Advertisements
Chapter 36 Reading Me Kamar Sarki Book 2 Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Me Kamar Sarki Book 2 Hausa Novel

Author :  Yusrah Musa Category :  Complete Novels

Chapter   36 / 67

105K to 108K   out of 200.4K words

tazo kusa meye yazo kusa Malam irin wannan fara'a kodai kasar zaku bari"? Ta karasa maganar cikin sha'kiyanci kai ya d'aga mata daidai sauran su zauna yace "eh 'kasar zamu bari idan Allah ya kaimu jibi da rai nida mutumina Sadi" har had'a baki sukai wajen cewa "kasar waje dai Malam amma wacce kasar waye ya biya muku kud'in jirgi"? Murmushi malam Habu yai yana kallon su dad'i ya gama cika shi yana hasko yadda rayuwar su zata canza kwana kusa su dawo jin dad'i kamar da yace "ba'a jirgi zamu ba a mota ne" da mamaki Binta tace "amma Malam wacce kasar ce a mota daga nan ko Niger"? Kaiya girgiza "a'a Binta ba Niger zamuje ba Camaron ne".

"Amma Malam sana'ar me zakuyi"? "Nima ban sani ba yace dai ana samowa kud'i sosai acan saimun je komeye zamuyi fatana Allah yasa muje a sa'a na samu kud'i kona rufin asiri ne saboda ku kunyi ha'kuri ni nasan da haka amma kusa ranku a inuwa ku taya ni da addu'a Allah ya kaini a sa'a idan naje ko nima na samu d'an wani abu nawa harna manta rabo da naga biyar a hannu na wai da sunan tawa humm" ya fad'a abun na masa ciwo arai kafin ya sake d'agowa yana kallon su yace "amma shikenan nan babu komai kowanne irin aiki na samu duk wahalar sa zanyi saboda ku addu'ar ku nake nema kuyita min Allah ya dafa min ya zama shine jina da ganina da kafafuna sannan ya zama hannuna dazan ta'ba abu dashi zanyi kokari zan jajirce nasan ba'a maraya馃槪 sai rago".

Had'a baki sukai suna masa addu'a harda su Aisha dake gefe tuni suka aje d'inkin hula suna sauraren su farin ciki ya gama cika su ji suke dama Amatu tana nan da zatafi kowa nuna murnarta sun tabbata sai tayi kuka.

Cigaba malam Habu yai da cewa "to sai maganar kud'in mota kunsan dole zaiyi tsada ni kuma dai biyar ban ajiye ba a cikin ku akwai wacce take da kud'i ko dubu biyar ne ta ara min kafin na dawo inyaso ko gurin yaya Ilyah sai naje na ro'keshi da Allah ko zaiji tausayi na ya bani 'yar dubu goma shima na rage".

Zaro ido Binta tai tana kallon malam Habu tace "amma Malam kana da tabbacin zai baka"?.

Kai ya girgiza "a'a nima ban sani ba sai naje bana ji a jikina zai bani amma ya zanyi marar abu baya zuciya馃様 da inada gurin wanda zanje na kar'bo wallhi ko kallon yaya Ilyah bazanyi ba to amma yanzu idan nace bazanje gurin sa ba gurin wa zanje duk garin nan bani da kowa sai shi sai 'ya'yan yaya Sabi'u su kuma suna marayu abin kunya ne ina 'kanin ubansu ban basu ba nake nema a gurinsu nasan ba iya garin nan ba har 'kauyukan dake kusa damu sai sun taru sun tsine min".

"Ayya malam ka daina cewa haka insha Allahu yaya Ilyah zai taimaka maka".

Sauke ajiyar zuciya malam Habu yai yana cewa "umh Allah yasa amma banga alama ba, yanzu anan zan samu a gurin ku ne"?.

Da sauri A'i tace "a'a nikam gaskiya malam tayara ina olo (tsoro) kar naje na tafe d'an kud'in da nake juyawa kazo tafiya batai kyau mu shiga uku mu sake dulmiya cikin wata azabar talaucin kuma nidai kud'i na baifi dubu sha biyar ba kuma wani duk yana gurin 'yan bashi baza ka samu guna ba" ta karasa maganar tana soke d'aurin kwali.

Kai malam Habu ya jinjina yana cewa "ai dama bake na tambaya ba" shiru A'i tai tana murgina kai Saude tace "wallhi malam kud'in gurina yanzu baifi dubu biyu ba jiya yaya Saleh ya turo matarsa Ladiyo da dare yace na ara masa dubu ashirin na d'auka na bata gashi yau kana so rashin sani yafi dare duhu"

"A'a karki damu babu komai Saude Allah ya miki albarka magana mai dad'i ma sadaka ce".

