Advertisements
Chapter 30 Reading A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   30 / 33

87K to 90K   out of 97K words

Daren ranar kasa bacci gaba daya hafsat tayi,ta dinga zarya tana hango abbas da widad a idanunta,happy family,me zatayi wanda zai bata wannan jin dadin nasu?,bata samu hutu ba saida zuciyarta ta yanke mata abinda zata aikata musu,ta san yadda mata suka tsani riqo,musamman ma riqon dan kishiya,ba abinda zata cusgunawa widad din dashi saidai takai mata yaran,ta qara mata yawan aiki ta hanata hutu,wannan kuma tasan zaiyita hadata fada da abbas din,shikenan hankalinta ya kwanta.

Da wannan shawarar ta kwanta, washegari kuwa tunda safe ta soma hada musu kayansu,har sun sanya uniform tace su cire,ummansu nata fada da mita

"Dan hanyar samun alkhairin zaki toshe mana?"

"Nifa aure zanyi umma,don haka yaci gaba da riqe yaransa,babu me masa wahala,yanacan yana holewa da matarsa mu ya barmu da raino" hakanan badon umman taso ba ta tasasu a gaba,ta sakasu a napep sai gidan abbas din kanta tsaye.

Kusan kowacce safiya zaka samu gidan neat dashi,bama gidansu na katsina ba har na nan din,saboda basa kwanciya dama abar gidan da datti,har aminatu ta saba,ya zame mata jiki,duk inda takwas tayi ta gama komai,ta yi wanka ta yiwa affan din kansa wanka,saidai suyi wani abun daban kuma,kosu sake kwanciya bayan sunci abinci,ko suyi game na alphabet din arabic ko na english da dai sauran abubuwa masu amfani.

Tsaye tayi a tsakiyar falon tana qare masa kallo,an tsara komai na falon daki daki bisa sha'awa da burgewa,hakanan ya samu cikakkiyar tsafta da kulawa,ba abinda yake fitarwa sai wani irin sassanyan qamshi da ya hade da sanyin ac din dake Parlor din.

Muryarta ta ware cikin baqinciki ta kwarara sallama,aminatu dake daki ta jiyota,ta miqe ta fito tana riqe da hannu affan,hannunta daya kuma dauke da sajjad dake cikin wasu fafaren overall,ya cikata fam ma sha Allah,idan ka kalli yaran ba zakace twins bane ba.

Tsaiwa tayi tana kallon hafsat din cike da mamakin ganinta a gidan,saita kalleta da harara harara

"Ina mutan gidan?"

"Antyn tana wajen daddynsu....."

"Na sani,dalla malama kiramin shi mai gidan" ido aminatu ta fiddo,tunda take dasu bata taba buga musu qofa ba ai,ba zata iya ba,barema dokar widad dince,indai ba wani babban abu bane ya faru basa kiranta idan tana tare da daddyn

"Ba'a kiranta idan tana wajen daddy,kiyi haquri ki zauna ki jirasu,bari na kawo miki ruwa" ta fada cikin nutsuwa irin ta yarinyar tana sakin hannun affan,wanda mimi tayi caraf ta kamoshi

"Qani.....ka manta ni ko?,ya naga kana kumatu,muji ko bread ka boye" ta fada tana dariya gami da fara lallatsa masa kumatun,yaron bashi da saurin mantuwa,ya tunata sarai,sai kuwa yahau bagala mata dariya,dukkansu sai suka matso kuwa,abinda ya qarawa hafsat takaici ganin yadda suka yanyame yaron dukansu cike da qauna suna masa wasa,ta daka musu tsawa,duk sai suka koma suka lafe.

