Advertisements
Chapter 22 Reading Me Kamar Sarki Book 2 Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Me Kamar Sarki Book 2 Hausa Novel

Author :  Yusrah Musa Category :  Complete Novels

Chapter   22 / 67

63K to 66K   out of 200.4K words

a inda ya fito hannu tasa tana shirin d'id'oshi daga bakinta tsawar data sauka yasa a firgice ta matse jikin ta guri daya a bisa tsautsayi ta d'od'awa yatsarta cizo harda jini.

"Dauki kibar nan ladan aikin mu saiya ci zaki dawo nan da wata biyu idan kuma baki dawo ba mu zamu nemo ki har inda kike kada ki saki kiyi kuskure idan kin tafi ba waiwaye kada ki fad'awa wani koda d'anki ne".

Mi'kewa Ramatu tai jiki na 'bari tabar gurin ba takalmi ba d'an kwali balle gyale duk ta zubar dasu haka ta ri'ka cin gudu har taje bayan gari tsayawa tai tana haki ganin babu kowa yasa tayi ta shiga wani gida dake farkon gari sunyi shanyar kaya ta zari hijab babu tambaya tai gaba abinta.

Da yake tunda Ilyah ya gama gidansa ta koma can da d'akin ta da komai nata yasa kai tsaye ta wuce gidan a gaban murhu taga Bara'atu zaune tana aikin abinci batare da tai mata sallama ba ta wuce d'aki a gajiye tsaki Bara'atu taja cikin takaici tace.

"Wannan mata sai nayi maganinki da ina zaune lafiya haka kawai ya wani kawo min ita wannan ai jaraba ce duk tazo ta addabi rayuwa ta wallahi bazai yuwu ba bari ya dawo koya sauya min gida ko kuma ya sakeni gara na hakura da aurensa"..........

Jitai Ramatu tace "ke me kike cewa dan uwarki"?.

Mamaki ne ya kama Bara'atu jin yadda babu mutunci Ramatu take kallon tsabar idonta tana zakin iyayen ta.......

Katse mata tunani Ramatu tai "dake fa nake yar matsiyata wato na lura saboda da dacan kin samu guri kin bararraje kina cutar d'ana kina d'ebe masa kud'i ki kaiwa matalautan iyayen ki yanzu kuma nazo na kafa na tsare akan dukiyar d'ana shine kike zagina ko dan an rufa miki asiri an aureki shekara uku baki haihu ba amma keda za'a kora har kike batun a raba gida dan gwafar ubanki bari Ilyan ya dawo sai naga wanda zai za'ba tsanani na dake shed'aniya".

Ta karasa maganar tana daukar kwano taje ta dauko d'umamen tuwo ta koma d'aki tagumi Bara'atu tai cike da bacin rai wannan wacce irin masifa ce dan iyayenka basu dashi sai aita goranta maka harda haihuwa cigaba tayi da aikinta Ramatu dake d'aki sai aiko mata da zagi take ta tafar sauke bata ce mata ba.

Sai aikin sharar hawaye kawai take shigowar Ilyah kenan ganin tana kuka yace "ke kuma fa lafiya"?.

Daga d'aki Ramatu tace "dani ne ka saki wannan matsiyaciyar matar taka saina yi maganin ta zatasan wace Ramatu" d'an tsaki Ilyah yaja yana cewa "na saketa kamarya meye kuma ya faru"?.

"Au meye ya faru ma kake tambaya"? Jin yayi shiru yasa ta fitowa ganin ya juya zai fice daga gidan ga kuma ba'kar leda ya aje a kusa da Bara'atun yasa da gudu taje ta dauke har zaninta na neman fad'uwa kasa tace.

"Kai Ilyah zonan so'ko'kon banza so'ko'kon wofi har dan nayi maka magana akan wannan figaggiyar matar taka zaka wani fice ka barni ina 'ba'batu kamar zakar da take 'kwai wannan abun cikin ledar uban me ka sayo mata".

Dakatawa yai batare daya juyo ba yace "kifi ne zatai mana abinci dashi" yana fad'in haka yai waje.

