Advertisements
Chapter 7 Reading A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 33

18K to 21K   out of 97K words

wata qaramar dariya cikin nishadi da jin dadi,ta tako cikin rashin damuwa ta fara tsince kayan tana dibansu zuwa dakinta,sai a sanann ta lura da mimi dake sharar qwalla

"Ubanki kike a wajen?,wato an saka uwarki kuka shine kikazo kika rabe a nan kina naki kukan,zaki tashi ki wuce ciki ko sai nayi ball dake?" Ba shiri yarinyar ta zame ta wuce daki tana tura baki gaba hadi da ci gaba da goge qwalla.

Rub da ciki takeso tayi kukanta yadda takeso ko zata rage zugi da radadin da zuciyarta ke mata,amma tudun da takeji a cikinta ya hana,dole sai saman pillow ta dora fuskarta tana sakin kuka sosai.

Jiki a matuqar sanyaye ya qarasa shigowa dakin,sai ya kasa qarasowa ya tsaya daga bakin qofa yana kallonta,shi kansa baisan me yake damunsa ba,baisan me yasa yake wasu abubuwan ba,duk da abinda yakeyi din bata taba nuna damuwarta ba,koda ta nuna mintuna kadan take sakin fuskarta kamar ba'a yi ba,sai ayau data nuna fushinta har haka.

A nutse ya qaraso ya zauna gefanta,tunda ya buda mata qofar daki tana jinsa amma bata nuna tasan da shigowarsa bama,hannu yasa a tausashe ya zare pillow din ya maye gurbinsa da tattausan tafin hannunsa,sai tayi saurin kawar da fuskarta daga wajen kamar ya dora mata wuta,yasan halin kayarsa,ta iya rigima a duk sanda taso ko aka tabota,don haka yayi amfani da dukka qarfinsa ya azata saman jikinsa.

Dukka qarfinta ta sanya ta zame a jikinsa,bai gaji ba ya sake maidota yana kiran sunanta tare da qoqarin son su hada idanu amma taqi bashi wannan damar.

Kin zama tayi bare ta saurareshi ba,haka ya gaji da son yin magana da ita ya haqura ya fice yana sauke ajiyar zuciya,ransa gaba daya a jagule babu dadi.

Da kanta ta lallashi kanta,saidai a ranar ta yiwa kanta hukunci qauracewa abbas din da dukka abinda ya shafi hafsat dama cikin gidan,ba zata iya gani ba bazata iya jura ba,duk jarumtar ta abun ya taba ranta,tana iya bakin qoqarin bashi farinciki da son ganin walwala da nutsuwarsa.....gefe guda yana bawa hafsat go ahead tayi duk abinda yake shine dai dai,yana kuma mara mata baya,ta yaya ita tata zuciyar zata samu nutsuwar bashi nutsuwa?.

Washegari ranar girkinta ne,tun safe tana kwance a dakinta wanda tun dare ta saka muqulli ta rufe abinta,tana da abubuwan ciye ciye da yawa a dakinta da bata rabo dasu,don a lokacin abbas da ya shafe babin fita da iyalinsa zuwa wasu guraren shaqatawa a baya,a yanzu widad din ta dawo masa da wannan dabi'a tasa,ko rana daya hafsat din bata taba yunqurin binsu ba,sai mugun haushi da takaicin da take fama dashi,har zuwa sanda zasu dawo cikin gidan,takan ce ita tafi qarfin zuwa nan wajen.

Zamu iya cewa borin kunya ne takeyi,don tun sand yake marmarin kaita take watsa masa qasa a ido,take nuna tafi qaunar ya bata abinda za'a kashe a wajen ta adana,har abun ya fita a kansa,ko ssnda ta haifi su mimi yana son kaisu amma bai samu wannan qwarin gwiwa daga wajenta ba,don haka sai a jima bai fita da yaran ba sai sanda ya samu hutu mai tsaho,gaba daya ita din opposition na rayuwarsa ne totally,bata kuma taba sawa a ranta ta sauya wani tsari yanayi hali ko dabi'a tata saboda shi ba,saboda a samu dai daito da zama me dorewa.

