Author : Yusrah Musa Category : Complete Novels
kawai take ya mutu tabalbaleshi dad'in abun ma a kofar gida sukai masa ba a gaban yan matan nasu ba su suna cikin gidan gurin dangin Bara'atu.
Da dare yayi ganin yadda mutane akai shimfid'a a waje kowa ya kwanta dayake lokacin zafi ne yasa Hassan kiran Bara'atu gefe yana cewa.
"Wai umma a ina 'yan matan mu zasu kwanta ne dare fa yayi barci sukeji"?.
Kallon sa Bara'atu tai tana cewa "a ina kuwa zasu kwanta baga shimfid'a nan anyi ba zata wadaci kowa".
Zaro ido Hussaini yai "kai akan tabarma kuma tabdijan gaskiya bazasu kwana a kasa ba".
Baki bud'e Bara'atu tace "au a sama zasu kwana kenan"?.
"A'a ba'a sama zasu kwana ba amma dai katifa zaki basu ko taki ko ta baba".
Kai Bara'atu ta jinjina tana cewa "lallai yaran nan baku da hankali nice zan baku katifa ta tana kan gadona na fito da ita wasu 'kattin su kwanta cab hummm".
Kallonta Hassan yai yana cewa "to meye ba surukanki bane basu isa kiyi musu haka ba ba'kin naku ne fa bikin 'yarku suka xo".
Kafin Bara'atu tayi magana Hussaini yace "abin haushin ma wai harda wasu 'kattin? Kai Hussainan tawa ce 'katti"?.
Wata uwar harara Bara'atu ta sakar masa tana cewa "au bazan fad'a ba sannu ubana saika rufeni da duka saboda nacewa wasu 'katti sai naga budurwa tafi uwa ko irinku ko"?.
Kau dakai Hassan yai "nidai Umma duk ba wannan ba kisan yadda zakiyi ki nemo musu katifa suna mota fa suna jiranmu Hassana har gyangyad'i take tsakani".
Tsaki Bara'atu tana cewa "wallahi indai bazasu zo ku kwanta a inda kowa ya kwanta ba saidai su kwana a motar wai me kuke haka ga guri nan malala da yawa amma dan masifa danku d'aga min hankali kunzo kun dameni haba da Allah gafacan kuban guri" ta karasa maganar tana wucewa ta koma cikin baranta ta nemi guri kusa da yan uwanta dake ta aikin yanka alayyahu dasu albasa za'ai sabuwar miya gobe ma gagarumin biki za'ai sannan da kusan magriba amarya tad'au hanyar birni kamar yadda take fata.
"Kan bala'i Hassan kaga wata shariya a gurin Umma wai da gaske take a cikin wadannan mutanen zasu zo su kwanta haka kawai su zuba musu 'kwar'kwata a kyakkyawan gashinsu馃ぃ.
Tsaki Hassan yai yana cewa "wallahi bazasu kwana a kasa ba muje d'aki shegiyar amaryar ba bikinta suka zoba ta d'aga tata katifar ta basu ko naci ubanta" yana rufe baki sukai d'akin Nafisa a kwance suka sameta har tayi barci wani duka Hassan ya sauke mata wanda a firgice ta tashi cikin gigin barci ganin basawa tsaye a kanta yasa tace.
"Meya faru"?.
Harararta Hussaini yai yana cewa "ubanki ne d'aga mana katifa yan matan mu zasu kwanta".
Jin abinda yace yasa Nafisa tace "kai dan Allah Hussaini daga yau nima fa shikenan nayi bankwana da katifar kuma a kasa zan kwana"?.
Dundu Hassan yai mata yana cewa "a bola zaki kwana dan uwarki ba kasa ba har ana magana kina mayarwa mutane wato ke ga amarya ko rainin amarci ya shigeki wallahi so kike yanzu nan na karya miki qafa sai naga gaggawar zuwa gidan mijin shegiya 'kwartuwa馃檲 zakici ubanki da qafafunki zaki nemi hanyar qauyenku ki gudu idan kikaji maza馃檳.
SUBAHANALLAHI WADANNE IRIN YAYU NE WANNAN馃槀.
Tsayawa Nafisa tai tana kallon sa cikin tsawa yace "zaki d'aga ko saina hautsinar dake".
