Author : Yusrah Musa Category : Complete Novels
fita a gurin da kallo Isham ya bita yana girgiza kai sannan ya mayar da hankalin sa kan Asad yana cewa.
"Ni kuwa Buddy ya batun abinda kake nema ka gano yarinyar ko har yanzu a'a"?.
Kai Asad ya d'aga masa ''ban ganota ba amma dai bincike ya nuna min 'yar Nigeria ce zuwa gidan da nayi tazo min a mafarki tayi min bayani sosai akan 'kungiyar kuma na yarda da abinda ta fad'a min domin dajin da suke ciki tabbas ba dajine wanda yake a bayan qasa ba dajine na siddabaru ba'a iya ganinsa kuma dole saida wata sar'ka ake iya shigarsa tace min akwai sar'kar a wuyan kowanne d'an 'kungiyar to amma Isham abinda na gagara fahimta har yau shine ita yarinyar mutum ce ko aljana idan mutum ce taya ta sani bayan tana karamar yarinya kuma ba wata babbar ma'aikaciya ba a cikin bincike na nagano bata da ala'ka da wani wanda yake neman 'kungiyar kuma batasan ana neman 'kungiyar ba sannan kullum suna cikin yi mata barazana duk ranar data fad'awa wani zasu hallaka ta amma haka bai bata tsoro ba a halin yanxu maganar da muke dakai mafi yawancin abubuwan da suke aikatawa ta sani d'ai-d'ai ne suka 6oye mata shi sai dai Isham nayi iya kokarina amma na gaza ganota na rasa inda take da kamar ace zanyi sa'a ta kunna location d'inta shine zansan inda take kai tsaye amma matukar mukaci gaba da tafiya a haka har abada bazan san komai ba".
Sauke numfashi Isham yai yana kallon sa yace "to yanzu mafita d'aya ce mezai hana kayi mata magana kace ta bud'e location d'in''?.
"No Isham link d'in shafinta baya aiki ai basu barta banza ba sun lalata mata komai ta yadda bazata iya tura sa'ko ko a turo mata ba shiyasa suke nuna mata komai sun san daga laptop d'inta babu inda zata iya share d'insa".
Kai Isham ya jinjina yana cewa "kai amma abun baiyi dad'i ba duk da haka Asad kada ka sare kaci gaba da jajircewa kamar yadda ka saba kullum insha Allahu zaka samota".
"To Amin Isham saidai bansan ta inda zan fara binciken ba"?.
"Tunda a Nigeria take acan ne idan kaje ya kamata ka tsaya ka bincika koda ace zaka dawo".
"Ok shikenan Isham zan jarraba".
"Yauwa Asad Allah ya bada sa'a Allah yasa ka samota a wannan karon" Amin yace masa ganin lokacin sallah yayi yasa suka mi'ke suna fita daga cikin babbar rumfar barrack d'in da suke.
馃彆锔廞AUYE馃彆锔
________ Yau Dauda da Indo suka sauka uhm mamaki kowa keyi musamman wasu harda masu rantsuwa ba Indo bace saidai wata matar Dauda ya aura acan masu ganin 'kwa'kwaf saida suka zo suka tabbatarwa kansu Indo d'ince da gaske nan fa akaita gulmar abinka da qaramin gari ko'ina anji harda masu zuwa sannu da dawowa dan suga meke going.
Indo tayi mamakin jin wai Dalah ta koma gidan babanta Balarabe gaskiya bata ji dad'i ba a fili qarara ta nuna rashin jin dad'inta da hakan Aliyah ta nuna Mata yanxu fa ba irin da bane Balarabe ya sauya Asabe bata da iko dashi ya dawo cikin hayyacinsa jin hakan datai yasa tad'an ji dama-dama amma duk da haka bata le'ka gidan ba a ranar sai washe gari da yake shigowar yamma sukai.
Tun safe taiwa Irfan wanka ta shirya shi itama tayi wankan bayan sun karya Dauda ya sa'ba d'ansa a kafad'a domin yanxu ya riga ya waye hakan ba komai bane suka tafi gaishe da Dalah suna shiga da sallama Dalah ta zaro ido waje tana cewa.
"Indo kune a gari"?.
Murmushi Indo tai tana kallon kofar d'akin Asabe batai magana ba ta karasa gurin Dalan sakamakon d'aki akwai zafi yasa ta d'auko musu tabarma waje zama sukai suna gaida ita fuskarta fal da fara'a ta amsa balle dama tun jiya yara suka zo suka yi mata albishir Indo ta dawo.
