Advertisements
Chapter 32 Reading A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   32 / 33

93K to 96K   out of 97K words

akwai kasala sosai a jikinta,taja kujera ta zauna gaban mirror tana kallon lallausar farar fatarta daketa sheqi.

A nutse aka turo qofar bedroom din,ta cikin mudubi suka hada idanu dashi,kamar an manne idanun nasu guri daya,sai kuma kowa ya janye idonsa daga na dan uwansa yana basarwa.

Saman sofa bed ya zube kayan hannunsa,ta jawo mai ta fara shafawa

"Sannu da zuwa" ta fada ciki ciki ba tare data kalleshi ba.

Dubanta yayi kadan hannuwansa cikin aljihun wandonsa,kamar zai magana sai ya fasa ya amsa mata da yawwa,ya juya kadan ya fara cire kayan jikinshi.

Mamaki ya kamata ganin yadda yau ya yada zango a dakinta,neman rigima ne ko kuwa?,daya gama din yaja towel ya daura saman gajeran wandon jikinsa daya tsaya masa iya cinya.

A bayanta ya tsaya,ya saka hannunsa ta gefen fuskarta ya shafi wuyanta zuwa fuskarta da zummar jin ko da zazzabin a jikinta?

"Alhamdulillah" ya furta qasa qasa harda sakin ajiyar zuciya,sai ya taka ya wuce bandakin,ta bishi da satar kallo,har sai da ya shige sannan ta dauke idanunta,ta saki ajiyar zuciya saita maida man shafawan nata saman madubin kawai ta sanya hannuwanta dukka biyun tayi tagumi.

Komai ya tsaye nata a rai,da alama wannan karon abbas din ya fita fushi,hankalinta sam ba'a kwance yake ba,sai yanzu ta sake ganowa azabtar da miji ko sanyashi cikin baqinciki ko yaushe na iya jefa mace cikin jarrabawa,sai taji qwalla ta cika mata idanu,taji kuma ta damu sosai da fadan nasu,wanda bata taba damuwa kamar yanzu ba,don a baya tana ganin kawai wahala zata sha cikin dake jikinta.

Sanda ya fito a haka ya sameta,sai ya dauke kansa kamar bai gani ba,duk da qasan Zuciyarsa shima cike take da damuwar fadansu,to amma kuma ya koyi darasi daga zamansa da hafsat,ba ko yaushe kake barin mace da zabin kanta ba,hakanan bako yaushe kake barin mace tayi abinda takeso ko kuma abinda yayi mata suger ba.

Yadda ya kauda kai kamar bai kula da taguminta da qwallar dake cikin qwayar idanunta ba sai ya sake sanyaya mata jiki,ta gaza daurewa,sai kawai ta miqe tsaye da sassarfa ta nufeshi,ta fada jikinsa sanda yake ware towel din jikinsa ta ruqunqumeshi.

Cak wutarsa ta dauke,saboda tayi masa ba zata,uwa uba kuma yadda fatarta me santsi da laushi ta manne a jikinsa,sai ya gaza ci gaba da riqon towel din ya sakeshi ya fadi a qasa, yasa hannu ya tarbeta cikin jikinsa da kyau amma kuma cikin dakakkiyar murya da kuma basarwa yace

"Meye hakan?" Muryarsa na danson yin rawa yana qoqarin daidaitata

"Kayi haquri don Allah uncle,wallahi bazan sake ba"

"Laifin me kikayi?,ba haka kikeso ba?,so nake dama na gama shiryawa yanzu ina yin sallar isha'i muje a zubar din,kinga nan da next year na auro wata meson haihuwar harta haifamin babies" ji tayi maganar tasa ta soketa sosai,sai kawai ta kasa riqe kanta ta sakar masa kuka sosai tana kwantar da saman qirjinsa hadi da rungumeshi da kyau cikin jikinta tana cewa

"Na tuba Allah bazan qara ba" sautin muryarta kawai yana sanya masa nutsuwa,wani bangaren kuma yana sakashi yaji ya buqatu da yawa da ita,sai ya dinga lumshe idanunsa yana jin yadda yanayinsa ke canzawa,saboda sautin kukantan sai ya zame masa kamar fami cikin kunnuwansa da kanta dake kwance a allon kafadarsa.

