Advertisements
Chapter 23 Reading Me Kamar Sarki Book 2 Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Me Kamar Sarki Book 2 Hausa Novel

Author :  Yusrah Musa Category :  Complete Novels

Chapter   23 / 67

66K to 69K   out of 200.4K words

jitai kanta yana juyawa lokaci guda taji hajijiya na dibanta ko ganin gabanta batai ta kama hanyar fita daga gidan babu ko d'an kwali akanta.

Daidai Rakiya matar Sabi'u ta fito da buta a hannunta ganin inuwar mutum yana tafiya yasa a tsorace taja da baya tana cewa "a'uzubillahi minal shaidanur rajim" jikinta na 'bari ta haska da fitila cikin salati ganin wacce take shirin fita yasa tace "Babah ina zakije a wannan tsohon dare kanki fa ko d'an kwali babu"?.

Ganin tayi banza da ita yasa da sauri ta koma d'aki tana taso Sabi'u a gigice ya fito bai tsaya sa takalmi ba aguje ya fita waje can ya hango tayi nisa sai tafiya take ga karnuka na mata haushi cikin azama yaje yasha gabanta yana haki yace "Babah ina zakije"? Bata bashi amsa ba kuma bata kalleshi ba ganin haka yasa ya sake cewa "meya sameki ne ko baki da lafiya"?.

Namma shiru tayi masa kanta kuma yana kallon 'kasa ta'ki d'agowa mamaki ne ya kama shi sosai har ya kasa ce mata wani abu sai hannunta daya ri'ke yana janta don ya mayarta gida amma sai yaji ta tirje kamar yaja irin kafaffiyar bishiyar nan juyowa yai yana kallon ta tare da zaro ido waje jin 'karfi a jikinta kamar doki zaiyi magana kawai yaji ta kwashe da wata iriyar dariya da sauri ya saketa yana ja da baya dariya take sosai kamar zararriya d'ifff kuma yaji tayi shiru tare da dafe kanta ta kurma ihu tana yanke jiki ta fad'i 'kasa, da gudu Sabi'u yazo yana durkusawa a gabanta girgiza ta ya soma yi amma shiru mi'kewa yai cikin jarumta ya d'agata yana sa'bata a kafad'a yai gida da ita saida ya kaita har daki ya kwantar kafin ya fito yana mamakin ina Rakiya tayi ne nasu d'akin ya shiga can ya hangota saman gado ta lullu'ba sai kakkarwa take karasawa yai yana janye bargon yace.

"Rakiya meya sameki, baki da lafiya ne"?.

Jin muryar sa yasa ta bud'e ido tana cewa "a'a ina lafiya ihu naji da dariya daidai nasa hijab na fita zanbi bayanka shine tsoro ya kama ni na dawo gida ina Baban take ka ganta"?.

"Eh tana d'aki jira nake gari ya waye muje asibiti ni abun ne da tsoro kamar ciwon hauka ne ya kamata saboda ganin abunda takeyi itace fa me wannan ihun da dariyar kamar zata fasa gari" zaro ido Rakiya tai "itace kuma innalillahi wayyo Allah na meya samu Babah ne ban ta'ba ganin irin haka ba".

Zama yai yana sauke ajiyar zuciya yace "ni kaina Rakiya ban ta'ba gani ba sai yau Allah yasa dai ba aljanu ta had'u dasu ba" Amin Rakiya tace tana tashi zaune daga tashi tai tana le'ko kofar d'akin da Salamatu take ciki tana cewa "nifa ina jin tsoron karta 'kara fitowa bamu sani ba tayi waje ka taso muje gurin ta gara mu tsaya zuwa wayewar gari a gurin ta" mi'kewa yai yana cewa "shikenan muje" fita sukai suna shiga d'akinta a 'kan'kame suka sameta ta 'ka'k'kafe idanuwanta sun juye babu ko d'igon ba'ki sai fari tana wata irin jijjiga abin tsoro.

Rakiya dake kan gaba da sauri ta koma baya tana salati jikinta na rawa ganin abinda yafi 'karfin ta kuka ta kama cikin tashin hankali tana cewa "ta ya zamu bari sai gobe baban hajiya gaskiya musan yadda zamuyi a daren nan kalli fa abinda takeyi sai nad'ewa guri d'aya take kamar taya dan Allah kayi wani abu".

"To mezanyi wanda ya wuce addu'a ina zamuje dare ya riga ya raba mu ba asibiti ne damu a gari ba saidai muyi hakuri mu jira wayewar gari".