Kar'bar yaron tai tana kallon sa da murmushi a fuskarta tace "masha Allah Balah (Irfan) yayi girma lallai kun dad'e rabonku da gida ai jiya ina zaune Yusufa yaron gidan malam Hamza ya shigo da gudu ni harna yi zaton ko irin tsokanar nan ta yara yayo aka biyoshi na fara masa fad'an ya daina tsokanar kar wata rana ya tsokani wanda yafi karfin sa ya dakeshi sai yake cemin ba tsokana yayiba wai kune kuka dawo yazo ya fad'a min harda d'a um alhamdulillah Allah ya raya gashi babanki bai dad'e da fita waje ba ko kun had'u a hanya"?.
Kai Indo ta girgiza "a'a bamu had'u ba".
Dalah nayiwa Irfan rawa tace "to ta yuwu ko nisa yayi amma tunda anan zaki wuni harya dawo ku gaisa".
Tana rufe baki Balarabe yayi sallama da kaya a hannunsa ganin wadanda suke zaune yasa ya karaso yana cewa "Indo kece ko kuma ido nane"?.
Sauke ajiyar zuciya Indo tai itama tana kallon shi tace "nice baba ina kwana"?.
Zama Balarabe yai da fara'a yace "lafiya kalau fatan sun sauka lafiya"?.
Kaita d'aga ''lafiya alhamdulillah".
"To madallah" mayar da hankalin sa kan Dauda wanda ke gaidashi ya amsa yana cewa "Allah yayi maka albarka Dauda Allah ya baku zaman lafiya da zuriya dayyiba" Amin Dauda yace yana mi'kewa ya fita a gidan kar'bar d'an shima yayi sai kallonsa yake xuwa wani lokaci ya d'ago yana kallon Indo da suke zance da Dalah yace.
"Am Indo dan Allah kiyi ha'kuri ki yafe min kuskuren dana aikata miki a baya wallahi bansan meya sameni ba nake irin wadannan abubuwan na sani kinyi ha'kuri a gidan nan kin sha wahala amma yanzu ga ribar ha'kurin nan kina gani Allah ya miki babban arziki kina zaune lafiya a d'akin mijinki ido ba mudu ba amma yasan kima Indo ko ba'a fad'a ba ansan kinajin dad'i a hannun yaron nan Dauda ya rikeki da amana Allah ya baku zaman lafiya mai dorewa sannan bazan gajiya ba da neman gafararki ba dan Allah Indo ki yafe min kuskuren dana aikata miki a baya"?.
Kai Indo ta girgiza tana cewa "a'a baba bakai min komai ba na yafe maka albarkarka nake nema".
"Allah ya albarkaci rayuwar ki Indo" Amin tace cikin jin dad'i tana kallonsa rabon da ta zauna wai Balarabe ya fad'a mata magana mai kyau ta ruwan sanyi harta manta wannan lokacin.
Tashin Asabe kenan daga barci jin maganganu yasa ta fitowa ganin wadanda suke zaune ga Indo da gaske kamar yadda labari yazo mata cewa sun dawo harda d'a tayi ki'ba ta kara kyau Asabe batasan lokacin data sake murje ido ba ganin da gaske dai Indon ce yasa tace.
"Indo Indo wai dama da gaske yara suke jiya da naji anzo ana cewa Dalah kin dawo harda d'a"?.
Kallonta Indo tai batare da ta kawo komai daya faru a baya ba tace.
"Eh nice baba Asabe ina kwana"?.
Kamar Asabe zata fasa ihu da'kyar tana had'a ba'ki tace "la la lafiya kin dawo lafiya"?.
"Lafiya kalau ina Bahijjah"?.
Shiru Asabe tai bata iya ce mata komai ba zuwa wani lokaci tace "ta mutu" tana fad'in haka ta koma daki zaro ido Indo tai tana kallon Dalah tace.
"Innalillahi Bahijjah ta mutu"?.
Kai Dalah ta girgiza tana cewa "a'a bata mutu ba tayi aure ta auri wannan yaron Iluh d'an garuwa wanda farko yace yana sonki har sun kawo rokon arziki aka fasa sakamakon zuwa gurin mai gari da akai to shine ya aureta saidai da yake Asaben bata so inaga shiyasa tace miki ta mutu".
Indo bata sake cewa komai ba har Asabe ta sako hijab tazo tana cewa Balarabe "na shiga gidan Markah"?.
"Sai kin dawo".