"Ka yafemin don Allah" ta fadi tana qoqarin zamewa ta duqa,yayi hanzarin tattarota zuwa jikinsa,don ko daya bayason ta matsa daga jikin nasa,dumin jikinta ya masifar yiwa jikinsa dadi

"Na yafe miki,na yafe miki har abada,but don Allah.....karki sake zancen zakiyi abortion,kalma ce me muni,don zaman aure mukeyi ba dadiro ba,inason kowanne qwayar halitta data fita daga jikina ta bayar da d'a,ko ana ciki sau goma nine ubansa,kuma inaso" ya fadi yana kallon tsakiyar qwayar idanunta ciken mayen so da qauna.


*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 46


*_TURK'ASHI!,BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE,KU MARMATSO KUJI,GIDAN KOMAI DA RUWANKA_*

*LIFE STYLE NIGERIA for everything that makes your life style complete*

*GIDAN KOMAI DA KOMAI RUWANKA*

_kama daga kan_


Furnitures
Decoration
Kitchen items &
Boutiques

_our tittle_

Quality is our watch word at lifestyle

shop kano/kaduna

Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot


Instagram@ Lifestyle_Nig
Facebook@ Lifestyleng
Tik tok@ Lifestyle_Nig
Delivery nation wide

_ku tuntubemu ta wannan number_

08036414048

*Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah*
_______________________________

"Na daina uncle" ta fada tana cusa kanta tsakanin qirjinsa tana shaqo qamshinsa mai kwantar mata da hankali,wani ciki ta samu a wannan karon meson qamshin jikinsa,sai ya saki murmushi yana shafa sumarta

"Nima kiyi haquri,nasan kinyi missing jikina ko?" Ba kunya ta gyada kai tana sake cusa fuskarta cikin gargasar dake qirjinsa,tsigar jikinsa ta dinga zubawa,shima haqurinsa yakai qarshe,dama shima din kawai basarwa yakeyi tsahon lokacin,sai ya zura hannunsa ta baya ya kwance towel din jikinta ya sulale ya fadi qasa ta koma kamar yadda yake,ya maidata jikinsa sosai suka zama abu daya,kowannensu ya dauke numfashi na wucin gadi sannan suka zuqoshi da qyar,cikin rawar jiki ya dauketa cak ya wuce da ita saman tsaftataccen gadonta da baya gajiya da kwanciya a kai.

Ranar dai sai a dakin sukayi sallar isha'i shi da ita,sunyi kewar juna ba kadan ba shi da ita,sun kuma gane yadda suka azabtar da junansu.

Suna gaban madubi yana sharce mata gyara mata gashin kanta kafin ta saka kaya ta kalleshi ta cikin mudubin

"Uncle"

"Babyn uncle" ya amsa mata softly

"Don Allah zaka iya yimin wata alfarma guda daya zuwa biyu?"

"Kinki qarfin komai a wajena" ta dauki hair mist dinta ta miqa masa ya soma fesa mata sanann tace

"Ka yafewa mummyn mimi don Allah,ta roqeni na roqar mata wannan alfarmar"

"Na yafe mata,Allah ya yafemu gaba daya" ya fada kansa tsaye,donshi wani lokacin ma mantawa yakeyi ya taba aurenta,sai idan dalili ya ratso.

"Na fadi ta biyun?"

"Eheen,ina jinki" ya fadi yana buda mata doguwar rigar da zata sanya

"Kasan tsakanin uwa da d'a sai Allah,ta roqeni na gaya maka don Allah ka dinga barinta tana ganin yaran nan....." Kallonta yayi da sauri sannan yace

"Wait......wai zuwarmin gida ma takeyi ba tare da na sani ba?"

"Relax uncle manaaaaa" ta fadi tana juyowa da sauri cikin wata narkakkiyar shagwaba hadi da zube masa fararen manyan idanunta,sai ya dan lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya

"Uhmmmm.....u have all my ears"

"Bata taba zuwa ba sai yau,kaima ka sani,tunda duka duka yaushe muka dawo qasar uhummm?"

