Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
gami da kyansa da wani irin kamala.
Gwaggo hassanar tana ganinsa sai tayi shuru,ta wuce dakinsu sumi sumi,ya tsugunna yana gaida gwaggwo mero tare da tambayarta me ya faru
"Fitina ce kawai sukeson ja kafin hafsatu ta fita a gidan nan"
"Bata tafi ba?,zaman me takeyi?" Ya fada fuskarsa a hade,sai ya miqe ya nufi dakin, gwaggwo mero ce ta dakatar dashi
"Ka barsu muga iya gudun ruwansu,neman wanda zai tayasu dama sukeyi" .
Dole ya haqura da shiga dakin,amma ya kasa ya tsare yaqi barin gidan,daga qarshe ya zauna daga bakin gate yana amsa waya.
Abinda baiyi zato bane ya sameshi,wato qarin matsayin da yaketa addu'ar tabbatuwarsa idan da alkhairi,hadi da tafiya course na watanni shida america.
Dai dai sanda hafsatu ke fitowa da jakarta fuska qozai qozai ita gwaggwo mero,don gwaggwo fanteka tace ita fa babu inda zata sai an gama suna taci abinda tazo ci,idan sun koma dai tazo gida ta sameta ta sake jajanta mata,bayan sun fita taja tsaki tana gunguni
"Yarinyar da ba mutuncin kowa take gani ba, zamanta da yaron nan har yai alkhairin da ita qanwar cikinta ya samemu ta sanadinta,ita da ya shekara kusan takwas da ita har ta gama zamanta bamu sameshi ba,yo na meye zan damu kaina?,saina gamacin qwai kaji da nama,ina gani an tirke sa za'a kayar kawai sai na yiwa kaina na tafi rakiyar sakakkiya?,da yake nice maqunshin gishiri"(😂😂,niko nace gaskiyar ki hajiua fanteka,shi mutum mai yawan alkhairi dama maqiyinsa ma wataran masoyinsa yake komawa,Allah kada ka jarrabemu da hannun 'yan dambe).
"Alhamdulillah, Alhamdulillah,Allah ya tayaka riqo,kai nayi farinciki,inama ace yar uwata tana raye taga wannan rana da taketa roqa maka ita" gwaggwo mero ta fada zuciyarta a karye,abinda kuma ya shiga kunnen hafsat kenan wanda ya sakata tsananin rudewa,ko ba'a fada ba tasan wani promotion dinne ya samu,dai dai sanda take fita a rayuwarsa?,wannan wacce irin hasara ce ta tafka.
Ko gwaggwo mero dake ban baki tare da musu fatan sauka lafiya basu kalla ba,suna fita wajen gidan ta damqi hannun gwaggwo mero
"Na shiga uku mero,ya samu promotion,kuma wallahi babban matsayi ne ya samu wannan karon" ta fada qwalla na zubo mata
"Eh to dai hakanan zakiyi haquri,duk wani abun rashin haqurinki ne sila,yqnzu gashi kin bar mata gidan kin bar mata mijin,kin bar mata yaran" maganar gwaggwo hassana saita zama kamar kamar wani fami ta yiwa hafsat din,taji kamar itama tana layin maqiyanta ne,amma dole haka ta danne don tana buqatar dan rakiya,bazaiyiwu ta tafi ziqau ba abun sai yayi mata yawa.
Abinka da ba 'yan halak ba,isarsu keda wuya laifin yaso ya koma kamar na gwaggwo hassana ne ma,ummanta tana salati tana komai amma tana fadin su gwaggwon basu kyauta mata ba,ta yaya suna wajen zasu bari ya qarasa tsinke ragowar igiyar da tayi saura?.
Abun duniya ya taru ya ishi gwaggwo hassana,ta kama baki kawai tana kallon qarfin halin umman hafsatun,wato shi dai abun arziqi bai karbi kare ba wato,hakanan matsiyaci ko a tandun mai aka sakashi haka za'a fiddashi qamas,haka ta karkade zaninta ta tashi ta wuce gida cikin takaici,abun arziqin da tasoyi ya koma na tsiya,can kuma ga daula da gagarumin bikin sunan da za'a yi ta yiwa kanta rasa rasa,sai ta yiwa gwaggwo fanteka barka da batayi biyu babu ba.