Goge hawaye Rakiya tai tana cewa "shikenan Allah ya kaimu Allah ya bata lafiya" amin yace tare da fara karanta mata addu'a haka suka kwana cur basuyi barci ba saida akai sallar asuba sannan ya samu wani d'an ma'koftansu mai mashin ya nemi alfarmar yakai su asibiti amma dayaje gida ba damar da zata iya hawa mashin dan tana nan a san'kare guri d'aya hatta yatsarta baya tan'kwasuwa balle ga'bo'bin jikinta rasa mafita Sabi'u yai dole karshe sai mashin d'in ya kar'bi aro yana fita wajen garinsu ya samo motar haya da'kyar suka fito da ita kamar itace haka suka sata a mota suka nufi asibiti.

Habu bai sani ba sakamakon baya gari ya tafi cikin Kano sarin kaya sai bayan ya dawo yaji labari ko hutawa baiyi ba ya tafi asibitin a zaune ya samu Sabi'u da Rakiya sunyi shiru cikin damuwa yace.

"Yaya Sabi'u dama Babah bata da lafiya? Wallahi ban sani ba dawowa ta kenan yanzu Binta take fad'a min ya jikin nata fatan da sauki"?.

Numfashi Sabi'u ya sauke tare da girgiza kai yace "Habubakar ban sani ba abun da tsoro tun safe muka zo amma har yanzu babu likitan daya fito balle muji wani labari da zaisa muji d'an dama dama".

"To meya sameta ne"?.

"Humm habu Habubakar to me zance na kasa ganewa 'kwa'kwalwata bazata dauka ba irin abubuwan da take da dare ya bani tsoro baka gani ba yadda take sandarewa kamar busashshen ice harda ihu".

Zaro ido Habu yai "innalillahi meya faru haka ko aljanu ne"?.

"Ban sani ba Habubakar Allah yasa dai ba wani mummunan abu ne ya sameta ba" Amin Habu yace yana samun guri ya zauna suna jiran tsamani kafin likitan daya kar'bi Salamatun ya fito.

GIDAN BALARABE

Dalah na zaune a kofar d'aki tana tajewa Indo gashi taji an rafka sallama tana d'aga kai taga mace ta shigo mamaki ne ya kama ta ganin Asabe a ranta tace ita kuma wannan lafiya ba dangin iya ba na baba katse mata tunani tai da cewa.

"Ke haka ake kar'bar ba'kuwa kin barni a tsaye kamar bishiya"?.

Da sabon mamaki Dalah ta kuma kallonta tana cewa "sannu da zuwa 'karaso bismilllah ga kujera ki zauna".

Zama Asabe tai tana 'karewa gidan kallo kamar wacce tazo duban tsafta zuwa wani lokaci tace humm tare da ta'be baki tana yiwa Dalah kallon uku saura sisi takaici ne ya gama cika Dalah ganin mace tazo mata har gida zata raina mata wayo tace.

"Wai meya faru ne kinzo bakice komai ba lafiya"?.

Gyara daurin kwalin kanta Asabe tai tana soke shi a gaban goshi tareda dauko cingum daga cikin Jakarta tasa a baki tana taunawa sannan ta soma magana "humm Hajiya Dalansi dama nasan zaki mamakin zuwa na saidai da baki wahalar da kanki ba domin ba wani abu ya kawo niba kawai nazo ne mu gaisa naji ya d'iya ta take".

Baki bud'e Dalah take duban Asabe jin abinda take cewa tace "kinzo ne mu gaisa kiji yadda lafiyar d'iyarki take"?.

Gira Asabe ta d'age "eh haka nace ranar baki ga tazo miki da 'kosai ba? Ai nice na bata har nake cewa idan tazo tace ina gaida ke ko bata fad'a miki ba"?.

"Eh bata fad'a min ba mun gode".

Karya kai Asabe tai cikin yanga zatai magana taji gyaran muryar Balarabe alamar ya shigo gidan cikin tane taji yana hautsinawa na shakku da tsoro tuna abinda 'kawarta Meroh tace mata akan Balaraben mi'kewa tai tana susa kamar me ciwon 'kazuwa tana rarraba ido tare da satar kallon Balarabe da yake tsaye ganin ta a gidansa muryarta na d'an rawa tace.

"Barka da gida ina yini"?.

Wani kallo ya mata yana d'auke kai bai amsa ba sai tambaya daya jefo mata "meya kawo ki gidana me kikazo yi shin kinyi ajiya ne"?.

