Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
zuwa sabon gidanmu,idan na hada hankalina waje daya saimu tsara yadda zamu gyara komai,muga kuma yadda Allah zaiyi".
A ranar saita samu walwala sosai,daga ganin anty ummeen sai taji kamar matsalarta tazo qarshe,ta dan jima a gidan,wanda bata fita a gidan ba sai data yagi wani abu daga jikin hafsat,bata hanata ba,don itama yanzu taimakonta take nema,daga qarshe ma sai data bawa dan riqon gidanta dan yayan abbas din key din motar ta ya maida anty ummeen gida.
Sau biyu tana fitowa tana shige kitchen amma tana ganinsa a zaune inda ta barshi,kusan awa guda kenan yana zaune a wajen,yaran suna kwance daga gefansa sunyi barci.
Tunda ya dawo ya watsa ruwa ya zauna zaman cin abinci,ta dire masa abincin ta qara gaba,don tun ranar da widad ta haihu haka take masa,zafinsa takeji,saidai ko.sau daya bai taba nuna mata ma ya gane wai fushi take ba,don shidai kaf a abinda ya faru baiga abin yiwa fushi a ciki ba,shi yasa ya tattara ya bawa banza ajiyarta.
Cikin zafi yake amsa wayar tsahon awa gudan kenan da gurbataccen turanci (brooking),da alama yana magana da wasu cikin yaransa ne akan abinda ya shafi aikinsu.
Fitowarta ta qarshe daga kitchen din ya sauke wayar a kunnensa bayan yaja tsaki,sau da yawa ire iren abubuwan dake janyo musu bacin suna kenan daga wajen al'umma suke musu kallon abu daya,yanzun ya zama dole ya tafi kaduna a gobe
"Zoki dauke yaran nan ki kaisu daki" kakkausar muryarsa da amonta babu wasa kwata kwata a ciki ta ratsa kunnenta,saita ratso ta tsakiyar kujerun ta fara daukesu daya bayan daya,shi kuma ya buda warmer din abincin yana qare ma abincin kallo.
Bacin ransa ya sake daduwa sosai,ya maida murfin ya rufe,ya koma.ya jingina da kujera yana sauke ajiyar zuciya,ya dade da sanin irin muhimmancin widad cikin rayuwarsa,amma nisan da tayi dashi a yanzu ya sake haska masa girman da muhimmancin da take dashi ga rayuwarsa.
"Idan kinkaita ki dawo" saita tura baki gaba tana cure fuska kamar wadda aka yabawa kashi,tana tsammanin yana buqatar wani abune daga gareta,indai.kuwa hakane yau a jikinsa zata fanshe abubuwa da yawa da ta qudirta,don haka koda takai nawwara sai da taja lokaci sannan ta dawo cikin falon,zuwa sannan ma har ya shiga kitchen ya hada coffe da kansa,don ya gwammace ya shashi ya kwanta akan yaci wannan qaddararren abincin nata.
Gefe ta zauna tana hada rai, baice komai da ita ba sai daya gama sha ya dire cup din,ya jawo system dinsa dake cike da rubutu yayi saving ya kasheta,sannan ya bude briefcase din gefansa ya ciro kudade ya ajjiye mata.
"Nasan hajiya ta gaya miki gobe zaku wuce kano suna,gashi nan,kudin transport ne dana amfanin gida,nasan zasu isheki harda ragowa ma" ya qarashe maganar ba tare daya dubi fuskarta ba,sai jakarsa da yake rufewa
"Ni ba inda zani fa,saboda haka sai sun dawo" wani kallo ya watsa mata bayan ya miqe yana kallon cikin idanunta
"Ba shawararki nake nema ba,umarni ne na baki, bijirewa magana ta kuma bazatayi miki dadi ba,banason doguwar magana,gobe zaku kano period" ya juya a nutse yana tafiyar nan tasa majestically kamar bashi da sauran damuwa,duk kuwa da cewa qasan ransa bacin rai ne fal,ga na shirmen da aka masa a office ga matsalar hafsa din da har yau babu alamun gyaruwa ko nutsuwa a tattare da ita sam sam.
