Advertisements
Chapter 31 Reading A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   31 / 33

90K to 93K   out of 97K words

widad,Allah alhakim,Allah mai iko,Allah me gaggawar hukunci mai sakayya da hisabi tun a nan gidan duniya,wai yanxu hafsat ce haka?,kamar wata almajira?,cikin shekara guda kacal,cikin wata mummunar kama da siffa.

"Naji dadin ganinku haka mimi,duk da dama raina yana rayamin ba za'a samu wata matsala ba,kuna cikin aminci da kulawa,don na tabbatar ban barku a mummunan hannu ba" hafsat ta fada tana sharce hawaye

"Na gode,Allah ya saka da alkhairi,Allah ya biyaki da yadda kika riqemin yarana" ta sake fada tana kallon widad kamar me kunyar su hada ido.

Duk mamaki sai ya kama widad din,hafsat dince ke mata godiya har tana yabonta,lallai kaji tsoron duniya kaji tsoron ubangijinka

"Ba komai,d'a ai na kowa ne,da dukiya da d'a babu wanda yasan me morarsu sai Allah"

"Haka yake" ta fada tana jinjina kai,gami da tuna tata dukiyar data dinga salwanta daya bayan daya,har ta zamana a yanzun bata da komai bata mallaki komai ba.

Ta jima da yaran a falo widad ta basu waje suna hira,sunata gaya mata abubuwan da suka faru da kuma zamansu a america,a ranar taji farinciki da nishadin data jima bataji irinsa ba,damuwarta ta ragu qwarai da gaske,ta sake gasgatawa lallai yaran sune sanyin idaniyarta.

Data tashi tafiya cikin d'ari d'ari tace da widad

"Don Allah zan roqi alfarma guda biyu a wajenki idan zan samu"

"Babu wata damuwa,ki fada ko menene"

"Don Allah ina roqarki ki yafemin duk abubuwan da nayi miki,sannan ki roqarmin babansu shima ya yafemin,duk da nasan saimai qarfin imani ne zai iya yafewar"

"Allah ma muna masa laifi kuma ya yafe,duk abinda ya faru ya riga da ya faru,shima zan gaya masa,zai kuma yafe din in sha Allah"

"To na gode qwarai qwarai....alfarma ta biyu don Allah ki sake roqarmin shi,ya dinga barin yaran nan suna zuwarmin,koda ba kwana ba,ko basu yini bama don Allah" tausayinta ya sake kama widad,kaida yaranka amma saika roqi a baka su ka gansu

"Xan gaya masa,kada ki damu kinji" godiya sosai ta sake yiwa widad din,sannan ta miqe tana musu sallama

"Gashi ban kawo muku komai ba,kuyi haquri babu dama ne" cikin son kwantar mata da hankali tayi murmushi

"Karki damu fa,suna da komai mummyn mimi" kai ta jinjina

"Shikenan,na gode Allah ya saka da alkhairi" tsaidata widad tayi ta wuce bedroom dinta,cikin matuqar sanyin jiki da kuma tsoron halin duniya ta dauko hand bag dinta data dawo da ita ta buda,ta laluba kudin ciki,duka duka dubu goma ce tayi mata saura kudin nigeria,saita shiryasu ta fita dasu ta miqawa hafsat.

Jikinta na rawa cikin mamakin yawan kyautar da tayi mata tasa hannu biyu ta karba qwalla tana cika idanunta,shekara guda kenan rabonta da riqe kudade irin wadan nan,godiya sosai ta dinga yi mata,sannan ta juya ta fice hawaye wani yana korar wani.

Haqiqa duk wanda baiji tsoron Allah ba yana tare da wahala,duk wansa baibi duniya a sannu ba matsala bata qare masa ba,a yau yaran da take banzatarwa gasu tana ganinsu tana qaunar su rabeta,tana qaunar zama dasu amma sunfi qarfinta,don tasan ko sama da qasa zasu hade a yadda taga sun samu kwanciyar hankali da kulawa abbas bazai taba bata ko daya daga ciki ba.