"To malam me kake nufi ni kuma Allah ya tsine min kome"?.

"Ni bance miki haka ba, ke dama Binta nasan baza'a samu a gunki ba tunda ba komai kike ba shikenan dai bari zuwa goben muga abinda zai faru Allah yasa na samu ina son barin garin nan kodan ku naje nayi aiki tu'kuru na samu kud'i na faranta muku ranku".

Kallonsa suke cikin girmamawa domin gaskiya Malam Habu mutum ne na 'kwarai baya so yaga wanda yake 'kar'kashin sa cikin 'kunci suna haka Asma'u Aisha da Jamila da suke dur'kushe kowa ta tashi tana shiga d'akin su kamar sakan biyu suka fito suna sake dur'kusawa a gabansa kowa da kud'i a hannunta kallonsu yai da mamaki cikin sanyi Asma'u tace.

"Baba ga wannan kud'in ka kar'ba na tabbata zai isheka kud'in mota basai kaje gurin baba Ilyah ba dan Allah".

Hannu biyu Malam Habu yasa yana kar'bar kud'in cikin mamaki yace "a Ina kuka samu kud'i Asma'u"? Asma'u kanta na sunkuye ji take kamar ta fara zubar da hawaye tsananin tausayin babanta ya kamata muryarta tana rawa alamar ta fara kuka tace "baba jiya ne muka sayar da hulunan mu da muka gama d'inkawa gashi munsa wasu kayi kud'in mota da wannan d'in".

'kirgawa malam Habu yai na Asma'u dubu hud'u na Aisha uku na Jamila dubu biyar da yake ta fisu iya d'inki tata har dubu biyar da d'ari biyar ko shida da biyar tana yi haka malam Habu ya had'a kud'i dubu goma sha uku daidai yasan duk da haka bazai isa ba amma ya 'kyale ya ha'kura da zuwa gurin Ilyah tambayar ya taimaka masa kamar yadda 'ya'yansa suka bukata albarka da addu'a mai kyau ya musu kafin suka tashi suna komawa can gaban d'akin su sukaci gaba da d'inka sabin da suka saka dama Amatu da yawa tayo musu yankin da zaren ta bayar akai fulo kawai saidai subi su tisa zubi da ciko A'i dai ta cika tayi fam saboda tun jiya take lallamin Jamila ta bata kud'in ta kara akan jarinta ta'ki ashe rabon malam Habu ne dukkan 'yar 'kwafa tai tana kallon Jamila ji take kamar ta tashi taje ta rufeta da duka kota huce haka ta tashi kamar mara lafiya ta shige d'aki harda hawayen ba'kin ciki tai ta kasa zama tayi nan tayi can sai hasko sanda Jamila ta mi'kawa Malam Habu kud'in take.

Tabdijan A'I kina da abun fad'a bawan Allah yana kokarin yaga ya faranta muku馃え ke kina wani tunani daban akan dubu biyar mstttt馃檮 aikin kawai ki turo account number d'inki zansa FANS d'ina kowa ta tura miki 10k馃槀馃槀 ina shikenan? an wuce gurin FANS kada ku bani kunya 馃棧锔忦煑o笍馃棧锔廼na sis Zarah Musa d'an Adam馃ぃ maza fito ko takan 馃棧hajia o'o masu ido da dan ciki zamubi nasan akwai money馃挵馃挵馃挵馃拑馃拑 yana nan a 'boye a banki馃彟 dila-dila馃檯馃槀馃槀馃槀karma kice baki da shi ehe馃檮 matar nan kwanan nan kika sake sabuwar mota馃殬馃じ馃じ fil a leda kin bar wasu da kwanan gida wunin gareji馃槶馃槀馃榿馃榾馃槅馃ぉ馃槣馃槤馃槢馃馃き馃か馃槆馃樄馃樆馃樅馃檲馃じ

Tofa reader's ayi hakuri typing 馃摬 din yau ba yawa ba kamar na kullum ba na gaji ne ku lalla'ba zuwa gobe idan Allah ya bamu aron rai da lafiya saimu karasa.

MRS 脙L'脜M脡脡脩 脕HM脙D C脢馃槝馃槝.

MAI TAMBARIN YMA DUTSE馃彏锔 馃啎WORLD馃審 馃啎LIFE馃寣 馃啎STYLE鉀拆煄○煔勷煄.