Tana ji ya fad'i haka ta fice da sauri tana tafe kamar zata kifa harta qarasa gidan tun daga zaure take kwala Kira.
"Markah Markah fito ki tayani kallo yau na fito rana na tagayyara shikenan nikam tawa tazo qarshe na shiga uku na lalace wayyo Allah na" ta karasa maganar tana fashewa da kukan ba'kin ciki da damuwa.
Hankali tashe Markah ke tambayar ta "qawata lafiya miya faru haka"?.
Kai Asabe ke girgizawa cikin takaici tace "yanzu na fito daga d'aki na tarar Indo a zaune harda d'anta ga Dalah da Balarabe sai zance suke nifa yanzu a gidan nan na dawo 'yar kallo bani da kata'bus a cikinsu duk kwarjini na ya disashe kina gani tsinannan yaron nan Iluh tunda yabar garin nan bayan auren ko le'kowa bai sakeyi saboda ya samu abinda yake so baron ma tana shago a rufe koda ubansa yake ciyar da ita acan d'in".
Sauke ajiyar zuciya Markah tai tana cewa "to kema Asabe fa ba haka ake ba kindau abun da zafi tunda kika ga an d'aura auren nan ya kamata ki sallama kiyi ha'kuri amma kin 'ki alhali kinsan kinada hawan jini ga ciwon zuciya so kike ki kashe kanki a banza ko"?.
Asabe na shar'bar hawaye tace "na rasa yadda zanyi da rayuwata ne Markah wannan masifar har ina"?.
"Kinga Asabe yanxu abinda za'ai ki shirya muje ki gano garin da Bahijjan take tunda ni na sani idan hankalin ki ne ya tashi"?.
''ni hankalina bai tashi ba rass nake Bahijjah na sallama ta idan ta dawo garin nan ma saidai ta nemi wata uwar tunda ni ban isa da ita ba".
Kai Markah ta girgiza ''bafa haka bane kin gane ki mata uziri dan Allah ki shirya muje ki ganota kar kice a'a wa Bahijjah take dashi duk duniya bayan ke duk bacin rai haka zakiyi hakuri tunda me faruwa ta riga ta faru".
Shiru Asabe tai tana ta sharce hawaye Markah na bata ha'kuri da kwantar mata da hankali musamman saboda kar tasa ciwonta ya tashi azo a samu matsala da lallami ta samu ta daina kukan sannan tace ta shirya da d'an abun arziki su tafi wa Bahijjan dashi kar ayi mata gori ace tunda aka kaita ba'a je an ganota ba.
EMIRATE
Ana saura kwana biyu d'aurin aure Asad ya shigo masarauta daga Marshalls islands saidai tunda yazo ba harkar su Ajeeb ne a gabansa ba su kad'ai suke kayansu shikam ko fitowa bayayi yana part d'insa ya tsaya tsayin daka yana bincike damuwarsa ya samu abinda yake so a yanxu shine karshen zancen.
Haka gidan malam Habu ma shirye shirye ake sosai ba kama hannun yaro Asma'u tayi abubuwa sosai saboda business Alhaji Musa ya bud'e mata Mai girma take juya dollars Jamila ma sai wannan karon ta dawo Nigeria tunda aka d'aura aure suka tafi d'anta namiji har yayi wayo sosai shima dai takwaran Alhaji Musa ne suna kiransa Arfat hum Jamila ma ta cika sosai ta murje ta goge ta gano kasar waje da turawa sai bada ki labari take a ranar kwana sukai a d'aki ita da A'I har asuba suna hirar yaushe gamo basu iya runtsawa ba duk da kuwa dama a gidan babu wanda yayi barci sakamakon shirye shirye da akeyi na biki ayi wancan ayi wannan duk wasu kayan cinye cinye Asma'u ce tad'au nauyinsa zata kama musu Hall inda za'ai DJ a gwangwaje data fad'awa Malam Habu ya hanata yace gara tayi sadaka da kud'in zaifi alkairi shine ta ha'kura akai walima馃巼馃帀 madadin dijen da aka so yi.
MRS AL'AMEEN AHMAD CE馃槝.
We will meet again nagode馃.
TYPING馃摬 Mon Sep 2/24 4:15PM
YUSRAH MUSA ABUBAKAR馃拫馃帬.
馃憫M毛 k盲m盲r s盲rk茂馃憫
_____________________________
___________________________________
______________
馃挮 ANNUR WRITER'S ASS馃挮
Home of hospitality and harmony 馃 gidan karbar mutane hannu biyu da zaman lafiya馃檯馃徏鈥嶁檧锔.