"Naji,ni banaso tana shigomin gida,kada ta cutarmin dake wataran,i will send her the kids duk sanda naga ya dace,ama bance zasu kwana ko daya ba,kada ta qara zuwanmin gida please" ido ta lumshe gami da gyada kai,ita komai ma mamaki yake bata,ta yaya zata samu miji irin abbas indai ba mummunar qaddara ba tayi saken da zai kufce mata?,the best husband ever.

Sajjad da sajid ne suka fiddasu don dole,suka zauna dukkansu suda yaran a table mat suna cin abincin cikin wani irin yanayi da zai nun maka kyakkyawar rayuwa da mu'amala ta gari da kuma cikakkiyar tarbiyya da suke samu,kai kanka idan kana wajen sai familyn yayi mugu mugun burgeka.


***********Katafaren gidan da ya zama na daban cikin layin shaqe yake da jama'a,gida ne da ya zama mallakin IG(inspector general of police) ABBAS TURAKI,tako ina kana hangen yadda tun daga layin har zuwa bakin titin dazai shigo dakai ainihin kayin ke shaqe da al'umma da kuma ababen hawa na alfarma,ko ina shaqe yake da jama'a,yadda manyan riguna da kuma fararen kaya keta nuna kansu,na wannan yana wane wancan,da kuma yadda busar algaita ke tashi kadai zai gaya maka cewa wani katafaren daurin aure akeyi.

Ta cikin microphone din dake fitowa daga masallacin,kana iya jiyo muryar wani qaqqarfan mutum na cewa

"An bawa muhammad yasir matawalle auren Dr raheema(mimi) IG abbas turaki akan sadaki naira dubu dari lakadan ba ajalan ba......eh diya ga shugaban duk wani dan sanda dake nigeria" ya sake bayani cikin kambamawa irin na maroqa.

Dai dai lokacin da IG abbas ke zaune daga can wani sashe na masallacin cikin shigar alfarma ta farar shadda da babbar riga me asalin tsadar,fuskarsa cike da wani irin haiba kwarjini da kuma cikar kamala,sanarwar data haifar da wanzuwar murmushi saman nutsatsiyar fuskarsa,ya sauke boyayyr ajiyar zuciya yana godewa Allah da ya fara nuna masa auren diyar cikinsa ta farko.


*C I K I N G I D A*

Wani kebantaccen falo ne dake da matuqar kimar da ba kowa take bawa damar saka qafarsa a ciki ba,falo ne na musamman da aka tanadeshi saboda hutawar IG,yake kuma samun kulawa qarqashin uwar gida sarautar mata wato hajiya widad,kamar yadda komai na IG din yake qarqashin jagoranci da kulawarta,duk kuwa da ma'aikatan dake gidan.

Duk girman falon su biyu ne a ciki,ita da amarya mimi dake lullube cikin wata lafiyyayar alkyabba,hannunta dake dauke da Wani irin lalle yana sanye cikin tafin hannun hajiya widad da yasha lafiyayyen jan lalle da bata rabo dashi,wadda tana zaune ne a gabanta suna fuskantar juna,tana karanto mata wasu addu'o'i tana maimaitawa.

Ta dauketa ne daga cikin taron hayaniyar jama'ar saboda yadda tunda satin bikin ya kama take fama da koke koke,ita batason tafiya tabar maami,ita ba zata je ba,hankalinta na sake tashi idan ta tuna a yau zatabar qasarta ta haihuwa,zata tafi wata uwa duniyar zaman aure ita da mijin da Allah ya bata wato muhammad yasir.

Sai data gama karanta addu'o'in kaf yadda maamin tata ta karanta mata,sai suka hada ido,widad tayi qoqarin danne raunin zuciyarta don kada ta karya ma mimi qwarin gwiwar data samu