JIGAWA DUTSE S脌BUWAR DUNIYA KUZO KUYI KALLO DA'DI YANA JIGAWA GARIN ILIMI GARIN ADDINI ZAMAN LAFIYA JIGAWA 馃崌馃崏馃崕馃尮馃馃彽锔.

馃拫YUSRAH MUSA ABUBAKAR馃拫

We will meet again馃 na gode馃檹馃檹馃檹 much appreciated 馃憣 yabonku gareni ni馃馃.

TYPING 馃摬 FRI, JUL 12/24 7:13PM YUSRAHMS ABUBAKAR馃馃馃馃.

馃拵ME KAMAR SARKI 馃拵

AWA

馃挮ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 馃挮 HOME OF HOSPITALITY 馃 AND HARMONY馃晩锔忦煂答煂.

WANNAN PAGE DIN NA SADAUKAR DASHI GA DUKKANNIN 馃憠馃憠MASOYAN ANNABIN MU MASOYIN MU SAHIBIN MU ABIN ALFAHARIN MU MANZON MU SHINE RAYUWAR MU SHINE MUTUWAR MU SHINE GATAN MU SAYYIDINA MUHAMMADIN RASULULLAH馃憟馃憟 馃挄 MUNA SONKA FIYE DA RAI馃憣 DA IYAYE馃槝 DA DUKIYA馃挵 MUNA SONKA FIYE DA DUKKA MURADI NA ZUCIYA ANNABI MU MUGANKA SHINE BURI NA ZUCIYA LAMUNCE MU GANKA YA MAI SALSABIL DA KHAUSARA.

BANDA KAMAR KA YA RASULULLAH A DUNIYA BANDA KAMAR KA YA RASULULLAH A LAHIRA.

馃晫馃晪馃晫

馃げ馃げ馃げ馃げ馃摽馃摽馃摽馃摽

H膧PPY J脷M脙'脗T M脺B脜R脛K

馃崌馃崕馃崏馃崒馃崓馃ゥ馃馃崚馃馃崜馃崗馃馃崋馃崘

=_==_==_==_==_==_==_==_==_==_=

KUNA INA FANS KU FITO YAU RANAR MUCE MASOYAN MANZON ALLAH SAW.

馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮

馃尮 馃尮 馃尮 馃尮

馃尮 馃尮 馃尮

馃尮 馃尮

馃尮 馃挀ANNABI馃挀 馃尮

馃尮 S*A*W 馃尮

馃尮 馃尮

馃尮 馃尮

馃尮 馃尮

馃尮 馃尮

馃尮

KUCE MINI SAI MANZON ALLAH馃

KUCE MINI SAI MANZON ALLAH馃

HABIBI HABIBI HABIBINA HABIBI MA'AIKI RASULULLAH馃挄馃挒鉁.

ANNABI NAKE 'KAUNA ABADAN BAZAN MAI KISHIYA BA ALLAH KA YARDA NAI YABO GURIN MAHMUDU SHA YABO WANNAN DAKE RABON RABO KYAUTA BA'AI YASHI BA.

YA MUSTAPHA ANNABI HASKEN IDANU NA YA MUNTAKA YARDA DANI YA MASOYI NA馃尮馃挀馃挆馃挅.

馃挒MANZON ALLAH S*A*W馃挒

You are the

YUSRAH MUSA ABUBAKAR INA YI MUKU BARKA DA JUMA'A FATAN DUK ALKHAIRIN DA YAKE A CIKIN WANNAN RANA ALLAH YA SADA MU DASHI DOMIN HASKEN MASOYIN MU馃檹 ALLAH YA GAFARTAWA MAHAIFAN MU馃槶馃槶馃槶 MUSULMAI MAZA DA MATA WANDA SUKA RASU ALLAH YA MUSU RAHMA YA LULLU'BE ZUNUBAN SU馃檹馃檹馃檹馃檹.

馃憞馃憞馃憞

It's Friday don't forget to recite suratul Al-khaf may Allah bless you and your household may Allah open the door of success 4u all Muslims.

Juma'at Mubarak by Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty 馃拑馃拑馃拑馃拑.

47~AL-WADUD

The Loving

48~AL-MAJID

The Glorious

23~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Munzirinah.

