Advertisements
Chapter 33 Reading Me Kamar Sarki Book 2 Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Me Kamar Sarki Book 2 Hausa Novel

Author :  Yusrah Musa Category :  Complete Novels

Chapter   33 / 67

96K to 99K   out of 200.4K words

yake shirin yi Hassan yaci gaba "wallahi bazan rabu da ita ba saina aureta ko zakai bunga馃檴馃檴馃槀" zaro ido Ilyah yai yana sake duban Hassan takaici ya gama cika shi yace.

"Hassan Hassan tabd'ijan amma wallahi baka da hankali kayi hauka ne ni kake fad'awa haka"?.

Ran Hassan a had'e zaiyi magana Hussaini dake gefe yana cin abinci yace "ai bakai ba Hassan koni akwai wacce na hasko a cikinsu Aisha 'yar gidan Saude kuma babu wani so'ko'kon dazai hana na aure ta ban ganshi ba馃槻馃榿馃槼" 馃槀tabd'i tashin hankali wanda ba'a sa masa rana Ilyah kallon su yake a fusace ji yake kamar yayi hauka tsabar ba'kin cikin da suke cusa masa yama kasa magana sai sunkuyar dakai yayi yana shiru kallon juna sukai suna dariya Hassan yace.

"Baba karfa ka zauna 'bata lokacin ka wajen tunani da nazarin ya zaka 'bullowa al'amarin bari na baka shawara wallahi gara ka koma gefe ka zuba mana ido dan aure kamar munyi inace 'karfin zumunci zamu ninka ka manta me yanke zumunci babu shi ba rahmar Allah kai kuma kake kokarin rabawa tab kaji fa Hussaini meye makomar baba"?.

Batare da Hussaini ya d'ago yace "makomar sa suya da babbaka wuta ce idan aka wullashi saiya 'kone ya toye ya dangwalo 'kasan bakwai馃槻" had'a ido sukai suna fashewa da dariya Ilyah tsabar takaicin da suka 'kunsa masa ji yake kamar ya zubar da hawaye Bara'atu ce ta karaso gurin ranta a 'bace saboda tana jin komai dukkan su biyun ta kalla tana cewa "wai shin kun gamu da ciwon hauka ne a garin da kukaje kome? Uban daya haife ku kukewa dariya馃槨 gaskiya tunda har yanzu bakuyi hankali ba bansan yaushe zakuyi ba gani kuke riba zakuci ku tsaya ku gyara halinku wannan d'abi'ar da kuka d'auka bazai kai kuba".

"Yo umma ai kina jin fa abinda yake cewa miye a ciki馃し dan kawai muce yan matan kawu Habubakar muke so ba abin farin ciki bane yana matsayin yayan sa amma harda wani wallahi tallahi wallahi tallahi wallahi tallahi kaji rantsuwa uku ko 馃槀馃槀 baza ku aure suba mu kuma wallahi tallahi saimun auresu ko mutum zaiyi bunga馃檴馃ぉ馃槀馃槀馃槀馃ぃ Hassan ya karasa maganar yana tsayar da idonsa tarr cikin na Bara'atu.

Kae Bara'atu ta jinjina tana cewa "tabdijam babbar magana kenan d'an sanda yaga gawar soja Hassan Hussaini yaushe kuka zama haka har ana fad'a muku magana kuna mayarwa dan raini to bari kuji maganar gaskiya koni ban amince muku ku auresu ba kun dai ji dakyau na fad'a muku inba shashancin kuba ai da gaske yake fatararran ne uwar me yake dashi yanzu wanda lomar abinci take masa wuya kowa yana gudun auren 'ya'yansa saboda kar talauci ya shafe shi ku kuma tsabar 'batan basira kuna cusa kai zakuje ku yayo mana masifa ku kawo mana gida lokacin da suke matasa kamar ku wanne irin wulakancin ne Habubakar baiwa ubanku ba har sha'ke masa wuya ya ta'ba yi ya hankad'a shi gaban Baffah duk wannan cin mutumcin dayai masa amma tsabar sakarci harku so 'ya'yansa uwar me zakuyi dasu meye abin so a jikinsu gayyar talauci da 'kas'kanci yanzu kaf garin nan ba wanda yakai gidan Habubakar fatara da shan wuyar rayuwa to wallahi baku isa ba kuji dakyau na fad'a muku".

Ta'be baki Hussaini yai yana kallon Bara'atu yace "wallahi umma saimun aure su ko mutum zaiyi bunga馃槵 garama kiyi shiru ki daina 'bata bakinki akan mu ba wani so'ko'kon dazai rabani da Aisha saiya shirya duk wanda yai yunkurin shiga tsakanin mu saina jajjaga shi nayi 'kuli 'kulin kubura dashi馃槻馃槀".