Ba arziki da gudu Nafisa ta d'aga tana ficewa d'aga d'akin tsaki Hussaini yai yana cewa "idan ba jaraba bama wannan yarinyar ina ta isa aure kaga fa yan matan mu dame muka fisu amma a hakan iyayensu sunce mana yara ne mud'an kara jira hummm zata ci ubanta ne kama muje" d'aukar katifar sukai waje.
Da gudu Nafisa ta karasa gurin Bara'atu tana kuka tace "Umma Kinga su Hassan sunje ina barci na suka daddake ni sannan suka qwace min katifa ta wai yan matansu ne zasu kwanta".
Dafe kai Bara'atu tai tana kallon ta tace "Kinga Nafisa daina kuka iya yau ne zaluntar taki gobe iyanzu koda kud'i bazasu ganki ba balle su zalunce kin saidai su zalunci kansu tashi kije d'akina ki kwanta" mi'kewa Nafisa tai tana shiga d'aki.
Bara'atu kuma ta tashi tana zuwa kofar d'akin su Hassan harsun shimfid'a katifar sun sa bargo su d'ame sun d'auko fulo guda biyu sun jera suna kafa 'kusa zasu daura musu net tabi Bara'atu ta ri'ke tana cewa.
"Yanzu ku kun kyauta kenan yarinyar tana barci tsabar ba'kar mugunta kuje ku daketa hakan bai isheku kuka murgineta kuka kar'be katifar yayi muku kyau".
Daina kafa 'kusar Hassan yai yana cewa ''to Umma tsakani da Allah kuma fa ba haka akeyi ba taya zamuzo da ba'ki tun daga wata 'kasar ku kasa tarbarsu da abun arziki alhali hadisi ne guda cewa "wanda ya bada gaskiya da Allah da ranar alkiyama ya girmama ba'konsa" kodan kuba sani kukai ba gashi yanzu na sanar daku gobe saiku tashi da wuri ku nema musu kayan kari na Alfarma don baza suci abincin biki ba sannan a ragunan baba a yanka musu daya ko a bamu kaji biyar gobe mu kaisu masu suya su sayo musu kuma naga wannan shegiyar yarinyar anyi mata gara to wallahi kar mu tashi tafiya ace ba'a d'iba musu ba tunda muna da mota har Kanon zamu bita muje mu d'ebo musu".
Sauke numfashi Bara'atu tai jin zai mayar da ita sokuwa ya d'ora mata ciwon kai bata biyewa maganar saba ta juya tana cewa.
"Allah ya shirye ku".
Dariya Hassan yai yana cewa "Amin Umma addu'a ce mai kyau kikai mana kai Hussaini jeka shigo dasu Allah yasa basuyi barci a cikin motar ba aiduk laifin umma ne kaga fa mu yadda suke mana acan ga mahaifansu na sonmu in munje suyita hidima damu amma nan sunxo gurin kwanciya mai kyau ma ya gagara haba" fita Hussaini yai yana shigowa dasu suka zo suka kwanta su kuma sukai waje domin ba sosai dare yayi ba.
Washe gari ranar yinin biki amarya an'ki zama guri d'aya ayi yu ayi nan fuuu sai sallama takewa mutane kamar bazata sake dawowa garin ba har abada bakinta har kunne yau zatai kwanan birni la'asar nayi motocin d'aukar amarya suka fara jerowa harsu biyar ras amma sakamakon yanayin dawowa saboda idan sun kaita acan zasu kwana su d'anyi mata gyare gyare sai su taho shiyasa aka za'bi mutum shida kadai motar amarya ita kad'ai sai Maimuna sannan sauran motar mutum had'un suka shiga aka dau hanyar birni dan tsabar d'oki da'kyar Nafisa ta tsaya aka d'anyi mata nasiha sai mi'kewa tsaye take ana dur'kusarta馃 a haka aka gama fad'an ba lallai nasihar ta shiga kunnen ta bama hankalin ta ya kad'a gaba haka ta tafi tabar su Bara'atu da Ilyah cikin farin ciki da murna 'ya ta koma rayuwar city馃彊锔.