"Basai nace miki komai ba mimi,bani da haufi a kanki,kowanne d'a namiji zaki iya zaman aure dashi,ki kuma mallaki zuciya da hankalinsa babu boka ba malam" kai mimi ta jinjina,ita shaidace yadda maamin nasu ke tafiyar da mahaifinsu,koke 'ya mace akewa haka sai an samu kanki fiye da zato,wata irin macace da batasan ya zata fasaltata ba,a taqaice ta zame mata wata role model dinta,tana kuma alfahari da ita,hakanan tana kiranta da uwa a duk inda ta shiga a duniya,maamin ta zamewa rayuwarsa alkhairi,dukkan mutumin da ya shigo rayuwarsu daga baya yana mata kallon mahaifiyarsu ce data tsugunna ta haifesu,ta basu abinda dukka uwa ke bawa yaranta,harma abinda wasu uwayen suka kasa bawa yaran nasu,koda wasa bakinta bai taba kiran widad a matsayin uwar riqo ba bare wani suna na kishiyar uwa,kullum kallon mahaifiya suke mata,duk da sunsan asalin wadda ta haifesun,amma ko ita kullum gaya musu takeyi widad dince babarsu,itakam kawao naqudarsu tayi ta kawosu duniya,amma idan suna neman uwa itace.

Zamewa tayi ta tsugunna gabanta

"Maami ki yafemin don Allah tsahon zamanmu idan na taba bata miki...." Da sauri ta kama kafadunta ta dagota ta zaunar da ita sosai

"Bakiyimin komai ba mimi iya zamana daku,kun riqeni kamar mahaifiyarku,saidai nan gaba zakiyimin laifin" da sauri ta daga kai ta dubeta,saita sakar mata murmushi tana jinjina kai

"Eh,muddin baki zauna lafiya gidan mijinki ba,muddin bakiyi haquri dashi ba,muddin ya kawo qararki gida ya zamana kece da laifi"

"Bazan miki laifi ba kuwa har abada maami,saidai in har ajizanci irin na dan adam" ta fada kuka na qwace mata,idan batayi zaman aure bama ai bata yiwa maaminta adalci ba,ta basu dukkan misalai na rayuwa da zamantakewa a baki da kuma a aikace,su shaida ne sun gani.

Juriya da jarumtar nan tata ce kawai ta hanata kuka,tayi qoqari ta saukar da mimi daga kukan da takesonyi tana tsokanarta,dai dai sanda khadijatou (diya mace qwaya daya da widad din ta haifa qanwa ga mimi) taturo qofar a hankali tana baza ido

"Na shigo maami?" Ta fada a dan shagwabe tana leqo da kanta

"Meye haka kamar munafuka?,shigo ki rufen qofa banason wancan me zuciyar matan(affan) yasan muna ciki yazo su hadu suyita ma mutane kuka kamar cewa akayi idan ta tafi ba zata dawo ba" murmushin yaqe khadijatou kawai tayi,don itama daurewa kawai takeyi,anty mimin she's the part of their lives,ta iya tafiya da qannenta cikin kulawa da qauna,bata fada amma ta iya hukunci,ta iya wasa da dariya amma idan gyara yazo babu wannan wasan,dukkansu sun dauketa kaman abokiyar wasansu,amma kuma suna girmamata sosai,itama ta iya zama da kowa a cikinsu da halinsa,sun taso da shaquwa da qaunar junansu qwarai,ba zaka taba cewa ga wadanda suke uwa daya uba daya ba,yanzun haka khadijatou tafi nawwara jin tafiyar mimin,har gwara yusra ma,itama duk da haka affan ya fita rauni,saboda anty mimin abokiyar sirrinsa ce,kuma abokiyar gulmarsa,sai mimin taji abunsa maami widad bataji ba.

"Wai dangin angon sun sakeyin tuni,sha biyu zasu wuce airport din,jirgi qarfe uku zasu bi" ta fada qasa qasa tana satar kallon anty mimin nasu,kai widad ta jinjina

"Yayi gamu nan" a sanyaye khadijatou din ta juya ta fice tana matse qwallarta.

Hannun mimi maami widad ta riqe cikin nata, suka ratsa falon suka fita ta qofar baya suka wuce kai tsaye suka sashen da aka sauki mummy hafsatu da danginta.

Da sallama ta shiga matsakaicin falon sashen,mummy hafsatu na zaune saman kujerun falon,sanye da wani lace wanda widad dince ta dinka mata shi da kudinta,tace koda bataci arziqin abbas na kai tsaye ba tunda tana da igiyar auren wani a kanta ba,amma zataci arziqi sa darajar yaranta su mimi.