******Kwananta biyu cikin matsanancin hali na kuka da damuwa,har daga qarshe umman nata ta gaji da ji ta zaunar da ita
"Nifa wannan koke koken naki ya fara isata,wai shin abbas shine autan maza koko ya aka fara?,kinga fa babu ta inda Allah ya rageki in gaya miki,kin samu a jikinsa kin tara abinda kika tara,ki gama iddarki ki gyagije ki fara zawarci me lasisi,wallahi da gudu zaki samu manema,ai sai wani ya yar wani yake dauka,abu daya zaki.masa ki rama,kema da zarar kin gama iddarki ki rattaba aurenki kawai,shine qarshen baqincikin da zaki cusa masa,yara kuma ya baki abinki,ta nan ma kadai zamu sake samun wasu kudin shigar".
Da wannan shawarar suka dinga shige da fice saida aka saka baki aka bata su mimi,kallonsu kawai yakeyi,yasan manufarsu,don haka dukkan abinda ya tashi bayarwa na amfanin yaran qeqe da qeqe yayi musu,na watanni uku cas ba qari babu dadi,haka umman da hafsat din sukayita zaginsa sunayi dashi a gaban yaran,mimi da nawwara saidai su bata rai,babu damar yin magana,don tun randa nawwara tayi magana da yake ta danfi mimi tsiwa uwar ta gwabje mata baki basu sake cewa komai ba,saidai suyita bata fuska,takaici da baqinciki ya ishi hafsa,don ko widad aka zaga a gabansu sai fuskarsu ta canza
"Shegu an goga musu baqin hali" haka hafsat din ke fada.
Watanni uku aka bawa abbas din kafin tafiyar da zaiyi america, office zasu gama masa dukkan shirye shiryen tafiyar,sun bashi damar tafiya da mata daya da yara uku zasu dauki nauyinsu,idan yana buqatar qarawa kuma wannan saidai yayi a aljihunsa.
Hankali kwance cikin wata irin nutsuwa yake dukka shirinsa,yanason tafiya da widad amma baisan ya zata kasance ba,saidai yana mata shirin ba tare data sani ba incase koda zai buqaci hakan,don bayajin zai iya nesa da ita na wadan nan watannin.
Gefe guda kuwa widad din ta gaya ma kanta aikine sosai ya sameta,idan a baya su biyu ne yanzun ita daya ce dashi,uwa uba kuma riqe namijin da a baya yake da mata biyu yanzu ke daya ce dole saikin zage damtse kin ninka shirinki,duk da hafsat din akwai ya babu ce,amma dai duk tsiya macace itama.
Ta tsaya ta gyara kanta da kyau,ciki da waje ta fara canzawa tana komawa yarinyarta danya shakaf,ta sake shiga classes kala kala da groups groups 'yan gaske na manyan matan da suka fita gogewa a komai, groups na hajiyoyi masu mutunci da tarbiyya da ake mugun qaruwa,ta shiga ne ta sanadiyyar su anty fanna da a yanzu suka zame mata madubi kuma makaranta,gefe guda kuma ga su anty madeena da anty deena da sauran yayyenta da kowannensu yanzu zaman lafiya sukeyi sosai,dama can widad din akwai sauqin kai da bin na gaba da ita koda tazarar shekarunku babu yawa,to har kawo aure bai canzata ba,saima sake riqe yayyenta da kyau datayi.
Ga mummynta itama da bata jin kunyar yi mata bayanin komai,widad din kawai gareta diya mace,sauran dukka maza ne,don haka ta sake zage damtse tana gyare yarta tsaf,kama daga tarbiyyar jiki data zamantakewarta da mijinta.
Cikin lokaci kadan ta sake gigita abbas din,idan sun zauna bashi da zance sai yace
"Kina haihuwa kina sake zama mace,kina kuma sake dada wayo,kina kuma mallakeni wuudd" dariya yake bata
"Allah ka daina fadan mallakar nan,banason jinta,kada wataran kayi subutar baki a dauka da gaske mallakar nayi maka".