"Kifii馃馃悹" Ramatu ta fad'a harda zaro ido tana bud'e ledar ganin su tayi da yawa kai ta jinjina "ah lallai kam yanzu wannan uban kifi daya sayo da bana nan shikenan saidai kici naci sauran ki tattara ki kaiwa almajiran gyatumin ki ko? To Allah ya tuno asirin ki yau ina nan za'a gama girki sai an zuba min nawa ina kallo dan baza'a ri'ka cuta taba haka kawai nida haihuwa keda morewa".

Ita dai Bara'atu tana shiru batace mata komai ba cikin hararrami Ramatu tace "ke ba dake nake magana ba dan 'kwanjin ubanki nace ki dauko kwano na juye" mi'kewa Bara'atu tai takaici fal ranta taje ta dauko tana kawo mata kad'an ta zuba tana cewa "wannan ya isa abincin wannan kuma nawa ne nan da gobe ina ci a hankali zan cinye kayana dauki kije".

Saida ta bari ta d'auke ta koma gaban murhun tana gyarawa da cire 'kaya saboda soyayye ne farat Ramatu tace "ke Barah tashi anan yau nice zanyi girkin bake ba daga yau bi da bi za munayi" tsananin mamaki ne ya kama Bara'atu har batasan lokacin da tace "bi da bi kuma? Sai kace kishiya ta".

Mi'kewa Ramatu tai daga inda take zaune tare da cewa "au sai kace kishiyar ki? Dan malafar ubanki nice kikewa haka dan darar ubanki shigiya tsinanniya mai siffar angulu zaki ban guri ko saina karya miki kafa kika tsaya ina magana kina kallo na da baka'ken idanu kamar kwallon d'inya ko nayi mike kama da tamilalliyar uwartaki ne me zubin itacen rimi da siraran kafafu kamar na sauro ai indai bala'i ne yanzu kika fara sha a gidan nan dan darar ubanki" ganin zata bangaje ta yasa da sauri Bara'atu ta matsa gefe ta bata gurin.

Zama Ramatu tai tana kallon yadda mai yake yawo a saman abincin tace "humm yo abune ga d'an talaka ba'a saba ba ansha fura an mutu idan ba tsabar ke ba'kar gidahuma bace taya zaki kwarar irin wannan man a cikin abinci sai kinsa mun harbu da ciwon bayamma au wato so kike Ilyasu ya sha mai da yawa ya mutu dan ki samu gado tunda baki haihu ba ko? Tab tirrr da halinki in Allah ya yarda saikin riga Ilyah mutuwa gadon da kike kwad'ayi baza ki samu ba balle har kiyi tunani gyarawa fatararrun iyayen naki ru'babben gidan su".

Ko bari abincin ya dahu Ramatu batai ba ta d'iba tare da zubawa akan kifin data baiwa Bara'atu asa a girki kawai ta koma d'aki tana cewa "na d'ebi rabo na sai kije kiyita cin kasa inda babu mai ba maggi muguwar mace wai ni zata asirce dama ai naji ance har rubutu kandiya take kawo miki kina mana abinci dashi dan ki mallake mu to bari kiji wallahi munfi karfin ki nan gani nan bari d'umamen maiya".

Shiru Bara'atu tai tana kallon kofar d'akin Ramatu kafin ta d'an girgiza kai tana daukar tukunyar tayi taku daya biyu taji sallamar 'kanwarta d'an waigawa tai cikin danne d'aci da takaicin da ta kwasa tace.

"Lawisa kece shigo mana ya kika tsaya anan"?.

Bata karaso ba tace "eh babah ce ta aiko ni wai......................

Bata karasa fad'ar abinda take son fad'a ba Ramatu ta fito daga d'aki da gudu tana zuwa inda suke cikin kalan fitina tace "me naji kina cewa kamar a taimakawa da mayunwatan iyayen ki abinci? Amma ba abincin gidan nan ba? Haram giya a gidan liman bazai yiwu ba idan Ilyasu yaci gaba da zama dake zaki talauta shi yau saidai ki kwanan gidan ku maza dauko gyalen ki ku tafi tare da shegiyar 'kanwartaki sakin uwar miji ma sakine dan haka kije na sake ki馃槀 yanzun nan ki kwashi kayan ki kibar gidan nan kafin na shiga d'aki na fito" komawa d'aki Ramatu tai Lawisa dake ri'ke da baki tace "tabdijan yaya Barah kedin dama irin wannan zaman 'kuncin kike a gidan amma bakije gida kin fad'a an dau mataki ba gara da akai a gabana na gani muna zuwa gida zan zayyanewa baba baza ki dawo gidan Ilyah" tari dabai kama Bara'atu ba batai ba tana tsaye a guri daya ganin ta'ki dauko gyalen su tafi yasa Lawisa shiga ta dauko mata tana cewa "yau zaki barci cikin salama muje" kai Bara'atu ta girgiza cikin damuwa tace "Lawisa ki fahimta ba Ilyah ne ya sake ni ba bashine yace na bar masa gidan saba dan haka babu inda zanje domin shine yake aurena dan shi nake zaune".