馃彊锔廗ANO馃彊锔
________Uhm Allah yayi amarya Nafisa a gidan Nurain yaudai mafarki ya zama gaskiya buri ya cika anzo birni za'a bararraje a gwangwaje a d'ebi nishad'i balle wadanda suka rakota ba yawane dasu ba daga mutum biyu ta bangaren Ramatu sai dangin Bara'atu suma su biyu sai kuma Maimuna da Salma suna zaune a part d'in da aka baiwa Nafisa sai zizzilla ido suke suna santin gidan Nafisa tazo aljannar duniya haka Nurain ya kawo musu kayan abinci da abun sha iri iri na alfarma masu tsada wanda basu ta'ba ganin irinsa ba wani tsoro sukaji kar suci ya jawo musu matsala sannan yace su tsaya su kwana saboda dare yayi musu gobe da safe sai yasa a mayar dasu aiko dad'i ne ya rufesu jin zasuyi kwanan daula.
Har Nafisa na tambayar Salma "amma dai Salma badake zasu koma ba? ki tsaya kimin sati tunda bikinki sai watan gobe zansa Nurain ya miki sayayya sannan ya kaiki har gida da kansa".
Zaro ido waje Salma tai tana kallon Nafisa dake wani fari da gwalli irin na amare kafin tayi dariya tana cewa "ni yar ubana rufa min asiri ban shirya zaman birni ba wallahi tare dasu zamu koma ba zaman da zan kimaji na fad'a miki dan kada ma kisa rai ehe bazan zauna ba".
Marairaice Nafisa tayi "haba ke kuwa Salma yanxu in kuka tafi bansan ranar had'uwar muba idan ba garin nazo ba dan Allah ki tsaya kiyi min sati"?.
Kai Salma ta girgiza tana cewa "kefa wallahi bazan zauna ba ko kwana d'aya ne yadda muka zo tare dasu tare zamu koma garama kibar ro'ko na".
Kallon maimuna Nafisa tai tace "dan Allah umma Maimuh kisa mana baki a zancen nan ko Salma zata yarda ta zauna min zansa Nurain ya mayar da ita".
Itama Maimunan da yake bata goyon bayan zaman Salman bataga me zata zauna tayi ba a yanxu dan haka cikin zillewa da wayancewa tace "a'a ni ba ruwana da safgarku ta shirme ku daina sani a ciki kuyi iyaku" ta fad'a tana kau dakai Salman ma ta kafe bazata zauna ba dole haka Nafisa ta ha'kura da niyyar idan Nurain ya shigo zata fad'a masa ya lallmi Salman ta zauna tayi satin.
washe gari ma saida suka wuni suna shishshirya mata abubuwa da suka gama sukai wanka bayan la'asar Nurain yasa drivern Daddy yazo ya daukesu domin ya mayar dasu gida haka suka bar Nafisa ko d'an irin jin kewar nan babu itadai kawai tazo birni shine abinda ranta ya d'auka kuma idan ta tuna take jin girman Kai ya hauta.馃
Misalin karfe takwas na dare Nafisa anci wankar taryar ango an bad'a kwalliya a fuska pawder tayi fau kamar biri馃惖 an fesa turare anhau gado an lullu'be jiki da mayafi ana jiransa ya shigo tana zaune shiru shiru taji an bud'e kofa an shigo ta d'auka shine harda sake gyara rufe mayafin zuwa fuskarta tana murmushi yau gata ga Nurain sunyi aure a birni wani irin dad'i ne taji yana ratsa ta har tana lumshe ido a ranta tace yanzu lokacina zai fara daga yau zan bud'e sabuwar rayuwa..........................
Katse mata maganar zucin da take akai da cewa "hum'um kan bala'i lallai ya Nurain ya fad'o yanxu mine abun so a village girl harzai aurota yasa a gidansa heyeee ke madam 'kwas-'kwas bud'e wannan banzan mayafin naki ki kallemu sannan ki bud'e kunne ki saurare mu munzo miki da wasu maganganu ne".
Bud'e mayafin Nafisa tayi tana kallon su cike da mamaki tace "su waye ku"?.
Wata iriyar ba'kar harara tai karo da ita daga dukka su hud'un kafin Mimah tace "oh wai kina nufin baki gane muba humm to bari na miki bayani wannan uwarki ce wannan ubankice wannan kanwar ubanki ce ni kuma kanwar uwarki ce yanzu kin gane mu? kiji min shegiyar yarinya fa Meelat wai har tambayar mu take suwaye mu"?.