Gidanta da take ganinsa kamar mallakinta,ta kasa kula dashi,ta banzatar dashi gashi a yau yafi qarfinta,ta fita ta barwa wadda tazo gidan daga baya.

Mijin da take banzatarwa,ta kasa tsayawa ta gyara kurenta,ta kasa tsayawa ta karanci abinda yakeso da wanda bayaso,ta kasa bashi abinda yake muradi cikin rayuwarsa.....gashi qaramar yarinyar da a haife ta haifeta,tazo ta sha gabanta,ta shiga rayuwarsa ta maye masa gurbin komai.

Idanunta sun rufe,amma a yau suna bude kansu da kansu,tsantsar kishin banza da jahilci mara ma'ana yasa tabar gidanta, mijinta da yaranta dukka yanzu sun zama mallakin wata,saboda anyi mata kishiya ta kasa haqurin zama a gidanta,ta fita daga raminta ta fada ramin wata,tabar ramin data gina ta fada ramin wata,watar dake gallaza mata ita da mijin da baisan darajarta ba (babban qalubalen dake damun mata, mijinki da yasan darajarki,gidanki da kikasan ciwonsa,yaranki da basu da kamarki,dukka sanadin miji zai qara aure saiki watsar dasu kice saiya sakeki,bayan bai wulaqantaki ba,yayi hakanne saboda wani qarin auren a qaddararsa yake bai isa ya tsallaketa ba,babban abun mamakin kuma shine,sai ka ganta can ta buge da auren wani me matar,wai shin da ramin daka gina da kanka?,da wanda wani ya gina ka shiga zai zamto daya a wajenka gurin samun 'yanci da komai ma?,mata mu nutsu mu yiwa kanmu karatun ta nutsa,kishi yana da ciwo,yana da matuqar zafi,babu komai ke gane hakan sai masu zaune da kishiyoyin,to amma kuma ita addu'a maganin komai ce,sannan duk wanda ya miqa lamarinsa ga Allah,Allah ya isar masa,Allah yasa mu dace,yasa mufi qarfin zukatanmu amen).

Widad ta dade tana juya abun cikin ranta,ta dade tana tuna fuskar hafsat,Allah abun tsoro duniya abun tsoro,sai jikinta ya sake sanyi,hakanan ta sake lafkewa akan kujera,tana tuna ko akwai inda ta sabi ubangijinta?,iya tunaninta bata tuna ba,amma saita samu kanta da istigfari,zuicyarta kuma ta sake tsarkaka,tare da sake daura aniyar kula da yaran tsakaninta da mahaliccinta,duk da dama ko sau daya zuciyarta bata taba bata wai ta zaluncesu ba.

*H A F S A T*

Sai data tsaya a soron gidan ta gyara zaman kudin sosai a jikinta cikin zaninta sannan ta sanya kai cikin gidan qirjinta yana dukan uku uku.

Da ita kuwa ta fara hada ido,tana tsaye a gaban falonta,gaban hafsat yayi wata mummunar faduwa,tayi saurin janye idanunta,sannan da hanzari ta doshi dakinta kamar zataci da baka,tasa hannu ta tura qofar ta bude kai tsaye don dama bata kulle qofar ba,saboda bata ma da ikon don zata fita ta rufe qofar dakin nata.

Falo ne falle da daki a ciki,kujerunta ne tun na aure,wanda su kadai ne suka tsira mu'awiya bai dauka ya siyar ba,maimakon ta samu guri ta zauna saita maqale jikin window din tana leqen tsakar gidan,tana kallon sahura dake mazaunin kishiyarta tana hararar qofar dakin nata,sai kuma ta daga zaninta ta ciro wayarta tecno keypad.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" hafsat ta fada jikinta yana rawa,tasan yau ta kade daga ita har ganyenta,dama tasan tunda ta fita batayi mata sallama tare da gaya mata inda zata ba yau ba ita ba kwana lafiya cikin gidan,tana jinta tana cewa

"Ma'a,kazo gata ta dawo.....oho muku,can ta matse muku" sai taja mugun tsaki ta kashe wayar tana mita.