Sosai aminatu ta cika plate da kayan kaiwa baka ta ajjiye gaban hafsat dake tsaye,tabi kayan da kallo,rai naso amma kuma zuciyar ta hana,baqinciki qyashi da kishi mara amfani ya rufe mata ido,taso ta basar amma ta kasa,saita faki ido ta dauki lemo ta jefa a jaka,ta dan rarraba ido taga hankalinsu bai kanta,ta sake zarar wani abun ta jefa,tana kan jefa na uku ne qofar bedroom din abbas ya bude suka fito shi da ita,sai tayi sauri ta saki abunda ta dauka,saidai tuni sun gani,amma sai sukayi kamar basu gani ba.

Riqe suke da hannun juna,perfect match couples da kowa ya kallesu sai sun bashi sha'awa,sanye take da wata rigar wani material da aka yiwa wani kyakkyawan dinki da ya zauna mata sosai a jiki,kanta ba dankwali sai sassalkan baqin gashinta me yauqi wanda kullum bata gajiya da gyaransa da yi masa style kala kala harda nasu bead,yau matseshi tayi cikin band ta kuma yiwa jelar kitso guda daya ta barshi yana yawo a bayanta,jikinta ba abinda yake sai fidda sassanyan qamshin turarukan jiki dana hayaqi data tsuma kanta dasu.

Shima abbas din shirye yake tsaf cikin qananun kaya wadanda suka sake qara masa kyau da quruciya, hannuwansu cikin na juna,tana riqe da wayarsa da kuma takalmansa da baikai ga sakawa ba da alama wata magana suke me muhimmanci,don kowannensu fuskarsa dauke take da walwala,duk da kusan ko yaushe haka suke su din,zaiyi wuya kaga sabani a tsakaninsu.

Kanta ta dauke kamar zatayi aman zuciyarta,saidai a fuska kuma bata nuna hakan ba,amma wannan yanayin ya bayyana har saman fuskar tata

"Oyoyo mimin daddy,oyoyo nawwaraty.....a'ah ga baby yusra" widad din ta fada cikin farincikin ganin yaran,suka taho da saurinsu suka rungumesu duka har uban,sai ta sanyasu cikin jikinta sosai,tausayinsu yana ratsata,inama ace abban nasu zai bar mata su.

Yana zaune yana gaisawa da yaran nasa daya bayan daya yana bincikar lafiyarsu ba tare daya dubi ko sashen da hafsatun take zaune ba,widad kuma na tsugunne gabansa tana sanya masa takalmi a qafafunsa,sun share hafsat din kamar ba ita a falon,tun bayan sannunku da zuwa da widad tace mata ta amsa da qyar sai itama ta watsar da ita,don a yanzun kuma bataga wani alaqa tsakaninsu ba bare ta dameta.

"Yaranka na kawo maka,don nima aure zanyi" maganar data fada kenan cikin gadara,dai dai sanda widad ta gama saka masa takalman,sai ya miqe tsam ba tare da yabi takan maganarta ba yana fadin

"Allah yayi miki albarka,zan fita amma idan na taho zan kiraki,karkiyi nesa da wayarki" ido ta lumshe tana gyada kai

"In sha Allah daddy" har ya daga qafa saita tsaidashi

"Kamar kai mummynsu mimi keson gani"

"Ohhhh....." Ya fada yana dan sosa girarsa

"Yara ta kawo,kuma tayi abinda ya dace,shikenan ta ajjiyesu ta tafi,idan kuma akwai sauran wani damuwan ki wakilceni kawai dear,nasan zaki iya komai.....i trust you" ya fada yana jinjina kai fuskarsa kwance da murmushi.

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 43


Sake baki kawai tayi tana kallonsa,ya gama kasheta gaba daya,babu kunya ko kara a lamarin nasa?,sai ya kashe mata idonsa guda daya ya juya ya fice abinsa a falon hankalinsa kwance.

Yana gama fita ta waiwayo ga hafsat din

"Ki zauna sai....."