Tana jin motsinsu daga parlor din amma bata ko motsa ba bare tayi yunqurin fitowa,ciye ciyen da tayi a daki ya dauketa fes,don dama bata iya cin abinci me yawa,yana zaune dining area amma hankalinsa yana kan qofar dakinta,jiya da abun ya kwana dashi ya tashi,duk kuwa da yadda hafsat din keta qoqarin mantar dashi da wasu salo da sam baibi jikinta ba bare ya dace da ita,don ba dabi'arta bane.

Ya kammala shan tea din da babu qamshin komai a ciki saina Lipton da milo,ya ajjiye cup din ya miqe yana sauka daga wajen,hafsat din na zaune tana kallonsa batace komai ba,tanason ganin ya za'a qare,ya isa qofar dakin nata ya tsaya a nutse ya fara knocking yana amsa wayar data shigo masa a lokacin.

Taso ta shareshi taqi bude qofar,saboda Wani mugun zafinsa da takeji har cikin ranta,amma sai taga hakan bai kamata ba,tunda tasan a lokacin kowa yana parlor,ta kuma tabbatar hafsat din tana ganin komai da zai faru,don haka ba'a son ranta ba ta miqe a hankali tana gyara zaman yaloluwar rigar jikinta ta zura bedroom slippers dinta ta nufi qofar.

Tana bude masa ta saki qofar ta koma,yabi bayanta da kallo tsigar jikinsa tana zubawa,ko kadan baya gajiya da ita,baya qosawa da ita,kwanaki biyun da basu tare mugun yunwar ta yakeyi,yaci gaba da kallonta yana dan hangen cikinta daya turo kadan,wanda sai ka saka ido da tsananin kula zaka iya ganinsa.

Guri ta samu ta zauna ta gaidashi ba tare data kalli fuskarsa ba,yanata qoqarin su hada ido amma taqi

"Ya jikin naki?"

"Lafiyata qalau" ta amsa masa a shashance,ya sake duban fuskarta sosai yadda taketa basarwa,sai ya ajjiye mata kudin cefane yayi mata sallama ya fice.

Dashi da kudin gaba daya tabi da kallo, zuciyarta ta tsinke kuka yaso qwace mata amma ta danne,ta kalli agogo sannan ta miqe ta shiga bandaki ta watsa ruwa,ta fito taa shirya cikin dinkin doguwar ruga bubu gown ta yane kanta da madaidaicin mayafi ba tare data daura dankwali ba,fuskarta tayi kyau,ta sake wani fresh da haske mai daukan idanu,inda ya ajjiye kudin cefanen ta isa ta dauki kudin,sannan ta qarasa inda wayarta take ita dauketa tare da daukan wasu abubuwan masu amfani sannan ta fito falon.

Babu kowa,sai ta zarce kitchen,ta dan samu abinda zataci wanda bazai mata wahalar narkewa ba,don yanzun matsalar da take fama da ita kenan.

Ta gama ta dauraye cup din ta maidashi inda ta dauko tana kallon yadda kitchen din ya hargitse,kamar ba kwanaki biyu baya ya koma hannun hafsat din komai fes bisa tsari,saika dauka watanni aka dauka ba'a gyarashi ba.

Baki ta tabe ta fice abinta,yau daga kitchen din har Parlor din babu inda zata sama hannu,itama tasan dadin jikinta,kawai dai tanayin komai ne don samun walwala da nutsuwarsa,tunda ta fuskanci babu abinda ke daga masa hankali a rayuwa irin qazanta,amma tunda bai gani itama ba zata dinga wahalar da rayuwarta ba,zata barsu shida hafsat din tasa.

Tana isowa falon sukaci karo da mimi

"Ina kwana anty?"

"Oyoyo mimin daddy,kin tashi lafiya?"