Kallonsa Asabe keyi ganin yadda yai mugun had'e rai yasa jiki a sanyaye tace "kayi hakuri dan Allah yanzu zan tafi dama nazo ne mu gaisa".

Da yake mutum ne mai fad'a a hasale yai kanta yana cewa "da uban wa zaku gaisa dama kina zuwa min gida ne? Karki sake na sake ganin ki a gidannan idan ba haka ba zaki bayani saikin yabawa aya za'kin ta fita min a gida nacee" ya karasa maganar cikin tsawa yana nuna mata hanyar 'kofar fita jiki na 'bari Asabe tai waje kamar zata kifa tsabar sauri tana haki.

Juyawa yai cikin fad'a yana kallon Dalah yace "kece kika bud'e mata kofa kika bata lasisin shigowa gidana ko kuwa duniyanci ne ya kawo ta fad'a min naji"? Cikin shakku Dalah tace "kayi hakuri wallahi bansan komai ba kawai ganinta nai ta shigo wai tazo mu gaisa taga d'iyarta".

"Taga d'iyarta? A gidan uwar wa Indo na ta zama d'iyar yar duniya irinta kuma bari kiji daga yau na kafa doka kada ki kuskura na sake ganin wannan matar a gidan nan kin jini"? Kai Dalah ta d'aga "eh insha Allahu zan kiyaye kayi hakuri" tsaki yai yana yin hanyar ficewa daga gidan sai balbali yake d'an d'aga murya Dalah tai tana cewa "ga abincin ka" a fad'ace yace "bazan ci ba bana so" rike baki Dalah tai "oh ni Aminatu yau naga ta kaina Allah ka tsare ni da sharrin matar nan kada tai silar mutuwar aure na" ta karasa maganar tana kallon Indo tace "dauko min hijabi na a d'aki muje na kara ki gidan kitson nan Allah yasa Suwaiban bata aiki yanzun nan tayo miki na dawo gida na d'ora abinci kar dare yayi maza tashi ki dauko min" mi'kewa Indo tai tana daukowa rufe d'akunan Dalah tai tana sa hijab din suka fita.

Asabe na fita daga gidan Balarabe tayi anguwar babbar 'kawarta Markah hankalin ta a tashe tana zuwa ta yada gyale da jaka ta soma zaga tsakar gida tana jan tsaki da maganganu ita kad'ai Markah na gefe tana yanka loma ganin yadda Asaben ke zarya tace "a'a 'kawar arziki na ta'ba ki da alkairi wannan abinda kike nasan bakya cikin nutsuwar ki akwai wani wanda ya 'bata miki rai wa kike zagi"?.

Zama Asabe tai tana sake jan dogon tsaki cikin takaici kamar zata fashe da kukan ba'kin ciki idonta fal da ruwa tace "wannan mara mutuncin ne ya tozarta ni dan kawai naje gidansa harda cewa uban me ya kawo ni".

Cikin alamar tambaya tace "wa kenan akan me kike magana ne"?.

Cizon yatsa Asabe tai tana zama tace "waye kuwa Markah bayan masifaffan nan Balarabe kalar jaraba wai kawai dan naje gidan sa bakiji wulakanci ba kamar wacce naje maula".

Dariya Markah tai tana cewa "kema dai Asabe kina da shishshigi kinsan waye Balarabe meyasa zakije masa gida"? "Humm Markah kenan sonshi fa nake da gaske so nake na aureshi banajin dad'i idan ban ganshi ba" baki Markah ta ta'be "tab aiko kin hada kanki da wahala Asabe maganar gaskiya Balarabe bazai ta'ba sonki ba balle ya aureki gara ki ha'kura" zaro ido Asabe tai "kinsan me kike cewa kuwa na ha'kura fa kikace Markah"? Kai Markah ta d'aga "eh shine mafita kema kya hutar da zuciyarki daga 'kuncin da kika jefata" mi'kewa Asabe tai tana daukar gyale tace "inaa bazai yuwu ba Markah ya yau d'in nan zanje gurin boka na" zaro ido Markah tai "haba Asabe a yau kuma"? Kaita d'aga "eh yanzu ma kuwa kinga tashi ki raka ni" kallonta Markah tai kafin ta she'ke da dariya harda tafa hannu da sakin gud'a cikin zolaya da sha'kiyanci tace "sai kinyi hajiya Asabansi amarya a gidan malam Balarabensi mai kayan gwanjo in Allah ya yarda" hade rai Asabe tai tana cewa "kinga idan zaki rakani kawai ki taso muje wallahi indai kika taimake ni na cika burina zan baki kud'i naira dubu hamsin kyauta kiyi jari ki bud'e kasuwanci a gidanki" dafa 'kirji Markah tai "da gaske kike 'kawar arziki? Aiko yanzun nan makuwa zamuje tab irin wannan samun gara'basa da ganima haka ahh muje akwai gurin wani ri'kekken boka a cikin wani ba'kin daji sunansa 'kadaga aikinsa me kyau ne yanka daya ne saidai akwai kashe kud'i da tsada" jin haka yasa cikin azama Asabe tace "indai aikina akan Balarabe zaici ko maye zan bayar ko meye zan 'batar dashi naga na samu kansa ya soni ya aureni" "shikenan 'kawar muje" Markah ta fad'a tana dauko gyale suka fita tana sake fad'awa Asabe shaharar bokan da irin aikin da yake farin ciki kuwa tuni ya cika Asabe hango Balarabe kawai take a tafin hannunta tana jujjuya shi kamar yadda ranta yake so.

