Author : Yusrah Musa Category : Complete Novels
d'in fa yarinyar akwai nutsuwa da gani babu tambaya ko ba'a fad'a ba.
"Amatullahi ki saurare ni dakyau ki fahimci abinda dazan fad'a miki Ajeeb tunda yake zuwa gurin ki ya ta'ba fad'a miki shi d'an biyu ne kuma kamarsu d'aya ba'a bambance su''?.
Kai Amatu ta girgiza jiki a sanyaye tace "a'a bai fad'a min ba".
Cigaba Mami tai "ok yayi miki laifi sosai gaskiya Ajeeb su 'yan biyune akwai d'an uwansa sunan Asad dashi aka d'aura miki aure bada Ajeeb ba duk zuwa gurin ki da Ajeeb yake yi domin d'an uwansa yake badan kansa ba kuma baiyi haka dan ya 'bata miki raiba a'a yayi haka ne abisa kyakkyawar zuciya da kyakkyawar niyya da kuma kyakkyawar manufa fatan zaki fahimce shi sannan jin ba dashi akai auren ba kada ki tada hankalin ki wannan ba komai bane ki qaddara dama can ba Ajeeb d'in ne mijinki ba Asad ne kuma kada kiyi ba'kin ciki insha Allahu kinyi dace Asad na qwarai ne Ina fad'a miki haka a matsayina na uwa gareki bawai matsayin mahaifiyar Asad ba Amatullahi nice na haifi Asad na raineshi har ya girma dan haka nafi kowa sanin dukkan halayyarsa yana da zafi da saurin fusata sannan shi murd'add'an mutum ne wanda ba'a gane masa amma fa a cikin hakan idan kika bi wasu matakai ina tabbatar miki da Asad zai dube ki na farko ko maye zai faru kada ki kuskura a gabansa ki nuna raki kada ki nuna gajiyawa da karaya ko sarewa karki nuna kina jin tsoron magauci karki nuna masa bakida zafi karki nuna ke raguwa ce ki ri'ka nuna jarumtarki a fili koda a gabansa kada idan yayi magana ki razana ko ki firgita ki tsaya tsam ki saurareshi kuma ki fuskanceshi ki nuna masa cewa zaki iya ji da komai Amatullahi indai kika bi wadannan hanyoyi iya wannan kad'an d'in dana fad'a miki kina zaune Asad zai nemeki da kansa a lokacin da baki ta'ba tsammani ba abu na qarshe shine zanci gaba da 6oyeki anan bazan ta'ba nunawa Asad kina cikin masarautar nan ba koda ya dawo zanga zai nemeki ko zanyi min magana a kanki ki kwantar da hankalin ki kisa tunaninki guri d'aya kiyi rayuwa cikin farin ciki ina tare dake fatan kin fahimci duk wani abu dana fad'a miki"?.
Kai Amatu ta d'aga tana sau'ke numfashi a hankali tace "eh Mami na fahimta sosai kuma nagode Allah ya saka da alkhairi sannan Ajeeb yabar neman yafiyata babu abinda yai min na fahimce shi insha Allahu Mami zaki sameni mai ladabi da biyayya zanyi dukkan abinda kika umarce ni fatana Allah ya dafa min".
Cikin jin dad'i Mami tace "Amin takwara ta Allah ya miki albarka Allah ya baki nasara Allah yasa kece silar canzawar Asad".
Tun Amatu batai magana ba Ajeeb yace "Amin Mami saidai wani hanzari ba gudu ba Amatu na manta ban fad'a miki abu guda ba shi Asad ba doctor bane irina sannan baya d'aukar wargi abu 'kalilan zakiyi yanzun nan ki fusata shi soja ne shi" ya karasa maganar yana mata alamar harbi da bindiga.
Kallon Ajeeb Amatu tayi lokaci guda taji wata muguwar fad'uwar gaba ta sameta har tana d'an dafe 'kirji tare da cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
Dariya Ajeeb yai wanda Mami ta harareshi tana cewa "ya haka Ajeeb meye na tsorata ta dan soja ne sai akai ya? Kinga Amatu share shi kinji babu wani abu Asad yana da sau'ki sosai idan ka tsaya ka fahimce shi Ajeeb ya fad'i haka ne da wasa kada ma ki dama tunaninki a kansa kinji".