Tun kafin Lawisa tai magana Ramatu tayo waje wuf tana cewa "au bazaki tafi ba naji kince ko? Yau kuwa zan nuna miki kalar nawa tsaurin idon" tana gama fadin haka tayi wajen turmi tare da dauko ta'barya tayo gurin su tana cewa "wallahi saina 'bare miki kai da ita" da gudu Bara'atu da Lawisa sukai waje yayin da Ramatu tabi bayansu har tsakar gidansu tana rafka kiran.

"Kandiya ke kande fito yau sainaci dambun uban 'ya'yanki".

Da sauri kandiya ta fito tana cewa "subahanallahi lafiya Ramatu na ganki da ta'barya ko takalmi babu balle mayafi".

Ramatu na haki take nuna Lawisa da yatse tace "yau saina ci uban daya haife ki zakisan wace Ramatu ke kuma nace na sake ki babu ke babu d'ana har abada idan kunne yaji jiki ya tsira matsiyaciya mara zuciya ana korarki kina mannewa saboda kinga kud'i ke kuma kandiya ya rage naki kiwa yarki fad'a ta rabu min da d'a idan ba haka ba sai munyi 'batacciya daku wallahi" tana fadin haka tai waje da ta'baryar ta a hannu kamar sabuwar kamu.

Mamaki ne ya kama kandiya tana kallon Bara'atu dake kuka tace "wai meya hada kune harda biyoki da ta'barya kuma"?.

Share hawaye Bara'atu tai tana cewa "babah kinsan halin matar nan ko ba'a fad'a miki dama da ya akai auren balle nayi shekara uku ban haihu ba akan haka tana goranta min da tsine min tace Ilyah ya karo aure wai ya auri Maimunan gidan san 'kira yar gidan malam Sa'idu to yau kuma sai ya shigo da kifi nasa a abinci ta kwace kifin ita kadai hakan bai isa ta zage ni ta hana na karasa dafa abincin ta goranta min sannan tace wai kina kaimin rubutu ina dafa musu abinci dashi ana haka Lawisa taje kawai dan taji muna zance shine tace wai kin aika a kar'bo miki abinci dan haka ta gaji sakin uwar miji ma saki ne naje ta sakeni".

Dafe kirji kandiya tai "kai jama'a mun shiga uku kinji wata masifar ko? Ni dama tun farko shiyasa ban goyi bayan auren nan naki da Ilyasu ba saboda nasan halin Ramatu koba dad'e koba jima sai wani tashin hankali ya shigo dacan ma maye balle yanzu kun dawo zama gida daya ni gara da haka ta faru ma ya sake ki yafi alkairi da wannan zaman damuwar da kike da mahaifiyarsa mu ri'ke talaucin mu bazaisa ki rasa wani mijin auren ba".

Tsaki Lawisa tai tana cewa "kinsan Allah innarmu da ace nice nake auren Ilyah wallahi Ramatu bata isa min haka ba koda taga Barah ba magana ce ta dameta ba da ace nice hummm da an d'ebi yan kallo".

Harararta kandiya tai "ke da Allah rufawa mutane baki sakarya kawai idan da ked'in cema me zaki iya yi wallahi a tsiwar ki yadda Ramatu bata da mutunci da yanzu ta dad'e da karya miki 'kafa tana daidai da zamaninki".

Ta'be baki Lawisa tai tana shigewa d'aki a ranta tana jin da fa ace itace bazata dauka d'in ba kamar yadda ta fada, kallon Bara'atu kandiya tai tana cewa "kinga Barah kiyi hakuri kinji shiga d'aki Allah yasa haka ne mafificin alkairi" Amin Bara'atu tace tana bin bayan Lawisa yayin da Kandiya tai zaman dirshan cikin jimami da damuwar tsiya da suka gayyatowa kansu na auren Bara'atun da Ilyah.