馃寗 LEAVE TAKING ND WED馃寗

Episode 47_48

_____Kwana biyu tsakani kamar yadda Sadi ya fad'awa Malam Habu haka ne ya faru sun tafi Cameron cikin 'kwarin gwiwa da zummar neman kud'i ta hanyar halal basu sare ba musamman Malam Habu tsabar farin ciki kasa ko shan ruwa yai har suka tafi nan labari ya karkad'e gari malam Habu da Sadi sun tafi neman kud'i Cameron kowa da abinda zai tofa wasu na fatan alkhairi wasu na fatan tsiya harda masu cewa kowa yai ta kansa kwanan nan malam Habu arzikin sa zai dawo ya manta da rayuwar 'kunci.

馃彊锔廌UTSE MOPAL-BASE馃彊锔

Cikin shiri Amatu da Maryam harda Nabilah suka fito harabar gida Maryam na d'auko musu mota zasuje Miyetti kar'bo d'inkin ashobi d'insu idan sun dawo zasuje benin galadima a musu saloon sunsha gyara kamar sune amaren Maryam ce ke driving lokaci zuwa lokaci tana kallon Amatu dake ta faman murmushi cikin mamaki tace.

"Amatullahi na tambaye ki"?.

Juyowa Amatu tai tana kallon ta har lokacin da murmushin ta akan fuskarta tace "eh meya faru"?.

Daidai Maryam zata sha kwanar asibitin police clinic ta shiga takur site zuwa gidan 'kanwar ummansu tace "nifa na kasa ganewa tun d'azu muna breakfast naga sai murmushi kike akwai abinda ya saki farin ciki ne"?.

"Kai Amatu ta d'aga tana cewa "eh akwai kawai na matsu sosai gobe tayi ne".

'Dan zaro ido Maryam tai har tana hadawa da dariya tace "saboda kece Aunty Lailah amarya"?.

Kai Amatu ta girgiza "a'a kawai na tuna gobe umma zata zo zan ganta ta ganni kuma na tabbata babanmu zaizo d'aurin aure Allah yasa domin ambatonsa danai har yasa naji ina kewarsa ke kuma har kikai min wata fassara daban wai amarya rufa min asiri ina zaune lafya amarya a gidan wa".

Le'kowa Nabilah dake baya tai tana cewa "amarya a gidan mijinki koba haka ba"?.

"Eh ba haka ba waye miji na"?.

"Mai sonki mana".

"Waye mai Sona"?.

"Hhhhh ji Amatu da wata tambaya dan Allah taya zan sani abu a duhu kodan banace ba ko wannan zuwa gidan da kikai wani yace yana sonki".

"Oh Nabilah zaki fara ko? Please kiyi shiru".

"Shikenan nayi shiru馃き Nabilah ta karasa maganar tana rufe bakinta parking Maryam tayi da mota suna fitowa suka shiga gidan da ya kasance gate ne amma ba mai gadi kuma ba laifi gidan Masha Allah ya matukar had'uwa matar gidan tana zaune a parlor tana kallo suka shiga da sallama ganinsu yasa ta d'au remote tana rage 'karar vidion tace.

"Tofa Antin gida (Maryam haka take kiranta saboda sunan yayar mijinta ce) yau kune a cikin namu sannunku da zuwa bismilllah ku shigo man kuke ra'bewa kamar wasu ba'ki" zama sukai suna gaishe da ita ta amsa da fara'a taba kallon Amatu tace "wannan yarinyar ce 'yar gidan Binta yayar Bashir ko"? Kai Maryam ta d'aga "eh itace Aunty Umma munzo kar'bar ankon mu a gurin telan momy shine nace bari mu karaso mu gaisa ke"

"Aiko kun kyauta Maryam nagode muku kunfi Ahmad zumunci gashi a kwanakin nan kusan zuwanku hudu amma yaron nan shiru kamar baya gari rabo dana ganshi harna manta sai yanzu da bikinsa ya tashi zanje mu had'u ai sai naci 'kaniyarsa".

'Yar dariya Maryam tana mi'kewa tace "ina Ikram ko bata nan banji motsinta ba"?.

"Oh Ikram tana kitchen wai saurayinta nefa zai zo daga nan-nan Yadi shine take masa iyayi tun d'azu a kitchen ko uwar me take girka masa oho shima da bajajjan hancinsa a gurin".

Murmushi Maryam tai tana cewa "bari na gano abinda take yi ku jira ni" Maryam na rufe Nabilah tace "ai gara kizo mu tafi dan Allah wallhi yanzu idan kika shiga gurin Aunty Ikram sai mun 'bata lokaci muzo munata jiranki baki fito bakuma kin manta zamuje saloon"?.