馃AYI HAKURI YAU TYPING 馃摬 DIN BABU YAWA KUMA BANI DA CHAJI馃摫 GASHI SABODA INA MATUKAR 'KAUNARKU A GIDAN BIKI NAYI MUKU TYPING馃崌馃槝馃ぃ.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE 馃槝

Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty 馃槀馃ぃ馃馃尮鉁岋笍.

馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮

馃實Duniyar da za'a barta

Me ya kawo had'ama?馃え

馃彊锔廟ayuwar da zata 'kare

Ina wani farin ciki?馃槯

Ana sauraron mutuwa馃槩

Ina wata walwala?

Jikin da zai zama gawa 馃様

Me zaisa alfahari?

'Karshen da makomar sa kabari 馃槶

Me zai jawo girman kai?

Duk wanda ya manta da wannan 馃槦

To ina yabar hankalin sa?馃.

馃尮馃挒MU'KAMIN KA DA GIRMA YAKE ME KA'ABU DA ZAHIDU KA TAKA DAI DAI UBAN GIDANA YA RASULULLAH馃挅馃挐.

A baitin farko sunanka ne ya Al Aliyu ina tawassuli ga annabin nan almakiyu sirrin wadatuwa wanda ya zamma madaniyu albarkacinsa nazo kai mini ya 'kawiyyu ka 'kara bani dama in wa'ke nuru zatullah.馃挒馃挊

Summas salatullahi alam daharujjanani mai kausara da zam zam ya sahibul bayani mai kyau da kyan gani ya sirrin samun sukuni wadatuwar wadata kaine ayyunul ya'kini lale wa marhaba bika ya kairu kal'ki indallah.鉂わ笍馃挐

Ranar kowa yana kasa kai kuwa kana buraka mala'ku rundunar Allah na bayanka suna ta gaisuwa da sallamar su a gareka ranar dukkan annabawa ne fadawan ka ashe kwa zamu sha kallo matsayin rasulullah,馃馃尮馃

Niko nace ka taka daidai abban kasim ina isar waninka a yau ya jikan hahim aljannah taka ce makiya ba uhm ba um um ashe kwa zasu sha narko tunda sun 'ki sallallah馃挄馃挌.

TYPING 馃摬 {Sat 20Apr 24 02:18PM}%馃尮馃憠 YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

馃憫ME KAMAR SARKI 馃憫

WHATSAPP NO:234 905 527 3614.

Story and written

鉁嶏笍Mrs Al'ameen Ahmad ce maman little Zaran aunty 馃拝.

Wannan page din naka ne d'an uwa rabin jiki ha'ki'ka kai jarumi ne a cikin jarumai jarumtacce a cikin jarumtattu u're the champion 馃弸锔忦煉 best hero in the world 馃尮 d'an uwa na Allah ya tsare mana kai ya tsare ka daga sharrin miyagun makiya annabi na wannan daji Sambisa馃槪馃槬 Allah ya dawo mana dakai gida lafiya cikin aminci alfarmar Manzon Allah saw Amin 馃げ馃憦.

CPT. SALISU ABDULLAHI (*()*) KOLI馃崯 ME TAMBARIN NO GOING BACK馃懏馃挭馃敨馃敨馃馃憡馃挘.

YUSRAH MUSA ABUBAKAR MRS AL'AMEEN AHMAD CE MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY 馃拑.