Har dare Ilyah bai dawo gida ba dan haka baisan me ake ba Ramatu kuwa tabarma ta dauko tana zama a waje ta kasa ta tsare tana jiran shigowar sa amma shiru har ta fara gyangyad'i sai dare sosai haka taji tafiyarsa da sauri ta bud'e ido ganin ya nufi kofar shiga d'aki tace.

"Ilyasu me zakai anan dama jiranka nake gidan uban wa ka tafi kayi dare haka baka dawo ba"?.

'Dan juyowa yai yana kallonta zuwa wani lokaci ya shige d'akin batare daya bata amsa ba dariya tai tana sake mi'ke 'kafa tace "zanji me zaka ce na karasa sauke ma damin bala'in dana dauko".

Wuf ta ganshi a kanta kamar wanda aka jefo shi cikin alamun tambaya yace "ina Bara'atu taje"?.

Wata uwar harara Ramatu ta zafga masa tana cewa "sannu ubana to matse ni saina fad'a maka inace duka na kazo yi dan irin wannan 'kerere da kayi a kaina duka kawai nake jira".

'Kara hade rai yai jin abinda tace shifa uwarsa ce amma harga Allah ta fara isar sa lamarin ta ya gama cika masa ciki...............

"Dan ubanka me kake kallo tunanin wa kake amma dai ba wannan tsinanniyar 'kai'kasashshiyar matar taka ba?.

"Wai dan Allah baba me kike yi haka ne"? Ilyah yai maganar ransa a mugun 'bace cikin fad'a Ramatu tace "dambun ubanka nake yi haka, wato dama akan shegiya matarka bankad'add'iya zaka gaya min magana? A lallai Ilyasu wuyanka ya isa yanka".

Takaici ne ya cika Ilyah shi ya rasa gane kan Ramatu kodai ta fara samu zarewa ne bai sani ba dan yaga abun nata yana neman wuce gona da iri amma bari ya bita a sannu tsuntsu me wayo ta wuya ake kamashi zama yai yana cewa "kiyi hakuri nifa dama ba akan wani abu na tambaye kiba mubar maganar d'azu bayan na fita alhaji Munniru yai Kira na akan zai sayar da wata gonar sa kozan saya saidai kafin mu gama ciniki kawai shegen nan Habubakar yaxo ya sayeta da filin kusa da gidan Buba haka mafa kwanan baya gidan me doki wanda ya rasu 'ya'yansa da suka d'aga zasu sayar shine ya saye ga gonar wajen gabar inda yake noman shinkafa kiga girman ta duk shekara saiya d'inke kusan buhu d'ari a bai samu da yawa ba ya samu buhu saba'in ko tanin komai aka d'aga a garin nan za'a sayar shi zai saya na rasa a ina yake samun kud'in sai kace me kud'in ganye ko matsafi kuma fa akwai haihuwa a gabansa amma tsabar had'ama alhaji Munniru ya kara masa kud'i shima da yake mitsiyaci ne ya sayar masa".

Zaro ido Ramatu tai tana cewa "kace da haihuwa a gabansa waye me ciki Saude ko Binta"?.

"Eh Binta ce harya tsufa kuma kwanan nan zai sake auren A'in gidan su me guga har ankai ro'kon arziki".

Dafe 'kirji Ramatu tai "au kuma shine tsabar hassada Salamatu bata zo ta gayyace niba aiko wallahi zan rama har ayi bikinka da Maimuna bazasu sani ba mitsiyatan mutane kawai duk sun asirceka ka'ki abun arziki amma na samo hanyar tarwatsa su kada ka damu Ilyah Bara'atu tayi gida nice na saketa domin bata haihuwa gara ka kara aure".

Kai ya d'aga cikin so kwantar mata da hankali yace "shikenan zan kara amma dan Allah ki bari na dawo da ita nifa ina son mata ta".

Shiru Ramatu tai tana kallon sa kamar me tunani zuwa wani lokaci tace "to shikenan ka dawo da ita amma ba yauba ba gobeba ba jibi ba sai an gama komai na maganar aurenka da Maimuna an tsayar da rana tukuna idan ma zan yarda ka dawo da itan kenan".