Wucewa Maryam tai tana cewa "a'a ban manta ba ku jirani minti daya shigewa hanyar da zata kitchen tai tun kafin ta karasa taji Ikram na sakin ashar loya-loya a waya da sauri ta karasa tana cewa.

"Iki miya faru kike zagi"?.

Da sauri Ikram ta rungume Maryam cikin murna tace "ke sis yaushe kika zo kullum ina kiran wayar ki amma ta'ki shiga"?.

Had'e rai Maryam tai "humm ban yarda ba Ikram ganin idona yasa kika ce haka"?.

"Ke wallahi da gaske bata shiga but idan kin koma ki tambayi ya Ahmad zai fad'a miki ai shi muna waya dashi".

"Na'ki na tambaye shi idan da gaske ne ki bari saina koma zan tambaye shi domin daga nan Miyetti muka nufa bari na tafi dama Nabilah tana can a falon Aunty umma tana min 'korafi".

"Oh harda Nabilah kika taho"? Ikram tai maganar tana d'auko abinda data dafa masa da wanda ta soya dukka ta d'ebo musu shi zuwa falor amma Maryam tace bazasu zauna ba kar lokaci ya kure a yau zasuje saloon da lalle gashi yaune farin biki yace sai anyi 'kauyawa party suna shirin tafiya Ikram tace.

"Ku jirani kawai bari na dauko kayana mu tafi nima tunda nasan umma zuwa jimawa zaki le'ka kema ko"?.

Kaita d'aga mata "eh zanje mana zamuje mu gano 'kauyawa party dole" wucewa Ikram tai tana d'auko kayanta a jaka zasu tafi sukaiwa Aunty umma sallama .

Saida suka gama safgoginsu sannan suka kar'bi ashobin suna komawa gida ko zama basuyi ba iya kayan suka aje cikin sauri ganin lokacin yana neman fita musu suka tafi saloon basu suka dawo ba sai la'asar sosai a harabar gida suka ga Ahmad da wasu abokansa suna magana ganinsu yasa yace.

"Amatu dama ke nake nema dan Allah ki fad'a min ya shigar 'kauyawa take mun rasa yadda zamuyi"?.

'Dan harararsa Amatu tai tana had'e rai tace "ai nima ban sani ba saidai kayi sacin a gogul zaka gani" dariya Ahmad yai "haba ke kuwa sorry gani nayi ke kin sani shiyasa Allah kuwa serious nake tambayarki ki fad'a min yadda zanyi"? "Shikenan zan fad'a maka sai zuwa jimawa dan wallhi yanzu a gajiye nake" .

"ok ba damuwa ki huta zamuyi magana an jima kafin lokacin shiri yayi" to kawai Amatu tace masa tana wucewa ciki domin ita yau bata jin dad'i sosai zazza'bi ne yake neman rufeta tana shiga bedroom kwanciya tai taja bargo dan har taji sanyi ya mata kad'ata kallonta Maryam tai "Amatu yada kwanciya"? Kaita d'aga "eh bana jin dad'i ne".

"Ok Allah ya sauwake amma da kin tashi kinga la'asar fa tayi idan an Kira sallah saiki kwanta" "eh zam tashi wanda nake son maybe hakan zaisa naji d'an dama dama zazza'bi keson kamani".

"Subahanallahi Amatu zazza'bi kuma Bari naiwa ya Ahmad magana yazo ya duba ki".

"A'a karki kira shi ban tabbatar ba tukuna sanyin da nakeji ne ga jikina yai zafi" tun kafin Maryam tayi maja Ikram taja tsaki tana jan hannun Maryam tace.

"Ke dan Allah zo mu tafi yar rainin hankali wai tazo birni ta waye sai wani wahalar dake take wai ita ga maamaa kema kina biye mata muje share ta" murmushi Maryam tai tana dafa goshin Amatu da gaske jikinta d'au yake da zafi kamar wuta kai ta jinjina tana cewa.

"Amatu zazza'bi man kike bari na kirashi" fita sukai Ikram sai harararta take tabe baki Amatu tai tana gyara kwanciyar ta tace "wannan budurwar akwai yar jin kai amma babu komai ina daidai da zamaninki wallhi ba kyaleki zanyi naga take-takenki nima zan fito miki cikin kalata idan ba haka nayi miki baza mu zauna lafiya ba baki isa raina niba dan daga 'kauye nazo".

Bayan sallar magriba suka fara taruwa a harabar gidan inda zasuyi 'kauyawa kowa

36 / 67