Mi'kewa Hassan yai yana cewa "kaima kenan Hussaini balle ni akan Amatu ai inaga saidai na markad'a mutum nayi farfesu dashi馃ぃ馃槃 nikam nayi gidan kawuna Habubakar yau acan zanci abincin dare馃檴" yana rufe baki Hussaini ya ture kwanon abincin dake gabansa shima yana mi'kewa ya kalli Bara'atu data bisu da ido yace "umma munyi gidan kawun mu Habubakar acan zamuci abincin dare karki d'ora damu idan kuma umma Maimuh ce itama ki fad'a mata karta dafa damu yau ko 'kasa aka dafa a gidansa shi zamuci馃檳" suna kallo basu da damar hanawa haka suka fice numfashin daya tokarewa Ilyah a 'kirji da'kyar ya fisgoshi yana sake kallon hanyar fita yace.

"Na shiga uku Bara'atu kiji wata masifa da yaran nan suke neman d'ora min kawai ina zamana da arziki na zasu auro masu 'kashin tsiya su sa na talauce to wallahi bada yawu na ba lallai zasuga fushi na akan wannan al'amarin idan basu rabu dasu ba".

Bara'atu dake tsaye guri daya ta kasa gaba ta kasa baya sai maimaita maganar su take na cewa wallahi tallahi saimun auresu ko mutum zaiyi bunga akwai matsala gagaruma ko itama bata kaunar wannan auren dole ne ta dakatar dasu da 'karfin tsiya.

"Wallahi baku isa ba inna yarda kun auresu ni ba 'yar halak bace shegun yara dan kunga kun zama samari karfin ku ya kawo shikenan kuke ganin kamar kunfi 'karfin kowa zanga ta yadda zakuyi auren ba tare da yardar muba harda ba wani so'ko'kon dazai hana tabd'i gaskiya yaran nan sunyi nisa".

Cikin takaici Ilyah yace "dani suke so'ko'kon wai ko zanyi bunga?馃槶馃槶 akan iyalan gidan Habubakar suke fad'a min haka amma shikenan nima take d'in zanga uban dazai amince ya d'aura musu auren a 'kauyen nan ban ganshi ba dan ko mai gari ne wallahi bai isa ba yasan sauran ai tunda yana amfana ta kud'i da kayan abinci yai min gardama yaga yadda ake wasan tsutsa馃悰 a rana馃寘 su kuma zasu dawo gidan su sameni dan ubansu tunda dawowa sukai domin su d'ora min hawan jini su kashe ni saidai su koma inda suka fito akan su auri 'ya'yan Habubakar gara idan sun tafi karsu dawo garin nan har abada zaifi min kwanciyar hankali da abinda suke 'ko'karin jawo min".

Maimuna na d'aki tana sauraron su bata fito ba dan kar ace tayi gulma tunda ba abinda ya shafeta bane kuma Ilyah dan bazai gane bane rashin biyayyar dayai wa Baffah ne alhaki ya fara bibiyarsa kuma zaici gaba da bibiyarsa har karshen rayuwar sa tunda bai nemi yafiyar Baffah ba baiyi zaman d'a na gari dashi ba taya zaice dole 'ya'yansa sai sun bishi bayan shima bai kasance mai biba dukkannin halin Ramatu na mayar da martani da rashin 'kyaliya su Hassan shi suka d'ebo dan haka zaisha kwasar ba'kin ciki damuwa yanzu ya fara gani kiran ya shiga uku ya jira dai lokaci ne gaggawar me yake tafiya dai wata rana saiya kasa furta wata kalma balle ya samu bakin magana ko kad'an bata jin haushin duk wani abu da zasuyi masa domin taga kalar wulakancin da sukewa Malam Habubakar shida Bara'atu talauci aiba hauka bane tana jin tsoron gaba Ilyah zai iya taka matakin da malam Habubakar yake ciki yanzu daga baya Malam Habun kuma Allah ya d'aga shi ya zama wani abu amma duk rashin kunyar Ilyah a wannan lokacin tasan bazai iya fuskantar shi da sunan ya yafe masa ko ya taimaka masa ba domin Allah yana taimakon bawansa matukar bawansa yana taimakon d'an uwansa musulmi sauke ajiyar zuciya tai tana sake gyara kwanciyarta domin ba itace da aikin gida ba gara tai bacci datayi ta sauraron zancen su tunda taga Bara'atu ma layinsu d'aya da Ilyah zuciyarsu bamai son ganin d'an uwa cikin farin ciki bane amma Bara'atu da bazata manta ba itama fa haka iyayenta suke a fatare a talauce auren Ilyah datai ne ta samu guri take d'an aika musu da kayayyakin abinci ai Ramatu batai 'karya ba da tace tazo a 'kar'kashe ta samu guri ta zama 'bukekiya kamar alade馃悥 hummm rayuwa ce ba wanda yasan gobe馃え subi a hankali su taka a sannu akwai ranar nadama ranar da zasuyi kuka da idonsu.