Da sallama ta shiga,hafsat da dangin hafsat din da suke tare da ita suka fara yiwa widad din sannu,don ko maqiyinta ya yaba mata,yaga yadda ta kasa tsaye ta kasa zaune kamar diyar data tsugunna ta haifa take aurarwa.

*_TURK'ASHI!,BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE,KU MARMATSO KUJI,GIDAN KOMAI DA RUWANKA_*

*LIFE STYLE NIGERIA for everything that makes your life style complete*

*GIDAN KOMAI DA KOMAI RUWANKA*

_kama daga kan_


Furnitures
Decoration
Kitchen items &
Boutiques

_our tittle_

Quality is our watch word at lifestyle

shop kano/kaduna

Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot


Instagram@ Lifestyle_Nig
Facebook@ Lifestyleng
Tik tok@ Lifestyle_Nig
Delivery nation wide

_ku tuntubemu ta wannan number_

08036414048

*Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah*

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 47 END


*_TURK'ASHI!,BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE,KU MARMATSO KUJI,GIDAN KOMAI DA RUWANKA_*

*LIFE STYLE NIGERIA for everything that makes your life style complete*

*GIDAN KOMAI DA KOMAI RUWANKA*

_kama daga kan_


Furnitures
Decoration
Kitchen items &
Boutiques

_our tittle_

Quality is our watch word at lifestyle

shop kano/kaduna

Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot


Instagram@ Lifestyle_Nig
Facebook@ Lifestyleng
Tik tok@ Lifestyle_Nig
Delivery nation wide

_ku tuntubemu ta wannan number_

08036414048

*Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah*
_________________________________


Gaban hafsat taje ta tsugunnar da mimin sannan ta zauna daga gefe

"Mummyn mimi,ga mimi tazo neman albarka,yau dai Allah yayi zata tafi nata gidan,sai ayi mata sauran nasiha a kuma saka mata albarka" hawaye hafsat din ta fara sharewa,farinciki ne fal zuciyarta na samun uwar riqo ta gari da sukayi,ta tabbatar inda a hannunta suke babu lallai mimi din ma ta samu miji irin muhammad yasir,wanda ba abinda ya fara burgeshi da mimi din sai tarbiyyarta da kuma nutsuwarta,shine babban abinda ya fara jan hankalinsa

"Aikin gama gaya mata komai,nikam babu abinda yayi saura da zan gaya mata wanda baki gaya nata ba, abinda zata samu daga bakinki yafi wanda zataji daga gareni,abu daya zan gaya mata shine,tayi koyi dake,tayi koyi dake,tayi koyi dake,don kin zamewa rayuwata alkhairi,kin maida yarana abun kwantace abun sha'awa,kin gyatta tawa rayuwar nima a yanzu na dace da mijin da yasan darajata,kin rabani da mu'awiya,Allah ya hadani da mudassir kin kuma tsayawa rayuwata da jari da sana'a,wanda yayi maka wannan me zakace dashi?"

"Babu...babu" shine amsar da yan uwanta da a yanzun suke zumunci ta kuma.kamasu da amana irinsu anty uwani amsar da suka bayar kenan,a yanzun suta riqe ta watsar da irinsu anty ummee duk da suma jikin ta qaura yayi la'asar, rayuwa ta gama karanta musu nata karatun.

"Allah ya albarkaci rayuwarki,ya baki ikon yin koyi da babarki widad" shine maganar hafsat na qarshe,akayi addu'a sosai sannan suka miqe don sadata da dangin banbanta su gwaggwo mero sukayi sallama.

Sanda akaxo sanyata a mota don su wuce kasa tsaiwa gurin widad tayi,don dukka dauriyarta ta qare,yaran duka affan sajjad sajid khadijatou nawwara yusra al'ameen harda auta fadil kuka sukeyi,sun riqeta kyam sai da IG yazo ya tsawatar musu yana hararar affan

"Kai dai kam anyi yaayan banza,ita kanta yanzun mimi din ba kaine yayanta ba?" Akasa dariya gaba daya,sai affan din ya fara ciccijewa kuma yana

32 / 33