YUSRAHMUSA65@GMAIL.COM INA MASOYA 'YAN UWANA MA MAKARANTA (READER'S)馃摎 INA MATUKAR FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA GA WATA BABBAR DAMA TA SAMU YAR UWA KO DAN UWA MAKARANCI KANA NEMAN LITTAFI SABABBI KO TSOFAFFI NA TARIHI KO NA YA'KE YA'KE WANNE A CIKI KAKE DA BUKATA? HUMM MAZA KA MATSO KUSA GA BABBAR DAMA TA SAMU TASKAR HAUSA EBOOKS TA SAMAR MUKU SABUWAR DUNIYA WATO SHAFIN SU NA MR HAUSA EBOOKS KUMA KODA LITTAFI KA RUBUTA KANA SON YA'DAWA ZASU DORA MAKA SHI SHAFIN SU NA GOOGLE TWITTER FACEBOOK DA TELEGRAM KAI HARDA INSTAGRAM KAWAI YAN UWA KU DANNA WANNAN LINK 'DIN.

Taskar Mr Hausa Ebooks

http://tnovels.com.ng/novels/ sai kuyi serch kuna kasa sunan littafin da kake so kai tsaye zaka shiga shafin sai kayi downloading duk littafin da kake so馃.

#VOTE

#SHARE

#COMMENTS

#FALLOW

31~AL-KHABIR

The all Aware

33~AL-HALIM

The Forbearing.

16~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Nadiminah.

Bintu Musa jikar Abubakar Muhammad.

馃寗 INFANT ND PRETENDING 馃寗

Episode 31&32

Har dare ya fara nisa wajen karfe sha daya babu likitan daya fito balle su samu wani d'an labari dazai sanyaya musu rai a gajiye Sabi'u ya kalli Habu dayai tagumi yana cewa "Habubakar ya Kamata kaje gida dare kada yai nisa ga Rakiya ku tafi tare" kallonsa Habu yai tare da girgiza kai yace "yaya Sabi'u bazan iya tafiya na barka ba cikin kad'aitaka ga damuwa bayan babu likitan daya fito balle muji abinda ya sameta bazan iya zuwa ko'ina ba anan zan kwana" dafa shi Sabi'u yai yana cewa "a'a Habubakar na sani kayi matukar damuwa da hakan amma zan baka hakurin dan Allah ka tafi gida ka dawo da safe kaji"? Shiru Habu yai tare da sunkuyar da kansa kamar me tunani zuwa wani ya d'ago zaiyi magana Sabi'u ya dakatar dashi "a'a dan Allah kar kace komai ka tashi ku tafi" mikewa habu yai batare daya sake cewa 'kala daidai Rakiya ma ta tashi tana d'iban kwanuka Sabi'u ya d'ora da cewa "yauwa habu gobe da safe kaje gidan malam Zayyanu kace wannan kud'in dana bashi ya baka na fasa sayan gonar baba ce bata da lafiya zan biya kud'ad'en asibiti" kai Habu ya d'aga "to zan fad'a masa saida safe" Allah ya tashe mu lafiya" har wajen asibitin ya rakosu yana sake jaddadawa Rakiya tazo da wuri.

Ramatu na zaune da safe a kofar d'aki Ilyah ya shigo da sauri sai ganinsa tai a kanta kamar an jefoshi har haki yake binsa tai da kallon mamaki tana cewa "kai makau lafiya meye hakan zaka shigo min a wani hargitse kamar sabon kamu meya faru"? Kasa zama Ilyah yai sai kaiwa da komowa yake harda gumi yace "yanzu naji labari wai babah Salamatu bata da lafiya an kai ta asibiti" tsaki Ramatu tai tana zafga masa harara tace "au Salamatu bata da lafiya shine na wannan shigowar a gigice kana dawurwuri kamar me neman wani abu saime dan tana jinya asirin tane ya fara tonuwa irin 'kulle 'kulle da makirce makircen da take ne ya fara dawowa kanta kaga yanzu kowa zaisan ita ba mutuniyar arziki bace sungungumar asarace" "kai dan Allah wai me kikeyi haka"? Gyara zama Ramatu tai "ubanka nakeyi haka asararran banza asararran wofi wanda ya rako maza meye hadinka da Salamatu ne dan malafar ubanka fad'a min naji idan ta fini martaba sai nasan matsayin daka ajiye ni tunda dama ka fara nuna matarka ta fini mu'kami inaga nan gaba zakace banice na haifeka ba" jin abinda Ramatu tace Ilyah yasan fitina kawai take nema saboda kwana biyu babu Bara'atu da take saukewa damin bala'i shiyasa zata koma kansa amma bari ya bita a sannu zama

23 / 67