Tsaki meelat tai tana cewa "ke kika tsaya yi bayanin mu suwaye maiyasa data tambaya baki kifeta da mari ba wanda azaba zata sa ta gane yaren da kike nufi domin wannan akuyar tana bu'katar dusa but not now mubari zuwa gobe zaki bayani barka da shigowa kabarin ki kuma lahirarki ke da'ki'kiya fatan kinzo da likafani? Idan baki zo dashi ba kisa ya Nurain ya sayo miki gobe kuzo mutafi kada yazo ya same mu muna nan kuma tsautsayi yasa ki fad'a masa cewa wasu 'yan mata sun shigo gunki humyim wallahi gobe saimun canza miki halitta".
Kallon Mimih dake tsaye Mimah tai tana cewa "ke baki magana ba ko sai goben"?.
Kai Mimih ta girgiza tana kara dukawa akan Nafisa tare da sake bud'e mata dukkan girman idonta kafin tace.
"Unbelievable sannu amarya ya kike ya gida"?.
Da mamaki sauran suka kalleta Meelat da hartaje bakin kofar fita da sauri ta dawo tana cewa "Mimih me naji kince mata sannu amarya humm tofa ashe zata samu shiga ta bangaren ki ko"驴.
Cizon yatsa Mimih tai tana jin kamar ta d'aga hannu ta kwad'awa Nafisan mari kafin tace "heeeyy tabd'ijan dan'kari anan ake bele'u kuturun ubancan yanzu ya Nurain duk kyansa da jin kansa amma ya haure city ya tafi can wani dabban stupid d'in qauye yaje ya auro wannan ba'kar jahilar yasata a cikin familyn mu ta haifa mana da'ki'kan yara munana irinta hum'um kalleta da Allah wai amarya guda amma babu suturar arziki kalli wani banzan jakin lalle a kafarta wannan tsaya da saltif sukai ne ko kuma tsabar kauyanci haka aka dam'bara lallen? kutumelesi kiji wani wani kafurin d'oyi馃檴 babu d'an kamshi da yake tashi na amaren nan sai tsamin kanta ke buguna tayi kitsone ma wannan jakar kauyen"? Ta karasa maganar tana fisge kwalin dake kanta a d'aure kallon 'kyama taiwa kan tana shirin 'ka'karin amai tace.
"Subahanallahi kai ku muje wayyo zan mutu da wari" ta karasa maganar tana fifita hancinta da hannu.
Ri'ke kunnenta Meenah tai cike da kishi da tsana tace "oh wai dama akan wannan ya Nurain ya rud'e ya mayar da hankalinsa qauye har saida ya aureta ya samu nutsuwa tabbb na rantse da Allah wannan kazamar yarinyar ko 'yar aikin gida bazan yarda a gidanmu a d'auke taba balle wai mata matar ma ta ya Nurain anya ya Nurain kansa d'aya kwakwalwar sa bata fara ta'buwa ba gaskiya ya kamata ya je hospital a duba shi domin wannan tsinanniyar ko 'yar goge takalminsa bata kai ba" ta karasa maganar tana hankad'a Nafisa baya ta fad'a saman gado.
Tsaki Meelat tana cewa "Humm kema dai kya fad'a Meenah gadaita nan a gashe ba mai'ko a dafe ba moro zataci ubanta ne damu take wasan badai kin aureshi ba? zaki bayani" Mimah kuzo mu tafi dan idan naci gaba da tsaiwa wannan tinkiyar ba'kauyiyar zatasa nayi aman fruit salad馃 dinan da muka ci yanzu" tana rufe baki ta dunguwa Nafisa goshi kafin suka fice daga bedroom d'in.
Tsumu-tsumu Nafisa tai tana zaro ido waje kamar zata fashe da kuka ta shiga uku馃檰 daga dirowarta garin tazo da farin ciki wadannan kuma su waye zasuzo su d'aga mata hankali daga ina suke waye ya turosu? Wannan tambayoyin sune fal ranta ta rasa yadda zatai gashi harsun hautsina mata ciki rasa inda zata sa kanta taji dad'i tayi saidai ta juya can ta kalli nan har Nurain ya shigo sai sannan ta d'an samu nutsuwa shikam baisan meke faruwa ba sai baje mata baki yake yana kallonta itakam saidai tayi masa murmushin ya'ke gashi sun gargad'eta akan kada ta kuskura ya sani duk wani farin ciki da take ji ya koma ciki haka dai kamar mara lafiya sukai abubuwa.