Dakinsa ya wuce ya ajjiye jakar sannan ya fara hadawa kansa ruwan wanka a mugun gajiye,abinda baisan dashi ba muddin kwanan widad ne,koda ya gama gado kawai ya haye,sannan yaja wayarsa ya kira widad din don ya tabbatar zai samu relief.
Ya samu har fiye da yadda yakeso ma,ta sauke masa dukkan wani bacin rai dake ransa,daga qarshe ma video call sukayi ita dashi,ta nuna masa duk wata kwalliyar suna
"Wannan ai tsomo ni kawai zakiyi,nayi missing......nayi missing sosai,ina da aiki amma banda haka ya kamata nazo naga kwalliyar sosai"
"Za'a yi maka wadda tafi wannan,kada ka damu,ka maida hankali ga aikinka,wanda na tabbatar muhimmncin da kake bashi shine mabudin dukkan wannan nasarorin da kake samu"
"Sirrin kuma nasarorin kece ba......nutsuwar da kike bani widad.......I don't know how to explain it to you,you become part of me".
Irin wadan nan hirarrakin dake qara dasa kowanne cikin zuciyar dan uwansa su sukaci gaba da gudana,daga qarshe yace a karbo masa muhammad zai ganshi,dole ta ajjiye wayar duk da yadda takejin kunya don yana hannun 'yan suna,ta samu nujood ta lallabata ta karboshi.
Ya jima yana kallon yaron ta cikin video call din sannan ya sauke ajiyar zuciya
"Bazan iya hana wannan taron sunan ba,amma don Allah..... please na roqeki,ki kulamin da kanki,ki kuma kularmin da yaro na,kada ayita wannan shige da ficen da shi" dariya ma ya bata yadda ya marairaice,kuma yake maganar da gasken gaske
"Oh...... dariya ma na baki?, seriously madam......am in pain na yadda za'a kallemin ke a gobe,don Allah ki kula"
"Nifa taka ce,mallakinka ce ta har abada,infact ma saboda kai Allah ya halicci widad,no need ka damu,kayi aikinka hankalinka kwance don Allah" maganganu tayi masa masu kwantar da hankali,dole daga bisani sukayi sallama saboda yadda aketa kiranta daga falo.
Suna gamawa ya ajjiye wayar yayi addu'ar kwanciya barci,yaja duvet abinsa ko takan hafsat baibi ba.
Sanda ta gama baqin ran nata tana zaton zai biyota taga bai biyota ba saita shirya ta taho,koda ta iso tuni ya jima da yin baccinsa,abinda ya qara mata baqinciki da takaici,ta kasa kwanan dakin ta rufe masa qofa ta koma nata dakin.
********Tun asuba ya shirya ya fice abinsa,bai sake tada mata zancan zuwa kano ba alamun zabi kenan ya rage nata.
Duk abinta tasan iya lokuttan da take iskancinta,ta sani sarai idan ya kafe bashi da dadi sam,dole ta fara shirin tafiya,bayan ta kira muneera taji qarfe nawa ne tafiyar.
A ranar sai data fidda kayan sawarta daga cupboard dinta gaba daya amma ta rasa wanda ya dace ta saka,kowanne akwai nashi illar,sutura iya sutura masu tsada,don abbas baya siyan abun banza,saidai idan ita ya bawa kudin ta siya na banza ta soke sauran kudin,wannan kuwa ko ta kanta baya bi.
Wata rigar tasha squeezing,wata bata ga dan kwalinta ba,wata na buga tsami,saboda an saka an maidata cikin kayan ba tare da an wanke ko an barta tasha iska kafin a maidata din ba.