Kai Amatu ta d'aga "to Mami na gode".
"Ok takwara ta wanne sunan zan ri'ka kiranshi dashi ne domin gaskiya kin d'auko babban suna"? Mami ta tambaya tana kallon ta da murmushi.
"Ai kawai Mami ki ri'ka ce mata takwarar ma yayi idan Asad ya dawo yaji haka sunanki ne da ita maybe ya sau'ko da wuri".
"A'a Ajeeb ba takwara zance mata ba ni jewel鉁 zance ai yayi"?.
"Wow jewel? Tab lallai kice ke Amatu kinzo a sa'a kiji sunan da Mami zata ri'ka kiranki dashi uhm mu kuwa daga Ajeeb sai Asad babu wanda ta saurayawa suna".
Murmushi Mami tai tana cewa "ai kuma ba sunan ku Ajeeb da Asad ba ko"?.
"Eh Mami sunan mu Aliyu, to amma ai itama sunanta Hauwa'u ake ce mata Amatullahi Kinga an raba ba wata jewel da zakice mata gaskiya idan ba haka ba nima saidai ki dawo ce min diamond馃榾"?.
Dariya Mami tai tana cewa "waye zan cewa diamond tab amma dai bakai ba saidai ka bari idan kayi aure kaima taka matar sai nace mata diamond tunda naga kishi kake da Asad ko"?.
''A'a niba kishi nake dashi ba Mami".
"To me kake inba kishin ba"?.
"Tsokana nake".
"Uhm ai a irin wannan tsokanar taka kake tsokano Asad d'in kazo kuyi tayiwa mutane hauka a gida kamar qananun yara Allah ya shirye ku dai".
"Amin Mami bari naje ina so Annur zai rakani wani wuri kar lokaci ya 'kure" ya karasa maganar yana mi'kewa tsaye.
"Ok sai kun dawo".
Fita yai yabar Mami da Amatu suna zaune su kad'ai Mami tana sake yi Mata bayani sosai tana qara bata qwarin gwiwa kada ta yarda ta nuna tsoron ta a gaban Asad idan ba haka ba zata sha wahala koda ace tana jin tsoron tafi bayyana jarumtarta wannan zai taimaka mata kuma zai ceceta zama da Asad sai jarumtacce balle ita da zatai rayuwar aure dashi ba zaman wuni d'aya ko kwana d'aya ba.
B'angaren Shaukiyyah amare a gidan Aliyu Ameer tana zaune Khaldiyyah da Khimiyyah sunzo mata amma banda Makiyyah domin dama kwana tayi tana kuka batai barci ba da gari ya waye ta tashi da zazza'bi mai zafin g tryaske ma kuwa ko ruwa ta kasa had'iya balle taje ga breakfast.
Cike da tsokana Khaldiyyah ta kalli Shaukiyyah tana cewa "a'a Shauki amarya a gidan prince Ameer yau ya naga babu shauki a fuskarki sai wani jaa d'auu datai ga idonta a kumbure miya faru ne ko duk kewar mu kike ai gamu munzo ko? sai abar kuka" ta karasa maganar tana kunshe dariyarta.
Harararta Shaukiyyah tai cike da takaici tace "ban sani ba idan ma isgili kike min kema ai baki haure ba abinda ya sameni yana nan zuwa kanki gara nima iya kuka nai ke wayasan me zakiyi"?.
Rufe baki Khaldiyyah tai tana dariya tace "au sorry ayya aina manta ashe fa ke d'in amarya ce dan anga kinyi kuka ma bai kamata a tambaye ki kukan meye ba bayan kowa yasan keda ango ne tab uhm Shaukiyyah ina kallonki haka ashe dama ke raguwa ce"?..
Cikin haushi Shaukiyyah tace "raguwar uban me? Kinga Khaldiyyah bana son rashin mutunci idan dama abinda ya kawoki gurina kenan sa ido tashi ki tafi".
Zaro ido Khaldiyyah tai tana cewa "to haba amaryar prince Ameer yada korata dan kawai nazo gaida dake nifa zuwa nayi na taya ki wuri wato daga kwana d'aya har kinsan dad'in miji shine zaki min gori"?...