"Lafiya lau anty,yau duka baki fito ba"

"Banajin dadi ne,ungo wannan ki kaima mommynki kice kudin cefane ne inji ni" ta hada dukka kudin da abbas din ya bata ta sanyashi a hannun mimi,sai da taga ta shiga dakin sannan ta fice abinta harabar gidan.

Kai tsaye boys quaters ta nufa wajen maari matar baba mai gadi,sosai taji dadin ganinta kuwa,don bata taba zuwan mata ba,ko yaushe widad din tafi ganewa zamanta daki tayi kallo ko chart,ta marabceta sosai suka fara dan taba hira,tun widad din bata sake ba har ta saki jikinta suka shiga hira sosai,kasancewar hajiyan bata nan,babu wani aiki cikin gidan haka suka wuni tare.

Maari din saita tuna mata da latifanta,cikin awanni kadan ta gane tana da kirki matuqa da jan mutum ajiki,har tafi tsohuwar me aikin hajiyan data dinga tayata kwana sanda abbas yake tafiya bauchi ba tare da ita ba.

Tayi musu faten tsakin masara da yasha gyada da yakuwa,batayi zaton zata iya ci ba,sai gashi taci sosai sunata hira,kirkin widad da yadda take girmama kowa cikin rashin nuna qyama ya sanya maari ma taji ta shiga ranta,ba kamar hafsat din ba,dake dagawa izgilanci da wulaqanta na qasa da ita.

Hafsat na tsaka da barci taji mimi na qwala mata kira saman kanta,da qyar ta bude idonta tana jan mugun tsaki,kafin daga bisani kuma ta buda hancinta sosai saboda warin bayan gida da take jiyowa,dole ta wartsake ta miqe sosai ta zauna tana duban mimi

"Ban hanaki idan ina bacci ki dinga tashina ba don ubanki?" Kebe fuska yarinyar tayi kamar zata saki kuka

"Ai ban tasheki ba harma su nawwara sukayi kashi,yanzunma anty ce tace na kawo miki kudin cefane"

"Kudin cefane kuma?"ta tambayeta da mamaki,saita jinjina kai,ta miqa mata hannu ta saka mata kudin,ta waresu tana irgawa.

To me yarinyar take nufi?,nufinta ta ajjiye girki kenan saboda abinda ya faru jiya?,aiko ba zata sabu ba,ita dinma ai ba jaka bace da zata zauna tayita girka musu suna ci.

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02


Page 10


Kamar ta bawa mimi kudin ta maida mata,sai taga kada tayi asara,ta bata kudin kuma tazo batayi musu girkin ba,don haka sai ta ajjiye kudin tanata qananun mitoci.

Tun tana saka ran ganin widad din ta shigo sashen har ta fidda rai,don yamma ta riga tayi,ga yunwa suna ji ita da yaran,dole ta shiga kitchen ta dora dafa dukan shinkafa.

Tana kitchen din tana fama ga magrib ya kawo jiki widad ta dawo,dakinta ta wuce kai tsaye,bata bi ta kan jagulallen parlor din nasu ba,tana mamakin yadda suke iya hargitsa guri har haka suci gaba da zama a cikinsu abinsu hankali kwance.

Ta taho da sauran faten tsakin daxu,da zafinsa don a wani warmer mai kyau da hajiya ta bawa maari yake a ajjiye,saita hada ruwa me zafi ta cire kayanta ta shiga toilet tayi wanka ta gasa jikinta sosai,ta dawo ta zura wata armless riga da iya tsahonta gwiwa,ta wadata jikinta da turare,ta sake jona humidifier sannan ta dawo tana laluben hijabin da zatayi sallar dashi wanda zai saukar mata har qasa.

Sosai yau ya hado yunwa da kuma gajiya a jikinsa,ya tabbatar zai samu dukkan wani hutu da kulawa hadi da kwanciyar hankali daga gurinta,wannan yasa ya hada dukkan yunwarsa ta yinin ranar,bai wani tsaya yaci cikakken abinci ba,don yasan zai tarar da irin taste din da yake muradi,har fiye ma da yadda yakeso.