Bata taba jin haushin irin abun ba sai yau,so takeyi tayi shiga ta kece raini,amma maimakon taji haushin kanta sai haushin ya tattara akan widad da abbas,kamar dole sai taje sunan?,amma kuma data tuna maganar anty ummee da tace gwara taje ta ganewa idanunta barnar kudin da yayi musu sai taji babu case,taci gaba da bincikawa,da qyar ta dace ta tsamo wata ABC england dark blue,itama a yamutse take,saidai atamfa ce mai laushi cotton sosai,don haka ta fesa mata ruwa ta zauna akai ta samu tadan miqe.
Duka mayafanta masu tsada da abbas ke siya sanyasu takeyi cikin kayan siyarwarta ta saida,a nan ma da qyar ta samu wani baqi ta dora,sanann ta laluba jaka da takalmi duka ta yamutsa abinta.
Idan kika ganta zakiyi tsammanin amaryar 'yar talla ce daga wani qauyen ranar fitowa daga gidan miji na farko,ga jambaki ja ya kama ya haska baqar fatarta data rasa gyara bare tayi kyan da masu duhun fata keyi idan ta samu kula ba tare da canza launin fata,to amma da yake ba saban bace ta fannin ado da kwalliya,sai take ganin ta gama qure adaka,qarfe goma na safe motar da abbas ya sanya ta kaisu kanon ta iso ta dauketa suka wuce.
Daga ita sai gwaggwo mero qanwar hajiyarsu,sannan muneera yaaya bara'atu,sai gwaggwo fanteka da gwaggwo hassana matan uncles dinsa,da kuma qanwar abbas wadda take binsa nasma.
Tunda suka dau hanya babu wanda ta kula a cikinsu,saboda kowa fuskarsa babu alamun damuwa ko bacin rai sai ita kadai,har gwara gwaggwo hassana da yake suna da alaqa da ita,takan tabe baki lokaci lokaci ko tayi magana qasa qasa akan tafiyar.
A can kano kuwa ko cikin family ranar kowa yasan sha lelen ummu ta haihu,gata tako ina a ranar ya nuna kansa,ba daga wajen mommy mahaifiyarta ba,ba kuma daga wajen ummunta ba,ba daga wajen tsoho mai ran qarfe alh salim ba ko mahaifinta Alhj mahmud da Allah ya dorama son jikan nasa,kamar a kansa aka fara masa haihuwar jika ba,ga kuma mai dungurungum din wato DSP abbas turaki.
Wani kalar suna ake gudanarwa,irin sunan da tsiya da babu suke gudu da qafafunsu, komai a wadace,hatta da almajirai da mawadata ranar sun shaida sunan,tun da sassafe widad ke sanya sutura tana canzawa harta fara gajiya,qarfe sha biyu saiga motarsu hafsat tayi landing cikin tsakiyar harabar gidansu widadπππ
_to mai karatu,ya zata kaya ne?,anya kuwa hafsat ayau zata iya cinye kishinta?,kuzo dai mu rakasu ciki mu gani_πππΆπΎββοΈπΆπΎββοΈπΆπΎββοΈπΆπΎββοΈπΆπΎββοΈπΆπΎββοΈ
*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 18
Tun daga harabar gidan ta fara fahimtar daga wanne irin gida widad din ta fito,daga yadda taga abubuwa suna gudana tun daga farfajiyar gidan da aka cika da rumfuna jikinta ya fara sanyi,wani irin kishi da bacin rai yayi mata tsaye a wuya,a haka dai ta daure,ta fita a motar,suna biye da hajjaa data zame musu jagora cikin gidan.
Tarba ta girma akayi musu bisa jagoranci anty deena,ta shirya komai yadda zai qawatar da baqin cikin girma da karamci,komai kasa cewa tayi,sai idanunta dake biye da komai na gidan,tun daga falo zuwa wani falon da aka tanada don su kadai,ko da mutum guda bata gaisa ba,sai ido da takebin mutane dashi,sannan ta watsar kamar babu ita a wajen.