"Ba zama nazo yi ba,ga yara nan Allah ya karemin su ya kula dasu,idan kuma aka cucesu Allah ya isansu basu yafe ba" wani lafiyayyen murmushi widad din ta sakar mata hankalinta kwance,ta koma ta zauna saman kujerar ta dora qafarta daya kan daya tana kallon hafsat din

"Ki kwantar da hankalinki,kowanne tsuntsu fa kukan gidansu yakeyi,mu namu kukan me dadi kyau da ma'ana ne,haka aka koya mana,yara kuwa sunzo gidan ubansu inda yafi dacewa dasu,inda zasu samu kulawar da suka rasa kaf iya tsahon rayuwarsu,na meye kuma zaki damu?,idan ka shuka alkhairi ai baka tsoron ranar girbi......oh......na manta,kina tsoron kada na maidasu 'yan wanke wanke ba?,ko masu yimin shara ko wanki,ko kina tsoron kada na dinga basu wankin kashin su affan ko su sajjad?" Saita girgiza kai

"Allah ya tsareni,banason ranar girbi na ta zamemin ranar kuka da nadamar baragurbin shukar dana dasa da hannuna,don haka kije kiyi baccinki harda minshari,zasu samu kulawar da ke kanki kika gagara basu,idan iya abinda ya kawoki kenan sai nace ki gaida gida,na gode da kyautar dan mutum sukutum da kikayimin har rai uku ba tare da nayi naqudarsu ba" saita qwalawa aminatu kira tace ta wuce ciki dasu.

A karon farko hafsat tabar gidan jiki a matuqar sanyaye,kalaman widad sun bugeta qwarai,anya batayi gwaari ba data dauka yaranta duka ya danqa mata su?,sai shaidaniyar zuciyarta ta jaddada mata tayi dai dai,dole yaran zasu dameta,kuma shine kawai abinda zatayi ta baqanta musu rai,batasan wannan abun da tayi shine abu na farko data yi wanda ya faranta ran widad ba,don kuwa cikin kwana uku kacal yaran suka fara hawa saiti,farincikinsu ya qaru,dadi kamar suyi me babu ma kamar mimi da taji a duniya an gama mata komai,ta dawo waje antynta.

Wannan kawo sun shi ya bawa abbas damar fara musu shirye shiryen tafiya america din gaba dayansu,ya kashe kudinsa sosai amma baiji komai ba,farincikinsa shine kasancewa da iyalinsa,sai a yanzu yakejinsa cikakken namiji kuma cikakken mutum,widad ta hada masa kan iyalinsa gaba daya,idan ka shigo gidan kai kanka sai ya burgeka,komai a tsare bisa doka da tsari,yaran sun soma samun wata cikakkiyar nutsuwa da kuma tarbiyya.

Ranar da suka bar nigeria ranar hafsat din ta daura auren da ta dinga fatan abbas din yana nan zata daurashi,to baisan ta daura din ba don tuni jirgi ya lula dasu,koda yaji dinma babu abinda zai dameshi,don a duniya bayajin akwai wanda ya fishi farincikin rabuwa da ita,ya yadda KADDARARSA ce zama da ita,a yanzun kuma yana kyautata zaton yaci jarrabawar da Allah ya saukar masa,shi yasa yayi masa tagomashin rabuwa dashi.

Rayuwarsu a america tazo da sabon tagomashi qarin wayewa da kuma budewar ido,don a nan ne widad tayi amfani da result dinta tayi course akan kasuwanci na shekara daya,don sun samu qarin wasu watanni shidan,a nan ta hadu da mutane sosai kala kala data qaru dasu,ta fannin gogewar Rayuwa mu'amala da zamantakewa, nau'in girke girke harma da gyaran kai gyaran jiki da kuma kula da iyali da miji gaba daya,ta samu experience na rayuwa me tarin yawa,bayan sun cika shekara suka tattara suka dawo,dukka yaran sun canza,sunyi dima dima sunyi fresh dasu,sai suka zama wasu ababen kallo,widad business dinta ya kankama,don tayi business sosai tacan,ta kawo kaya a shekarar kamar ba gobe,ta rabawa yan uwanta duka harda dangin miji,kowa ya samu alkhairi yayi murna,don sun qaru da ita,wasu har qaramin jarinsu suka tayar,hannunta me albarka ne sosai da komai ta taba sai ya siyu da tarin alkhairin ubangiji,ne yiwuwa zuciya me kyau da take da ita ne ya zame mata silar hakan.

