana huci yace.
"What!!!? Ni commissioner zaiwa haka ni zai wulakanta Safyan kaine silar komai kai kaja min asarar rasa aikina wai shin ranar gidan uban wa kaje kabar bakin office d'in nan har wannan tsinannan commissioner ya shigo min office batare da izini naba"?.
Sunkuyar dakai Safyan yai yana cewa "yalla'bai kayi hakuri bada sona bane".
Cikin tsawa ya d'aga masa hannu "zancen banza kenan hakurin uwar wa? Ya zanyi bayan ka jamin masifa ai duk silarka ne komai ya faru munafiki mai ba'kin ido馃檴 yanzu me zakace min shashashan banza shashashan wofi da nace ka tsaya a kofar da baka bar gurin ba taya commissioner zai shigo ya kama ni da wannan yarinyar saboda cin mutumci maimakon ya rufa min asiri mu rufe maganar a office d'ina amma dan ya muzanta ni ya nuna ni 'kwarto ne a gaban yarana ya tozartani ya nuna ni ba mutumin arziki bane eh me zakace akan haka"?.
Shi dai Safyan shiru yai yana sauraron sa dama yasan irin wannan ranar zata zo kullum mutum ka girma amma kana da budurwar zuciya da son lalata yaran mutane kawai ka basu kud'i da motoci dan jin dad'i kamar kai baka haifa ba.
"Safyan tunanin uban me kake ne? Wato ina magana ka mayar dani majnun ko? Yanzun ina commissionern yake"?.
"Ai yalla'bai ba shine yazo ba wani drivern sa ya baiwa shine kawo kuma bai zauna ba tafiya yai".
Komawa yai da baya takwash ya zauna akan kujerar yana sake kallon takardar dasa hannun Governor shikenan ya shiga uku ya fito rana gashi wasu ma'kudan miliyoyin kud'ad'e da yake jiran shigowar su 'karshen wannan watan ne ga bala'in daya same shi tonan asiri biyu babu wanda yasan yayi danniyar kud'in na al-umma ne da gwamna ya bayar ayi musu aiki ya 'boye amma yasan dole yanzu kowa ya sani har gidajen TV za'a yad'ashi dafe kai yayi ransa na 'kuna kansa ya d'au zafi yace.
"Zaka iya tafiya".
"To yalla'bai a huta lafiya" Safyan ya fad'a yana fita "uban na huta ina cikin masifar taya zan samu lokacin hutu" ya karasa maganar yana huci shiru yai yana tunani zuwa wani lokaci ya rasa abinda yake masa dad'i jin ana kiransa a waya yasa ya d'auka jikinsa har rawa yake ya d'aga yana cewa.
"Hello haba commissioner ya zakai min haka wannan wanne irin cin mutumci ne da cin fuska ka nuna min"?.
Daga can 'bangaren commissioner yace "Prof ya kake"? Haushi maganar ta bashi kamar zaice ban sani ba sai kuma yace "ina lafiya amma yanzu abinda kai min ka kyauta kenan commissioner"? Cikin basarwa commissioner yace "oh sa'kon ya iso gareka kenan? Jin yai shiru yaci gaba "idan ka duba zakaga from Governor ne bani ba nima dan aike ne kawai aka bani kuma na isar dan haka yace a fad'a maka babu kai babu 'kara yin aikin gomnati har abada bayan haka yace sisi bazaka samu ba sannan wannan miliyoyin kud'ad'e da kace sunyi 'batan dabo watan daya wuce yanzu yace a fad'a maka ya samesu ta asusun jarinka da yake Australia na kamfanin ka ta hannun Mr wiliyam Emmanuel ka gane gobe zai aika ayi masa 'kwakkwaran bincike acan da abubuwanka saiya tabbatar wannan kamfanin iya kud'in kane Babu na gwamnati a ciki".