TO YAU KAM NA GAMA TYPING SAI ALLAH YA KAIMU GOBE DA RAI DA NISAN KWANA INSHA ALLAHU ZAMU D'ORA LITTAFIN ME KAMAR SARKI 馃憫 A INDA MUKA TSAYA馃檯.

Kudai ku kasance da馃憞

MRS AL-AMEEN AHMAD CE 馃槝.

TYPING 馃摬 ME KAMAR SARKI 馃拵馃憫馃帶 馃拫YUSRAH MUSA ABUBAKAR馃拫 馃尮馃.

馃憫ME KAMAR SARKI馃憫

馃憣 SABUWAR DUNIYA KUZO KUYI KALLO DADI YANA JIGAWA GARIN ILIMI GARIN ADDINI ZAMAN LAFIYA JIGAWA 馃崌锔忦煑火煆烇笍馃寖.

AYI HAKURI IDAN AN SAMU TYPING 馃摬 ERROR 馃敶馃洃 MATSALAR KEYBOARD NE馃か.

鉁嶏笍Mrs Al'ameen Ahmad ce 馃槝.

Inai muku barka da wannan lokaci fatan kuna cikin kyakkyawan yanayi馃寗 Allah yasa haka Amin 馃げ馃憦馃檹.

DON'T HARM ANYONE馃か DON'T ALLOW ANYONE TO HARM YOU 馃槨馃槧

_____________________

43~AR-RAQIB

The watchful

44~AL-MUJIB

The Responsive

21~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Muhsininah.

馃寗 PALACE ND DISPLEASE馃寗

Episode 43&44

Masarauta gabadaya yau ahlin gidan suna tare guri daya suna wani babban d'akin shan iska 'kawatacce mai girma sosai mai martaba Alhassan yana waje daya da matansa shima mai girma Alhussain yana gefe da nasa sai sauran samarin da 'yan matan suma can suna ta hayaniya kowa fira yake cikin jin dad'i saidai amma a 'bangaren mai girma Alhussain idan ka duba zakaga akwai matsala domin sultana Hadizah ta cika tayi famm kamar zata fashe sai huci take tana kumbure kumbure shi kuma yana mata magana.

"Hadizah wai me kikeyi haka kinsan abinda kike fad'a kuwa d'an gidan nawa (Asad) zance na yanke ala'ka tsakani na dashi tsabar rashin hankali dan kawai ya daki Khimiyyah? ta farfad'o ne kin tambaye ta laifin me tayi masa ni bana abu da ka bazan ta'ba yarda da komai ba sai Asad ya dawo zanji inace Khimiyyah is my daughter"? Dan haka ki rufe min baki".

Takaici ne ya kama Sultana Hadizah jin abinda yake cewa dama tasan ko kashe Khimiyyah Asad yai mai girma Alhussain bazaiga laifin saba zaice laifin Khimiyyah ne ta rasa wanne irin so ne a tsakanin su amma zatai maganin abun dole ne ta dau mataki tunda ta fahimci mai girma Alhussain yana goyon bayan dukan da Asad yai mata idan har bata tashi a tsaye ta dakatar dashi ba yadda jinin su bai had'u ba tofa wata rana saidai aga gawarta ta sani sarai Asad zai iya kasheta kuma ya kashe banza..........................,...............

Katse mata tunani mai girma Alhussain yai da cewa "kin dai jini ko? Saiki kiyaye kada ki kuskura naji wata magana daga baya da bakisan halin Khimiyyah bane saiki d'aga hankalin ki".

Sabon ba'kin ciki ne ya 'kara lullu'be Sultana Hadizah cikin tsananin takaici ta juya tana kallon yadda Sultana Hauwa (Mami) take dariya ga Sultana Fatima na taya ta mai martaba Alhassan kuma yana murmushi wato iyayensa (Asad) suna cikin farin ciki basu damu da jinyar 'yarta ba su kuma gasu shaid'an ya baza musu gariya馃槀 sai fad'i in fad'a suke 'kwafa tai tana dawo da kallonta kan mai girma Alhussain tace.