Murmushi kawai yake binta dashi,ta shiga kowanne lungu da saqo na rayuwarsa ta tsaye masa cakkk,yasha rayawa a ransa zama da hafsat da rabon haihuwar su mimi ne qaddararsa,bansa haka,inda ace widad din ya fara samu babu abinda zai sanyashi sake wani aure anan dai gidan duniya,saidai hurul'een na aljanna.
Wata biyu kacal ta gama gyaran kanta,idan ka ganta ita da yaranta ko ke mace saita baki sha'awa ta burgeki,yaran su dukka ukun affan da sajid da sajjad (twince dinta)dukansu masu kyau ma sha Allah,sun debo kyau wani daga na widad wani daga na abbas,sai kyansu ya zama wani kala daban me ban sha'awa,bul bul dasu dukansu,idan ka gansu su ukun ba zakace ita ta haifa yara ukun nan ba(daya daga cikin sirrin auren wuri kenan,zaki tara yaranki tunda quruciyarki,baki san dadin jikinki ba,sanda zaki gama haihuwa da sauran qarfinki,sai ayita mamakin wadannan duka yaranki ne,ayita sha'awarku,Allah ya bamu haihuwa me albarka,ya albarkaci wadanda muke dasu).
Sai da suka cika cika watanni uku sannan sukayi shirin shiga garin bauchi,suka shirya tsaf da tsarabar da widad din tayi da kudinta,ita da yaran da aminatu da fahad wanda a yanzun yake tare dasu,sun fara gaba ne,abbas din yace washegari zai biyosu,akwai wani case da zai rufe ne a ranar.
Zuwa tayi ta tarar an yiwa gidanta sabon gyara,wancan gidan nasu kuma da hafsat ta kwashe kayanta duka anata masa aiki,an canza masa fasali da tsari gaba daya,wani irin gini ake masa na tashin kai.
Washegari da azahar ya iso, yaran duka suna wajen aminatu ita kuma tana wajen mai gayya mai aiki tana kula dashi,sai da yayi wanka yaci ya qoshi sannan yace mata su shirya suje suyi gaishe gaishe,ta shirya yaran duk da dama ko yaushe tsaf suke,suka fita gaba daya a sabuwar dalleliyar motarsa daya canza,ita kuma yabar mata waccar.
Sun zaga dangi sosai,widad kuma tasha sanya albarka sosai ita da yaranta,bayan sun taho hanya abbas ya kalleta
"Waini hajjaju,jarin naki duka kike kwashewa kike kyauta dasu?" Murmushi tayi masa tana narkar da wuyanta,ta masa wani kallo na qasan ido
"To yallabai ko me zan basu ai ban fadi ba,danginka ne fa?,abun tutiya wa yarana,kuma ka manta ribar da na samu a wannan shekarar?,ko ka manta ina shirin bude shago?"
"Tuba nake,na manta fa da hajjajun gaske nake magana ba da jabun ba" sai suka saka dariya a tare tana dora kanta a kafadarsa bayan ta kaiwa bayan hannunsa duka.
"Mu samu wani eatery din muci abinci,banason mu koma gida kice zaki shiga kitchen din nan girki,nidai yau na sauke miki"
"Godiya nake" ya fada tana hade hannayenta guri guda,ya sakar mata murmushi,yasan duk da yayi hakan tabbas saifa ta shiga kitchen ba fashi,ko Black tea saita dafa masa hankalinta zai kwanta,dun rintsi duk tsanani bata taba bari rana ta fito ta fadi baici komai daga hannunta ba.
Gaba daya ta tattara hankalinta akan baqin mutumin da za'a iya kiransa matashi,don bai qarasa shekarun abbas ba,aqalla abbas din yana iya bashi shekara biyar,tun wancan sati biyun da ta kammala idda ya fara zuwa wajenta,amma tun lokacin taji sam baiyi mata ba,a tsukin maza kusan uku sunzo mata,amma duk wanda ta daga kai ta kalla sai taga baikai mata zatin abbas ba,tana da buri.....tanason bawa mara da kunya,tanason tayi auren huce takaici,tanason tayi auren da za'a san bataci baya ba,zatayi auren da abbas zai ciji yatsa,widad kuma tasan cewa tayi mata nisa,ta kuma yi mata tazara da ratar da bazata taba iya kamota ba.