Tunda uwar hafsat ta haifeta bata taba ganin bala'e'iyar mace irin sahura ba,bata gajiya da fada da bala'i,mita kuwa saita kwana tana zarya a tsakar gida tana yinta,dare baya mata kaifi haka rana bata damunta, bala'i idan ta kwan biyu bata yishi ba jinta take kamar mara lafiya,jikin hafsat ya dauki rawa,ta fada dakinta tana laluben kayan da zata sakawa jikinta da suka dan fi wannan kauri,tunda taji tana kiransa a waya lallai yau babu makawa jibga zatasha,babu kuma me qwatarta sai sarki Allaha.

Ai hijabi kawai ta gama sawa taji anyi ball da kwanonta dake falon sannan ya fara magana da qarfi

"Kina ina munafuka,fito nan nace miki" yayi maganar yana nade danqon dake hannunsa,jikinta na mazari ta fito ta qaraso gabansa ta durqusa,baiyi wata wata ba ya fara lafta mata

"Ka tsaya don Allah nayi maka bayani,wallahi ba wani guri naje ba"

"Qarya take munafuka,dama ta saba bin maza,kana fita take sanya qafafunta ta fice,saita dai daici kana dab da dawowa sannan takes shigowa gidan nan" .

Baiko tsaya jin bayanin bakinta ba ya dinga laftarta,garin qoqarin zillewa kudaden da take maqale dasu suka zubo,sahura ta saki salati,ita da mu'awiya duka suka duqa lokaci daya suna qoqarin dauke kudin,sahura da ta fishi son abun duniya ta rigashi dauka,tahau lissafawa.

Dubu tara da dari takwas cif,don tayi kudin mota a ciki

"Ka gani ko,tabbacin bin maza ta koma,kaima Allah ya qara maka,ta yaya zaka dauko matar me kudi kace zaka iya riqeta,aiga irinta nan"

"Miqon kudaden nan" ya fada yana miqawa sahura hannu,wani kallon banza ta jefeshi dashi

"Uban kuturu ma yayi kadan bare na makaho,ka manta kudina daka dinga karba sanda zaka aurota?,ai da haka zan gama fanshe asarata,don ni wallahi mun raba hanya da asara,bana daukarta" daga haka ta soke kudin a brassiere ta fice abinta.

Bulalar yayar cikin baqincikin rashin samun nasarar daukar kudin,ya zauna saman kujera yana huci

"Tashi ki zazzage jikinki ko akwai sauran wasu kudin" haka ta miqe ta zazzage masa kanta,saidai ko sisi bai fado ba,yaja mugun tsaki

"Ki rufewa mutane baki ki daina musu kukan banzan nan"

"Wallahi bana bin maza,Allah maawiya sharri takemin"

"Dalla rufemin baki,bazan taba yarda ni dake ba...."

"Na'am" ya katse maganar yana amsa kiran sahura da taketa qwala masa kan ya fito yaja mata ruwa a rijiya,sai ya fice da sauri kamar wanda zai amsa kiran uwarsa.

A wajen ta zube tana kukan baqinciki,dama haka qazafin zina yake da ciwo ?,haka widad taji lokacin data qulla mata sharri?,sau daya tayi mata ita,amma sai gashi ita kuma Allah ya hadata da kishiyar da kullum ta Allah daga fitowar rana zuwa faduwarta saita jefeta da wannan qazafin,saita rushe da kuka tana tuba zuwa ga Allah,tana tuna irin tashin hankalin data saka widad a ciki,bama ita kadai ba,hatta da abbas din,banda kiyayewar ubangiji da zuwa yanzu yana dauke ciwon zuciya ko kuma mummunan hawan jini,tati amfani da irin son da taga yana mata,ta saka an dasa zargi me qarfi a kanta cikin zuciyarsa,sannan ta jefeta da qazafin,ashe duk jifan da kayi wataran kanka zai dawo,bayan saki data rabauta dashi a wancan karon,yanzun kuma gashi tarihi ya maimaita kansa.