Kai tsaye suka sauka a tsohon gidansu da suka bari ana yiwa sabon gini,wani irin tsari aka yiwa gidan me matuqar jan hankali kamar a turai,masu sannu da zuwa da zuwa ganin sabon gida aka yita tururuwar zuwa, widad nata jin kunya tana boyen qaramin cikin data dawo dashi,a lokacin duka duka shekarar su sajjad daya da wata shida,ita a ganinta sunyi qanqanta da ayi musu qani,duk da sanda ta haifesu affan ma baikai haka ba.

kuka ta dinga yi tace ita bataso

"Ya kikeso yanzu ayi dashi"

"Nidai a zubar"

"What!!!" Ya fada da mugun qarfi

"Eh lallai na yarda baki da hankali,kuma har yau baki girma ba,bari kiji abun Allah ya kiyaye Allah ya tsare,ko cikin shege nayi miki ai baki isa ki zubarmin da ciki ba" cikin wannan rigimar tasu suka iso nigeria,yana shareta tana shareshi,kowa yana ganin yafi dan uwansa gaskiya.

Yau tunda ta tashi batajin dadin jikinta sosai,don haka koda safe ma tana jinsu suna sabgoginsu daga can babban falon gidan amma bata leqo ba,tasan aminatu zataji da komai,ga adda mimi kamar yadda tasa suke ce mata,yarinyar akwai qoqari,duk wani aikin zaka sameta tana taya aminatu,widad din bata taba hanata ba,saboda tana tuna wahalar data ci sanadiyyar rashin iya komai a aikin gida,duk da gatane na goyon kaka,tafison idan ta tashi aurar da mimi din kamar yadda take fata wanda duk zai auresu ya qare rayuwarsa yana shi mata albarka.

Tana kwance abbas din ya gama shirinsa,yazo kanta ya tsaya,saita dauke kanta gefe,yakai hannunsa ya taba wuyanta,sai ya sauke ajiyar zuciya jin bawai zazzabin da yake takurata ne a jikinta ba,yana mamakin yadda ta iya shareshi da gasken tsahon kwanakin,sai yasa hannu yadan shafi fuskarta kadan yana fadin

"Sai na dawo"

"A dawo lafiya" ta fada ciki ciki,sai kuma tabi bayansa da kallo,bayan ya fitanbta lumshe ido tana fidda numfashi mai sanyi.

Abbas miji ne na musamman,idan tace na musamman tana nufin hakan,duk yadda sukakai ga fada ko sabani da juna saidai iya kan harshe kawai,amma duk wata kulawa basa fasa baiwa junansu.

Agogo ta kalla,qarfe daya saura,ta yunqura zata miqe ihun sajjad ya kawo mata har nan inda take,tasa hannuwanta ta toshe kunnuwanta

"Allah ya yiwa aminatu albarka" ta fada idanunta a runtse,batason hayaniya kwata kwata,banda akwai aminatu da mimi da batasan yadda zatayi ba,dole yanzun ta fita,tasan filin dambe aka bude tsakanin affan sajjad da sajid,wataqila yusra na gefa tana tilliqa dariya,nawwara na qoqarin shigarwa affan mutuminta,saita sauko kawai ta shiga bandaki ta wanke fuskarta da bakinta ta fito ta zura wata sassalkar abaya a jikinta,already da wankanta dama,don bata iya kaiwa haka batayi wanka ba sam,ta zura wasu lausasan slipper kalar abayar ta fito tana daura siririn dankwalin rigar a kanta wanda bai rufe komai a gashin kanta ba.