Ajiyar zuciya ya sauke sanda ya kashe motar tasa,ya waiwaya baya ya dauko ledar fruit din da ya siyo da chocolate nasu mimi ya fito,ya kashe motar sannan ya nufi cikin gidan.

Tun kafin ya qaraso ya fara buda hancinsa yana tsammatar samuwa sassanyan qamshin nan dake masa maraba a duk sanda girkinta ya shiga,saidai babu shi ba alamarsa,duk da haka yaci gaba da takawa cikin hope da kuma karsashi.

Sosai mamaki ya cikashi sanda ya yaye labulen falon ya sameshi a tarwatse,komai yana zaune zaman kansa,sai su mimi dake ta hada hada da kayan ciye ciye na leda irin wanda yake siyowa ya jibge musu,ko ina tarkacen kayan ledojin da tsinken sweet ne,dukansu suka watsar da abinda yake hannunsu suka nufoshi suna rige rigen qarasowa,ya tsugunna ya tarbesu gaba daya.

Miqewa yayi yana dauke da nawwara mimi na hannunsa,yaji motsi a kitchen,don haka zuciyarsa ta bashi widad ce,sai ya wuce kitchen din dasu kanshi tsaye yana amsa tarin tambayoyinsu da suketa damunshi dasu.

Tun bai gama shiga kitchen din ba idanu da hancinsa suka gaya masa ba widad bace,hafsat ce sanye da doguwar rigar wani material ruwan qwaiduwar qwai,sulbinsa ya sanya dinkin da aka masa a wasu sassan ya zazzame yayi zare zare,tana goye da yusra daketa mutsu mutsun son a sauko da ita,ya qarasa yana amsar yarinyar,ta sauke masa ita tana masa sannu da zuwa muryar a cunkushe.

"Ina antyn nasu?"

"Tana dakinta mana" hafsat ta amsa adan fusace tana juya dafadukan data fara kamawa

"Lafiyarta qalau?" Juyowa tayi kamar ta banka masa harara,amma kwarjinin nashi idanuwan sun shallake nata

"Aiba wannan ya kamata ka fara tambaya ba,kamata yayi ace ka tambayi wanda ya bamu abinci wunin yau,ta shige daki saboda ta samu daurin gindi tayi kwanciyar ta wuni guda ta barmu da yunwa ni da yara" sam hankalinsa bashi akan maganarta, zuciyarsa da tunaninsa sun karkata kan sanin lafiyarta da abinda ya hanata fitowa wunin yau,sai ya juya yana sabe da yusra ya fice a kitchen din.

Ana fara knocking ta gane shine,ta riga ta saba da komai nasa,hatta takun takalminsa ya banbanta dana kowa,tana kuma iya banbancewa,ranta yadan quntata,itakam ko son ganinsa batason yi,space take da buqata, batason takura,to amma batason tayi wani abu na rashin girmamawa a gareshi gaban yaransa,dole ta ajjiye qaramar hular da take qoqarin sanyawa sassalkar sumarta daketa sheqi saboda yadda tayi oiling dinta da mai,tana tura baki da shagwababbiyar fuskarta ta isa qofar ta bude masa,sai taja ta tsaya daga bakin qofar,kamar wadda aka zo gayawa saqo take jira a gama gaya mata a fita ta kulle qofarta.

Tun daga kwanyarsa har zuwa tafin qafarsa wani abu ya tsarga masa,yadda batasaka brassiere ba amma hakan bai hana na shanunta tsaiwa kyam suna nuna kansu ba,lafiyayyun cinyoyinta sun fita sosai ta cikin tsingilalliyar rigar,yadda ta turo bakinta gaba kuma ya qarasa kunnashi,soft pink lips dinta daketa sheqin lip gloss,sai yaji kamar ya jata cikin jikinsa ya kama bakin ya tsotse,amma yusra na kafadarsa,tilas ya daure,ya qarasa gefan gadon ya zauna ya dora yarinyar saman cinyarsa

"Sannu da zuwa" shuru ya ratsa maimakon ya amsa mata,ya tsareta da ido yana jin yadda kallonta kawai yake saukar masa da kasala

"Banda na shigo na nemeki bakisan ma na dawo ba kenan?"