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine abinda Prof Jibril yake maimaitawa bayan jin jawabin commissioner muryarsa na rawa yace "commissioner ka taimaka min dan Allah ka roki Governor ya rufa min asiri karya sanar da mutane komai karyaje Australia bincike wallahi zan kar'bo kud'ad'en da kaina zan na dawo dashi amma dan Allah karya fitar da wannan maganar tunda babu wanda ya sani" kai commissioner ya girgiza "a'a prof aikin gama ya gama bazan iya taimakon kaba maganar gaskiya laifin ka babbane ba kowa zai iya gyara maka ba saidai kayi hakuri ka d'auka cewa kamar da bakai aikin gwamnati ba kuma bawai dan mun kama ka da wannan yarinyar bane ko d'aya kar kayi tunanin haka dama gwamna ya gano cewa wadannan kud'ad'en ba 'bata sukai ba kaine ka dannesu ka gane"? Tsaki Prof yaja mai karfi wanda yasa commissioner cewa "oh tsaki ma kake min? To ai shikenan bari na barka da gwamnan sai naga yadda zaka 'kwaci kanka tunda kaiba mutumin arziki bane" jin abinda commissioner ke cewa yasa Prof yace "a'a dan Allah commissioner kayi hakuri kar muyi haka dai kai kasan duk lokacin da akace rai ya 'baci hankali ya 'bata to hankali ne ke nemoshi kaine ka fusata ni shiyasa kaja nai maka tsaki" kai commissioner ya jinjina yana cewa "hakan yayi kyau ai gara dana fusata ka tunda har ka gane idan hankali ya bata hankali ne ke nemoshi kaga da kanka kace hankalin ka ya 'bata kana lalata yaran mutane kamar ka manta kai baka haifa ba amma idan akaiwa naka baza kaji haushi ba haka ne"? Muryar Prof da tsawa yace "enough is enough malam commissioner karka nemi fad'a min magana dan kaga ina kas da kai ina neman taimako a gurinka baka isa ka wulakanta niba" shiru commissioner yai cikin mamaki jin Prof yace "hello kana jina"? Yasa yace "bana jinka amma tunda kai kana jina ka huta gajiya sai anjima" a gigice prof ke cewa "hello hello commissioner please karka kashe min waya ka tsaya ka saurare ni" jin d'if yasa ya kalli secreen din wayar wato ya katse wani wawan tsaki yaja yana buga wayar a jikin bango a fusace ya fice daga office d'in yai hanyar gurin parking din motoci a miliyon ya d'ebi motar da gudu sosai ko lura da yanayin hanya bayai haka ya isa office d'in commissioner ido rufe ba neman izini yaje fakam fakam zai shiga securities suka tare shi kokarin 'kwacewa yake wani gurmujejen 'kato ya kinkime shi yana fita dashi daga gurin saida ya kaishi har waje zai ja kofa ya rufe sannan ya kalleshi yana cewa "commissioner ne ya bada umarni duk wanda yazo karmu barshi ya shiga domin yana aiki ne" yana fadin haka yaja kofar ya rufe.
Kallon kofar ya tsaya yi kamar zai fasa ihu dan ba'kin ciki kafin a fusace ya shiga mota hankali tashe ya nufi gida horn d'in daya sakarwa mai gadi har Saida ya tsoratashi aguje ya tashi yana bud'ewa ko a tsiyace ya danno kan motar wanda a d'ari mai gadin yai gefe cike da mamakin meya samu mai gidan nasa yau ko parking bai gama daidaitawa ba ya bud'e murfin motar cikin azama ya fito yana yin hanyar shiga ciki dan sauri har takalmansa ya zubar da hular kansa duk ya had'a gumi yana karasawa cikin falon ya soma zunduma kira.
"HALIMA KE HALIMA KINA INA FITO YAU MASIFA TA SAMENI馃槪" da gudu ta fito ta ganshi sai kaiwa da komowa yake ya cire babbar rigarsa yayi jifa da ita gefe cike da mamaki tace "alhaji lafiya na ganka a haka"?.
"Hummm Halima ina fa lafiya yau na shiga uku na fito rana dama na mutu kafin naga irin wannan 'bacin ran daya sameni yau".
"Tofa subahanallahi alhaji wani abu ne ya faru"?.
"Meye ma bai faru ba nida wannan tsinannan commissionern ne yasa gwamna ya dakatar dani aiki har abada indai na gwamnati ne ya 'bata takarduna".
Zaro ido tai "to duk meya kawo haka kaidin meya had'aku dashi har abin yai zafi haka"?.