Duk inda takai ga kaidi da jaraba da bin malamai sahura ta dameta ta shanye,a yanzunma ina taga kudin da zatabi malaman?,abinci ma wataran cikin gidan gagararta yakeyi sai tayi biyayya sannan sahuran zata san mata,tunda kusan fiye da rabin qarfin kula da gidan itace.

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 45

Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn Whatsapp
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏
_______________________________


Wanne irin hakki ne haka yake binta?,ta shiga uku,mu'awiya mutumin da yazo mata a matsayin air vice marshall,ashe kurtu ne,kurtun sojoji wanda akewa alfarmar daukarsu a aiki,suke dan aike aike wa manyansu,amma tsabar hakki da kuma ranar girbar abinda aka shuka da take dab da fadawa ta kasa ganewa,tun daga yadda yazo mata,ba wasu cikakkun suturu na alfarma da zasu gaya mata wayeshi,babu wasu securities da akasan dukka masu matsayi irin masa na yawo dasu ko da yaushe ko kuma motoci yaci ta gane amma idonta ya rufe, kwanyarta ta toshe, duka batayi wannan tunanin ba,matsayinsa ke mata kuwwa cikin kunne,ta tuna ranar da ya raina mata hankali yasa ta koma eatery karbar canjinsa,data koma masa da batun sunce ba'a binsu kudi sai yace

"Ayyah,inatason tsaidaki,ai kina shiga ina ganin alert,sunmin transfer yanzu yanzu" da haka ya shashantar da maganar,ashe duka ya shirya aurarta ne ya cinye duk abinda ta tara da abinda ta mallaka,don yanzun haka bata da komai,ko wayar hannu tafi qarfinta,sai azabar da take qunsa daga hannunsa da kuma wajen kishiya.

Watanni shida baya ummarta ta rasu,aka rabon gadon da mahaifinsu ya bari wanda a baya ba'a raba ba saboda ummar ta hana a taba,kowa kuma yana tsoro haka yayi Shuru,nata kason bata sani ba mu'awiya yayi ruwa yayi tsaki ya saida mata,yan uwanta kuma sukace babu ruwansu,sun dauka da hadin bakinta ne,hatta anty ummee yanxu tana gida tana zaman zawarci da nakasar ido daya da mijin ya tsiyayar mata,bayan ya gane dogon lokacin data dauka tana ha'intarsa tare da sanyashi yana cin zarafin uwar gidansa ta hanyar amfani da kissa,ita kanta yanzu ta zama abun tausayi,tayi nadama tayi nadama har babu iyaka,kissa bata amfaneta da komai ba sai dana sani da wahala a rayuwarta,ya karbe dukka yaransa dake wajenta ya danqawa uwar gidansa,ita kuma tana kulawa dasu cikin amana da kulawa
(Babu inda ba na gari,babu kuma side din da babu baragurbi,daga iyayen gidan har amaren,saidai mata muji tsoron Allah,mu yiwa Allah mu yiwa muhammadur rasulillahi S A W mu daina wahalar da junanmu,ke idan zaki shiga gidan me mata kiji tsoron Allah,ki tsarkake niyyarki,ki shiga da niyya me kyau,wallahi wallahi idan kikayi haka bata isa taga bayanki kota tozartaki ko ta samu nasara a kanki ba,indai kinyi da zatin Allah,kiyi haquri da wasu abubuwan ki dauke kai a wasu,amma kada ki yarda da cin xarafi,kema uwargida ki sanyawa zuciyarki haquri,ansani kishi yana da ciwo,amma ki dauka haka taki qaddarar tazo,ki sanya Allah a gabanki,ki toshe kunneki daga 'yan gulma da yan bani na iya masu kawo miki labaran da zasu daga hankalinki,karki yarda ki cutar da ita bayan ta shigo koki qoqarin fiddata daga gidan,kada ki manta ko meye kikayi wallahi ba'a cin bashin Allah,duk wanda yaci sai ya biya ko 'ya'yansa sai sun baya,ko bakya raye kinga kin bar musu musiba,ki kama girmanki karki bada qofar da za'a rainaki,ki yawaita addu'a sai kiga Allah ya kwarjantaki an girmamaki ko ba'a so daga ita har mijin,ki dauki girman da Allah ya baki,Allah ya bamu haquri da juriya gaba daya).