Had'e rai Shaukiyyah tai tana cewa "uban nasan dad'in miji indai abinda yayi min jiya shine abun dad'i to kema ina miki fata Allah ya kawo miki miji ko yaune a d'aura miki aure kema ki d'and'ana abinda na d'and'ana ba isgili kike min"?.
Dariya Khaldiyyah tai tana kallon yadda Shaukiyyah tai da fuska kafin tace "ba Amin ba daina min fata tunda kinsan wanda nake so Annur ne kuma nasa a raina matukar bai amince ya aureni ba bazanyi aure ba gara na qare rayuwata a haka sannan shi prince Annur gentle Man ne".
"Au haba taya kika sani haka shi ya fad'a miki"?.
Kai Khaldiyyah ta d'aga ''kwarai ma kuwa na sani domin alamar qarfi tanaga mai 'kiba a iya yanayin sa kinsan nutsattse ne bazai bazai gigita mutum ba".
Kai Shaukiyyah ta jinjina tana kallon ta tace " to shi kuma Ameer burkitaccen mutum ne shiyasa ni yaci ubana kike nufi kome"?.
"No ba haka nake nufi kawai dai komai a sannu yake yinsa cikin sanyi kin gane"?.
"Uhmm" kawai shine abinda Shaukiyyah tace domin Khaldiyyah batasan komai ba ita kuma yanzun data sani batasan ta yadda zataiwa Khaldiyyan bayani ta fahimta ba sai kawai ta kyaleta suje a hakan zata tuna mata sai ranar datai aure washe gari itama zataje ta rama Khimiyyah kam tana gefe komai suke tana jinsu ko tari batai ba hankalinta yana kan wayar dake hannunta tana chatting da Hudayyah.
*** ** ***. ** *** ** ***
Nurain ne a zaune yana kallon Nafisa wacce idonta ya cika fal da hawaye yanata zuba ransa a mugun 'bace yace.
"Nafisat da izinin wa kika je kika zubar da ciki batare da sani naba dama nace miki bana son haihuwa ne ko kuma rainin wayo ne yasa kika aikata min haka"?.
Yana rufe baki ganin Nafisa ta kallo su Mimih tana shirin magana da sauri a gaggauce Zainab ta hana Nafisan dake shirin cewa wani abu ta zafga mata wata uwar ba'kar harara tana cewa "ke kinga ki rufawa mutane baki banza kawai jaka 'yar qauye wacce batai karatun addini ba jahila tsabar ke da'ki'kiya ce zakije ki xubar mana da babynmu yau saikin gane gaskiya kin cuce mu" ta karasa maganar tana kallon Nurain daya sake fusata kamar zata she'ke da dariya tace.
"Kuma abun haushin my choice nima har ina murna da farin cikin Auta ta kusa samun qani sai kuma na dawo aiki naji su Mimih suna cewa wai sunga Nafisa ta dawo daga asibiti da takarda a hannunta tana kuka da suka tambaye ta tace ciki gareta bata so ka sani dan Allah su rufa mata asiri tsabar gidadanci da qauyanci batasan cewa in ciki ya fita dole sai an gane ba humm gaskiya Nafisa baki kyauta mana ba kinyi mana asarar babyn mu" ta karasa maganar tana kau dakai gefe sakamakon dariyar dake ciciyarta ganin yadda maganar data fad'a ta sake sanya Nurain zabura ji yake kamar ya d'aga hannu ya sharara mata mari kasa-kasa Zainab take dariyar mugunta ganin yadda Nafisan tayi shiru ta kasa magana sai hawaye dake zuba tace.
"Kayi hakuri my choice tunda cikin dai ya riga ya fita shikenan saidai ai mata uziri kasan mutum idan bai karatu ba matsalar auren jahila kenan batasan doka ba inaga saidai ka sata a makarantan islamiyyah amma dai yanzun kayi hakuri idan ta sake ka d'au mataki me tsauri a kanta dan gaskiya babu wanda za'aiwa irin wannan abun bai d'auki hukunci ba".
Shiru Nurain yai ya kasa furta koda kalma d'aya tsabar ba'kin cikin da Nafisa ta cusa masa Mimih data d'auko littafi kamar gaske dan taji abinda suke tazo wucewa da sauri ta tsaya tana cewa.