馃挩馃挩馃挩馃挩馃挩馃挩馃挩馃挩馃挩馃挩馃挩馃挩馃挩馃挩
馃挦馃挦馃挦馃挦馃挦馃挦馃挦馃挦馃挦馃挦馃挦馃挦馃挦馃挦
馃挱馃挱馃棷锔忦煑笍馃挱馃挱馃棷锔忦煑笍馃挱馃挱馃棷锔忦煑笍馃挱
St么ry wr卯tt锚n nd 锚d卯t卯ng馃憞馃徔
鉁嶐煆糓rs 脛l'盲m毛毛n 脛hm盲d c毛馃槝
OH NI ALLAH CIKI NA馃ぃ HABA KU KUWA FANS TSORON ME KUKE HAKA馃? NAJI KUNA CEWA DAN ALLAH KAR NA CIRE AJEEB A LABARIN LITTAFIN BAZAI DAD'I馃槪 BA KAR NACE AJEEB MUTUWA馃様 ZAIYI, NIIIIII馃 DA YAUSHE NACE HAKA馃槼 HASASHEN KUNE KAWAI KUDAI KU BARI KUJI YADDA KOMAI ZAI FARU KU BIYO NI A SANNU CIKE DA NUTSUWA CIKIN PAGE NA GABA ZAKU JI KOMAI馃槑.
馃殑Kudai kawai keep your eyes馃憖 open馃槀馃挴馃拑.>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
馃檱馃徏鈥嶁檧锔廇yi ha'kuri idan an samu typing error馃敶 matsalar keyboard ne.
69~AL-QADIR
The Omnipotent
70~AL-MUQTADIR
The Determiner.
34~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin Afralil auwalina wal akhirina.
馃寗MARVEL HEYDAY 馃寗
Episode 69&70 馃憫PALACE馃憫
Da yake Sultana Fatima 'yar Nigeria ce danginta har sun fara zuwa ana gobe d'aurin aure dangin Mami suma haka sukazo daga Bahrain da yawansu larabawa kyawawa farare kar-kar dasu harda 'yan mata su hud'u had'dd'u suna zaune cike da farin cikin had'uwar su guri daya domin ba gari daya suke zaune ba wasu na Riyadh aure wasu na Bahrain d'in wasu a misra Aunty Aleemah kuwa a California mijinta yake aiki suna can tare shekara kusan biyar bata samu tazo Bahrain ba sai yanzu da bikin Ajeeb d'in ya tashi miryoyinsu kad'ai ke tashi a parlon suna zaune sunsa Mami a tsakiya ana hira mai dad'i Ajeeb ya shigo da sallama kallonsa Aunty Futuha tai tana cewa.
"Yauwa Ajeeb dama tun d'azu nake nemanka kaida Asad amma shiru ban ganku ba ina kuka shiga ne kai kana yawo kamar ba ango ba kodai gurin amaryar taka kaje ne? dan da alama kai baban soyayya ne".
Murmushi Ajeeb yai yana zama akan kujera yace "eh gurin ta naje kinsan bana iya nutsuwa idan ban ganta ba a rana ina zuwa gidansu kamar sau goma".
Zaro ido sukai Aunty Aleemah tace "kaiiii Ajeeb soyayyar har takai haka"? Kai ya d'aga "ai harya fi haka ma Aunty Aleemah ko romiyo bazai nuna min yadda ake soyayya ba"?.
"Oh haka ne da gaske"?.
"Kwarai kuwa I have confirmed it".
"Ok shikenan amma Ajeeb in an jima zamuje Arabian night馃寖 ko baza ayi ba"? Kai ya d'aga "eh za'a mana ai dama na sanar mata ni dangin mahaifiyata larabawa ne kuma ko ban fad'a ba ta sani da gani babu tambaya menene ni馃し"? Har had'a baki sukai da cewa "Balarabe kuma basarake馃ご馃槏" hannu ya bud'a yana cewa "to kin gani yanzu dame kuka zo min nasan kuna tafe yau shiyasa banyi shirin komai ba kune zaku za'ba min kalar shigar da zamuyi nida amarya ta a gurin yadda zamu burge kowa".