*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 42
Matashin ya sake gyara zamansa yana gyaran murya
"Sunana AVM mu'awiya mani adam" da hanzari hafsat ta daga kai tana dubansa
"AVM kuma?,air vice marshall kenan fa?,dama babban mutum ne shi din haka me muqami yaketa binta tana wulaqanta shi?,wato Allah yayi tana da rabo,da tayi wasa da damarta,saita gyara zama tana sakin masa fuska sosai harda murmushi
"Ayyah,afwa yallabai,inata bata maka lokaci ko?,kasan komai sai Allah yayi" shima murmushin ya saki,da alama tarkon da ya dana yayi kamu
"Ba komai,yau ai gashi zamu tattauna sosai" sakewa yayi yana bayyana mata waye shi da irin abinda yake dashi,cikin mintunan da basu gaza talatin ba taji ta gamsu ta kuma amince dashi,kuma lallai ta samu mijin auren da take fata wanda yafi abbas matsayi da dukiya,saidai ya nuna masa kyau,take ta bashi damar turo magabatansa,sukayi dan ciye ciye suka kuma sake tattaunawa,ganin shima din mawadaci ne sai bata boye masa komai ba ta gaya masa irin business din da takeyi,da kuma abinda ta mallaka yanzu haka,don ma tanata fama da ummanta dakeson ta hau kan kudin a dinga murqushewa,banda ta bade idanunta da toka zuwa yanzu Allah ne kadai yasan nawa za'a rugurguza,bayan kudaden abincinsu mimi da ake kawowa suke kashe mu raba,shi yasa taji ta matsu tayi aurenta ta samu inda zata sauke dawainiyarta ta daina facaka da kudinta.
Sosai take kashewa kanta kudi,ita ala dole bataso aga ta canza bare ayi tunanin baqincikin barin gidan abbas ne yake damunta,idan tayi aure kuwa tunda ta samu mai farcen susa,zata tsula tsiyarta yadda taga dama,sai tasa widad taji ta muzanta.
Ya jima wajen masu biyan kudi sannan ya qaraso wajen motarsa yana mita
"Sai suce su basuson Dollar dole saida naira za'a biyasu,bayan ribarsu ne idan aka basu dollar din".
Kanta ya sake fashewa ta saki murmushi
"Rashin wayewa ne kawai yake damunsu"
"Wallahi kuwa,duk da haka saida suka riqe canji na wajen 5k" kamar ta juya taje ta karbo,amma sai taga kamar ajinta zai zuba,haka ta kanne sukaci gaba da tafiya.
Tana tsaye tana jiran ya bude mata ta ciki motarsu abbas ta faka daga gefansu,tunda motar ta tsaya hankalinta ya dauku a kanta,don ba qaramin burgeta motar tayi baba jimawa ya bude ya fito cikin wani lallausan yadi da aka yiwa dinkin zamani.
Mummunar faduwa gabanta yayi,abbas din ya canza yayi mugun fresh,ga qiba mai kyau daya hada,fatarsa ta qara haske,gaba daya qamshinsa ya cika wajen.
Sanda madam widad kuma ta fito cikin wani fitinannen dinkin bubu sai yawun bakinta ya ida qafewa,abbas din ya sunkuya ya karbi sajjad daga hannunta,sajid yana wajen aminatu shida affan,sannan ya karba hand bag dinta ya riqe suka jera zuwa ciki.
"Ina zuwa" tace da AVM mu'awiya tana komawa ciki da sauri saurinta kamar wadda tayi mantuwa,so take ta tabbatar da abinda idanunta ke gane mata,widad dince ta koma kamar wata basarakiya a fadar masarautun larabawa.