"Ai yaya idan baka sani d'auko tan dakai daga wannan mummunan qauyen ka kawota tsakiyar birni baiyi mata amfani tunda gashi ba'aje ko'ina ba ta fara nuna maka ta waye ta hanyar zubar da ciki kayi tunanin gaba me zata aikata humm ba'a sani ba kawai yaya ka saketa yau ta koma karkararsu"?.
Mimih na rufe baki Nafisa ta d'ago a firgice tana kallon Nurain wanda shima ita yake kallo kai ta soma girgizawa cikin kuka tace.
"Dan girman Allah kayi dan Allah wallahi ba laifi na bane"?.
Zare mata ido Mimih tai tana cewa ''ba laifin ki bane laifin uban kine"?.
"Ke Mimih kada ki sake zaginta duk da kin fita koma dai yaya ne matar yayanki ce ita ya kamata ki bata girmanta".
Zainab tai maganar tana kashe mata ido murmushi Mimih tai kamar gaske harda d'an risnawa tace.
"Oh sorry na manta ne 'bacin ran rashin babyn mune yasa nace Mata haka kiyi hakuri Aunty Nafisa na馃槀" ta karasa maganar tana sakar mata zazzafar harara ganin ta d'ago tana kallon ta kafin ta kad'a kai tayi gaba Mimih na wucewa Zainab tace.
"My choice kayi hakuri kar kasa damuwa a ranka komai ya wuce".
Tsaki Nurain yai batare daya kalli inda Nafisan take ba dan ko ganinta yanxu bai son yi muryarsa da alamar fushi yace.
"Get to the point".
Tsiru-tsiru Nafisa tai domin batasan me yace ba kuma bata kawo da ita yake ta d'auka ko tsakaninsa ne da Zainab saida taji cikin tsawa yace.
"Ki 6ace min da gani kafin na 6allaki" jin abinda yace yasa da gudu Nafisa ta mi'ke tana kuka tabar falon tsaki ya sake ja a karo na babu adadi yana cizon yatsa Zainab kam tana gefe sai murmushi take tana rausaya kai mi'kewa yai zai fice yace.
"Ina da tafiya zuwa Singapore ranar Monday ki kira Mimih yanzu su d'auko Auta zamuyi sallama dasu"?.
Kai Zainab ta d'aga "ok my choice amma idan babu damuwa ka biya min kud'in jirgi na zuwa sai nayi na dawowa ina son zanga qasar please" ta fad'a a marairaice.
"Ok shikenan" shine kawai abinda yace mata kafin ya fice tsalle Zainab tayi cike da murna domin tasan tunda ransa ya 'baci indai baiyi nesa da Nafisa ya huce ba tofa akwai matsala shiyasa take so ta bishi su tafi tare taje ta d'auke masa hankali su dad'e basu dawo yadda Nafisan zata gaji ta gudu qauye koda tasan ma bazata iya zama ba domin su Mimih bazasu barta Tasha koda ruwa ba tsabar wuyar da zasu d'an'dana mata.
馃寫馃寶INSIDER馃寶馃寫
BAYAN WATA HUD'U
_____Khimiyyah ce zaune tare da Hudayyah a gurin Muheed dake d'aure Hudayyah na sake jaddada masa cewa har yanzu yana da damar cewa yana sonta zai aureta shima yana fad'a Mata kalma d'aya bazai ta'ba auren taba koda ace zai rasa rayuwarsa ne.
Gurin Prof Jibril da Mr Famous dake gefe Khimiyyah tayi ga kuma Danual Chai daya koma wata kalar siffa a gabansu yana fad'a musu sirrin daya sake binciko musu ta yadda mutum zai iya zaka kowacce halitta yake son komawa karaawa tai tana cewa.