"Wallahi akwai mugunta a cikin al'amarin nam kawai dan ka'ki yarda ne amma na tabbata Khimiyyah babu abinda taiwa Asad zaluncinsa ne kawai ya motsa ai dama ya tsaneta tun tana yarinya bata had'a inuwa d'aya dashi baya barin ta tayi wargi tsabar ba'kar zuciya da......,......................

'Daga mata hannu mai girma Alhussain yai yana cewa "Hadizah ya isheki haka ki rufe baki tun kafin ki fusata ni zanyi abinda bakya zato wanda baza'a ji dad'i ba umarni nane wannan zan baki ba shawara ba".

Kuka sultana Hadizah ta fashe dashi tanajin kamar ana mata yayyafar wuta a jikinta muryarta na rawa tace "yanzu tsakani da Allah wanne irin hukunci ne wannan ka yanke min wallahi yarinyar nan bata da laifi itace da gaskiya dan ka'ki yarda ne sonsa ya rufe ma ido".

"Ko kuma ke son 'yarki ya rufe miki ido ba zan gamsu ne kawai idan Asad ya fad'a min abinda tai masa amma bazan kar'bi uzurin kiba koda Khimiyyah ce ta farfad'o bazan amincewa abinda zata fad'a min ba balle ke da mukaje wajen tare bakisan abinda ya shiga tsananin suba kamar yadda nima ban sani ba".

Jin abinda mai girma Alhussain yake fad'a yasa sultana Hadizah kara sautin kukanta wanda ya jawo hankalin sauran cikin mamaki da tashin hankalin kar ace waya akayo musu cewa Khimiyyah ta mutu mai martaba Alhassan yace.

"Lafiya ko jikin Khimiyyah ne"?.

Kai mai girma Alhussain ya girgiza yana kallon yaran nasu da suma suka bada tension yace "Ajeeb ku d'an bamu guri zamuyi magana" mi'kewa sukai Ameer na cewa "hospital zamu koma yanzu zamuyi magana da doctor Amar yaya yake ganin jikin nata da sauki idan yace a'a gaskiya ina ganin gara mu fita da ita zuwa India ko kuwa dai me kuka ce"?.

"Eh haka ne Ameer yanzu muje ko a hanya saimu karasa maganar domin ni banga amfanin zamanta a asibitin ba tunda ba wani cigaba kullum kaje tana nan a yadda take bata motsa koda yatsarta ne" Annur ya fad'a yana yin gaba suka bi bayansa harda su Shaukiyyah.

Bayan fitarsu mai martaba ya maida hankalin sa kan mai girma Alhussain yace "uhum ina jinka meya faru kukan me Hadizah take"?.

Juyawa mai girma Alhussain yai yana kallon Sultana Hadizah da mamaki wato har lokacin bata daina kuka ba yace.

"Babu kukanta mara dalili ne akan me? Idan Khimiyyah yarta ce nima 'yata ce sannan yaya kaima 'yarkace a tunani na ba bare dukan mu d'aya ne koda Khimiyyah ta mutu kwananta ne ya 'kare wallahi bazan ta'ba kallon Asad matsayin shine ya kashe min ita ba amma wannan matar tana da abinda fad'a wai kuka take akan bazata yarda ba tsabar rashin hankali harda maganar zuwa kotu馃檴 tana son fad'awa duniya cewa bamu zama tsintsiya ba laifin d'an uwa daud'ar gora ne amma ita sam ta'ki fahimta saboda shashanci" ya karasa maganar ransa a 'bace.

Sultana Hadizah data kifa kai cikin Alkebba tana kuka jin abinda yake cewa yasa ta d'ago cikin kuka "wallahi bazan yarda ba dama can Asad da Khimiyyah jininsu bai had'u ba tun suna yara Asad mugu ne ba 'kaunarta yake ba kowa zai sake ya nuna shi d'ane amma banda ita indai yana guri ya riga ya zame mata dodo kullum sai tayi mafarkinsa da ihunta wani lokacin har a fili zakiji tana kuka kamar gaske tana kiran yai hakuri dan Allah harda wu'ka wani lokacin tace tana ganinsa a mafarki yana binta zai kasheta kuma akan haka me za'a cemin bayan ya gama cuta ta.........鈥.......................

"HADIZAH YA ISHE KI HAKA馃槨" Mai girma Alhussain yai maganar cikin tsawa ko kunya haka Sultana Hadizah ta sake d'ora hannu aka tana fashewa da kuka "na shiga uku na lalace wayyo Allah na wai ana neman kashe min 'ya kuma nayi magana saboda d'an gidan kane shine kake min tsawa..................,........