Komai dake gudana gwaggwo mero na ankare dashi,har zuwa sanda suka kadaita a falon,aka kuma turo musu widad dake shirye cikin wani dandasheshen lace da mummyn ta ta dinka mata,wanda kudinsa yakai dubu sittin.
Lace dim shine abu na farko daya fara tsone ma hafsat din idanu,tasan kudinsa sarai tunda sana'arta kenan,wani tashin hankali ya rufto mata,har ta gaza dauke idanunta daga kan lace din,tana jin kamar ta tashi ta yageshi daga jikin widad.
Duk yadda taso ta tausa zuciyarta ta amsa gaisuwar da widad din ke mata,ranta fes fuskarta cike da walwala amma ta kasa,daga qarshe ma sai tayi bandaki kamar wadda wata buqata ta kama.
Kasa riqe kukanta tayi,sai data matsi hawaye sosai sannan ta fito bayan ta waske da dauro alwala,ta riga kowa tayar da sallah tun farkon muhtarin sallar azahar.
Tana kan abun sallah ba tare data waiwayo ba,tana jinsu suna yaba yaron da aka shiryashi cikin wasu irin kaya masu asalin kyau da tsada na qasar saudiyya,kowa ya daukeshi sai ya fadi kyau da kuma tsantsar kamannin dake tsakaninsa da babansa,abinda ya sake dagula mata lissafi kenan.
'yan awannin da sukayi ta shiga quncin da sai data gwammace bijirewa zuwan tayi koma meye suyi da abbas din,idanunta sunga abubuwa kala kala,wadanda da wannan bacin rai tayi guzurinsu zuwa gida.
Taro ya watse lafiya cike da tarin alkhairi da yaron ya zoma iyayensa biyu dashi,widad kuma ta shiga ci gaba da samun kulawa irin ta tsaffin da sukaga jiya sukaga yau,gefe guda ga gudunmawar yayyen zamani irinsu anty deena anty madeena,da matan abokai na qwarai irinsu fanna da sha'awa.
*_DUKKAN ME RAI MAMACI NE_*
Cikin sati biyu kacal muhammad da suke kira da affan ya fara wayo da wani irin girma dake alamta qiba zaiyi,daga shi har mamansa widad fatarsu ta qara gogewa,sunyi wani irin kyau na samun nutsuwa da kulawa,jegonta take hankali kwance,kulawa da soyayya tako ina,kusan ko yaushe suna manne a waya ita da abbas din,sukan shafe lokuta sosai suna hira,irin hirar dake debe kewa da sawa zuciya nutsuwa.
Kwana biyu kacal yin wayarsu yadan ja baya,data tambayeshi yace hajiya ce bata jin dadi a kwanakin,a ranar sau biyu tana kiran hajiyan taji jikinta,cikin dauriya da murmushi take amsa mata
"Da sauqi fa,kawai abbas ya tashi hankalinsa ne" kiran data mata a washegari da safe wanda shine kiran na kusan biyar hajiyan ta daga suka gaisa,ta tambayi dan jikallen nata wanda yake kamar shi daya ne jika a wajenta saboda yadda takejinsa a ranta
"Allah yayi miki albarka widad,ya dafawa al'amuranki,kiyi haquri,kiyi juriya,Allah ya baki ikon kula da mijinki da dukka abinda ma zaki haifa a gaba" bata kawo komai a ranta ba,saima nauyin addu'ar hajiyan ta qarshe,duk da haka saita samu kanta da cewa
"Ameeen" suka dan sake gaisawa sannan sukayi sallama da hajiyan.
A ranar duka basuyi waya da abbas ba,tadan shiga damuwa amma daga baya ta bayar wataqila yanayin aiki ne,wanda wasu lokutan dama idan ya sakasu a gaba basu da wani sauran sukuni har sai sun gama sannan suke samun sauqi.