"Daddy please kayi wani abu akan wannan yarinyar yanzu fa maganar da nake maka tana cikin masarautar mu ta auri wannan ma'kiyin cousin d'in nawa wanda ya kusan kasheni sannan itace masaniyar wannan 'kungiyar tamu ka gaggara d'aukar mataki a kanta kasan cewa fa wanda aka aura mata yana son samo inda muke kayi tunani daga ranar daya gane da akwai sirrin mu a hannun wannan yarinyar akwai matsala fa shikenan mun fad'a tarko kuma shi mutum ne mai matukar fikira wanda ba'a iya tararsa ya gagara idan muka bari sai bayan yasan bayanan mu zamu d'au mataki tofa gaskiya bazamu iya ba sannan mun rusa tasiri da qarfin da muke dashi bayan haka Ina alkawarin da kuka d'aukarwa shugaba Diranah kafin ta baku amanar 'kungiyar ta sadaukar da ranta saboda tasan ko bayan bata nan zaku iyaji da koma wanene mai son ganin bayan kungiyar da maison ta rushe wannan sadaukarwa da shugaba Diranah tayi ya kamata a girmama hakan ta wajen ganin an sake sabon tsari ta yadda zamu sake komai ta inda ba'ai zaton mu ba baza'a iya gano mu ba mu qarawa qungiyar mu karfin da duk wanda yace zai tukareta zai hallaka ne ya zama mun sake tashi tsaye muma mun jajirce fiye da da abin kunya ne ace duk yawanmu mun kasa baiwa 'kungiyar mu tsaro yadda ya kamata abu na qarshe please Daddy ka goge dukkan bayan da ka sakarwa wannan yarinyar domin itama jar wuyace jaruma ce barazana ce ga kungiyar mu".
Ta karasa maganar tana kallon Prof wanda ke gyad'a kai kamar yana jin music馃幎.
"Daddy magana nake ba kace komai ba"?.
Dariya Prof yai yana dad'a risawa kamar mai sonyin rawa yana kuma kallon yadda tsafin da Danual Chai ke nuna musu kafin yace.
"Never mind kada ki damu Khimiyyah kema jaruma ce sannan bazumu kasa ba wannan kungiyar a shirye take taga bayan koma wanene yake son ganowa babu wani abu da 'yan tawagar mu baza taji dashi ba kin gane zan d'auki mataki amma kafin nan a daren yau zan saki shafinta na internet sannan zanyi amfani da wannan damar naga abinda nake hari ya yuwu idan tarkon mu ya kama kurciya guda biyu tofa fa'kat karshen magana bamu da wani tashin hankali sama dasu biyun nan kowa ya gajiya yayi laushi cikin lamarin mu wasu sun ha'kura my a sun qaryata cewa babu mu zamusa hakan yayi aiki ace babu mudin a dakatar da masu binciken mu mukuma a daidai wannan lokacin ne zamu bayyanawa mutane muyi ta'bargaza mu kashe na kashewa mu d'ebo na debowa mu karawa qunkiyar mu qarfi kinsan da jini take aiki"?
Kai Khimiyyah ta d'aga "ok Daddy na gane amma fa sar'kar daka bani na rasata sam kuma kaga dole saida ita zan samu damar shigowa nan".
"Wannan ma nasan da haka muna so zamu sake sabuwar sar'ka ne Mai tambarin sifelin din sunan kungiyar mu sannan za'a rabawa kowanne d'a 'kungiya ta yadda idan za'ai taro ka sani inda matsala ka sani kin gane ko"?..
Kaita d'aga "eh na fahimta Daddy" ta fad'a tana mayar da hankalin ta kan Hudayyah ganin ta saita Muheed da bindiga zata harbeshi yasa da gudu taje tana fisgewa tace.
"Haba Hudayyah me kike yi wannan gayen shine rayuwar idan kika kashe shi ke kuma kiyi yaya"?.
Fashewa da kuka Hudayyah tai tana dur'kusawa a gurin tace "ai dama na ha'kura dashi ne zan kashe shi tunda baya sona sannan Nima na kashe kaina domin rayuwata batare dashi ba batada amfani ki bani bindigar nan Khimiyyah''.
Ta fad'a a zabure ta mike tana kokarin kar'ba hanata Khimiyyah tai tare da janyeta daga gurin Muheed tayi wani 6angaren da ita domin ta rarrashe ta.
馃寖 MARSHALL ISLANDS馃寖
_____Marshall islands misalin qarfe d'aya da rabi na dare Asad yana zaune a bedroom baiyi barci kawai laptop ce gabansa yana aiki iya Isham ne kwance ya bararraje yana sharar barci ya rufe jikinsa duka da bargo jin Isham d'in yana magana yayi tunanin ko farkawa yai amma sai yaga ya sake juyi kai ya girgiza yana mayar da hankalin sa fuskar laptop d'in..
"Asad