Can ta gansu suna magana da receptionist din,tana dan jifan abbas din da harara,gurin zaben abinci ne,sun saba kuma irin haka,akwai saboda da fahimtar juna sosai tsakaninsu da ma'aikatan wajen,wani abu ya tsaye nata a wuya, tsabar hassada da baqinciki ya rufe mata ido,ta nufi gurin dason nuna musu itama cikin wadata take,kuma tare take da mijin zata aura
"Hello" ta fada tana wani yatsina,tunda abbas ya waiwaya sau daya ya kalleta bai qara ba,a yadda yayi zaka tsammaci ranar farko ne daya taba ganin halitta me kama da ita,kuma basu da wata alaqa ko kusa ko alama,sai ya dauke kansa yanaci gaba da miqa musu atm dinsa kan su cira kudin
"Takeaway zaku hada mana kawai,basai mun zauna ci a nan ba" abbas ya fada yana duban ma'aikacin,widad da ta yiwa hafsat din kallo biyu cike da mamakin yadda ta tsomale kamar dattijuwar kaza ta maida dubanta ga abbas tana mamaki,yace anan zasuci amma yanzu ya canza,batadai ce komai ba,dukkansu sukayi shuru sai.muryar hafsat daketa qoqarin mata kwaskwarima,ita ala dole ga ajebo.
"Nice wadda muka zauna a wancan table din ni da AVM mu'awiya"
"AVM mu'awiya kuma?" Ma'aikacin ya tambayeta cikin mamaki
"Yes.....mijina da zan aura,akwai sauran 5k canjinsa dake wajenku.....idan ba damuwa zaku iya riqewa" junansu suka kalla cikin mamaki,saboda sudai sunsan indai wanda take magana akai ne da qyar ya cike musu balance dinsu ma,daya daga cikinsu ne ya girgiza kai
"Aah,muba wanda muke riqewa canji,saidai idan bai fada miki dai dai ba,ko bakiji dai dai ba" fuska ta bata ganin suna niyyar yarfata
"Me kake fada?,ya anyi muku alkhairi zaku saka ma mutane da sharri?"
"hajiya wai me kike fada?,mufa ba wani canji a wajenmu,kije ki sake tambayarsa dai"
"Okay,indai kuka sakani zuwa na dawo zaku gane kurenku,zaku gane da matar waye kuke musu" ta fada tana murza hannu,saita juya tayi hanyar fita tana taku dai dai,tanason murza power dinga a gabansu ko don yau ta hanasu barci.
Jajantawa suke a tsakaninsu na abinda tayin,abbas dake tsaye yana jinsu yace
"Inajin bata da hankali,ko damuwa ce tayi mata yawa" ya fada da salon shaqiyanci dariya tana cinsa yana dannewa,dubansa widad tayi da sauri ta galla masa harara
"Hafsat dince bata da hankali?"
"Oh.....wai dama kinsanta ne?" Yayi tambayar yana dubanta gami da dage dukka girarsa sama,sakato tayi tana kallon abbas din,sai kuma ta girgiza kai kawai,dai dai sanda suka juya suna barin wajen zuwa inda su aminatu ke zaman jiransu
"Dama ai dole kace baka santa ba,kana kishi" wata dariya ce ta qwace masa sosai,ya dinga dariya yana duban widad din,bai tsagaita ba har suka shiga mota ya tayar da ita sannan yace
"Bakisan tausayin wanda zai dauketa nakeyi ba?,niko a lahira horon da za'a yimin shine na sake zama da ita inuwa daya bare nan gidan duniya?,sam,haihata haihata,idan taso ta auri sarkin makka ma,ina mata murna,amma nikam abbas turaki har abada,ni kadai nasan me naji me na gani" shuru tayi tana girgiza kai cikin mamaki,wato mace na iya fidda kanta fit daga zuciyar namiji kenan,kamar yadda take iya kafa kanta kwatankwacin yadda ita tayi
"Su mimi ne a raina,banajin zan iya ci gaba da bar musu yarana gaskiya,kullum haqurina sake qarewa yakeyi a kansu"
"Yaushe zamuje ganinsu?"
"Gobe......in sha Allah"
"Yayi,Allah ya nuna mana" ta fada itama can qasan ranta da damuwa,Allah ya sani tana son yaran sosai,bataqi kuma a dawo dasu a mallaka mata su ba.