Washegari affan yana saman cinyarta tana shayar dashi cikin dakinta,ita dashi dukkansu sunyi wankansu fes,sai qamshi suke fitarwa,so take ta gama bashi ya qoshi ta kaiwa latifa shi ta goyashi,kamar daga sama sai taji muryar uncle muhsin daga falo,cikin zumudi ta zare maman daga bakin affan ta sanyashi a kafada tana shafa bayansa,don yana shirin fara rigima ne,don da alama bai gama qoshi ba,tayo falon dashi.
A tsaye ta sameshi shi da tsoho me ran qarfe da kuma ummu,yadda dukkansu suka bita da idanu haka kawai sai taji ta tsargu,saboda basu taba yi mata irin wannan kallon ba,duk sai taji qafafuwanta sunyi laushi,ta daure ta qarasa falon tana masa sannu da zuwa,ya miqa hannu yana cewa
"Bani takwara na,shiga kitchen ki yiwa latifa magana ta tayaki hada kayanki zamu wuce bauchi" sosai maganar ta daketa,ta dubeshi da kyau
"Bauchi kuma uncle?,ina cewa yanzu ka shigo?" Kai ya gyada mata
"Eh,rakani zakiyi,flight zamu bi,kuma yanzun haka da nasa a siya mana ticket saura awa daya duka duka lokacin tashinmu yayi" kasa ci gaba da tambayarsa tayi,kawai saita juya tayi abinda yace din,saidai ko latifa dake hada mata kayan batace komai ba,bata tambayi ba'asin irin wannan tafiyar ta gaggawa ba,sai ta sake jin cewa lallai akwai wani abu dake faruwa.
Samun kanta tayi da gwada wayar abbas don ta tambayeshi yasan wani abu akan tafiyarta?,ta kuma shaida masa tahowarsu amma amsa daya computer ke bashi wayar a kashe take,dukka.layukansa,da personal da na aikin gaba daya,saita jefa wayar jakarta kawai ta dauki mayafin abayarta ta roller ta fito.
Sallama ta dinga yi da mutanen gidan,duk da tana gaya musu zata dawo sai tayi arba'in zata koma,ba wanda yace mata komai daga uncle muhsin har ummu,a haka suka fice a gidan ta cikin motar daya daga cikin samarin gidan da zai saukesu a airport.
Tun saukarsu a garin bauchi taji gabanta yana wani irin faduwa mai tsanani,nutsuwarta tana neman barin gangar jikinta,ta dauka irin yanayin da take tsintar kanta ne duk sanda sukazo bauchin,amma saita karancin yanayin ya sha bambam da wannan da take tsintar kan nata a ciki,tayita kokawa da zuciyarta har zuwa sanda taga sun doshi hanyar gidan hajiya.
Waiwayowa tayi tana duban uncle muhsin
"Na dauka gidanka zamu sauka?"
"Aah" ya fada a taqaice,daga haka shi da ita ba wanda ya sake magana,har zuwa sanda suka gangara gefan titi suka shiga faffadan layin dake malale da kwalta.
Mummunar faduwa gabanta yayi lokacin da taga jama'ar dake zaune a qofar gidan,qarqashin rumfar tempol,qofar gidan cike yake jama'a,haka ta dinga ratsa mutanen qafafunta kamar ba'a jikinta ba, zuciyarta na wani irin bugu,ta kuma kasa tambayar uncle muhsin komai,burinta kawai ta isa cikin gidan ta gano abinda yake faruwa.
Bata tsaya ba har sai data isa falon hajiya da shima yake tanqam da jama'a,sai surutai kadan kadan da kuma koke koke,kamar wata mutum mutumi ta tsaya tana qarewa kowa dake falon kallo,bakinta ya gaza cewa komai
"Kamata ki zaunar da ita" taji muryar Gwaggo mero tana fada,sai a sannan ta samu qwarin gwiwar kallon hajja dake sama mata wajen zama bayan ta karba affan ta miqawa yaaya bara'atu
"Waye ya rasu hajjaa"
"Kiyi haquri ki zauna,hajiya ce Allah yayi mata rasuwa" kamar an qwala mata qarfe haka taji,kunnuwanta suka