Shiru yai ya kasa bata amsa domin bazai iya ce mata kamashi commissioner yai tare da yarinya ba duk da dama tasan neman mata halinsa ne amma yana jin kunyar ce mata ga abinda ya faru................,...
"Alhaji magana nake menene ya had'a ku"?.
Zama yai cikin takaici yana kallon ta yace "akan baby ne".
Da mamaki Halima tace "baby kuma馃檮馃槒馃槻? Humm tabdijam yau ake yinta wai tsakani da Allah dama alhaji baka daina mu'amala da yarinyar nan ba inace kayi alkawari ashe tuban ba'kin muzuru kai gaskiya ba ka kyautawa kaima ka haifa fa ya kamata ka daina abinda kakeyi ka roki ubangiji yafiya..........................
'Daga mata hannu yai "ya isa haka Halima ba wa'azi nace kimin ba I know abubuwan da nake aikatawa was improper saidai a halin yanzu ba wannan ne damuwata ba, ba wannan maganar nake bukatar jiba ki rufe min baki".
Dama tasan haka zai faru duk lokacin datai masa magana akan haka balbaleta yake da fad'an cewa babu ruwanta idone nata in duniya ce da more shagalin rayuwa yanzu ya fara".
Sauke ajiyar zuciya tai tana cewa "Allah ya baka hakuri" d'an tsaki yaja yana mi'kewa yace "yau zan tafi Australia zanje shima Mr Wiliyam d'in naci uban daya haifi ubansa mitsiyaci maci amana duk bashi kuka d'auka wallahil azim commissioner sai kunyi nadamar abinda kukai min bazan 'kyale kuba zaku sani".
Jin furucin da yake yasa Halima tace "a'a alhaji karkaje kayi abinda daga baya za'a zo ayi dana sani ka tsaya kayi nazari maybe kaine da laifi" tana rufe baki ya daka mata tsawa "Halima ya ishe ki kema tunda baki damu da damuwata ba kin goya musu baya to ki kyale ni nadau fansata" fuuuu ya wuce ta bishi da kallo tare da girgiza kai tace "tabdijan dama nasan koba dad'e koba jima sai wannan ranar tazo asirin ka zai tonu kullum ina tunatar maka amma ga irinta nan yanzu wa gari ya wayewa? Fatana Allah ya kyauta karka jawowa kanka wata masifar dan ko biyu bana rabawa idan kace zaka nunawa Wiliyam wani abu tofa za'ai babu kai mutumin da yake tsaface tsaface har kace zakaja dashi" mi'kewa tai tana bin bayansa da niyyar ta sake tausarsa ta hana shi zuwa Australia taga ko zata iya Allah yasa yaji maganar ta ya ha'kura.
Kusan karo sukai da shi zai fito da jaka a hannunsa tareshi tai da sauri tana ri'ke jakar tace "alhaji ina had'aka da girman Allah kar kaje ko'ina kana cikin fushi abin bazai maka dad'i ba" a fusace yace "sake min na tafi babu ruwanki" 'kara rikewa tai tana kallon yadda idonsa yai jajur tace "alhaji kayi hakuri amma kome zakai bazan sake maka jakar ba" 'karfin sa yasa ya fisge jakar zai wuce aguje ta sake shan gabansa tana cewa "please dan Allah kar kaje ka saurareni".
"Na saurare ki kike cewa bayan kinsan irin tashin hankalin dana shiga ko kin manta abinda ya sameni ne?.
Kai ta girgiza "a'a ban manta ba amma komai yana bukatar nutsuwa" wani kallo ya mata "nutsuwa? Nutsuwa kika ce? Nutsuwa fa? Wai da gaske kike? amma Halima baki da hankali" saroro tai tana kallon sa ganin yadda tayi yace "ke dalla matsa min gefe na wuce........,.............,...
Shiru yai jin ana ambatar sunan sa a TV yasa yaji jikinsa ya d'au rawa yawun bakin sa ya 'kafe idanuwansa kamar zasu fito waje ya zubawa gwamna dake jawabi ido ga Wiliyam zaune kusa dashi da d'ima d'imam jakakkuna sha'ke da