"A'a zaki yarda man na fad'a miki nifa ina son mata ta" hararar sa tai "sannu d'an masoya na gama magana matukar kana son sake bud'e ido kaga barakatu ko Bara'atu sunan nata? Indai kana son sake ganin ta matsayin matarka tofa saika kara aure".

Mi'kewa yai yana cewa "to shikenan zan 'kara saida safe" Ramatu data bishi da kallo tace "kowa ya kwana lafiya shi yaso馃榿" a'a kai jama'a wannan wacce irin uwace shidai tari da bai kama shiba bai sake yi ya shige d'aki.

Zunbur Ramatu ta mike tare da dauko maganin data kar'bo d'azu ta dauki bokiti da ruwa da sand'a tai waje tana yin hanyar daji ga ihun karnuka ya cika gari domin dare ya yi sosai yadda aka bata umarni haka ta aikata haka ta fara zuba magani cikin ruwan bokitin tayi wanka dashi kafin ta dauki gatarin da aka bata ta soma sara tana kiran Salamatu bayan ta tona tasa maganin ta rufe sannan ta dawo gida a bayan d'akinta nan ma tayi kamar yadda tai a dajin sai waige waige take kada Ilyah ya fito ta shiga uku tana gama tai wuf a guje ta fad'a d'aki tana gumi tare dayin dariya tace "haba malam sai yanzu naji daidai hankali na ya kwanta da wani ya kamani bansan me zai faru ba bari na kwanta mu jira wayewar gari muji me zai samu Salamatu"鈽癸笍馃槯 ta karasa maganar tana kwanciya akan katifarta da Ilyah ya sayo mata.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE 馃槝

Maman little Zaran aunty sai Allah ya kaimu gobe da nisan kwana馃槪 da rahmarsa garemu ina yiwa kowa da kowa fatan alkairi.

Yau typing d'in ba yawa sai hakuri.

馃毃 GARGA'DI DA TUNATARWA馃毃

Ban yarda a juyi ko kwafin wani bangare daga cikin wannan littafin nawa ba domin hakki na ne mallaka ta da gumi na basira ta na 'kir'kira na rubuta kada mutum ya min satar koda kalma daya ce idan kuma ba haka ba mutum zaiga sakamako kada ace na yanke hukunci ba sanarwa shiyasa na fad'a sai a kiyaye idan kunne 馃憘馃憘 yaji?.....................馃槧馃槨.

馃檲'YAR MUSA JIKAR ABUBAKAR MUHAMMAD TA KOWA CE馃憣.

Nayi kewar ku kwana biyu yan uwa fatan kuna lafiya ku fito mu warwasa zamu shiga duniyar nishad'i馃ぃ馃槀馃槄.

Bani da haushin kowa nifa i haven't girman kai if you are fushi dani to wallahi you are just 'batawa kan k lokaci 馃檭馃.

TYPING 馃摬 {WEND 13/24 8:10AM}馃拹馃拹馃拹馃拹馃拹馃拹馃拹馃拹馃拹

馃拵Me kamar sarki 馃拵

馃挮Annuri writer's association 馃挮 home of hospitality and harmony gidan karba hannu biyu da zaman lafiya.

Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty mai tambarin YMA dutse Jigawa new world new life and new style 馃憣. sabuwar duniya kuzo ku kallo dad'i yana Jigawa 馃槣 ga garin ilmi garin addini zaman lafiya Jigawa.

29~AL-ADAL

The utterly just

30~AL-LATIF

The Gentle

15~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Mustagfirina.

馃惁馃晩锔廦USRAHMS ABUBAKAR

馃yusrahmusa65@gmail.com.

馃寗 UNCARING ND TRAGEDY馃寗

Episode 29_30

Juyi Salamatu tayi cikin barci taji murya ana kiranta a firgice ta bud'e idonta ganin wani 'katon ba'kin abu tai a samanta yana yawo gashi bata ga alamar d'akin da take ciki a kwance ba "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda take maimaitawa 'kara matsowa abun yake taga yayi wani juyi wurrr ya rufo kanta da sauri ta tashi a guje ya sauka akan gadon sai kuma ya 'bace

22 / 67