Falon kuwa ya kacame gaba daya,duk sun ruda aminatu kamar tayi kuka,dama gata gwanar sanyi,saida widad tayi musu tsawa sannan suka dakata da abinda sukeyi,sai kowa ya fara shiga taitayinsa,suka matso kowa yana gaidata

"Maami ya jiki?" Suka dinga cewa,mamaki ya kamata,oh wato abbas yace musu bata da lafiya kenan?,zai hada mata case,yanzun idan suka dinga mata sannu har sai ta gaji,har sai an fuskanci abinda ke maqale a jikinta

"Jiki alhmdlh,na warke ai"

"Allah ya baki lafiya maami" mimi ta fada cikin damuwa da kulawa

"Ameen mimi na" tattarasu duka tasa aminatu tayi waje daya,ta kunna musu cartoon din da sukafi so,sai aka samu salama kowa ya nutsu,sai sajjad da sajid da lokaci bayan lokaci ake fama dasu ana bari bari.

Dining ta wuce ta duba abinda aminatu ta dafa musu,saita zauna daga can saman ta hafa baqin tea tana dan kurba kadan kadan tana kallon yaran,rai shida dukka yaran abbas,ga na bakwai a jikinta,kome zata haifa kuma Alla masani,cikin ranta ta samu kanta da addu'ar Allah ya raya mata su taga girmansu,ya bata ikon ci gaba da tarbiyyantar dasu.

Qarar wayarta dake gefe ya katseta,ta duba wayar saita saki murmushi,ummunta ce,ta gyara zama ta daga wayar cikin shagwabar da har yau bata iya daina yiwa mutum biyu a duniya ita,suma kuma har yau bata girma a wajensu,abbas da ummunta.

Ta sakankance sosai suna hirarsu kusan rabin awa,sai taga aminatu ta buda qofar falon ta fita,sai gata ta dawo,ta hauro inda widad ke zaune

"Maami baquwa kikayi,to mai gadi ya hanata shigowa waisai an gaya miki" mamaki ya cikata,bai tana hana kowa shigowa ba muddin ya yarda dashi sai yau?,da yake qarin matsayin da ya samu yana da me gadi cikin qananun 'yan sanda,hakanan an bashi driver da security

"Koma wace a barta ta shigo" ta fada tana maida wayarta kunne,idanunta akan qofar falon har zuwa sanda labulen ya dage fuskarta data jirkice ta bayyana,saita zame wayar daga kunnenta tana cewa ummu

"Zan kiraki ummu anjima"

"To babu damuwa" ummun ta fada tana a gaida mata kishiyoyinta da masu gidan.

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 44

Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn Whatsapp
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏
_______________________________


Har yanzu kallon fuskarta takeyi,tanason tantancewa itace ko ba ita bace.

Yadda itama take kallonta haka baquwar,kafin ta janye idanun nata ta maida kan yaranta dake zaune gaban tv sun bata hankalinsu,wasu hawaye masu ciwo suka tsatstsafo mata,dai dai sanda widad ta miqe tana cewa

"Sannu da zuwa" gami da gangarowa daha step na dining din

"Yauwa sannu" ta amsa mata murya a dakushe,widad ta qaraso wajen can gefe daga inda yaran suke tana fadin

"Bismillah zauna"

"Har ina iya zama?"

"Ba damuwa ki zauna......mimi ga mummynku,nawwara yusra?,maza ku taso,aminatu a kawowa baquwa abun tabawa" duk sai hankulansu yayo kanta,duk suka tsaya suna kallonta da kyau,kamar basu ganeta ba.

Itama ido ta tsura musu,hawayen da take riqewa ya silmiyo mata,sai suka miqe dukansu sukayo wajen uwar jiki a matuqar sanyaye,dadi ya kamata,ta bude dukka hannuwanta suna isowa ta rungumesu tana sakin kuka mara sauti.

Sun jima a haka,tausayinsu yana ratsa

30 / 33