"HADIZAH BANCE KI RUMIN MIN BAKI BA馃? ZAN AIKATA ABINDA ZAKI NADAMAR SA"馃槪.

"Hussain kayi shiru haka ina son zanyi magana ku bani hankulanku nan idan kun gama" mai martaba Alhassan ya fad'a yana kallon su d'aya bayan d'aya ganin shed'an ya shigo musu gida yazo yana son tarwatsa musu farin ciki.

"Kayi hakuri yaya raina ne ya riga da ya gama 'baci wannan matar da kake ganinta bata da kara ko kadan batasan me take ba idan ba rashin ta idon ba a barshi ni 'kanin kane sannan Sultana Shafi'ah abiyarta ce zata iya fad'ar komai a gabanta amma kufa mahaifan Asad ne take irin wannan wulakancin iri iri a gabanku saboda bata gaji arziki ba".

Har lokacin bakin Sultana Hadizah bai mutu ba idonta jajur ta kallo Mami tana cewa "ai ba laifin kowa bane bayan mahaifiyarsa itace ta goya masa baya ba iya ra'ayin sa bane ga ummul-gauwal (uwar munafukai) nan tana jina......................

Nunata mai girma Alhussain yai da yatsa cikin takaici jin abinda take cewa yace "kinga Hadizah kiyaye ni idan wasu ne ma suke zugaki zasu kaiki su barki baki ta'ba ganin fushi ba ko? Ki taka a sannu idan kika kaini bango zaki sha mamakin irin huluncin da zan yanke miki bake ko 'yan gidanku ba hatta danginki bazasu ji dad'i ba idan kina gani kamar wasa nake kici gaba kece zaki ba wani labari ki tsaya iya matsayin ki".

Kasa magana Sultana Hadizah tai sai huci mai zafi da turiri ne yake fitowa daga zuciyarta cike da 'kiyayya ta sake d'agowa tana kallon Mami da ta d'auke hankalinta sam a kansu tamkar bata gurin hakan datai ba kamaramin 'konawa Sultana Hadizah rai yayi ba lallai wallahi bazata ha'kura ta 'kyale ba koda zai zama sanadin mutuwar aurenta zata d'auka indai Asad zai wulakanta Allah yasa ya mutu acan Allah yasa bazai sake dawowa ba yayi karo da masifa 'yan ta'adda suyi masa kisan 'kyama.

馃槻馃槼TOFA SUBAHANALLAHI SULTANA HADIZAH YADAI馃 WANNAN WACCE IRIN 'KIYAYYA CE馃え馃槒 KIKE NUNAWA ASAD 'DIN MU?馃檮馃檮.

"Kun gama"? Mai martaba Alhassan ya tambaye ransa a 'bace.

Kai mai girma Alhussain ya girgiza yana cewa "kayi hakuri yaya ni bana d'aukar shashanci ne".

"Ai shiyasa nace kun gama"?.

"Eh yaya kayi hakuri".

"Shikenan ku saurara da kai zan fara Hussaini mene ya had'a ku har wannan maganar ta taso?.

"Yaya magana take akan bazata yarda ba idan Khimiyyah ta mutu wai harda sai taje kotu tsabar da'ki'kanci ni kuma a tunani na koda Asad ne da laifi kuma ya daketa harta mutu bazata bud'i baki tace komai ba saboda laifin d'an uwa daud'ar gora ne".

Kai mai martaba ya jinjina cikin mamaki yana kallon Sultana Hadizah domin ya kira Asad a nutse ya tambaye shi abinda ya had'a su kuma ya fad'a masa bai cewa kowa komai bane so yake sai Khimiyyah ta tashi ayi a gaban kowa dan yanzu kome zaice tunda har anyi haka Sultana Hadizah zataga kamar shima yana kare shine dan d'an sane baison laifinsa.

Maida hankalin sa kan mai girma Alhussain yai yana cewa "ba nace a bari sai Asad ya samu hutu yazo gida ba sannan ita kuma Khimiyyan ta samu lafiya na yarda na amince ayi bincike a sannan duk wanda yake da laifi a cikin zai fuskanci hukunci na bana so na sake jin wata magana indai akan wannan case d'in ne zan zamo uba mai adalci a tsakanin su"?.

"To yaya kayi hakuri in Allah ya yarda za'a kiyaye na tabbata Khimiyyah ce mara gaskiya ba Asad ba

33 / 67