"To me zanzo nayi maka?,bayan maganar matarka kawai kake ji" ta fadi haka cikin ranta,amma a fili saita sake tura baki gaba tana yamutsa girarta hadi da sarqafe yatsunta waje daya tana ballaqasu

"Zonan" ya fada a tausashe yana nuna mata kujerar madubin dake gabansa,ta kalli wajen sannan ta kalleshi,ko yaushe girma da kimarsa ke sakata ta kasa masa musu ko wasu dabi'u da basu kamata ba,ta sauke hannuwanta ta dawo inda ya nuna matan ta zauna,wannan karon idanunta cikin nasa tanason jin abinda zai gaya mata kuma.

Rage kaifin nasa idanun yayi kadan daga kanta sannan ya magantu

"Ya akayi gidan ya zamana yau duk a hargitse,infact ma yau girkinki ne amma baki fito kwata kwata ba,ko yanzun ma antynki ce cikin kitchen din" wani haushi ya kamata,aiki?.....a nan tafi kauri kenan, idanunta ta lumshe kadan tana daukesu daga kansa,abinda ya sake fusgarsa da wani madaukakin shauqi zuwa gareta,duk da ba tayi bane don ta burgeshi ko kuma da wata manufa

"Gida a hargitse?,ina cewa mummyn mimi tana cikin gidan,amfanin zaman mutum biyu kenan,idan dayan ya gaza ko ya gajiya sai dayan ya tallafa masa.......girki kuma ni na daina girki,na bar mata komai da komai harda kwanana" mamakin widad din sosai ya kamshi,yadda tayi maganar ya tabbatar da gamewar hankali a jikinta,don tana maganar ne with seriousness in her sound,baibi takan maganarta ta farko ba,maganarta ta qarshe tafi fusgar hankalinsa tare da tabashi,don abune da bayajin ko sama da qasa zata hadu zai amince da hakan

"Kin daina girki?,meye dalili?,da kuma izinin wa kika dauki wannan matakin?" Sake tura bakinta gaba tayi sosai tana hade fuska,ta kuma kaucewa dubansa

"Saboda gidan da mijin duka nata ne,so komai da yake cikin gidan yafi cancanta ya zama nata" sai yanzu ya sake gano inda ta dosa,can qasan ransa murmushi ya kubce masa,kishi take da gaske.....ta kuma ji haushin abinda yayi mata kenan fiye da yadda ma shi ya zata,amma bayason ta dore da haka don haka ya miqe yana dora yusra a kafadarsa

"Ki shirya komai kamar yadda kika saba,banason dawo da zance,abinda ya wuce ya wuce" sai ya taka yana ficewa a dakin.

Sam maganarsa bata bawa zuciyarta sassauci ba,saima tunzurata da yayi,bazai iya daukan mataki ba kenan kwata kwata?,indai haka ne itama bataga dalilin da zai sanyata saukowa ba,don haka yana fita sallar magariba ta sakawa dakinta key tayi sallarta ta jirayi isha'i ta bada ita sannan ta haye gado ta nutse cikin duvet hankali kwance.

Sai daya dawo daga masallaci sannan ya zarce dakinta don ya samu ruwan nan nata me wani irin dumi da qamshi don yayi wanka,ruwan da ita kadai tasan yadda take hada masa shi,don koshi ya hada da kansa baya jin dadinsa kamar haka.

A nutse ya tsaya yana knocking a bakin qofar,tana jinsa ta share,saita saka earpiece ma a kunnenta,don haka batasan adadin awannin ko mintunan da ya dauka yana bugun ba.

Sosai ransa ya quntata,don yadda yayi tsaye yana bugun har mimi taji ta fito ya tabbatar tana jinsa,ya kirayi sunanta kusan biyar shuru,dole ya juya dakinsa dakin kuma hafsat,tana zaune a qasa ta tara kayan qazantar yusra tana waresu,ya

7 / 33