Washe gari sai wajen karfe d'aya Nurain ya fita shima a bisa dole Yazid ne ya kirashi yace masa yana so dan su had'u yanzu a ina zai sameshi ganin Nafisan barcin safe take yasa bai tasheta ba kawai yayi wanka ya shirya ya fice duk abinda yake su Mimah suna ankare dashi suna jin tashin mota da qarar bud'e gate da rufewa sunsan ya fita kuma Zainab ma tuni ta wuce hospital iya sune a gidan har karo suke da juna sukai part d'inta tana kwance tayi d'ai d'ai akan gado ta bararraje tana she'ka barci harda munshari saboda bata samu tayi da daren ba馃槈.
Fridge Meenah ta bud'e tana d'auko robar ruwa mai sanyi har ra'ba take ta juyeshi a cup ta d'aga ta watsa mata jiki tana cewa.
"Ke jaka tashi a kwanciyar nan dama barci kika zo dan uwarki harda bajewa kinai mutane gwarci kamar rago" ta karasa maganar tana kware mata sauran ruwan.
A firgice Nafisa ta farka jikinta na kakkarwa tsabar sanyin ruwar kamar mai zazza'bi sai makyarkyata take bakinta na rawa ta kasa magana tana kallon su cikin tsoro.
"Keee uwarki kike kallo a jikin mu"? Meelat ta fad'a tana fisgota daga kan gado ta fad'o kasa Mimah tasa kafa ta take ta tana cewa.
"Ke jiya me muka ce miki dama kinzo hutu ne tabd'i humm aiko yau saikin gwammace baki ta'ba sanin waye ya Nurain ba a rayuwarki".
Dam'ko ta Mimih tai tana mi'kar da ita tsaye tana kare mata kallo kafin tace "kai ku duba min na shiga uku me nake gani yarinyar nan kamar kuka tayi kodai ya Nurain yayi first night da ita馃槼 "?.
Mimih na rufe baki duk suka zuba mata ido suna qare mata kallo zaro ido Meenah tai tana cewa "kuturun ubancan lallai kam wallahi maganar ki nakan hanya Mimih wannan tsinanniyar ta shigo familyn gaskiya ya Nurain ya qasqantar da ahlinmu yanzu tsakani da Allah matsayin mata yad'au wannan kucakar yarinyar"? Mtswww.
Ta'be baki Meenah tai tana hararar Nafisa tace "hum kema dai kya fad'a Mimih wannan bala'in har ina na rasa me ya gani a jikinta abinso ita ba kyau ba itaba dirarran jiki ba kalleta fa kamar ta'barya ko'ina kai d'aya babu shape saikace gongonin peak milk haba wallahi ya Nurain yana da abun mamaki".
Qwafa Meelat tai tana cewa "kunga karmu tsaya surutai harya dawo bamuyi abinda ya kawo muba ta wuce muje ta fara bautar daya kawota gidan ta wanke mana toilet ta gyara mata bedroom da part d'in Aunty Zainab sannan tayi mana abun breakfast muna tsaye a kanta kuma bata isa ta shiga kitchen ba a garden zatai da gawayi zaki bayani wallahi sai munci uban daya kawoki duniya da kafafunki zaki gudu karkara kuma zaki gani muje dalla gafara akuya kawai" ta karasa maganar tana hankad'a ta da gudu Nafisa tai waje su kuma suka bi bayanta.
MALAM HABU.
________Kamar yadda Hajiya Aisha ta shawarci Alhaji Musa ya samu malam Habu ya fad'a masa bu'katar sa kasawa yai idan sun had'un ma baya iya fad'a masa harsu rabu sai daga baya abin yake damunsa musamman yanzu da suke zuwa kallon Asma'un ta kile sosai ta kara wayewa an zama 'yan birni tuni yaji hankalin sa ya tashi dan haka daya kasa tunkarar Malam Habun sai kawai ya tura abokinsa Alhaji Aminu yayi masa bayanin komai yadda zai fad'awa Malam Habu din sannan duk yadda sukai yana jiransa ya dawo ya sanar masa.
Alhaji Aminu baiyi kasa a gwiwa ba yaje har kofar gidan malam Habu da dare ya zayyane masa komai abinda yake faruwa ya kara masa da cewa Alhaji Musan yace ya