Tana tsaka da wannan tunanin cikin tsananin qunci da tashin hankalin yadda rayuwa ke gare gare da ita aka bankado labulen dakin,ta firgita ta miqe ta zauna suna kallon kallo da sahura

"Badai kin aurar min miji ba?,wallahi babu ke ba sauran zaman lafiya,ki tashi kije ki wanke masa bangon bandaki,yace bai fita ba,bazai dauki wannan qazantar taki ba" daga wannan ta juya ta fita tana karkada mata mazaunai.

Ko second biyar bata qara ba haka ta miqe ta fito tun kafin ya dawo yaci zarafinta,jikinta nata ciwo tako ina saboda dukan da tasha,ta qarewa bandakin kallo,babu qazanta ko dis,kawai tiles din jikin bangonne da bata wanke ba,tunda ta fara zaman aure bata taba yiwa bandaki bautar da takewa bandakin gidan mu'awiya ba,bama bandaki ba,gidan gaba daya,wata muguwar tsafta ce dasu daga shi har sahura,kamar masu aljanun tsafta,sanda tazo da qazantarta taci wahala,kyara tsangwama daga baya harda duka kamar diyarsu,sai ayi shara kusan goma a gidan,bandaki kuwa duk bayan awanni haka zata tashi ta wankeshi tasss,tasha wahala sosai,don bata saba ba,zuwa yanzu kuwa ya zame mata jiki,saidai hausawa sukace ba'a sabo da wahala.

Tana farawa sahura ta dawo bayanta ta tsaya tana mata gyara cikin masifa,daga qarshe ta dauko kofin bandakin ta dinga sheqawa hafsat ruwan tana dirzawa,tana sane da gayya take hakan,don kusan rabin jikin hafsat din sai data jiqa mata shi,bacin rai yazo mata iya wuya,amma bata isa tayi magana ba yanzu suyi kamar zasu cinyeta danya ita dame gidan,yanzun zata hau mata gorin gidanta ne tunda filin da ginin gidan duka ita ta gina,shi kuma zai hau fadin eh dole ta bita,saboda gidanta ne kuma a gidan ta sameta,don mu'awiyan kamar qarqashin umarnin sahura yake rayuwa.

Tunda hafsat ta fita tabar gidan ta barta cikin mutuwar jiki mamaki da kuma juyayi,lallai duniya rawar 'yammata ce,na gaba ya koma baya,muddin bakaji tsoron Allah ba ka shiga uku duniyarka da lahirarka.

Sai zuwa yammaci ta samu ta qwarara jikinta ta shiga kitchen,don bata taba saukewa kanta kula da cikin abbas din duk rintsi indai suna a tare.

Ita da aminatu ne,don haka cikin sauri ta kammala komai,tabar musu gyaran kitchen din ita da mimi dake da himmar aiki,sannan ta dawo parlor din gidan zuwa bedroom ta tabbatar komai yana kan order,ta kuma cikashi da qamshi ta yadda zai dace da yammacin sannan ta wuce bedroom dinta ta fidda kayan jikinta ta fada wanka.

Ta jima a bayi sannan ta fito daure da towel,kome takeyi cikin mutuwar jiki take yinsa,baya ga lamarin hafsat

31 / 33