Mi'ko masa wata jaka mai kyau Aunty Futuha tai iya jakar ma abar kallo ce balle ajega abinda yake ciki tana cewa "Eh aiko munzo maka da kayayyaki da yawa domin dama tunda watan bikin ya kama muke shirin harda Abu Sultan ga abokin ka Shuraim dan gidan Ummi Sultana Liyuzah ya bada yallabiya a kawo maka da hirami sannan ya bada Abayat a kawowa amaryar ka muma duka mun taho maka da abubuwan bazata" kai ya jinjina cikin nuna jin dad'i.
Yace "sakallahu khairan gaskiya na gode sosai kuma naji dad'i har bansan yadda zan kwatanta muku ba saidai kawai nace Allah yabar zumunci" Amin 馃げ suka fad'a tare suna bud'e hannu suka shafa a fuska. mi'kewa yai yana cewa "bari na fita zuwa dare zan dawo" fita yayi a falon ya barsu suna ci gaba da hiransu.
Tun bayan sallar magriba ake shirin tafiya Arabian nights humm kowa da jallabiya amma Asad juyi duniya Ajeeb yayi akan ya shirya suje yace wallahi babu inda zaije dole haka Ajeeb ya ha'kura badan yaso ba suka tafi dasu Aunty Aleemah zuwa anguwar su Amatu inda aka kama Hall d'in da za'ai.
Tabd'ijan jama'a ku le'ko kuyi kallon ango Ajeeb da amarya wai zankad'i yasha kwalliya cikin farar kar d'in jallabiya anyi mata adon golden colour a wuyan rigar da hannunta sannan hirami shima golden takalmi ma haka humm dama gashi jinin larabawa abun aba magana fad'ar kyaun dayai.
Haka 6angaren amarya Amatu itama doguwar rigace fara da manyan fulawoyi golden ajiki takalmi da gyale duk golden sauran mutane kuma kowanne yasa ba'kar abayat masa sun sa coffee jallabiya kamar larabawan gaske kowanne ya kima rawani su Aunty Futuha da yake sune masana haka suka wuce gaba suka tsara musu yadda akeyi abun ya burge kowa haka aka qare abubuwa cikin shau'ki sai karfe takwas suka koma masarauta a gajiye duk sun baje suna hutawa amma Aunty Fadilah sakamakon bataga Asad ko kad'an ba yasa ta mi'ke ta tafi nemansa.
馃暟锔廙isalin 'karfe tara da mintuna na dare Asad yana zaune a cikin parlon part dinsa da laptop a gabansa sai faman aiki yake ya d'au zafi sosai gabadaya ya birkice sai yaga kamar ya samu wani d'an bayani game da abinda yake nema sai kuma yaga error ransa duk ya gama 'baci tsuka yaja mai 'karfi yana ture laptop din ta fad'i 'kasa mi'kewa yai jin duk jikinsa yana ciwo ga bai samu abinda yake son samu ba yayi hanyar bedroom domin ya samu yayi wanka.
Jin sallamar mace yasa shi kallon kofar shigowa ido ya zuba mata irin na yaushe gamon nan amma baiyi magana ba saidai ta hangi jin dad'in ganin ta a cikin fararen idonsa zama tai da murmushi a kan fuskarta tana cewa.
"Barka da dare Asad ya kake"?.
Komawa yai yana zama har lokacin bai daina kallonta ba yace "Aunty Fadilaty sannu da zuwa kun dad'e da sauka ne ke dasu waye ne ina budurwa ta馃槼"?.
'Yar dariya Aunty Fadilah tai tana cewa "oh har yanzu baka daina tsokana ba Asad karfa daga wasa abu ya zarce gaske"?.
"To Aunty Fadilaty idan ya zarce ma huluncin Allah ne a rubuce yake, amma baki fada min tare dawa kuka zo ba"?.
"Eh to munzo da Auntyn ka Ma'asumah da ummin mu tace dole ne tazo auren jikanta Ajeeb itace zata amshi amaryarsa".
'Dan murmushi Asad yai tuna cewa gobe iyanzu d'an uwansa Ajeeb ya zama ango sai yaji yana masa murna da hakan 'kwarai kuma ya naiwa Annur ma fatan kaiwa wannan matakin dama shikam baya lissafi da kansa babu aure a tsarinsa baya ra'ayin sa ko kad'an koda ace gaba zaiyi yafi son mace jaruma mara tsoro jajurtacciya wacce zata jure kowacce irin wahala shiyasa bazai iya auren macen da kawai hutu ta sani ba idan bai samu irin macen da yake so ba tofa bazai aure akan lokaci ba saidai idan yayi ritaya daga aikin soja馃槢.
"Asad tunanin me kake"?.
Dawo da kallon shi kanta yai batare daya bata amsa